Showing 390001 words to 393000 words out of 429394 words

Chapter 131 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

983

seda ya sake sabon Rarrashi dan yaga abinda tayi daya kunna system din be ce mata komai ba kuma ya bi recycle bin ya maido folder tana ta kumbure kumbure shidai be kulataba har suka je gida seda dare yayi yaga tana neman ta tada sabuwar fitina yasa ya lallabata ta haqura suka kwanta a ransa yana ayya su Mata gaba daya haka suke da Kishi, na Umaimah ne kawai ya fito fili.

UMAIMAH
A sannu a hankali nutsuwa ta fara saukar mata domin nauyin daya danne mata qirji fiye da kaso saba'in cikin dari ya sauka. Tsakaninta da Mama da Abba sun samu daidaito domin ta nemi afuwarsu kuma sunyi mata haka kullum cikin Istigfari take domin tun lokacin da Mama tayi mata tunatarwa akan babban laifin biyewa Safina da tayi ta kaita gidan yan tsubbo hankalinta ya qara tashi. Dare da rana cikin roqon gafarar ubangiji take haka ta rage bacci duk dare seta tashi tayi sallolin Nafila cike da yaqinin ubangiji ya yafe mata tarin laifukanta a garesgi. Ta rasa sallolinta babu adadi sakamakon yawon gidan Malamn tsubbu da suka ringayi da Safina, gaba daya hankalinta yayi nisan da bata taba hango illar abubuwan da ta aikata a baya ba se yanzu. Lokacin da Maman take sake tuna mata da cewar muddin tana so al'amuranta su daidaita seta nemi yafiyar mutanen data musgunawa a rayuwa domin Allah ze iya gafarta mata laifukan da tayi tsakaninta dashi muddin tayi kyakykyawan tuba ta kuma roqeshi amma babu sassauci a cikin haqqoqin data daukarwa kanta na mutane dan haka tilas ta daura damarar neman yafiyarsu amma babban tashin hankalinta ta inda zata fara? A ina zata nemo su?

Tijararta tun tana qanqanuwa takeyinta, bakin Manya da yara babu wanda bata dibarwa kanta ba banda tarin Allah ya isan yaran da take cin zali a Boko da Islamiyya yanzu ta ina zata nemosu ta nemi yafiya wasu ma sun mutu wasu sun bar inda take wasu bata ma sansu ba wannan tunanin ne yake qara dagula mata lissafi ta rasa inda zata tsoma ranta. Cikin manyan kurakuren data tafka a rayuwarta bayan tarwatsa rayuwar auranta da tayi A yanzu ne ta gane girman Al'amarin daya faru tsakaninta da Hadiza. Tana cike da nadama da dana sanin abinda tayi mata ta tabbatar da cewar iyakar haqqin Hadiza ya isa ya hanata nutsuwa a rayuwarta, a yanzu ita komawa gidan Khalil bashine burinta ba, buqatarta ya yafe mata, Hajiyarsa ta yafe mata irin tozarcin da tayi mata haka yan uwansa duk suyi mata afuwa daga baya idan Allah ya qaddara da sauran zama a tsakaninsu zata so ta koma masa idan kuma babu ta haqura ta karbi qaddara a yanda tazo mata sedai hakan yana nufin zata qare rayuwarta babu aure dan babu sauran matsuguni da wani Namiji ze samu a zuciyarta domin ta Khalil ce kuma har abada ba zata dena Sonsa ba.

Tana tsaka da wanke sauran kwanukan da akaci abincin rana dan har a yanzu babu abinda ya canza daga ayyukan da takeyi a cikin gidan, hatta Anty data ce ta karbi girkinta Abba yace ya hana ya kuma tambayeta dalilin da ya saka ta take umarninsa ta tabbatar masa da babu komai. A gaban Mama da ita Umaiman yayi mata tambayar dan Maman tana yawan yi masa tanbihi akan wasu sauye sauye datake gani daga Antyn, tana tsoron zamansu na shekaru ya canza salo a gargara dan ta tabbatar da mawuyacin abu ne su maimaita shekarun da sukayi a baya tare sedai wani iko na Allah. Anty ta dage akan ita babu komai Yayin da Abba ya dage akan seta fada masa dalilinta, cikin wani yanayi tace

"Allah ya sani Alhaji babu wani abu a zuciyata akan Mama ko yaranta. Kuma ni idan ma akwai wani abu dana kasa jurewa be wuce yanda tsayin lokacin nan tun dawoqar Umaimah gidan nan ka rasa walwalarka ba. Baka da isashshen lokacina hira me dadi yanzu bana samunta dakai Alhaji a koda yaushe idan ina tare dakai idan ba tunani kake ba to kana Sallah ko lazumi kuma se naga idan kana tareda Maman Yara kana walwala koda yaushe kana cikin tarairayarta da kwantar mata da hankali wannan abun ne yake damuna kuma zuciya bata da qashi se na ringa ganin kamar ka fifita buqatunta akaina bayan ni bani cw silar bacin ranka ba"

Gana daya sukayi shiru suna sauraronta jin tayi shiru itama Abban ya nisa yace
"Ina jinki Saratu se me kuma?" Seta ci gaba da cewa
"Idan nayi zancen da Qawayena ko yan uwana maganganun da suke gaya mun su suke qara sakani a damuwa amma koma menene yanzu ya wuce tunda kaima fara dawowa Alhajin dana sani shikenan"
"Oh Saratu kenan Saratu iyayen soyayya wato ke kulawar Mijinki da kika rasa itace tasa kika fara Kishi da yarki kina ganin ita ta dagula miki lissafi ko? To kiyi haquri, maganar kuma nafi tattali da bawa Malika kulawa ba abinda kia dauka bane ko Mutane marasa son a zauna lafiya suke gaya miki. Tabbas mun tsinci kanmu a cikin Jarabawa wadda dagani har Malika muna buqatar wanda ze lallashe mu ya jamu a jiki domin halin da muka tsinci kanmu ba qarami bane dole na shanye duk tawa damuwar na qarfafa mata guiwa amma baya ga haka babu wani banbanci ko bangaranci danake nunawa a tsakaninku kuskuren tunani ne kuma nagodewa Allah da beyi nisan da har wata baraka ta shigo tsakanin Iyalaina ba dan haka idan har a tsahon lokacin nan Saratu kina ganin cewar mun cutar dake muna neman afuwarki dani da Malika da kike ganin mun shiga haqqinki ke kuma ga Antynki nan ki nemi afuwarta akan muzguna mata da kikayi kika hanata samun sukuni da Mijinta" Abban ya sake fada gaba dayansu seda suka murmusa da jin maganar tasa se Anty tayi saurin sake cewa

"Haba Alhaji wlh babu komai yafiya kuma tuni ta nema dukda bata mun komai ba ni na yafe mata dama ai Umaimah tawa ce ita take qina kuma komai ya wuce a gurina daman nasan shedan ne kawai da maganganun mutane suka nemi suyi tasiri akaina kuma nima ina neman afuwarku idan akwai abinda nayi na rashin kyautawa ku yafe mun"

"Allah ya yafe mana gaba daya" Abban ya fada daga nan suka tashi kowa ya koma sabgogin gabansa.

Sallamar Maman Asad ce ta katse mata tunanin da takeyi, ta dauraye hannunta ta miqe tana mata sannu da zuwa tareda karbar ledar data shigo da ita. Seda ta rakata har dakin Mama kafin ta fito ta shiga kitchen ta debo Zobo da Kunun Aya na roba data farayi na siyarwa bisa shawarar Nuratu, itace ma ta bata Jarin Dubu biyar ta fara kuma Alhamdulillahi tana samun na kashewa tunda daman sana'ar Anty ce ta saki ta dena. Seda ta ajiye mata su ta dauka tana cewa
"Karfa mu karya Jarin"
"Haba dai, ina su Khairi kikazo ke kadai" Umaimah ta fada tana miqewa harta Juya Hajiyayyen ta tsayar da ita tana cewa
"Ni Umaimah wai baki da kaya ne se wadannan tsummokaran?"
*HALIN KISHI*

*NA MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATON*
*(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)*

Page 83

"Ina dasu Mana amma gaba daya sunyi mun yawa. Wadanda kika ga ina sakawa su kadaine suke zama a jikina shiyasa" Umaiman ta bata amsa hawaye na neman balle mata, abu kadan ke sakata kuka yanzu yanda kasan matar mamaci. Mama data fito daga dakinta tace
"Kema da sonbata bakinki kike daman tunda kike da ita kinga tana saka suturun arziqi ne? Ga dai kaya nan kamar su kasheta bata saka ba bata kyautar ba shekara da shekaru a haka duk zasu ratattake su mutu bata mora ba" se kuwa hawayen da take riqewa ya balle dukda Mama tace ta yafe mata abubuwan data aikata amma sauda yawa irin yanda take mu'amalantarta se taga kamar har sannan da sauran fushinta a ranta. Babu ranar banza da bazata fada mata maganar da zata sosa mata zuciya ba, idan bata goran ta mata cewar sa'anninta nacan a gidan aure suna aikin lada ba seta mata shaguben koda ace zatayi aure a gaba inta samu ma'aurin kenan abinda take gudu gidan me mata zata shiga, ta kaso auranta akan wata kuma zata auri Mijin wata me kenan tayi da sauran maganganu masu sosa rai kuma ko a jikinta zata yaba mata kuskure kadan zatayi ta rufeta da fada tasani Mama na da duk wata dama ta jin haushinta domin tayi abinda dole koma waye ya washsheta amma a kullum tana addu'a Allah yasa su yarda da nadamarta, su yarda da cewar tayi dana sanin duk abubuwan da suka faru a baya sannan a shirye take data gyara kurenta idan ta samu damar hakan.

Jiki a salube ta koma taci gaba da ayyukanta tanayi tana goge hawaye sosai zuciyarta take mata zafi, idan da ace tana da yanda zatayi ta goge baqin febtin da tayiwa kanta da tayi kota samu sauqin abubuwan data ke fuskanta a rayuwarta a yanzu. Ta tabbatar badan tasirin addu'a ba data zauce, ta kuma yarda abinda ta rasa kenan a baya rayuwarta ta ringa walagigi ta ringa ayyuka cikin rashin nutsuwa da tunani babu neman zabin Allah a cikin lamuranta abinda zuciyarta ta darsa mata kawai shine daidai a gurinta da ace tun a sannan ta karbi gyaran da masu sonta suka ringa yi mata da bata tsinci kanta cikin Halin nadama mara amfani ba. Harta gama wanke wanken ta wuce daki da tayi niyyar ta koma falon Maman suyi hira da Maman Asad amma ba zata iya ba ta lura yau Mama da uta ta tashi a ranta gara taja jiki ta koma gefe. Tana kwance Maman Asad ta shiga da jakarta alamar tafiya zatayi daman ba zama tazo yi ba, ta tashi zaune tana kallonta itama ta nemi guri ta zauna tana cewa

"Kwanciya kikayi?"
"Eh wlh so nake na dan huta kafin anjima" ta bata amsa seta gyara zama tana cewa
"Dan Allah ki ringa gyara jikinki Umaimah tsafta ai tana cikin Imani amma ki ringa yawo a gida yarkace yarkace dake duk wanda ya shigo ya fita se yayi dake meye amfanin hakan bayan kina da suturun sakawa ba baki dasu ba. Sannan wannan uban baqin da kikayi da rama bafa sune zasu nuna cewar kinyi nadama ta gaske ba, wannan tsakaninki da Allah ne da kuma ta hanyar ayyukanki za'a fuskanci hakan amma quntatawa ranki da kikayi babu abinda ze qareki dashi sedai ya haifar miki da ciwon damuwa dan haka ki saki ranki, qaddara dai kowa da kalar tasa ke kinga taki Jarabawar a rayuwa se kiyi qoqarin cinyeta amma damuwa kuka tunani duk ba zasu baki mafita ba Addu'ar dai ita zaki cigaba dayi ki nace da roqon gafarar ubangiji in sha Allahu komai ze daidaitar miki, komai ze wuce ki gani tamkar be faru ba".

Kanta na qasa har Maman Asad tayi shiru kafin ta dago fuska shabe shabe da hawaye tana cewa
" Yah Hajiyayye kenan ai wanda yake da nutsuwar zuciya shiyake kwalliya nikam a matsayin da nake in har kaya zasu suturtani sannan babu wata qazanta a jiki da zata kawowa Ibadah ta tangarda bani da matsala. Wanka ma idanta qure harda Klin inayi mai kuwa sedai ka shafa dan kar qaiqayi ya dameni amma badan wai fatata tayi kyai ko wani ba ba. Maman Asad, Allah kadai yasan halin da nake ciki irin zafin da nakeji a zuciyata baze misaltu ba. Nasan na tafka babban kuskuren da babu wanda zeyi mun uzuri amma ina fatan ubangijin daya ce idan munyi kuskure mu tuba saboda shi ze yafe mana ya dubi nadamata. Allah ya sani ina cike da nadama me tsanani da dana sanin ayyukana na baya, da ace ina da iko dana sauya rayuwata Yah Hajiyayye, da ace zan samu dama a karo na biyu danayi qoqarin wanke kaina a zukatan duk wadanda na batawa amma bana zaton zan zamu wannan damar, abu daya nake da buri a yanzu kafin na koma ga mahalicci na na samu damar neman gafarar duk wanda na zalunta a baya su yafe min shi kadai ne abinda ze samar mun da nutsuwa a rayuwata".

Hajiyayye tayi shiru, tausayin yar uwarta ya cikata ita shaidace da cewar Umaiman tayi laushi ta kuma gasgata Nadamarta ta gaske ce bawai wuya ce ta sakata saduda ba kamar yanda Mama take fada. A taurin kai irin na Umaimah ta tabbatar da ba aikin wahala ba ko kasheta za'a yi babu abinda ze canza mata ra'ayinta haka inda ace bata zubda makamanta ba bazata taba kulluwa tsayin shekara hudu da ranta da lafiya ba tareda ta fita ba koda ace hakan na nufin ta bar gidan kenan na har abada a Umaiman dasuka sani a baya zata iya zabar hakan tunda kuwa harta jure komai tsayin lokacin nan ta yarda da gaske takeyi sedai kamar yanda ta fada zeyi wahala mutane su yarda da ita har suyi mata uzuri amma yardar Allah ita Umaimah tafi buqata a yanzu domin idan harta gyara tsakaninta da Mahaliccinta komai zezo mata da sauqi sedai kamar yanda ta fada haqqin wadanda ta cutar baze barta ta samu nutsuwa ba harse ta saukeshi.

"Dan Allah Maman Asad zan roqeki Alfarma, karkice ba zaki mun ba. Banida hanyar da zan hadu da Khalil ko wani cikin Ahalinsa kinga bana fita sannan bani da waya kuma koda ma ace na gansu bani da kwarin guiwar da zan iya kallonsu. Kiyi mun wannan alfarmar koda ace shine abu na qarshe da zaki mun saboda Allah ki nema mun afuwa a gurin Khalil da Hajiyarsa a matsayinki na Jinina. Ina so na roqi Mama ko Abba suyi mun wannan alfarmar amma nauyi da kunyarsu baze barni ba, sun roqeni dana kwantar da hankalina a baya na toshe kunne na nayi abinda nayi a yanzu da komai ya rincabemun bazan iya roqarsu da su nema mun sassauci a gurin wadanda na batawa ba iyakar alfarmar da sukayi mun ta yafe mun muzgunawar da nayi musu ta isheni".

Shiru Maman Asad din tayi tana kallonta saboda abinda ta roqetan yayi mata girma ba kuma tajin ita kanta tana da qarfin guiwar da zata je nemawa Umaimah yafiya a gurin Khalil ko Hajiya. Iyakar murje idon da sukayi suke neman Yaran ya isa ba zata so ta tado da abinda ya shude ba ballantana radadin abun ya waiwayesu har a qarasa gutsire yar guntuwar alaqar da ake riritawa a tsakani. Umaimah ta kama hannunta idonta na zubda hawaye tace
"Nasan abin da wahala amma idan na mutu da haqqinsu nasan Allah baze dubeni ba Yah Hajiyayye. Na cutar da Khalil matuqa na sani kuma ba lallai ya yafemun ba amma dukda haka ina so ki gwada nema mun wannan alfarmar su yafe mun nauyin da nake ji nasu akaina ya ragu ko zan samu nutsuwar da kuke buqata ku ganni a ciki".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kalli Umaiman tace
"Ban daukar miki alqawari ba amma zanyi bakin iyawata dukda ni kaina inajin nauyi da kunyar abubuwan da suka faru. Tun gabanin haduwarki da Khalil na zauna da Hajiya ta kuna daukeni kamar yarta irin yanda ta riqeni yasa har tayi sha'awar hada jini damu ta dage har seda ta tabbatar da qulluwar aure a tsakaninki da gudan jininta. Duk abubuwan da kika aikata Hajiya bata taba kware miki baya ba. A gabanta kin zageta amma tayi miki uzuri har Mama ta umarci Khalil ya rabu dake Hajiya bata so haka ba a yanzu da nake miki magana tunda muke turawa a daukar Mana Yayanki ko a fuska Hajiya bata taba nuna wani abu ba tayaya kike so naje gurinta Umaimah na sake tado mata da abinda ya wuce wanda na tabbatar da ba mantawa tayi ba tsabar dattako da karamci irin nata ne yasa ta mayar da komai ba komai ba.
Zanso ki bar komai a yanda yake kici gaba da addu'a da neman yardar ubangiji muma muna tayaki in sha Allahu komai ze daidaita Umaimah kinji"

"Kina nufin ba zaki iya ba kenan?" Umaimah ta fada cikin kuka domin Maman Asad dince kadai dogaronta da zata iya nema mata gafara a gurin Khalil da Hajiya a madadinta, se Maman Asad ta kama hannunta tana cewa
"Ba haka nake nufi ba Umaimah. Kece mafi cancanta da ki nemi yafiyarsu abinda nale nufi kici gaba da addu'a har zuwa sanda komai ze daidaita ki samu damar neman yafiyarsu da kanki" seta sassauta kukan tana kallon Hajiyayyen tace
"Kina ganin zasu yafe mun?"
"Meze hana, a rayuwata ban taba ganin mutane masu karamci kamarsu ba Umaimah na tabbatar ko a yanzu sun yi miki afuwa tunda har suka bar Yaranki suke zuwa gurinki hakan yana nuna fushin da sukeyi dake ya ragu, kici gaba da addu'a yanadaga cikin tasirinta" Maman Asad ta fada kafinta miqe tana cewa
"Bari naje saqo na kawowa Mama daman se ranar Juma'a in Allah ya kaimu duk zamu zo Naziyya ma tana tafe ranar Alhamis kuma idan tazo karki kuskura ta sake barin garin nan baku warware gabar dake tsakaninku ba"
"Toh ai ba laifina bane, cewa tayi bata yafe ba idan na sake yi mata magana babu ita babu ni ni kuma naga haqqoqin da suke kaina da yawa balle na sake daukar wani shi yasa na rabu da ita amma Allah ya gani ni ba gaba nakeyi da ita ba maslaharta na duba" Umaiman ta fada tana miqewa tsaye itama seta juya ta fita tana cewa
"Nidai na gaya miki kuma ki fitar da kayayyakinki wanda suka miki yawanki bayar akai gidan Mama Nana ta rage miki ki dena yawo kamar wata Yar gudun Hijira"

"Kiyi haquri amma bazan kai kayana gidanta ba, ita ta ringa yawo dani a unguwar nan tana fadar abinda ya faru da Wanda ma be faru ba dayawanmasu shigowa siyan zobo fa badan Allah suke zuwa ba se dan kawai suga yanda na koma. Baki ga tururuwar da aka ringayi ba sanda Salman ya fita dashi yace an dawo yin Zobo a gidan nan, harda Maza A gulma Maman Asad ba kunya suke shigowa da girmansu wai siyan zobo ni wlh har fargabar ranar da zan sake fita daga gidan nan nakeyi nasan gaba daya labarina ya karade ko ina qila har Film da Novel anyi a kaina ko? Inaga bazan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login