Showing 234001 words to 237000 words out of 429394 words

Chapter 79 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1610

ga yana qoqarin yi ce tasa ya dakatar dashi dan har yana qoqarin hambarr da abincin da Anty ta kawo Abban yace
"Zauna Abdullahi, magana na kiraka muyi ba yawon tafiya gurin yan sanda ba".
Baba Abdullahi ya zauna Abba yaci gaba da cewa
"Nima a wannan gabar abinda ya faru beyimun dadi ba dan kaga ba'afi wata bafa nan ma suka yi wata rigimar har Asibiti ta kwanta dalilin daya sa Laure qanwar Malika take zama da ita yanzun kenan saboda anyi mata daurin Mahaifa kuma sukaqi fadar abinda ya hadasu daga shi har itan shiyasa ma ban tsaurara ba saboda nasan da tana da gaskiya zata fadi abinda ya hadasu..." Baba Abdullahi yayi saurin katse shi da cewa

"Au bama wannanne na farko ba ashe kaga ya daketa na farko yaci banza dole ya yanzu ya qara kuma da zakace bata da gaskiya ta ya akayi ka sani?"

"Koma menene yanzu dai anzo gabar da dole muyi interfering, duk abinda ze faru ya faru amma bazan dauki duba ba. Ban taba daga hannu na daki yar wasu ba dan haka nima baza'a dakar mun tawa yar ba yanzu abinda nake so dakai ai kana da Number Iyayensa ka kirasu ka sanar musu da halin da ake ciki, yanda aka qulla dasu haka za'a warwareta dasu dan daman a baya idan sunyi rigimarsu gurin Marigayi yake zuwa yanzu babu shi shine ze ringa daukar mataki a hannunsa to bazan lamunta ba" Abba ya fada, Baba Abdullahi ya ciji yatsa tareda yin qwafa kafin ya zaro wayarsa ya shiga kiran Alhaji Garba.

Tiryan tiryan ya kora masa jawabi kamar a gabansa akayi Alhaji Garba ya ringa salati ya shiga bashi haquri akan sam be sanda labarin nan ba amma yanzu ze kira Alhaji Abubakar zasu zo tsakanin yau ko gobe dan Allah suyi haquri. Ya kashe wayar yana cewa
"Ahto gara dai suzo, kuma sena rama mata marinta dan ma yaji da jinsa da gatanta" Abba dai murmushi yayi suka shiga karyawa Baba Abdullahi nata Mita har seda Abba ya gaji yace fita zeyi sannan ya tashi suka fita tare bayan sun gaisa da Mama itama ya dira mata Mitar ta shige daki ta barshi.
"Ke daga yau karki sake zuwa gidan nan duk abinda ya hadaku kije can gidana ki gaya mun, kina kallom wannan uwar taki kamar ma tafi sonsa akanki, ji ina mata magana yanda ta hade rai wato an tabo Zuciyarta haka kawai ba dole ma ya ringa jibgarji yanda yaso ba uwar data haifeki ma ta nuna masa bata qaunarki" Baba Abdullahi ya fada yana kallon Umaimah dake zaune har sannan a gaban Murhu Anty Laure kuwa ta cafe tace

"Kai ma ka fada Baban Nabila yo dan ma bakaji abinda take fada bane gaba daya fa ta toshe kunne fadi take haka kawai baze daki Umaimah ba dole da abinda ta masa ni na taba ganin inda ake haka ace ka zabi bare akan naka? Ai ko naka keda laifi kamata yayi ka mora masa baya in yaso a gefe ka nuna masa kuskurensa". Jin ya samu yar tayi se ya fasa tafiya yaja kujerar zama ya kafa suka dora Abba dai yayiwa matansa sallama ya fice a ransa yana cewa
"Ga inda Umaimah ta gado halinta su biyun nan basa son gaskiya qiri qiri suna kallo zasu take abu indai bayazo daidai da ra'ayinsu ba".

KHALIL
Bayanda ya iya haka yaje suka rankaya zuwa gidansu Umaimah. Yana tuqin ji yake kamar ya tsayar da motar yace su sauka saboda yanda suka rufeshi da fada wannan nayi wancan nayi a haka har suka qarasa qofar gidan. Salman daya hango su ya taho da sauri cikin ladabi ya gaida dattijan kafin Khalil ya miqa masa hannu suka gaisa yana tambayarsa Abba yana nan

"Suna ciki, Baba Abdullahi ya hada chamber guda ka shirya yau zakasha Rapping" Salman ya Fada Khalil yayi yar dariya yace
"Tare dakai zamu shiga ka tayani ji"
"Wani, bari dai na gaya masa kunzo" Salman ya fada yana gwalo ido kafin ya juya ya shiga gidan.

A palour Abba ko kamar yanda Salman ya fada yanda kasan wani taron daurin auran Bazawara Haka Baba Abdullahi ya tattago yan uwansu da Aminan Abba samada mutum bakwai, suna zaune yana qara zayyana musu qarya da gaskiyar da Anty Laure ta kora masa, Abba dai takaici ya hanasa magana kallonsa kawai yakeyi Baba Liman Aminin Abba ya kalli Baba Abdullahi yace
"Kai amma kuwa ban zaci yaron nan haka yake ba, ina masa kallon mutumin kirki shiyasa fa tsananta bincike nada kyau amma kaga duk sanda rigima ta taso se mu taru mu goya masa baya ba'a ma neman jin ta bakinta ashe dai shima da nasa halin".

Bude baki Abba yayi zeyi magana Salman ya doko sallama, sanar musu yayi da zuwan su Khalil Abba yace su shigo Baba Abdullahi aka gyara zama harda qara tamke fuska shi ala dole zeyi rashin M dan ya rantse ko an sasanta kafin Umaimah ta koma seya rama mata marin da aka mata ai ba jaka suka aura masa ba.

A qasa Khalil ya samu guri ya zauna ya shiga gaishe su, wasu suka amsa faran faran irinsu Baba Abdullahi da Baba Munzali kuwa iyayen daukar dumi da harara suka bishi shima be damu ba ya sake duqar dakai yana jira su gama gaishe gaishen ayi wadda za'ayi ya tafi amma fa duk bala'i badai Umaiamah ta koma masa gida yau ba.

Baba Abdullahi ya zabura ze fara magama Baba Liman ya dafe hannunsa ya girgiza masa kai dole ya koma yayi shiru Alhaji Abubakar yayi sallama tateda bude taro da Addu'a kafin ya fara koro bayanin ban haquri ya ringayi kafin Alhaji Garba ya karba shima ya dora nasa jawabin ban haqurin tareda roqon Alfarmar komai ya wuce yanzu Umaimah ta shirya ta koma dakinta. Yanda suka sadda kai suna bada haqurin ya saka jikin kowa yayi sanyi yan korar Baba Abdullahi da sukayi shirin yin tijara jiki yayi sanyi. Alhaji Abubakar ya kalli Khalil yace
"Kayi shiru, ga surukanka nan ka basu haquri ka dauki matarka ku koma shikenan magana ta wuce" kafin ma yace wani abu Baba Abdullahi yayi caraf yace

"Ai bazeyi magana ba, tunda ya daketa ya daki banza anzo ana bada haquri su koma kaga ya samu lasisi gobe ma ya qara. To wallahi bari kaji, ka sake ko dungurar mun Ya Three quater zan saka nazo na casaka har cikin gidan naka dan ka sani tambaye su kaji tsohon dan Dambe ne ni ban kuma manta komai ba balle ka dauka na fara tsufa zan kasa lallasaka". Dariya palour ya dauka banda Khalil daya daga kai ya kalle shi yana hasaso wai shi Baba Abdullahi ze daka, ai ko yanzu yake da ganiyar quruciya yasan qirar ba daya ba, lallasashi zeyi ya watsar balle yanzu da shegiyar rigimarsa ta tsufar dashi lokacinsa beyi ba dan idan ka ganshi seka dauka ya girmi Abban.

"Kayi shiru kuwa ana magana" Alhaji Garba ya fada a fusace jin Khalil din bece komai ba, seya dago da kansa a hankali ya kalli Abba da shima shi yake kallo ya sake maida idonsa qasa yace
"Abba kuyi haquri, amma kafin a yanke kowanne hukunci ina so a kira Umaimah tazo a gaban kowa ta fadi gaskiyar abinda ya faru, idan ina da laifi zan nemi yafiyarta da taku mu tafi kamar yanda kuka ce..."
"Idan kuma ba haka ba fa?" Sarkin katsalandan Baba Abdu ya tareshi harda miqewa tsaye kamar ze rufeshida duka se Alhaji Badaru wanda yake bin Abba yayi saurin tareshi shima yana cewa

"Aa Abdullahi maganarsa gaskiya ce ai ba'a shari'a da shaidar bangare daya, a kirata tazo din kamar yanda ya buqata itace shari'a ta gaskiya".
Ajiyar zuciya Khalil ya sauke dan baze sake daukar wani dakon laifin da beyi ba gara tazo in ma wata qaryar ta shirga ta warwareta da kanta kuma in har ta domin Allah za'ayi babu Wanda zece ta kyauta da abinda tayi masa.

A fusace Baba Abdullahi ya fice saga parlour ya tafi dakin Mama, a bakin qofa yaci karo da Umaimah da tunda taji qamshin turaren Khalil ta kasa tsaye ta kasa zaune. Tana can bacci bata san taron da Baba Audu ya hado ba shigowarsu Khalil ce ta farkar da ita saboda taji suna gaisawa da Anty ta kuwa fito da sauri amma sunrigada sun shige bangaren Abban se qamshin turarensa daya bari a iska tun sannan ta kasa zama Baba Abdullahi ya gama da ita wallahi. Muryarsa taji a tsakiyar kanta yana ta sako Hijabinta ta biyo shi. Ta zabura tana raba ido tace

"Uhm Ina zanje Baba?"
"Kizo muje wancan mara kunyar Mijin naki me yace wai se kizo ki fadi abinda ya hadaku, daman karki ji nauyin kowa ki fadi komai da kika sani idan shi be iya kama barawo ba ai shi ze kamashi. Ina Laure itama ta zauna cikin shiri dan itace shaidar gani da ido".

Jiki Babu Laka ta shige dakin Mama ta samo Hajibi, Maman dake zaune kan kujera ta kalleta tace
"Kinga da kika qi fada mun komai yanzu zakije gabansu ki fada in ma kece mara gaskiya kin jawowa kanki fadandaya fi wanda zanyi miki ai sannan a tafi dake a bakin duniya ana yamadidi kinga se kiji dadi" ta mayar dakai taci gaba da danna wayarta. Baba Abdullahi ya sake fafaro mata kira dan yana tsaye yana jiranta. Suna tafe yana qara qissima mata abinda zata fada harda qarin gishiri da Maggi har suka isa ta nemi gu daga bakin qofa kamar sabuwar munafuka ta shiga gaishe su suka amsa mata a kusan tare. Alhaji Garba da Alhaji Abubakar sukayi mata ya jiki ta amsa da sauqi kafin gurin yayi shiru.

"Mijinki ya nemi kizo aji ta bakinki akan abinda ya hadaku har kika dawo gida" Alhaji Badaru ya fada cikin kulawa yana kallonta. Umaimah ta dago kai ta kalli sashen da Khalil yake kafin ta hadiye miyau dakyar ta kalli Abba seta sunkuyar da kai tace
"Ni Dady komai ya wuce a gurina, daman dan sabani muka samu amma ya wuce"

"Ban gane komai ya wuce ba, zaki bude baki kiyi magana ne ko kuwa na kira Laure ita ta fada tunda naga alamar tsoronsu kikeji?" Baba Abdullahi ya fada se sannan Abba yayi magana yace
"Umaimah" ta dago ta kalle shi yaci gaba da cewa
"Me kika yiwa Mijinki da har ya saka shi ya dakeki ya shaqe miki wuya?"
"Ji wata irin tambaya dan Allah Yaya, kai anya ba Asirce mata iyaye kayi ba ace basa ganin laifinta se naka?" Baba Munzali ya fada nan cece kuce ya barke, wasu na fadin koma me ya mata tunda dai tace ya wuce to abarshi ya wuce din ta tattara ta koma dakinta ai damanko wacce Mace zaman haquri takeyi idan yaso shi kuma ya kiyaye kar haka ta sake faruwa Alhaji Badaru kuwa da yake nazarin Khalil da tunda ake maganar be dago ya kalli kowa ba ya kuma dubi Umaimah dake ta faman raba idanu alamun rashin gaskiya sun gama bayyanar mata ya dakatar da kowa, cikin muryar babu wasa dan daman shi bame wasan bane yace

"Kinsan Allah ko ki fada da kanki ta lallami ku kuma mu tashi mu tafi, duk ranar da kika bude baki kika fadi abinda ya faru se a sake zama danba zamu maidake cikin taraddadin irin zaman da kikeyi ba"

"Nidai wallahi Dady na yafe kuma yayi haquri kawai zan koma" ta fada tana fashewa da kuka se a sannan Khalil ya dago kai ya kalleta kafin ya kalli Alhaji Badarun shima yace
"Kuyi haquri Alhaji amma idan har Umaimah bata fadi abinda tayi mun da bakinta ba bazata koma gidana ba".

Shiru palour yayi kamar an dauke wuta Umaimah ko idanu ta zaro tana kallonsa bakinta na rawa amma ta kasa cewa komai, Baba Abdullahi ne ya ceceta ya furta abinda take so ta tambayi Khalil din yace
"Sakin ta zakayi?"
"Ko ban saketa ba bazan iya ci gaba da zama da ita ba har ze ranar data san daidai ta kuma koyi karban laifin da tayi ta bada haquri, daga nanzan duba idan da yuwar cigaba da zamana da ita dan wallahi ta kaini bango, Halin Umaimah ya isheni" Khalil ya sake fada cikin wani sauti dake nuna zallar takaicin dake cin zuciyarsa. Suka sakeyin shiru kafin cikin tsawa Alhaji Badaru yace mata
"Zakiyi magana ko mu tashi mu kama gabanmu dan duk muna da abinyi ba irinki ba"

Se sannan ta sake fashewa da Kuka, ta kalli Abbadaya tsura mata ido kafinta fara zayyano duk yanda akayi tundaga sanda ta fahinci Khalil yana kula Zahra, binsa gidansu da tayi, yanda ta lalata kayan dakinta har zuwa kwanciyarta a Asibiti da kuma sanadin Mari da shaqar da yayi mata.

Palour ya dauki shiru na kusan minti goma banda shashsheqar kukanta babu abinda kakeji tana cewa
"Dan Allah kayi haquri wallahi sharrin Shaidan ne, nikaina seda na aikata na fara nadama kuma da baka zo da fushi ba wallahi tun a sannan zan baka haquri
"Ki bashi haquri bayan kin cuce shi?" Alhaji Badaru ya fada cikin wani irin fushi da muryarsa ta kasa boyewa kafin yaci gaba da cewa yana kallon Baba Liman

"Zancen da nake maka zaman mu anan na wata kwangila da aka bayar a Office dinmu DG ya shiga ya fita ya bawa wasu qananan constructors se daga baya wai ya gano ashe yan Damfara ne ban masan Comapany Mijinta bane ashe yar iskar yarinyar nan ce take nema ta bata masa suna har yaushe zakiyi hankali Umaimah ki dena jefa mutane a masifa?

Yaushe akayi wancan Case din datayiwa yar mutane sharri aka gama saboda kin ga kinci bulus shiyasa kika sake kwanto masa wata kurar ko?
Daman tun wancan incidence din nake cike daku gaba daya yanda ace babu Wanda ya sanar dani se daga baya naji labari da kukayi yanda kuka ga dama. Dan ubanta da an dauki kwakwkwaran mataki akanta a sannan zata sake tunanin repeating any nonce like this ne?
Ita ga shafaffiya da mai, tayi tarnishing image din yarinya amma the only punishment she served was tayi video ta bada haquri shikenan taci banza saboda tsabar son kai da qin Allah irin naku. Idan itace aka yiwa qazafin iya abinda zamuyi kenan? Da yanzu wata magana ake ta daban because se nayi making sure that the culprit rot in jail, ai da aka tafi da ita ma be kamata ku bita ba se tayi sati ta fita hayyacinta sannan ta qara zaman prison kona shekara daya ne daga nan bazata sake dakkowa kowa magana ba amma yanzu gashi, ga abinda ta sakeyi saboda tasan qarqari kuyi mata fada shikenan ya wuce kai kuma lusari ka koma kaci gaba da zama da ita ba tareda ka nuna mata kuskurenta ba who does that?

Kinsan waye Dr Sabitu kuwa kin san irin tuggu da manaqisar daya iya hadawa?
Ubanwa ma ya saka ki shiga sabgar Business din Mijinki ina ruwanki dawa yake sabga dan ubanki idan ma uwar Zahra yace ze auro kina da matsala da hakan ko akan ki zata zauna eye?
To ai shikenan, yanzu kinyi yadda kike so ba daular da kike ciki kike baqin ciki wata tazo taci ba itama se ki shirya Allah ya kiyaye amma Jarabar da kika janyo masa sekin fi uban kowa dana sani wallahi dan ba'a shiga komar Dr Sabitu a fita lafiya musamman ta hado da wannan yar da yakeji kamar ransa".

Maganganun Alhaji Badaru ba qaramin tension suka qara a palour Khalil da yayi wuri wuri da ido yana kallon Alhaji Badarun, kalaman Uncle Anwar na sake dawo masa da yace
"Se kuyi taka tsantsan da duk wata contract da zaku dan Dr Sabitu mugune tsaf ze iya framing naku ya saka ku a matsa".

"Am nace kwangilar harta nawa ce ne haka?" Baba Abdullahi ya katse musu shirun a zafafe Alhaji Badaru ya sake cewa
"It worth billions of naira, inda yayi aikin nan Alkhairin daze samu Allah kadai ya sani amma yar baqin ciki ta hana"

"Biliyan kace, amma Umaimah anyi yar kutumar uba wallahi" Baba Abdullahi ya fada yana miqewa tsaye, kafin su ankara ya isa gabanta ya faska mata mari ya sake kifa mata wani Alhaji Garba dayafi kusa dasu ya riqe shi yana cewa
"Haba haba Alhaji ya haka kuma"
"Barni naci uban yarinyar nan ko bakaji abinda tayi bane?
Ai wallahi baka burgeni ba Khalil daka sani a Injin da kuke niqa sumunti ka jefa yar banza ka markadeta in yaso kazo kace mana ta bata kawai daga baya ka lallabo ka.gayamun abinda tayi maka mu taru mu rufe maganar wannan abin takaici har ina" Baba Abdullahi ya fada yana ciza yatsa, duk yanda suke cikin jimami seda maganarsa ta bawa kowa dariya suka murmusa banda Alhaji Badaru da Abba da yayi quri kawai yana kallon Umaimah. He can't believe it ace rashin tunanin Umaimah har ya kai haka. Maganar Alhaji Badaru ta katse shi da yake cewa

"Dallah rufe mana baki ba nan ka gama fuffuka da ihun zaka rama mata ba shine yanzu zaka zo da wata Dramar ka ta qarya. Ni dana san ma akan wannan yarinyar ne da babu abinda ze hanani komawa Abuja na zauna jin takaici, daman ki tashi yanzu ki shiga ki hada kayanki, tare zamu tafi gobe in sha Allahu zan wuce Abuja da ita tunda babu me iya wanke mata kwakwalwa a cikin ku to ni zanyi idan ta saitu ta dawo hayyacinta se a sake zaman".

Bala'i Alhaji Badaru ya ringayi kamar ze tashi gurin duk sukayi tsit aka rasa me dakatar dashi dan daman yan gidan su Abban ba laifi akwai bala'i dan zamanin suna yara idanka takali daya da fada tofa danginka kaf sun shiga uku haka zasu taso ku a gaba se randa Allah ya huci zuciyarsu. Dakyar Alhaji Badarun ya iya yin shiru kafin Baba Liman ya dora da Nasiha shi kuma yana nunawa Umaiman rashin dacewar abinda tayi.

Umaimah hankalinta idan yayi cikin tirela ya tashi da jin wai zatabi Baba Badaru, ita kuwa wane tsautsayi nr ze ritsa da ita haka? Ai wallahi gara ta koma Khalil idan gunduwa gunduwa zeyi da ita yafi mata sauqi. Tun suna yara bata taba sha'awar ko zuwa hutu gidansa ba duk kuwa yanda su Nuratu ke doki da rizgillin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login