Showing 240001 words to 243000 words out of 429394 words

Chapter 81 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1052

shaidarta da babu komai a zuciyarta se Alkhairi ba kuma ta nufin kowa da sharri ballantana ace ko wani mugun abu da take aikatawa ne take ganin sakayya akan Umaiman, kawai ta qaddara kalar tata jarabawar rayuwar kenan tunda kowa da akwai ta inda Allah ya rage shi ko yake jarabtarsa sedai suyi fatan Allah ya shirya Umaimah in tana da rabon shiriyar su kuma ya qara musu juriya.

Bayan La'asar bisa Umarnin Abba badan Maman taso ba ta shirya suka tafi mayar da Umaiman kamar yanda sukayiwa Waliyyan Khalil din alqawari. Daya kira Baba Abdullahi shi daya ce ta zauna goben ze mayar da ita cewa yayi in yaje Allah tsine masa, daman dan ya samu ya sauke fushinsa yasa ya hana tafiya da ita yanzu kuwa ko banza zata koma da tabon marinsa gidan Khalil. Dariya abin nasa ma ya bawa Abba, haka suka kama hanyar gidan qarfe biyar suka isa, a qofar gidan suka tarar da Khalil tareda abokinsa Nasir Tsohon Malamin su Umaiman ya kawo masa ziyara ze tafi ya fito rakashi.

Cikin ladabi yayi musu sannu da zuwa, suka gaisa da Nasir kafin yaja motarsa ya tafi yana jimanta abinda Khalil din ya gaya masa Umaimah tayi. Yanzun ma yana kallon yanda taja hijabi ta rufe fuskarta ruf kallonta yake mamakinta na kashe shi gaba daya ji yake kamar shine silar janyowa Khalil din wannan tashin hankali, da beje gurinsa ba ranar da beganta ba. Qila da yanzu ya auri wata matar yana cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.

A falon Hajiya rasa inda zata ajiye su tayi murnar dawowar Umaiman da kunyar Iyayenta duk suka dabaibayeta. Anty Amina, Jamila da Jalila da suka tarar a zaune suka gaishe su kafin gaba daya suka miqe dan su basu guri. Dakin Habiba suka shiga, Jalilah ta tabe baki tace
"Ai dole su maidota dan na tabbatar su kansu zaman ta addabarsu zeyi haba yarinya kamar jikar shaidan"

"Kedai Jalila kin fiya daukar dumi, tunda Mijinta yace ta dawo ai dole ta dawo nasan baze wuce sunzo su qara bada haquri bane kawai amma duk mugun halin da ai iyayensa bazasu gujeshi ba" cewar Jamila se Jalilan ta sake cewa
"Banda dai me irin halin matar Khalil, kana zaune ta jefaka a masifar da za'a kulleka a kurkuku haba ai wallahi Khalil dai beyi sa'ar aure ba kwata kwata kuma wallahi bari a nutsa, ko bokan kan dutse ne yake mata tsafi qarewar bin malamai se mun karya alqadarinta Khalil yayi aure dan bazan zuba ido ina kallo ta kashe mun dan uwa a tsaye ba haba".

"Rigimar gidan Khalil dai in kika shiga ke zakiji kunya, kuma ma keda yar dakin taki ina ta kinfi kowa shigar mata idan anje gidan tawa mutane iskanci kice tsokanarta sukayi?
Qiri qiri ta daki Lubnan Kaduna amma keda Hajiya kuka daure mata qugu wai rashin kunya tayi mata ni wallahi tun sannan nasan bata da mutunchi in ba haba daga zuwan baquwa dangin Mijinki ki kamata da duka ai kome ta miki kya jira Mijin yazo ya dauki mataki amma gata isashshiya to ai yanzu da abin yazo kan kowa kwa kiyayeta" Anty Amina ta fada.

A can Falon Hajiya kuwa bayan sun gaisa Abba ya shiga bawa Khalil harda Hajiyar haquri akan abinda ya faru, Hajiya ta tare shi da cewa
"Haba Alhaji, ai mune ya kamata mu bada haquri dan mu mukayi laifi. Ai dukiya bata fi lafiya ba kuma shima na nasa fada sosai akan abinda yayi be kyauta ba duk neman da yakeyi dan su wa yakeyi? Badan dai itan da Yayanta bane kuma dan an rasa wani abu shikeban se yace zeyi fushi da hukuncin Allah bayan ba laifinta bane?
Abu in rabonka ne kana kwance ze same ka in kuwa ba nakan bane ko ka saka a baki se kayi amansa balle kuma abinda tun farko a ka qullo shi ta sigar yaudara Allah nema ya kama shi yaga nufinsa nason cutar da yarinyar mutane ya hana qulluwar abun".

"Maganar gaskiya Hajiya abinda tayi ko kusa da daidai beje ba kuma mutum me cikakken hankali baze ringa tunani irin na Umaimah ba. Sannan Hajiya irin wannan goyon bayan da take samu a gurinki shiyake sakawa take raina Mijinta take masa duk iskancin data ga dama dan tasan zaki tsaya mata wanda ba daidai bane. Ni na haifi Umaimah nafi kowa sanin halinta zuma ce ita seda wuta ake cinta dan haka na roqeki Hajiya da ki dubi Allah ki ringa tsawatar mata idan tayi ba daidai ba. Idan ba zaki iya ba ki bar Khalil ya dauki matakin daya dace akanta ki dena dakatar dashi.

Hajiya Alkhairin Umaimah kawai kika sani na yarda kuma kina Qaunarta dalilin daya sa kike kasa hango duk tarin laifin da aka ce ta aikata amma a Yanzu Khalil Shi yake zaune da ita, koni bazan gaya masa Umaimah ba a yanzu tunda ta fita daga hannunmu shi yake tareda ita. Duk wasu mugayen dabi'u da take koya a gurin qawayen banzan da take mu'amala dasu ya sani dan haka idan yace ta masa abu ki yarda ki kuma kirata ki tsawatar mata saboda kin fimu kusa da ita a yanzu" Mama ta fada se Hajiya tayi shiru gaba daya jikinta yayi sanyi.

Gani takeyi kamar Maman tana nuna cewar cutar Umaimah take ta hanyar qin nuna mata gaskiya tabi bayanta a koda yaushe wanda ita tsakaninta da Allah har a yanzu rashin kyautawar ta data gani bata kai irin yanda suke zuzuta abin ba. Tana yi mata uzuri saboda ta kasance itama a lokacin da take ganiyar quruciya kamar ta Macece me tsananin kishi sedai ko kwatan abinda Umaiman takeyi bata aikata ba dan ita nata kishin baya ko barinta ta kula Mijin ballantana wadda yake tareda ita. Lokacin Babansu Khalil din ya auri Mahaifiyar Jamila wanda auran gaba daya sun yarda qaddara ce da rabon samun Jamilar harta rayu shekara daya tareda Mijinta ta rasu a yayin haihuwar Jamilan magana bata taba hadata da ita ba, haka shima Babansu Khalil din, daga randa Fatiman ta tare ta raba shimfida dashi seda suka kwashe tsayin shekara biyu har bayan rasuwarta kafin ta iya danne zuciyarta ta karbeshi a matsayin Miji shiyasa ko kadan bata ganin laifin Umaimah dan tasan menene kishi, ta san zafinsa da abinda ze iya ingizaka ka aikata idan har bakayi takatsantsan ba.

Har suka tafi jikin Hajiya a sanyaye yake, seda ta rakasu ta dawo kafin ta kalli Umaimah da tunda suka shigo ta rabe a jikin kujera bata motsa ba. Maganganun da Abba da Maman sukayi mata a hanya ne suketa nuqurqusarta, nasiha ce me ratsa jini da jijiya sukayi mata a hanya har suka iso gidan. Idan da ace kunnenta najin magana ne daga lokacin ko kallon banza ba zata sake iya daga ido tayiwa wani ba albarkacin roqon da iyayenta sukayi mata na ta tausaya musu ta zauna lafiya a gidan auranta.

Kusada ita Hajiya ta zauna tareda dafata Umaimah ta dago fuskarta data canza kamannin saboda marin Baba Abdullahi idonta ya kawo kwalla Hajiya tace
"Subhanallahi, wa yayi miki wannan aiki haka?"
Seta saki hawayen suka fara zuba, cikin tausayi Hajiya tace
"Ki dena kuka kinji komai ya wuce yanzu tunda dai gashi kin dawo. Dan Allah ki koyi haquri Umaimah duk abinda ya faru tsakaninku kizo nan ki gaya mun kar ki dauki hukunci a hannunki dan kinga dai har iyayenki sun fara ganin ni nake goya miki baya kina abinda kika ga dama ina ga sauran mutanen gari?
Yanzu ki tashi maza kije dakinki kiyi wanka ki huta babu komai in Allah ya yarda".

"Toh Hajiya Amma Khalil be haqura ba, kinga fa ko kallona beyi ba tsoro nakeji kar na koma ya sake yi mun wani abun ni dai zan zauna anan har zuwa sanda ze sakko daga fushin Hajiya" Umaiman ta fada tana kuka. Hajiya tayi murmushi kafin ta kalli bangaren da Khalil ke zaune bayan ya dawo daga rakiyar su Abban tace
"Ki rabu dashi babu abinda zeyi miki ko kallon banza ya sake yi miki a cikin gidan nan sena saba masa balle yace ze taba lafiyarki. Maza share hawayenki ki kuma cire damuwar komai daga ranki kodan saboda halin da kike ciki, ni se naga cikin ma ya rage girma gaba daya ma kin rame da alama bakya cin abinci, bari na kawo miki Tuwo maza kici kiyi wanka cikinsu Jamila wata ta raka ki Asibiti su sake dubaki dan bazan ma hadaki dashi balle kuje ya ringa miki muzurai".

Yanda kasan gunki haka yayi musu bema nuna alamar yaji abinda Hajiyar take fada ba balle ya tanka. Laptop din dake kan cinyarsa kawai yake dannanwa amma tunaninsa yana kan abinda Abban Umaimah ya gaya masa yanzu.
"Idan ka gaji da halinta babu me takura maka Khalil ka sawwaqe mata ni na haifi Umaimah idan kuma da ace kaine a matsayin Dana tabbas bazan goyi bayan kaci gaba da zama da kafaffiyar mace mara jin magana irinta ba. Ka bawa zuciyarka damar yin tunani in har kaga da cutuwa a zamanku ka sawwaqe mata kawai kowa ya huta" nazarin maganar yakeyi tausayin dattijon yana sake shigarsa. Sukam dai tasu jarabawar kenan kuma ze cigaba da haquri da ita saboda su zataci albarkacin su da kuma na Yaran dake tsakaninsa da ita amma wallahi da ace be haihu da Umaimah ba a wannan gabar da tuni ya sallameta dan be tabajin ta fitar masa a rai duk wani abu nata yayi masa baqi ba se a wannan karon, ya kuma tabbatar babu wani abu da zata sakeyi da ze wanke ta a idonsa ya dena tuna abinda tayi masa.

Jin Hajiya zata dame shi ma dan se magana take tana sako sunansa a ciki ya saka ya tattara ya bar gidan gaba daya, su Jalila ma dai datayi musu zancen daya daga ciki ta raka Umaimah Asibitin gaba daya zamewa sukayi kowacce tace tana da uzuri suka yi tafiyarsu gaba daya. Qarshe se ita da kanta ta rakata bayan tayi wanka sabon Driver da Khalil ya daukarwa Hajiyan saboda Khalifa ya koma makaranta ya kaisu. Likita ya dubata ya tabbatar musu da komai lafiya cikin kuma daman tun wancan karon ya sanar musu da yuwuwar ya qara lokaci akan lokacin daya kamata ta haihun a farko saboda jinin data zubar ze iya sakawa ya koma baya ga rashin nutsuwar da take ciki zata iya affecting cigaban girman jaririn dan haka dole seta haqura da duk ma abinda yake sakata damuwar kodan lafiyarta data abin cikinta. Ya rubuta mata yan magubgunan da zasu taimaka mata yace taje taci gaba dasha daga nan suka kama hanya tsabar daurewa qarya Ass Hajiyan harda saka Driver ya kaisu gurin da ake siyar da kayan maqulashe ta siyowa Umaiman da sam bakinta babu appetite. Tunanin yanda zata kwashe da Khalil kadai ya saka jininta yana neman hawa, idan ya kuma maimaita mata irin waccen shaqar ta tabbatar kafin azo ceto ta margaya ta yuwu ma ajaline yasa su Maman suka dawo da ita gidan ganin qarshe ta musu toh Allah ya jiqanta kawai.

Tas ta tarar da bangaren nata dan hatta da dakinta an zuba sababbin furnituresda suka fi wanda ta fasa kyau da tsada dukda ba'a gaya mata ba. Ruqayya ta kwalawa kira ta hau saman cikin rawar jiki ta sake gaisheta, Umaimah ta tambayeta yaushe aka saka kayan nan tace dazu da safe.
Sosa kai ta shigayi cikin son amayar da gulmae dake cikinta tace
"Ai tun jiya da Alhaji ya sanarwa Hajiya yau zaki dawo muna daga dakin Furera na jiya tana ce masa se ya saka a kawo miki sabon gado a saka. Yace baze siya ba, kinga rigimar da suka kwasa kuwa? Kai gaskiya Hajiya kinyi sa'ar uwar Mini matar nan tafi sonki ma inaga akan dan nata har cewa fa tayi zata saka azo a kwance nata gadon a saka miki tunda baze siya ba shine fa Alhaji hankalinsa ya tashi ganin tana neman tayi kuka yace ze siya. Wallahi Gadon ma ita ta zaba dan da safen tare mukaje wani kanti aka siyo kusan Miliyan nawa in gaya miki qarshe ma ita ta cika kudin dan abinda ya bayar be isa ba tasa aka zuba miki su".

Hannu kawai ta dagawa Ruqayyan akan taje ta zauna bakin gadon tana shafa katifar kamar wadda bata taba ganin ta ba se yau zuciyarta fal tunanin irin wannan Qauna da Hajiya takeyi mata. Turo qofa akayi da qarfi ta zabura dan a zatonta Khalil ne sega Mu'ayyad ya shigo da gudu Bibi na binsa a baya suka fada jikinta gaba daya suna ihun murnar ganinta.
"We missed you Mummy kullum muka cewa Daddy ya kaimu gurinki se yace gobe zaki dawo har na gaji da irga gobe" Mu'ayyad ya fada yana nuna matan goben daya irga da hannunsa. Qara jansu jikinta tayi tana murmushi dan itama tayi kewar yaran nata sosai tace
"To gani na dawo ai shikenan?"

"Yes Momy, meya samu face dinki it looks scary?" Ya sakw fada yana shafa fuskar tata da duk ta fita a kamanni ta swta riqe hannunsa kawai tayi murmushi dan bata san me zata ce masa ba,
"Where you involved in an accident?" Ya sake jefa mata wata tambayar, se kawai ta daga masa kai dan Mu'ayyad wayo ne dashi idan bata amsa ba ya ringa tambayarta kenan, saurin dagowa tayi jin muryar Khalil a dake yanayiwa yaran magana akan suje su kwashe kayan da suka zubda a falo. A firgice ta kalle shi dan bata ji shigowarsa dakinba kodan qofar a bude take shi yasa. Seda yaran suka fita kafin ya taka a hankali har ya isa gabanta, zuciyar Umaimah dake bugu kamar zata daka tsalle ta fito saboda tsoron yanayin fuskarsa. Tunda take dashi bata taba sanin ya iya hada fuska irin haka ba gaba daya se taga ya sauya mata ma tamkar ba Khalil dinta da koda yaushe idanunsa suke cike da bege da shauqin soyayyarta ba.

KHALIL
Kallon yanda ta firgita da ganinsa yakeyi daga inda yake tsaye yana jiyo yanda take fizgar numfashi tana dawo dashi da sauri da sauri kamar wadda Miciji ya ritsa. Kallon salihar fuskarta yake wadda take yaudarar mutane da ita ciki harda Hajiyarsa da ya rasa me Umaimah take mata da ta kasa ganin laifinta. A cikin fa wannan marrar data ja masa muguwar Asara Hajiyar ta tursasashi siya mata Gadon Miliyan daya, akan yace baze siya ba Hajiyar ta nemi zubarda hawayenta. Batayi masa kuka bama yana ganin ta kansa a hannun mace inaga tayi dolensa ya zare kudin ya bayar baqin ciki kamar ze qumeshi ya mutu. Wato tukuicin Asarar data janyo masa ya bayar yanda gobe idan ta tashi zata jijjigo wanda yafi wannan toh wallahi bataci banza ba, Hajiyar na fita ya dauki motar da Umaiman take hawa ya fita da ita ya siyar ya mayar da kudinsa garda riba. Da batayi masa baqin ciki ba ba Gado ba ko gida take so seya gina ya mallaka mata acikin abinda ze samu daga aikin da zeyi amma yanzu kuwa gadai gidan nan ta dawo ta zauna zata gane shayi ruwane za kuma tasan ba Lusaranci bane yasa yake dauke kai akan duk abubuwan da take masa a baya, tunda haka ta zaba yanzu zaman ze chanza zata san cewar shi Khalil ba kanwar lasa bene ba.

Juyawa yayi ya fice daga dakin Umaimah ta saki ajiyar zuciya ganin ya kullo mata qofa kafin ta miqe dakyar ta shiga bandaki saboda fitsarin daya matsota na tsoro, jan qafarta kawai take danhar sannan basu gama sauka daga kumburin da sukayi ba. Shirin bacci tayi gaba daya, seda ta leqa ta kira Ruqayya ta tambayeta ina yaran tace sun tafi gurin Hajiya da Yallabai kafin ta koma dakinta ta kwanta bayan ta jaddada mata ta tabbatar ta kashe komai kafin ta kwanta. Bata zaton zataji dadin me aiki ba se yanzu, haka ta raba dare tana sake saken sanda ya dace ta bawa Khalil din haquri har bacci ya kwasheta a sabon gadonta.

Washe gari kafin ta yi wanka ta shirya ma Khalil ya fice daga gidan, dan haka data fito kai tsaye dakinsa ta wuce da niyyar zuwa ta gaida shi tunda tasan a yanzu dai baze shiga dakinta ba kamar yanda suka saba. A kulle taji qofar dan haka ta shiga kwankwasawa ko daga ciki ya rufe, Ruqayya data hawo saman da kayan share ta gaisheta kafin tace
"Aiko ya fita Hajiya"
"Ya fita?" Ta maimaita a zuciyarta tareda tsurawa Ruqayyan idon tana mamakin ya akayi tasan Khalil din ya fita, kamar tasan me take tunani tayi saurin cewa
"Ina kitchen naji an bude qofa dana leqo se naga shine na koma, ga abin kari canna gama hadawa nan za'a hawo miki dashi ko na bari a qasan?"

"Ki kawo mun nan" ta bata amsa kafin ta juya dakinta. A nan falon saman ta karya kafin Ruqayyan ta gama gyaro mata dakinta ta dawo falon ita kuma ta koma ciki. Tun zuwanta daman Anty Laure ta zayyana mata ayyukan da zata ringayi, gyaran gidan gaba daya banda dakunan Khalil, Anty Lauren ke musu girki yau kuma da bata nan yasa tayi karambanin yi tunda kusan tasan me suke karyawa dasu da rana ko dare ne taga tana tambayar Umaiman abinda za'ayi.

Umaimah ko kan gado ta koma ta miqe gaba daya bata jin dadin komai, so takeyi ta kira Mama ta bata haquri amma bata san inda wayarta take ba dan haka ta tashi ta fito daidai Ruqayyan ta fesa Airfreshner ta dakata tana tambayarta ko akwai abinda take da buqata ne?
"Dakin da na zauna a qasa zaki duba mun ko wayata tana nan" ta fada mata se Ruqayyan tayi saurin cewa

"Tana nan kuwa, jiya da mukayi gyaran gidan na ganta se nasaka miki cikin drawer bari a dakko" da rawar jiki ta sauka qasa, Umaimah ta bita da harara, bata zaton zasu shirya gaskiya dan da ganinta zatayi tsugudidi ga shegen rawar jiki. Abinda yasa ma ta yarda da zamanta dan ta iya aikine kuma tasan ko mi maitar Khalil babu abinda zeyi da wannan kallo ma bata ishe shi ba sannan a yanzu tanada buqatar mataimaki kafin ta haihu ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login