Showing 309001 words to 312000 words out of 429394 words

Chapter 104 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

971

tayi dole ya kasa riqe kansa a gaban Unaizatu ya rungumeta kunya kamar qasa ta bude ta shige ita kanta Unaizatun babu shiri ta basu guri ya zauna akan kujera kafin ya dorata akan cinyarsa yana kallon fuskarta da tasha light make up. Dinkin doguwar riga ne a jikinta na wani Burn orage din Lace ya karbi farar fatarta ya mata kyau mara misaltuwa ga qamshibta da yake gigitashi kullum suka rabu se yayi wankan turare a mota gudun kar yaje gida Umaimah taji wani qamshi na daban tsiya ta balle. A baki yau ta ringa ciyar dashi saboda gataz Khalil ya lalace a gurin yana kallonta kawai kamar wani soko, Allah ya sani dauriya yake ba yar kadan ba amma da tuni ya dade da daukarta sunje wani gurin ya kashe qishinta daya addabeshi amma bazeyi hakan ba, yafi so ta samu kulawa kamarta kowacce Mace me gata ya kwanta da ita a cikin gidansu kan Gadon auransu dalilin daya saka ya rage aikin daya dakko kenan a gidan da yake so ya ajiyeta, Bene yaso ya dora amma ze ja masa lokaci dan haka ya barshi a flat din da yake amma ya canza masa fasali kuma yana saka ran aikin ze kammala a qasa da watanni biyu in Allah ya yarda.

"Wannan kallon fa haka kamar zaka cinyeni" Humaira ta fada cikin salon kissar da Anty Mariya da Unaizatu suke koya mata, seda ya gyara zama saboda yanda muryar ta shige shi kafin yace mata
"Kyau kikayi mun ji nakeyi kamar na daukeki mu tafi kawai"
"Mu tafi ina?" Ta tambayeshi tana bude ido seyaja hancinta yace
"Gidana mana ko ba zaki bini ba?"
"Aini banga alamar kanaso na kasance a gidanka ba dan babu wani shiri da naga kanayi" ta fada tana kallon gefe. Mamakin maganarta yayi se ya janyo wayarsa yana cewa
"Waya gaya miki haka? Kin san yanda abubuwa suka faru so fast ban taba tunanin za'ayi haka ba amma kalla ki gani tuni har anyi nisa a gyaran gidanki ke baki san na fiki qaguwa da ki tare bako kawai dan kince ke ba zaka zauna da matata bane da kawai bangarena zan bar miki kiyi zamanki a sama" ya miqa mata wayar bayan daya kunna mata video aikin gidan da akeyi.

Baki ta tabe bayan data gama gani ta sake cewa
"Wancan ai gidan matarka ne kaima da kank kana fada kuma ni bana raba abu da wani na fison nawa ni kadai"
"Gashi kuwa kin yiwa wata kwacen Miji" ya bata amsa cikin zolaya seta gimtse fuska tayi masa shiru wato abun ya motsa.
"Haba mana karki bata ranki hak kawai muje ki dan rakani wani guri mana" ya fada yana jan kumatunta seta miqe ta shiga tattara kwanukan da yaci abincin. Bayan dogon gargadi da jan kunne data sha a gurin Unaizatu suka fita taren, gidan Jalilah yakaita data kwarzabeshi akan seya kawo mata ita zasuje a aunata ayi mata dinkunan fitar biki. A gidan ya barta saboda Anwar daya kirashi suna da wani emergency daga qarshe se Khalifa ya saka yaje ya mayar da ita saboda Magriba tayi kuma har sannan be gama abinda yakeyi ba.

Yana komawa gida ya tarar da saqon Baba Abu da yaje be same shi ba, kamar yanda ya barwa Hajiya saqo cewar sunyi waya daga can Jalingo Alhaji Musa ya kirashi yana tanbayarsa gurin zama zasu siyawa yarsu Gado sun kuma tambayi Mama Hauwa ta sanar musu Basu rigada sun nuna guri ba dan haka ya kirashi da kansa dan yaji. Baba Abun ya bar masa sallahu bayan da Hajiya ta gaya masa shirin Khalil din na raba gida yana kuma kan aikin gyaran inda ze saka Amaryar ne. Baba Abu ya ringa fada yana cewa
"Wane irin gurin zama kuma yana nufin duk girman gidan nan babu daki fmda ze sakata a ciki ina a can sama ma a kwai bangare guda nasa ko kuwa ita uwar gidan duk ta baza kaya a ciki? To idan ma ta baza se ya gaya mata ta kwashe dan ba zan dauki wannan sakarcin ba a bar yarinya qarama da aure wannan ai ba girma bane duk karamcin da iyayenta suka mana bayannaje na gama cika baki akan a shirye yake shine ze zo da wani sabon shaqiyancu? Ni wlh ban zata za'a ci kwana uku ma be san abinyi ba gashi har sun gaji sun magantu to yazo ya share mata daki a nan a basu suyiwa yarsu jere yawwa".

Mamaki be kashe shi ba seda yaji cewar har a sannan matar gidan bata san da halin da ake ciki ba seya miqe yana cewa." Wannan kuma ya rage nasa da yasan be isa ba ya dakko abin Isassu? To ki gaya masa tun wuri idan ze ari Jarumta ya sanar mata yayi idan ba haka ba ni nan zanzo da kaina na shigo mata da Amaryar se muga qaryar boye boye, ki gaya masa na bashi daga nan zuwa rana irin ta yau Takwararki ta tare a dakinta idan ba haka ba kuma ze gamu dani".

Da wannan maganar ya kwana a ransa, idan ta qure dole ya ajiye Humaira da Umaimah a gida daya na wani lokaci amma ta yaya yanzu ze sanarwa da Umaimah wannan al'amari? Shine babban tashin hankalinsa da tunanin yake kwana yake tashi a kullum kuma ya tabbata dole komai dadewa maganar zata fito idan be gaya mata da kansa ba Baba Abu ya shammaceshi kamar yanda ya fada ya kuma san ze aikata kai qaramin abu ne daga ayyukansa ma.


*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 69

Yanda yaga rana haka yaga dare washe gari kuwa qarfe shida ya fita daga gida bayan ya shiga bangaren Hajiyarsa ya sakeyi mata magiya akan ta kira Umaimah da kanta ta gaya masa maganar auran.
"Babana kaida kake Mijinta ka kasa gaya mata se ni kake so na debi baqin jini bayan wanda na rigada nayi? Idan ba zaka iyaba ka kira Jalilah nasan da murna zatayi maka wannan aikin amma ni kagan ni nan idan ka shirya gaya mata ma ka sanarmun dan na bar gidan ranar kar tsautsayi ya rutsa dani" amsar da Hajiyar ta bashi kenan se kawai ya zabi daya bar gidanya tafi can wani gurin ya samu damar yin tunani da kyau.

Can kan hanya ya samu inda babu hayaniya ya faka motar ya lula cikin tunani. Duk Abokanansa daya nemi shawara amsa daya suke bashi akan wai ya sameta suyi magana ta fahinta ya nuna mata qaddara da muhimmancin yarda da ita sannan ya nuna mata cewar beyi aure danya wulaqantata ba ta qaddara cewar Allah ne ya hukunta faruwar hakan kuma ba zaka tsallake ba to idan banda abinsu a yaushe a kuma wanne lokaci zata samu nutsuwar fahimtarsa?
Ya tabbatar daga inda ya faro mata wannan nasihar tasan inda ya dosa ba duk kuma abinda ze biyo baya ya tabbatar da be me kyau bane.

Allah sarki Yaya Aminu, da ace yana raye kai tsaye gurinsa ze tafi ya kai kukansa kuma ya share masa yau gashi baya nan a lokacin da yake tsananin buqatarsa ya kuma kasa zama Jarumin da har a maganarsu ta qarshe seda ya goranta masa. Shi dai indai a gurin Umaimah ne baya zaton ze taba zamowa wannan Jarumin yanzu bayan Yaya Aminu se waye fada mata taji kuma tayi babu ja'in ja?

Mama Malika ce ta fado masa a rai, sosai kuma yayi na'am da shawarar zuciyarsa dukda wani bangaren yana so ya hanashi dalilin nauyi da kunyarta da yake nema ya kamashi. Yana ganin rashin kyautawar ba iya Umaimah yayiwa ba ita kanta Maman abin ya shafeta amma dukda haka uwa uwa ce yasan kuma a karamci irin nata ita kadai ce zata fahimce shi kuma ita take da kalaman Ladabtarwa da zatayi amfani dasu gurin kwantar masa da hankalin Umaimah.

Tayar da motar yayi kai tsaye ya kama hanyar gidansu Umaiman, be damu da lokaci ba da kuma kasancewar ranar Asabar qila mutanen gidan basu tashi ba haka yayi musu tsinke yaci sa'ar tarar da Salman a qofar gidan ze fita makaranta yana da Test, shi ya koma yayi masa iso ciki bayan sun gaisa Mama dake tsakar gida tana aikace aikace ta tsaya a gurin gabanta na faduwa jin wai Khalil ne yazo da safiyar nan daman daren jiya tayi mafarki da Umaimah, yanzu niyyarta idan ta gama abinda takeyi tabi Abban idan ze fita ya sauketa gidan Umaiman ta dubata dukda se kuma ga Khalil da farar safiya, Allah yasa lafiya.

Har qasa ya durqusa ya gaisheta ta amsa masa cikin dattako, yanayin da ta ganshi a nutse beyi kama da wanda wani mugun abu ya faru a gidansa ba ya sa hankalinta ya dan kwanta. Falonta ta bude masa suka shiga, yabi gurin da kallo dakin Dattijuwa kenan ko ina qal qal anyi shara an goge ga qamshin turare yana tashi ita kanta Maman dukda Dogon Hijabi ne a jikinta amma yanayinta ya nuna tayi wanka shiyasa be taba alaqanta qazantar Umaimah da kowa ba, Ya shaida Mamanta me tsaftace, haka duk yan uwanta babu wadda ya taba zuwa gidanta ya tarar da abinda ba haka ba. They are super neat gashi sun iya girki ita kadai ta fita zakka dalilin dan banzan son jiki data dorawa kanta da waya data aura, ita take hanata komai ta wuni tana Chatting da mutanen banzan da babu abinda suka qareta dashi se qara jefata cikin Jidali.

Fita Maman tayi bayan ya zauna bata dade ba ta dawo dakin ta Flask din ruwan zafi Sharifa na biye da ita da Try da aka dora kuloli qanana guda biyu da kofi da cokali ta ajiye gaban Khalil din tana gaishe shi Mama ta qarasa ciki ta dauko container Sugar sannan ta zauna tana cewa
"Kunun gyada ne ga qosai ga doya nan se ka saka wanda zaka ci, yau da muri mukayi abin karin saboda yara masu zuwa Tahfiz"
"Nagode" ya mayar mata kansa a qasa yana ayyana ta yanda ze fara gaya mata abinda ya kawo shi, se Mama ta miqe da niyyar ta bashi guri tace
"Bari na duba Abban naku naga ko ya tashi se ka shiga ku gaisa" tana gama fadar haka tayi waje tasan magana ce ta kawo shi koma wace iri ce tana fatan ta zama ta Alkhairi.

Sanda ta isa bangaren Abban ta taraddashi a falo yana duba wani Littafi da yake rubuce rubucen Cinikayyarsa ta zauna a kan Kujera, seda ya qarasa kwafar abinda yake nema a takadda kafin ya rufe ya kalleta cikin raha yace
"Hajiya Malika irin qamshi haka tun daga waje na jiyo shi nace Sarauniya ce tafe"
Murmushi tayi masa tace
"Yau kuma da zolaya ka farka kenan"
"Ba zolaya bace kema ai kinsan gaskiya ne azo a sammin turaren nima an jima zanje Daurin aure, ya maganar fitar taki kuwa tana nan? Koda yake ya kamata kije ki dubota dai gaskiya mu fita da wuri saboda nima na dan tsaya mu gaisa kafin na wuce daurin auran" Abban ya sake fada se Mama ta gyara zama tace

"Ai yanzu ma abinda nazo na gaya maka ga Mijinta can yazo dukda dai banga wani alamun tashin hankali a tare dashi ba na tabbatar dai zuwan bana haka kawai bane idan kayi duba da lokace, takwas ma bata cika ba ace Khalil yazo gidan nan kuma shi kadai ai da magana"
"Tohh Allah yasa lafiya, kije kiji abinda yake tafe dashi idan kuma ya shafeni toh se kuzo nan din nima naji"
Seta miqe tana cewa
"Wane irin idan ya shafeka kai ko abu ya shafa dumu dumu dan kasan babu abinda ze kawoshi gidan nan se maganar Umaimah kaga kenan kai keda ruwa sa tsaki a ciki".

Sanda ta koma Dakinta ta tarar da Anty suna gaisawa da Khalil din, bata shiga ba ta tsaya daga bakin qofar tana kallon kayan abincin da be taba ba tace
"Ka qaraso Alhajin ya tashi" seya miqe kamar daman jiran umarninta yakeyi ta matsa masa yayi hanyar dakin Abba ita kuma ta tsaya amsa Anty ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?dake tambayarta lafiya dai ko
"Lafiyar kenan" ta bata amsa kai tsaye tana bin bayan Khalil din.
A mutunce ya gaida Abba ya amsa masa yana tambayarsa su Hajiya se sukayi shiru gaba daya kafin Abban ya sake cewa
"Malam Khalil lafiya dai ko muka ganka da safiya ko mutuniyar ce tayi bore?"

Khalil dake zaune a qasa ya sosa kansa idanunsa na kallon qasa dan sosai yake jin nauyin abinda ya kawo shi amma bashi da wata mafita idan basu din ba, maganar Abba ce ta katse masa tunani da yake cewa
"Ka saki jikinka kayi magana Khalil kar kace zakaji nauyi ko wani abu" se Mama ta amshe da cewa
"Nasan dai baze wuce wani shedancin ta sake yi maka ba to ka bude baki kayi magana idan kuma kana jin nauyi ka kasa fada yanzu daman da niyyar zuwa gidan naku na tashi yau zanje na titsiyeta ita ta fadamun da bakinta me tayi tunda dai ita kunnen qashi gareta idan kuma aka jita shiru to wata tsiyar take qullawa"

"Aa Mama wannan karon ni nayiwa Umaimah laifi ba ita ce tayi mun ba shiyasa ma nazo gabanku da qoqon bara dan ku shiga cikin Al'amarin ku tayani shawo kanta tayi haquri" Khalil ya fada a sanyaye ba tareda ya daga kai ya kalle su ba, shiru sukayi gaba daya ya tabbatar a zukatansu mamaki sukeyi suna kuma ayyana wani laifi yayiwa Umaimah da har yake neman su shiga ciki.

"Ikon Allah, wane laifi kayi mata haka da har se mun shiga ciki zata haqura? Koda yake a kafiya da dan banzan rashinji na Umaimah na tabbata qaramin abu ta dauka ta maida babba saboda ta hanaka nutsuwa irin yanda ta saba to zata ci gidansu kuwa zanje gidan" Mama ta sake fada se Khalil yayi qundum bala cikin karyayyar murya yace
"Aa Mama dagaske a wannan karon nine mara gaskiya kuma ni nayi mata laifi, laifi babba da na cancanci ko wanne irin hukunci daga gurinta amma wlh nima ba laifina bane tsarine daga ubangiji wanda babu yanda na iya akai" se Mama da Abba suka kalli juna kafin suka sake kallon Khalil daya ci gaba da cewa

"Ban sani ba Mama ko ta gaya miki zancen ina neman aure tun kwanaki dan a sannan mun dan samu matsaloli da ita ta kuma nuna rashin amincewarta a lokacin har Hajiya ta goyi bayanta akan na haqura da batun auran tunda bata so to wlh Mama nima bansan yanda akayi ba, kawai na dauki duk abubuwan da suka faru a matsayin qudurace daga ubangiji wanda yake aiwatar da abinda yake so a kuma sanda yaso" tiryan tiryan ya labarta musu abinda ya faru dama matsayin da ake ciki a yanzun ya qarasa yana cewa
"Wlh Mama bani da wata masaniya akan haka ze faru kuma da ace sun sanar mun kafin su kai ga daura auran zan dakatar dasu saboda ban shirya ba amma Ubangiji ya rigada yayi nasa tsarin ba kuma ni da wani abu daya bi bayan na karbi abinda aka rubutamun".

Kallon Khalil sukeyi gaba daya harya kai qarshen dogon bayanin daya dakko, Mama dai tsam tayi a inda take kalmar aure tana mata yawo a kwakwalwa yana nufin yayiwa Umaimah kishiya kenan, Abba kuwa gyaran murya yayi kafin yace
"To Alhamdulillahi Khalil ina tayaka murna bisa wannan abun Alkhairi daya sameka Ubangiji ya Albarkace ku gaba daya ya kuma baka ikon yin Adalci a tsakaninsu, yanzu abinda ban fahimta ba anan shine laifin menene kake iqirarin kayi mata da har taqi haqura?"

Sake sunkuyar da kansa qasa yayi yana ajiyar zuciya saboda fitar da abunda ya tokare masa maqoshi ya hanashi nutsuwa da yayi se ya bude baki a hankali yace
"Nayi aure ba tareda saninta ba kuma wlh Abba nima..."
"Kai da Allah wannan rantse rantsen ya isa haka, kamar yaya kayi aure bada saninta ba? Ita zata nemo maka auran ko kuma ita zata baka muhalli da abinda zaka ciyar da matar da dole se ta san abinda kake ciki?
Sannan yanzu kake cewa tasan zakayi aure har kunyi rigingimu Mahaifiyarka tace ka haqura to Ubangijin daya halasta maka yin qarin ya nufa se kayi se akayi Yaya kuma Umaimah ta isa taja da hukuncin Allah ne, aure an daura Mata ta tare a gidanka to kuma duk tashin hankalin na menene yanzu?" Abba ya katse Khalil ita dai Mama kallonsu kawai takeyi tana kuma jinsu amma ta gaza ce musu komai.

Harga Allah a wanann gabar tausayin Umaiman seda ya kamata a matsayinta na mace ta saka kanta a matsayin ita akayiwa haka dole abin da ciwo musamman a gurin wadda take tsananin Adawa da tsarin zama da wata kamar Umaimah, tabbas dole Khalil ya rude ya kuma tsorata akan rashin sanin yanda zata karbi Al'amarin.

"Aa Abba Amaryar bata tare ba kuma a yanzu maganar da mukeyi ita Umaimah bata san da zancen auran ba na rasa ta yanda zan gaya mata saboda bansan a yanda zata dauki al'amarin ba Allah ya sani ina sonta kuma ina gudun bacin ranta musamman a wannan Halin da take ciki bata buqatar jin wata magana da zata tayar mata da hankali shiyasa naso ace har se zuwa bayan ta haihu sannan zan gaya mata amma jiya Baba Abu yazo akan iyayen yarinyar sunyi magana akan a nuna musu inda zata zauna, yayi ta fada ya kuma jaddadamun idan banyi wani abu kafin cikar sati daya ba to shi da kansa ze dakko Amaryar ya kaiwa Umaimah".

"Zancen banza ma kenan yanzu kana nufin yarinyar tana gidan iyayenta kenan saboda kana tsoro ka gayawa matarka tayi tashin hankali ka gwammace ka fara nuna rashin Adalci a tsakaninsu tun gabanin su zauna tare ko? Dan ubanta ita ba'a aure ka aureta kake kuma zaune da ita duk mugun halinta shine har zaka gwammace ka cutar da wata saboda kar ran Umaimah ya sosu to yanzu da menene shirinka? Idan iyayenta basuyi magana ba kenan haka zaka bar musu ya tayi ta zama da aure akanta ko?"
Girgiza kai yayi kawai saboda jin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login