Showing 312001 words to 315000 words out of 429394 words

Chapter 105 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

930

yanda Abban yake magana cikin fusata se yaci gaba da cewa
"Saboda Allah Khalil se yaushe zaka zama namiji a cikin gidanka? Kayi aure haka Allah yaso kaima ba tsarinka bane se kuma meya faru da bazaka iya zaunar da ita ka gaya mata ba har se kazo kana rara gefe kana neman wanda ze tayaka gaya mata ita ba musulma bace ai tasa san lamarin aure abune da babu me shiryashi haka babu me hana faruwarsa idan Allah ya kawo shi shi se anyi babu makawa ni gaba daya ma kai ka bata mun rai yanda kake wani karya murya kana fadar kayi mata laifi cika umarnin ubangiji ne laifin da kayi mata kome?

To ko Abubakar be dauki Amarya ya kai mata ba ni ubanta zanje da kaina na dakko yarinyar na kai cikin gidan domin duk muna da Yaya idan kuma wani ya aure su ya jingine mana su haka ba zamu ji dadi ba dan haka babu ta yanda za'ayi mu bada goyon baya ayiwa yar wasu haka. Ka tashi ka tafi duk ma yanda zakayi a yau ka sanarwa da Umaimah kayi aure kuma idan har iyayen Amaryar a shirye suke a gobe su kai yarsu dakinta babu abinda za'a jira zan kira Abubakar din yanzu ina gaya masa" Abban ya qarasa maganar a fusace se Khalil ya daga kai ya kalleshi yana zare ido jin wani zazzafan hukunci daya zarce na Baba Abu.

Shida ya rugo gurinsu da fatan samun Agajin gaggawa amma shine za'a sake yi masa turin jeka ka mutu da wane qarfin guiwar ze doshi Umaimah kai da Alama Abba ya manta akan wa ake magana gaskiya. Maganar Mama Malika ce ta cece shi da taja numfashi ta ajiye tace
"Alhaji da akalama baka fahimci abinda yake nufi ba, aure fa aka daura masa yau sati daya Matarsa bata da labari, kamar ka manta wadda ake magana akai kake cewa gobe zaka saka akai yarinyar mutane gidan haba Alhaji kadai tsaya ka duba wannan abu dakyau tabbas qarin aure ba laifi bane amma yanda al'amarin ya afku kowa cece hakan ta fada akanta dole taji babu dadi kuma zata buqaci a bata lokaci ta samu nutsuwar zuciya"

Wani Kallo Abban dake danna waya yana neman number Baba Abu ya watsa mata kafin yace
"Tunda batun kishiya akayi ai dole yau ki rikida kibi bayan yarki, duk iya shegen da ta ringa tata masa ina keda bakinki kinsha ce masa yayi auran ashe duk maganar ba taje zuci ba kenan iya fatar baki kike yinta yanzu kuma da ubangiji ya zartar da hukuncinsa zaki ce wani ba'a kyau ba saboda ku mata akan kishiya duk bakinku daya toh aure dai an daura amarya kuma zata tare a gidan Mijinta kuma dole tayi haquri ta karbi qaddara a yanda tazo mata yawwa" yana gama fadar haka ya miqe yana sake jaddadawa Khalil akan ze kira Abubakar. Dakinsa ya shige ya bar Mama da Khalil daya zabga tagumi dana sanin zuwa gidan ya kamashi tunda gashi ya zama sanadin da Mata da Miji auran sama da Shekara Arba'in suna Musayar yawu a dalilinsa.

Kallonsa Mama tayi cikin sanyi tace
"Kace bata san da kayi aure bako?"
"Bata sani ba Mama kuma wlh ni ban boye mata da wata manufa ba tsoron yanda zata karbi abun ya saka har yanzu ban gaya mata ba, kuma auran a yanda ya faru nima babu sanina a ciki Allah ne yayi" Khalil ya fada cikin yanayina karaya se Mama ta daga masa hannu tace
"Na sani Khalil kuma koda kayi hakan da niyya ba kayi laifi ba, Umaimah tayi maka abubuwa da yawa da ta cancanci hukunci amma ka haqura ka jure, yanzu da ubangiji ya saukar da qudurarsa yayi mata sakamako da abinda take qi wanda shine silar duk abubuwan da ta aikata hausawa sukace gudun qaddara guzurin taradda ita ai ba yinka bane yin Allah ne kuma bata isa taja da hukuncinsa ba dan haka duk abinda zatayi dole tayi ta haqura, babu damuwa yanzu kaje gida kamar yanda Alhaji ya gaya maka ka sameta kayi mata magana ta yanda zata fahimta, nasan abin da wahala amma ciwon da zataji idan ta tsinci maganar a bakin wani ze ninka wanda idan kaine da bakinka ka gaya mata in sha Allahu kuma ina fatan ta karbi qaddararta da kyakykyawan yaqini, yanzu kaje gidan jimawa kadan idan Allah ya yarda zanzo".

Kallon Mama yake da idanunsa da suka bayyana tsoro qarara kamar ba Namiji ba yace
"Wlh Mama bazaniya ba, ranar dana gaya mata ina neman aure a mota muna tafiya ta fizgi kan sitiyari badan muna da sauran kwana a gaba yanzu da wata maganar akeyi, kiyi haquri Mama bana nufin cin fuska a gareki amma Umaimah bata da tunani akan Halin kishinta idanunta rufewa sukeyi a shirye kuma take da tayi fito na fito da kowa da komai haka duk matsayin mutum bata tunawa a sanda zuciyarta ta qeqashe, ta rantse mun yafi sau nawa akan seta kashe duk wadda tayi gangancin aurena. Ni kaina tasha maimaita mun cewar zata kasheni kuma ta kashe kanta ina tsoro Mama ina tsoron kar wani abu ya sameta a yanzu bazan yafewa kainaba saboda nine sila" ya qarasa maganar kamar ze fashe mata da kuka Mama kuwa tsabar kidima kasa ce maaa komai tayi se dafe qirji tayi da hannu biyu tana kallonsa.

Tabbas a halin da Umaimah take ciki bata buqatar tashin hankali ballan tana taji baqin labari akan abinda idan aka ajiye mata zabin mutuwa ko kishiya tabbas zata iya zabar ta mutu da dai ta hada Miji da wata yanzu yaya zatayi ta fahimtar da ita ta kuma samu ta sassauta zuciyarta ta karbi abun da kyakykyawar zuciya?
Numfasawa tayi ta kalli Khalil dake zabga zufa tace
"Babu abinda ze faru da yardar ubangiji kaje gida zanzo din"
"Toh Mama" ya fada yana yunqurawa, yanda kasan kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ya ringa tafiya ji yakeyi gaba daya ma kamar ya sake dagula komai.

Khalil na fita Mama ta miqe cikin sanyin jiki ta iske Abban a daki yana waya data tabbatar da Baba Abu qanin Mahaifin Khalil ne bayan ya kashe wayar ya kalleta fuska a daure yace
"Ya akayi?"
Seda ta zauna a gefen gadon kafin tace
"Alhaji ina ganin kamar yanda yaron nan ya fada da za'ayi haquri zuwa ta sauka saboda kaga ba'a so me ciki ta ringa fuskantar tashin hankali. Sannan idan ka kalli Ita Umaimah a karan kanta ba abune me sauqi a gurinta ba aje mata da maganar kishiya, a baya kasan duk abubuwan da suka faru, a wai wai take jin Mijinta yana kulasu kaga irin tijara da diban Albarka babu wanda bata yiwa yaran mutane ba haka shima Khalil din be tsira ba, yanzu haka yace tace zata kashe duk wadda ta aure shi, ban yarda zata aikata ba amma zuciya sharrinta yana da yawa musamman idan ta hadu da fushi, gudun kar azo ana abun da be kamata ba kuyi haquri a barshi ya raba musu gida kamar yanda ya tsara wata biyun kamar yau ne hakan ze rage kaifin duk wata fitina da zata taso sannan ita kanta yarinyar se tafi samun nutsuwa dashi"

"Yaushe kika zama me son kai Malika? Yanzu a duniya har akwai abinda Yaron nan zeyiwa Umaimah da zakiga rashin kyautawarsa? Nawa tayi masa kafin wannan kuma idan kika kalli abun nan meye ma laifinsa a ciki? Daman ita jarabawar ubangiji babu ta inda bata zuwar wa mutum, Allah yakan jarabceka da abinda kake so kamar yanda shi ta zamar masa jarabawa haka nan idan yaga dama ya jarabceka da abinda kake qi ga Misali nan akan ita Umaiman dukka idan skayi haquri kayi tawakkali se kiga ka dace da rabauta a duniya da lahira kawai abinda ya rage miki a matsayinki na uwarta ki nuna mata muhimmancin haquri da tawakkalo sannan ta maida lamarinta ga Allah duk wani tashin hankali da zatayi babu abinda ze canza, babu wanda yasan Abinda Allah ya boye game da wannan auran idan ta matsa rabo yayi Ajalinta ai shikenan". Yanda Abban yake magana tamkar babu abinda ya dameshi, ganin baze fahimce ta ba yasa ta fita ta bashi guri jiki a matuqar sabule ta qarasa ayyukan da zatayi duk yanda Anty take ta rara gefe da son jin meya faru tayi mata banza, karyawar da bata iya yi ba kenan ta zauna jiran ya qarasa abinda yakeyi su fita fatanta Ubangiji ya sanyaya Zuciyar Umaimah ya bata haquri da juriya akan wannan al'amari daya fado mata.

Ita kadai ta fita saboda Abba wasu maqotansu da sukazo gurin Abba dan su tafi daurin auran tare da yake bikin Yaron wani maqocinsu ne ada dukda ya tashi daga layin amma har yanzu suna zumunchi sosai musamman shi Abba da yake kasuwarsu daya dan haka yana gaya mata uzurin nasa yace ko zata jira ya dawo tace Aa haka kuwa akayi da wuri ta fita dan ta rigashi barin gidan. Kai tsaye gidan Qanwarta Laure data daura aure babu jimawa satinta uku da tarewa kenan ta nufa. Sama sama suka gaisa da Angon Anty Lauren daya bude mata qofa,ta kalli qanwar Tata data ci uwar kwalliya da qananan kaya yanda kasan wata Titin Lagos ita a dole ga Amarya wani sabon takaici ya qumeta taja tsaki ta zauna akan kujera kawai ta rafka tagumi, data Sani Hafsa ta kira ko Hajiyayye sukaje tare.

Anty Laure ta kawo mata ruwa da Lemo ta zauna tana cewa
"Bari na soya miki Kwai akwai ragowar Dankali yanzu muka gama karyawa amma Yaya irin wannan zuwa da safe babu sanarwa lafiya dai ko?"
"Ba lafiya na Laure, yanzu dai tashi ki cire wadan nan abun dan Allah ki saka suturar arziqi rakani gidan Umaimah zakiyi"

"Kin san dazu nake zancen yar banzar yarinyar nan a raina rabona da ita tun ranar daurin aure kowa yazo yaga gida ya mun murna banda ita halan ta haihu wannan ciki dai ko na Aljanu ne ya isa a haifeshi haka dai" Anty Laure ta fada se Mama ta miqe tana cewa
"Laure ki tashi idan kuma ba zaki samu zuwa ba in tafi ni kadai"
"Wai Yaya lafiya kuwa?" Anty Lauren ta sake fada ganin Maman na shirin tafiya ta wuce daki tana cewa
"Yi haquri bari na shirya, da dai Yallabai yace bacci zamu koma amma wata kusan ai tafi wata".

Tsaki Mama taja abin takaicin Laure yawa ne dashi, wani abu take yanda kasan ba ta taba aure ba ita idan ta kallesu daga ita har Mijin nata ma haushi suke bata. A motar Mijin Anty Laure suka fita, a taqaice Mama tayi mata bayani a hanya Anty Laure data kusan sakin sitiyari ta gangara gefen Titi tana salati tace
"Yaya kice Khalil ya taro mana yaqin duniya na uku ni Lauratu naga abinda ya isheni wannan wace kalar jaraba Khalil ya janyo mana yaje yayi aure bata sani ba dan ubansa a ina aka taba haka? Nidai wlh da kin gaya mun tun a gida daman bazab biyo ki ba, nifa nasan Tijarar Umaimah sarai kawai dan Yata ce yasa nake take gaskiya nake bin bayanta amma mara mutunchi ta qarshe yarinyar nan toh Allah kaga zuciyata dan zumunchi zan rakaki Allah kasa na fito da raina da lafiyata kar tayiwa Angona Asarar wani abun a jikina".

Tsabar baqin ciki har sukaje gidan Mama bata sake ce mata komai ba. A waje ta ajiye motar a cewarta kar wani tsautsayi ya afkaqa motar Mijinta ta shiga uku.
Bangaren Hajiya suka fara shiga sun tarar da falon cike da yan uwan Hajiyar da yayayensu ga Akwatuna saiti uku masu hurhudu a bude kaya maqil a ciki iya kallonka da alama su suke dubawa.

A mutunce suka gaisa da jama'ar falon wasu sun santa irinsu Jalilah wasu kuma kamanninta da Umaimah yasa suka fahimci ko wacece, Falon Sama Hajiya ta kaisu, seda ta saka Habiba da me aikinta suka cika musu gaba da kayan sha dana ciye ciye kafin ta zauna suka sake gaisawa. Maganar dai guda daya ce aka maimaita, Hajiya ta kalli Mama cikin Jimami tace
"Wlh Hajiya tun da abin nan ya faru na rasa sukuni nan kullum yake zuwa ya tasani gaba akan se ni in sameta na gaya mata na ce masa bazan iya ba akan me ni zan kwashi baqin jini shida aure nida fadar bakin saqo daman yaushe aka gama rikicin tasowar maganar ma se gashi daga zuwa tambaya kawai suka daura aure kayan can da kuka gani yan uwan ne suka hada wai yau zasu kai Lefen saboda Qanin Babansu yayi rantsuwa se Yarinyar ta tare a cikin satin nan tun jiya abin duniya ya isheni Hajiya ko baccin kirki na gagarayi saboda tsakani da Allah na sani bamu kyautawa yarinyar nan ba, kuma da ace na san zasu tada maganar tariyar da wuri da tun sanda aka daura auran nan za'a gaya mata, amma gaba daya lissafinmu wata uku ne nan gaba saboda gurin da ze ajiyeta ma be kammala ba yanzu Kawun nasu yace sedai su zauna nan gaba daya idanma daga baya ze canza mata gida yayi haka amma yanzu ya rigada ya sanarwa da Iyayenta a satin nan zata tare".

Numfashi Mama taja tace
"Babu komai Hajiya haka Allah ya tsara kuma in sha Allah hakan ze zamo musu Alkhairi baki daya Mahaifinta ma dayaji fada ya ringayi akan me yasa Amaryar bata tare ba har yanzun ai tunda an rigada an daura aure duk kuma wani abu daga bayane, zan sameta yanzu zan kuma yi mata bayani ta yanda zata fahimta in Allah ya yarda ba za'a samu ko wacce matsala ba zata karbi al'amarin da sauqi nasan Umaimah nada rigima amma idan aka tafida ita ta yanda ya kamata da izinin ubangiji komai zezo da sauqi"

"Toh Allah ya yarda Hajiya Allah ya yarda" Hajiya ta fada tana gyada kai Anty Laure dai daman bata ce musu komai ba saboda wani mugun haushi daya turnuqeta, gani tayi abin nasu ma rainin wayo ne ita yanzu bata ma yarda da cewar wani babu shiri aka daura auran ba da ma sun shiryi abinsu idan ba haka ba duk a cikin sati dayan ne suka hada wannan uban lefen sannan yanda suke raha suna jin dadinsu kana gani kasan daman abin shiryayye ne kawai so suke su raina musu hankali to abiyar kowa ta bishi kuma idan anyi dan a wulaqanta yar Yar uwarta ne mugun nufinsu ya koma musu kuma dukkansu Mata ne suma kuma sun haifa in har sunyi dan su Musguna mata Allah yasa su gani a kwaryarsu.

Tsaki taja a fili Hajiya da Mama suka kalleta seta miqe tana kallon Mama tace
"Ki tashi muje Yaya, aure dai sunrigada sun masa duk wani jaje da za'a zauna anayi da taraddadin meze faru daga bayane, in har zuciya da gaske an ga rashin kyautawar abinda akayi me yasa tun gabanin ya afku ba'a dauki mataki ba? Kawai anyi abinda akayi bisa son rai kuma in Allah ya yarda tozartar da ake so tayi ba za'a ganta a kanta ba ehe".

Basu da buqatar ta fadi dawa take dan maganace tayi ta a fili tana kuma gama fada ta fice ta sauka qasan tana mita ko yayar tata bata tsaya jira ba, a falon qasan tana sauka taji wata zaqaqura tana cewa
"Ai ni live zanyi, bazan ma iya tsayawa wani recording sannan nayi posting daga baya ba tun yanzu ma nayi sanarwa qarfe hudu zanyi Live kowa ya shirya kallon Tambelen Kishi dan wlh yau se an fasa kwan nan a tsakar gida kowa yaji warin sa" suka kwashe da dariya. Da daddaya Anty Laure ta kalle au fuskar nan tata kirtif yanda kasanita akayiwa kishiyar ma ba Umaimah ba ta nuna Lubna da tayi maganar tace
"Ko banza akan Mijinta zatayi tambelen kishin ke kuwa banida buqatar a gaya mun a kwalta kike an rasa me, ku kuma da kuka zauna kuna tayata duk a gidajen aure kuke kuma yanda kishiyar batayi sallama da zata diro gidan taba haka kuma kowa ta jirayi tata tana tafe".

Qugu Lubna ta riqe zatayi mata fitsara Jamila ta riqe hannunta tana girgiza mata kai Anty Laure ta ce
"Da kin barta in nadawa yar iska duka inga abinda za'ayi aikin banza kawai" fuuu tayi waje ta buga musu qofa duk suka bita da kallo.
"Tab kice abin nasu Gado ne" wata daga ciki ta fada daidai nan Hajiya da Mama suka sakko Hajiya dai bakinta ya kasa dena bada haquri, bugun da Anty Laure tayiwa qofar yasa ta cije taqi buduwa dan haka Hajiya tace suje ta qofar kitchen, seda Maman ta fita kafin ta sauke ajiyar zuciya ta koma ciki ta tarar dasu suna hayaniya akan abinda Anty Laure tayi ita dai sama ta wuce dan jininta ya rigada yayi sama tun ma kafin me afkuwar ta afku.

UMAIMAH
Qarfe tara na safe ta farka daga baccin data koma dalilin kiran da Safina tayi mata akan zatazo, seda tayi wanka ta shirya sannan ta fito Ruqayya dake goge kayan kallo ta kalleta da fara'a ta gaisheta ta amsa tana yamutsa fuska saboda yunwar da takeyi kai gaba daya ma bata jin dadi ita bata taba ji cikin jikinta ya dameta irin yau ba dan haka ma ta tashi da niyyar da dare zataje Asibiti ita ko Inducing ne su mata ta haihu amma banda CS tunda naqudar taqi tazo. Tuwonta taci da Koko da already Ruqayyan ta hada mata su, a bakinta taji cewar da wurwuri Khalil ya fita a falon ta zauna bayan ta cewa Ruqayya ta hada abin karyawa zatayi baquwa yanzu tana hanya.

Wuraren goma da yan mintina Safina ta isa gidan Afujajan da ita kamar wadda ta dawo daga qauye, Umaimah ta kalleta ganinta da qatuwar jaka tace
"Ke kuma daga ina haka ga wata qwanqwamemeiyar jaka kamar wadda zakiyi tafiya?"
Safina ta zauna tana sauke numfashi tace
"Daga gidan Malam nake fitar ce tazo mun babu shiri tun Asuba n fita kai mun jakar ciki toh saboda tsaro me kuka rage a gidan?"
"Kamar na sani nace a hada miki abinci bari ta kawo" Umaimah ta fada kafin ta shiga kiran Ruqayya.

A daki suka qule seda Safina taci tayi nak kafin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login