Showing 27001 words to 30000 words out of 429394 words

Chapter 10 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

928

sun fara masa yawa.

Branch office dinsu ya fara aiki kuma shi aka bawa matsayin manager na bangarensu dan haka ayyukansu da yawa. Ga aikin gyaran gidan da ze zauna a ciki wanda yake da yan haya da a ciki suka tashi yana ta aikin gyara da yiwa gidan kwaskwarima saboda tsohon gida ne. Dukda Hajiyan su taso ya zauna a dayan bangaren da basa amfani dashina gidansu wanda yake mallakin Mahaifinsu amma yaqi yace gara dai ya zauna acan din.

Dan kanta da taga ya fita a sabgarta ta nemi shiri suka koma daidai, bata haqura ba da naci da mitar tsiya seda tasa ya chanza sunan Jalila daga Rabin Jiko zuwa twinny. Ranar ana yar dadi da kansa ya bata wayar yace ta chanza, bayan ta chanza ta shiga contacts, mesaagesa, hatta da whatsapp dinsa seda ta duba amma babu wani abun azo a gani da zesaka ta tada masifar tata. Abinda ya mugun mata dadi ganin yanda yake qin amsa saqon ni daga number da be sani ba, taga chats daga yammata amma data hau kububuwar fushin fuuu idan ta shiga chat din ta karanta kuma seta sakko ganin babu wani abu a ciki.

Saqonnin yammatan ne suke turowa, wasuma sunfi wata da watanni be bude ba se ita data bude su sannan. Bi ta ringayi tana tura musu da "shegiya mayya karki sake yiwa mijina magana" sannan ta bisu da block.

Ko a Jikinsa ta qaraci duk abinda zatayi ta gama ta bashi wayar shikenan zaman lafiya ya qara wanzuwa a tsakani tunda ta sake yarda da Khalil din nata ne ita kadai baya cin Amanrta da kowacce mace. Qauna kuwa se abinda yayi gaba aka ci gaba da tsinkar furen soyayya.


Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah se gashi Umaimah ta gama service ga kuma shirin aure dan ana maganar saura sati shida biki ne dan har an kawo lefen Nuratu sune suka zo da saka rana sati shidan dan haka na Umaiman ma aka ce idan sunzo da tasu hakan za'a saka.

A cikin satin da suka ce zasu kaqo legeTsautsayi ya samu Hajiyar su Khalil ta fadi a bandaki ta samu karaya a hannunta na dama. Anyi mata dori a Asibiti sedai tsorata da tayi lokacin da ta fadin ya saka jininta ya hau dole aka bata gado suna ci gaba da kula da yanayin jikin nata.

Kwananta biyu a Asibitin Umaimah suka shirya zuwa dubota, lokacin itama bata jin dadi tana fama da Malaria amma taji sauqi. Da yamma Khalil yazo ya dauke su ita da Nuratu suka tafi Dubiyar. Sun tarar da Dakin cike da yan uwan Khalil bangaren Hajiyarsa da suka zo dubiya suka gaishe su tareda yi mata fatan samun afuwa, Nuratu ta dire ledojin Fruits da suka taho mata dasu Hajiya se saka musu Albarka take tana nuna wa yan uwanta Amaryar Khalil.

Sun zauna can Khalil daya fita bayan daya raka su dakin ya dawo, yana zama wata fara kyakykyawa mai matsakaicin tsaho da jiki ta shigo dakin, tana ganin Khalil fuskarta ta fadadada Fara'a tace "Jinin jiki idon ka kenan"

"Cikin farin cikin ganinta ya miqe tsaye ya nufeta yana cewa " Dazu da zan fita daga gida naga shigar mota Layin kamar taku amma saboda banji anyi maganar zuwan ki ba shi yasa ban kawo ko ke bace".

Wata Ashar Umaimah ta lailayo a zuciyarta ta dire kafin ta dora da cewa "Ranar nan yace Rabin jiki yar uwarsa ce yau kuma Jinin jiki?" Hannu da suka gaisa akan idon ta ya qara ingiza wutar abinda take ji, lokaci daya idonta ya kada yayi jajir taji kamar jiri na neman dibanta daga zaune lokacin da taji wata mata na cewa

"Oh wannan qauna da shaquwa ta Khalil da Jamila an girma amma suna nan kamar lokacin yarinta".

Miqewa tayi, dakyar take daga qafarta Nuratu tayi qoqarin kama mata hijab amma ina tuni ta fincike tayi waje gaba daya yan dakin suka rakata da ido.

"Ko jikin nata ne ya motsa?" Khalil ya fada yana kallon Nuratu, ta gyada kai dakyar tana hadiyar yawu dan ita tasan ba jiki bane sedai idan Baqin HALIN KISHIN nata ne ya motsa, Khalil ya fita da sauri yana cewa "Bari na dubata, idan jikin ne se mu ga likita a nan ya sake dubata" yayi waje da sauri ya bi bayanta.


PROMO
PROMO
PROMO


BEFORE 4K NOW 2500

3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
KITURA SHEDAR BIYA =?G?
08162859027

AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA

INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO


SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI
*DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK*

*(UMMU-MAHEER)*

*MARUBUCIYAR*

*WATA KISHIYAR>?p?=?y? (ALKHAIRI CE KO SHARRI)*

*RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW*

*HALIN KISHI*

*HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500*

*GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*

*MARYAM UMAR FAROUK*

*SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*

Free page 9


Hangota Khalil yayi ta doshi hanyar waje yabi bayanta da sauri kamarta sani ta qarawa tafiyarta sauri, cikin sassarfa ya bita ganin har ta kusa isa gate din Asibitin ya daga murya yana kiran sunanta amma bata juya ba jefa qafunta kawai take tana tafiya, ji take ina ma data rufe ido ta bude zata ganta a gida tsabar yanda ta tsani Asibitin da Duk wadanda suke ciki sa.

"Umaimah meye haka ne kina ji ina kiranki ina zakije ko jikin ne ya tashin miki?" Khalil ya fada bayandaya tararda ita yasha gabanta. Wani shegen kallo ta watsa masa, yanda ya ke washe baki yana riqe da hannun wannnan matar ya dawo mata seta kauce shi taci gaba da tafiyarta ya qara tare ta cikin fada fada yace

"Wai ke meyasa kike haka, ina miki magana shine zaki wuce kici gaba da tafiya ina zakije? Idan wani abun ne ya faru ki gaya mun mana se muje na kaiki"

"Allah ya kiyeye na sake shiga motar ka kaje dai kaci gaba da diban wadancan jakan marasa kamun kai da kake kulawa, tsabar rashin kunya a gaban uwar data haife ka da sauran mutane kake kama hannun wata qatuwa kuna dariya"

"Jamilar ce baki sani ba? Meyasa idan wulaqancinki ya tashi se kin nemi abinda zaki cimun mutunchi ko yan uwana?" Ya fada yana kallonta cikin ido saboda yanda kalmar Jaka data alaqanta da yar uwarsa. Seda ta harare shi kafin tace

"Toh dan Jamila ce se aka ce ku tsaya kuna iskanci a gaban mutane"
"Iskanci Umaimah, nine nake iskancin?" Ya sake katseta yana nuna kansa da yatsa.

Dauke kanta gefe tayi tana qunquni qasa qasa wanda tsaf ya jita "toh idab ba iskanci ba menene zaka wani kama mata hannu a tsakiyar mutane ita kuma se wani murmushi take tana yaqe haqora" ta fada. Seda Khalil ya hadiye malolon baqin cikin daya taso masa zuciyarsa tana ayyana masa rashin dacewarsa da wannan mara kunyar yarinyar qarara.

Dakyar ya iya bude baki yace "ki jira na yiwa Nuratu magana ta fito na mayar daku gida" dan ko babu komai shi ya dakko su daga qofar gidansu kuma seda Abba ya jaddada akan su dawo da wuri dan haka dole ya mayar dasu daga baya ze zauna ya yankewa kansa hukunnci akan ta, dan ya fara hango dalilan da suka saka har mutum uku fasa auranta, sannan yaga tasa wautar qarara da yake qoqarin daukar ta ya kaita nasa gidan.

"Ni? Ai wallahi bazan shiga motar ka ba ita dai da bata da zuciya taje ta zauna seka maida ita amma ni kaga tafiyata, kuma ka qaddara daga nan gurin babu ni babu kai kaje can cikin yan uwan naka ka auri daya idan zaka iya" Umaimah ta fada cikin tsananin rashin kunya kafin ta murguda masa baki tareda baza Hijabinta da yake har qasa ta tafi ta barshi a gurin kamar wanda aka dasa.

Dakyar ya iya jan qafafunsa da sukayi sanyi ya koma dakin, yana shiga suka hau tambayarsa ina take lafiya dai? Ya rasa me zece musu ga tunanin maganar data fada masa da ke neman ruguzashi haka ya daure ya tattaro yawun bakin sa yace "Amai ne ya taso mata, gata can A mota Nuratu muje na mayar daku gida tace akwai sauran magungunanta da bata gama shanyewa ba".

Nuratu da duk ta tsargu dan tun fitar sa wata daga cikin matan ta fara qananun maganganu akan taga wani kallon wulaqanci da Umaiman ta watsa musu kafin ta fita, aka samu wata ta goyi ganin zasu tada hayaniya Hajiya ta tsawatar musu, ita dai tayi tsuru, Jamilan ta zauna kusa da ita tana janta da magana amma ta kasa amsawa se murmushin yaqe kawai take tasan Allah kadai yasan yanda zasu kwashe a wajen nan, Allah yasa kar tayi rashin hankalin nata data saba ta tarawa kanta mutane har magana ta dawo dakin su samu nayi shigowar da Khalil yayi ya sakata sakin ajiyar zuciya dukda a kallo daya da tayi masa ta gane akwai matsala Umaimah tayi tsiyar, yana cewa ta tashi kuwa ta miqe tana qara yiwa Hajiya Addu'ar samun sauqi ta fice.

Dama bata saka ran ganin Umaimah a waje ba tasan kuma shima ya fada ne kawai dan haka suna shiga motar tun? kafin yayi magana ta kalle shi tace
"Dan girman Allah Khalil kayi haquri, Al'amarin Umaimah se Addu'a se tayi abu kuma daga baya tazo tana nadama"

"Gaskiya I'm sorry to say amma Nuratu sam yar uwarki bata da tunani, could you believe ni ta kalla ta kira da dan iska a matsayina na mijin da zata aura? Ba tun yau ba take fada mun maganganu marasa dadi amma ina mata uzuri sedai naga a kullum a maimakon abin ya rage gaba ya ke qarayi.

Beside me nayi mata? Saboda kawai na gaisa da yar uwata shine ya bata damar da zata gayamun maganganu haka har tana fadin babu ni babu ita naje cikin yan uwana na nemi wata na aura me yake damun Kwakwalwar Umaimah? Ko kuma daman wannan rashin hankalin shine zafin kishin da take cewa tana dashi?.

Indai haka ne na godewa Allah daya nuna mun ainihinta tun kamin na aureta na aurar wa kaina damuwa, kuma banga laifin duk wadanda suka fasa auranta a baya ba saboda sam Umaimah ba macen aure ba. Macen da zata iya tsayawa a gabanka ta gaya maka duk maganar datazo baki ta ba tareda tayi shayi ko taga qimarka ba ai ba matar aure bace, dukda ma dai ta fada da bakinta babu ita babu ni Allah yasa hakan shi yafi Alkhairi, ki shiga ciki idan Abba yana nan kiyi mun sallama dashi dan Allah tunda wuri gara mu sama ma kanmu sauqi Allah ya hada kowa da rabonsa" Khalil da yau zuciyar yan maza ta motsa masa ya fada daidai sanda ya tsaya kofar gidan su Umaiman.

Ido kawai Nuratu ta saka masa tasan gaskiyar sa ya fada amma bata fatan yar uwarta ta rasa nagartaccen Namiji irinsa, shi kadai ne take tunanin ze iya chanza Umaiman gashi tun ba'aje ko ina ba shima ya sare da halinta yana zancen fasa aure.

Bude baki tayi dakyar tace "Kayi haquri Khalil nasan halin Umaimah sam idan ranta ya baci bata sanin me take fada..."

"Ranta ya baci da akayi mata me? Saboda na gaisa da yar uwata? Yayata ce fa uban mu daya. Haka kwanaki tayi mun saboda Jalila ta kirani twin sister na, ta ringa zagina har tana kirana da Mazina ci. A lokacin nayi mata uzuri a lokacin amma banda? Yayi da babu wani abu da bata sani a kaina ba. Yan uwana mata babu wadda ban gaya mata sunanta na nuna mata hotunansu ta yanda ko a hanya suka hadu zata gane su ba.

Saboda gudun bacin ran Umaimah na chanza layin da nake harkokin kasuwancina dasu. Ba dan ina tsoro ta ba, kamar uwar data haifeni duk sanda ta raya mata zata ce nabata wayata tayi bincike ban taba nuna mata rashin jin dadi akan hakan ba ko babu komai waya sirfi ce nima ina da sirrikana da ya kamata ni kadai nasan dasu amma ko mai da ko ina na bata damar shiga ta duba a wayata, hakan ne ya bata damar da zata tsaya ta zageni duk a sunan kishi? Kishi ko hauka? To nidai na haqura taje kawai Allah ya bata wanda ze iya da halinta" Khalil yayi saurin katse Nuratun a fusace dan ransa qara baci yake yi duk idan ya tuna maganganun data yaba masa.

Bude baki tayi da niyyar sake magana ya bude motar yana cewa "kije dan Allah, ki bar Abban ma duk randa na sake biyowa nan haka nazo. Ki bawa Mama haquri nasan babu dadin amma hakan shi kadai ne abinda ze sama mun maslaha dukda ina son Umaimah amma bazan iya auranta ba, a waje tayi mun haka inaga na aureta na kai cikin gidana kinga wannan kome tayi ni na siya da kudina".

Jiki a mace Nuratu ta fita daga motar daidai sanda Adaidaita ya tsaya a qofar gidan Umaimah ta fito daga ciki, kallo daya tayi musu daga Nuratun har Khalil din kafin ta maida ido ta kan Nuratu tace "kuma da kika shiga motarsa ke kadai Allah ya isa bazan yafe ba, idan ma Amana aka ci mutum yaje shida Allah" ta sake fada tana kallon Khalil kafin fuuu ta shige gida. Murmushin zallar takaici Khalil ya saki, ya fara hasashen yarinyar nan bata da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa ko kuma dai saitin kanta na gocewa ne lokaci lokaci.

koma dai yaya shidai he is done with anything concerning Umaimah, yana sonta amma dole ya haqura da ita dan beyi zaton Rigima da Hayaniyarta da Nasir ya ke fada ba ya kai haka. Koda yake ya so ya rufe shi ne amma banda haka ai kaitsaye kawai kamata yayi yace masa tana da matsalar saiti.
Gata dai mace har mace amma babu cikakken hankali Allah kenan me yanda yaso.

Haka ya juya Asibiti bangarorin zuciyarsa na mahawara da juna, tabbas yana son ta so me tsanani amma menene amfanin soyyar da babu kwanciyar hankali da girmamawa a cikinta. Idan ya tuna yanda take riritashi tana lelen sa idan suna yar dadi se yaji kamar baze iya rabuwa da ita ba, amma abinda tayi masa dazun ya saka shakku a zuciyarsa game da auranta.

Tayi kishi da yan uwansa na jini inaga kuma duk randa tsautsayi yasa ta ganshi da wata, bama wannan ba ita rayuwa bata da tabbas. Har zuciyarsa bashida burin ajiye mace sama da daya musamman ace Allah ya cika masa burinsa ya bashi mace irinta amma babu wanda yasan gobe, idan qaddarar sa ta auran mace sama da dayan ce fa yaya zasu kaya?

Yanda yanzu kullum ya kunna radio labarai ne marasa dadi akan mata sun kashe mijin ko sun kashe kishiyar toh maganin kar ayi kar a fara, indai soyayyace ze roqi Allahn daya saka masa ita a zuciyarsa ya cire masa ita kuma ze ci gaba dayi mata fatan Alkhairi ubangiji ya rage mata abinda yake damunta a zuciya amma tabbas baze siyawa kansa tashin hankali da kudinsa ba amma ta yaya ze tunkari Hajiya da wannan magana yanda take son Umaimah kamar ta goyata?

Bama wannan ba, gaba daya fa auransu befi sati hudu masu zuwa ba anya idan yace ze fasa yaya iyayenta zasuji dan shi su yafi tausayawa, mutanen kirki, Mamanta ta dauke shi kamar dan cikinta basu boye masa komai akan Umaimah ba tun fara zuwansa gurinta dan hatta da takaddun Asibitin gwajin kwakwalwa da aka mata seda Abba ya nuna masa amma sam shi be fahimci Al'amarin ba, be taba zata haka abin nata yake ba se yanzu da tafiya take qara nisa daman hausawa sunce Hali zanen dutse ashe lokaci take jira ta fara zayyano masa su, toh koma dai menene ze jira a sallami Hajiya ta koma gida kafin yaje mata da wannan maganar.

A can gidan su Umaimah kuwa rigima ce sosai ta sarqe tsakaninta da Nuratu dan tsayawa tayi daga cikin Gareji Nuratu na shiga ta hau kanta da kokawa itama batayi wata wata ba kuwa ta zage suka fara kwasar dambe dan a zuciye take da lamarin Umaiman, tayaya zatayiwa kanta asarar miji kamar Khalil wanda tasan muddin ta rasa shi bazata maida kamar sa ba sannan rantsuwar Abba ta bada ita sadaka ta tabbata kenan.

Dambe sukeyi haiqan har cikin gida sosai kuma Nuratun ta zage tana jibgar Umaimah dan ko a qirar jiki zubinsu ba daya bane. Nuratu doguwa ce me garin jiki dan ta?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ninka Umaiman da tsabar tsaurin ido ne ma ya sakata cukumarta da dambe.

Sosai ta lallasata, dan takaicin shekara da shekaru ta samu dama tana sauke mata shi yau akayi sa'a babu kowa a gidan dan suna fita ba dadewa akayi rasuwa a bayan layi dab haka su Mama da Antyn sun tafi Jana'iza se Salis ne kadai a gidan Dan Anty na biyu da suke sa'anni da Umaiman, shi kuwa yana leqowa daga dakinsu yaga abinda yake faruwa ya koma ciki harda turo qofa.

Yaya Aminu ne yaje gidan, tundaga waje yake jiyo ihu da kururuwar Umaiman tana zagin Nuratu a ransa yace "abin ya motsa kenan, ai kuwa yau zaki ci ubanki daman ina da cikin ki ai" se ya juya ya koma motarsa. Dorinar da yake ajiyewa saboda horon yaran sa idan ta kama ya dakko har wani murmushi yake yana hasaso irin dukan da ze mata kafin su Mama su dawo dan sunyi waya ta gaya masa sunje jana'iza amma gasu nan zuwa.

Yana shiga kuwa beyi wata wata ya shiga sakar musu duka kan me uwa da wabi saboda yanayin daya tarar dasu gaba daya kowacce jikinta na buqatar ya gaya mata. A zabure kuwa suka rabu kowacce ta hau sosa jiki dan dukan ya shige su musamman da daman rabi kaya rabi tsirara suke dan tun a Get aka tuge Hijabai da dambe yayi dambe kuwa aka ringa farke farken kaya.

"Ashe baku da mutunchi a cikin gidan kuke mana kokawa se kace wasu yan tasha?"

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login