Showing 219001 words to 222000 words out of 429394 words

Chapter 74 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1043

in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huWu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haWin sabaya=?
?* HaWin sabayarmu duniya ne ?ar'uwa. Baza muyi miki ?aryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga she?i, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haWin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk Wauri Waya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuWin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuSeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo=?
?=?
?=?
?*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 52

Tunawa yayi da furucin Dr na ya kirata ya bata haquri ko kuma ya manta da zancen kwangilar, wayarsa ya dauko takaici fal ransa, shi ta hada masa bala'i sannan kuma ya kirata ya bata haquri amma shikenan na dan lokaci ne. Kamar tana jira ringing daya ta daga wayar cikin shagwababbiyar muryarta da sam bata burgeshi tace
"Yanzu kawai dan na kiraka shine zaka rufeni da fada kana zagina akan matarka ko?"
"Oh daman cewa Dady kikayi na zageki kenan, yaushe na zageki? Ke baki ga abinda kika mun ba? Sau nawa zan gaya miki ki dena kirana qasa da qarfe goma na safe in dai bani ne na kiraki ba?

Kuma sannan duk abinda ya faru tsakanin mu se kin gayawa Dady a haka zamuyi aure duk abinda ya faru ki kwasa ki gaya masa ya kira waya ya ringa fada to wallahi ko ki canza ko kuma mu samu sabani dake haba da wanne mutum zeji" Khalil ya fada cikin bacin rai be idasha shaqar numfashi ba Zahran ta fasa masa kuka kamar wata qaramar yarinya. Takaici yazo masa wuya amma ya daure ya sassauta muryarsa yace
"To yanzu kuma me akayi da zaki yiwa mutane kuka uhm? Shikenan bazakiyi ba daidai ba a miki magana se kuka se tashin hankali?"

"To meyasa zaka ringayi mun ihu bayan ko Dady lallabani yake yi? Wallahi sena gaya masa ba yace zaka kira ka bani haquri ba shine kake mun ihu da fada se na gaya masa?" Ta fada cikin zallar sakarci, Khalil ya bawa kansa haquri kafin ya ce
"Toh kiyi haquri shikenan base kin sake gaya masa ba".

Banza tayi masa taci gaba da gunsheqar kuka, yana jiyo muryar mahaifiyarta na cewa ta tashi ta bar kusa da ita kafin ta maketa tunda ita bata da hankali da yaga dai bazata bar kukan ba dole ya sassauto ya shiga rarrashinta yana gaya mata kalamai masu dadi har ya samu ta haqura. Besan lokaci yaja ba seda suka kashe wayar ya duba Agogo tara harda rabi tayi yana tsaye a gefen hanya. Gabansa ya fadi sanda yaga Missed calk din Umaimah dan wallahi beji ma sanda ta kirashi ba yana fama da waccen psycho din yarinyar. Kiranta yayi back wayar ta qaraci ringing bata daga ba haka ya haqura ya cigaba da tafiya ya tabbatar dai yau kam Allah kadai ze fidda shi. A office dinma be iya yin wani abin kirki ba. Ga Zahra ta ishe shi da waya yaqi dagawa cibi ya zama qari haka dole yake biye mata qarshe tace ya biya idan ya tashi tana son ganinsa ba yadda ya iya haka yaje gashi sunyi da Umaimah idan ya taso ze biya ya dakkota su wuce gida dukda bashi da tabbacin bayan abinda ya faru zata jirashin amma haka ya wuce bayan ya gama da Zahran.

Yasha mamaki daya kirata ta dauka ya sanar da ita yana waje se gata ta fito fuskarta a washe suna sallama da Nuratu da itama zata wuce gida suka gaisa ta shige motarta kafin Umaiman ta bude bayan mota ta shiga fuskarta a dinke kai baka ce ita ta fito yanzu tana dariya ba. Bibi ce ta shiga gaba ya tada mota suka dauki hanya ta Rear mirror yake kallonta hankalinta naka wayarta da take dannawa har suka isa gida ya kasa ce mata komai dan gaba daya ya tsorata da yanayin fuskarta. Har suka kwanta batace masa qala ba abinda ya qara dugunzuma hankalinsa kenan dan shirun Umaimah ba Alkhairi bane, be manta yanda suka qare da Hadiza ba, bata yi masa magana ba seda komai ya lalace kafin ya tsinci zancen yanzun ma yana tsoron ta sake kwata wani da ze jefa su a bala'i gaba dayansu.

UMAIMAH
Yanda ta shiga gidan ya saka Maman Asad da Baba Talatu dake zuwar mata duk haihuwa suka juya suna kallonta. Mamakin zuwanta da sassafen ya kamasu ga yanayin data shigo da ko ba'a fada ba sun san ba lafiya ba. Dakin Maman Asad ta wuce kao tsaye Bibi ko daman kujera ta haye ta kwanta abinta dan bacci be isheta ba Baba Talatu ta kalli Maman Asad tace
"Hajiyayye leqata mana kiji lafiya irin wannan Asubanci bayan fitar safe ba halin uwar dakina bace".

A dakin ta sameta zaune a gefen gado ta zubawa qofar shigowa ido da gani tayi zurfi a tunani har Maman Asad din ta qarasa ta zauna gefenta tareda dafata sanann ta farga.
"Lafiya Umaimah, me ya faru?" Ta fada tana kallonta kamar tana jira kuwa ta fada jikin Hajiyayyen tareda fashe da kuka seda tayi me isarta gaba daya ta dagawa Hajiyayyen hankali kafin ta fara magana tana cewa

"Wallahi ko ni ko Khalil, se ya gayamun da shegiyar da yake cin amanata".
Numfashi Maman Asad ta sauke a zuciyarta tana yiwa Allah godiya da abin tsaya iya haka, yanda ta ganta da sassafen nan ga kuka ta dauka auren ne ya samu matsala ashe iskokan kishin ne suka motsa dan haka ta gyara zama tace
"Me kuma Khalil yayi keda bakya rabo da abin magana?"

"Wata yar iska ya samu take dauke masa hankali, daman na dade ina lura da ya canza taku se ya ringa wasu abubuwa irin na munafukai. Kwanaki na dauki wayarsa haka ya fitittike ya ringa mun fada akan me zan masa bincike saboda yasan akwai abinda yake aikatawa a boye da baya so na sani shiyasa se gashi yau Allah ya tona masa Asiri yanzun nan a qofar gidan nan mun tsaya Karuwar tasa ta kirashi" Umaimah ta fada cikin zafin rai. Harara Maman Asad ta balla mata kafin tace

"Umaimah ki iya bakinki, wai ke baki da hankali da zaki ringa danganta mijinki da karuwa ko kuwa an ce miki babu wata alaqa tsakanin mace da namiji seta iskanci? Wallahi samun Khalil din kikayi a bagas har yake takatsantsan da fushinki idan wani ne tunda ya fuskanci ke mahaukaciya ce bakisan abinda yake damunki ba ai sabgogin gabansa ze ci gaba dayi qarqari idan kin sani kiyi haukanki ki gama hakan bashi ze hana ya cigaba da yawon kula yammatan shi ba.
Kuma bari kiji, tun wuri idan zaki hada hankalinki guri daya ki kama kanki kiyi tun kafin ya kawo miki wata tazo taga ballagazancin da kikeyi da sunan kishi ta rainaki dan kinsan qarya kike kice ke kadai zaki zauna a gidan nan ko beyi niyya ba na tabbata se yan uwansa sun saka shi ya qara aure dan in kika cire Hajiyarsa a yanzu dai kaf cikinsu babu wadda takr ganinki da gashi kin zubar da qimarki a gabansu kuma ko mune matar dan uwanmu tayi abinda kikayi a baya wallahi baza'a rufe case din nan ba se mun masa aure muga qarshen tsiya, dan haka in zaki ajiye kishi ki fuskanci gaskiya kiyi dan na tabbatar da lokacin zuwan wata ne yayi ba kuma ki isa ki hana ba dan baki da hujjar hakan".

Kallonta kawai Umaimah take har ta kai aya yanda kasan ta kwashe ta da mari, yanzu ta kawo mata matsalarta a maimakon ta tayata jin haushi seta goyi bayansa harda qarin wani jafa'in take janyo mata to kuwa ya qare akanta, kishiya ba sedai ta ganta a gidanta ganin idonta wallahi.
Tsaki kawai tayi ta miqe ta bar MamanAsad da baki a bude tana kallonta, bandaki ta shiga ta wanko fuskarta haushin kanta ma data tsaya yiwa Hajiyayye bayani ya kamata bayan tasan tafi qaunar Khalil akan ta. Palour ta wuce dan neman abinda zata sakawa cikinta ta gaida Baba Talatu sama sama bata ko kula tsokanar da take mata ba ta shige musu kitchen a ranta tana ayyana wannan Yaqin tane ita zata kwatarwa kanta yanci, yanda ta rabashi da Hadiza ba tareda shawarar kowa ba wannan karon ma haka zatayi amma kafin ta san abinyi dole ta fara gano ita yarinyar a ina take da duk abinda ya kamata ace ta sani akanta.
Haka ta qarasa wuni a gidan bayan ta taushi zuciyarta ta saki ranta sukayi ta hidima bayan zuwan Nuratu, Anty Hafsa da Anty Zee.
Taga missed calls dinsa har biyu ta share saboda idan ta daga wayar danniyar datayi wa zuciyarta zata wargatse ta kokora masa Ashar shiyasa ta barshi dan bata san kiran me yake mata bama. Da yazo daukar su ma seda tayi da gaske ta iya shiga motar shiyasa ta zauna a baya har sukaje gida kuma bata ce masa komai ba.

Seda suka kwashe kwana uku tafi ka mutu bata ce masa ba, zatayi duk abinda ta saba a gidan girki da sauran ayyuka ammafa bazata shiga sabgarsa ba abin ya damu Khalil matuqa gashi baya so yayi mata wata doguwar magana ya kunnota Addu'a yakeyi abinda ya saka gaba ya kammalu kafin ta fashe, zuwa sannan yana da bakin yi mata bayanin komai game da Zahran amma yanzu kam akan tsini yake. Ita kanta Zahra da Mahaifinta sun taso shi a gaba akan ya turo magabatansa su shiga magana kullum cikin basu uzuri Yakeyi yana kuma Addu'ar Allah ya tabbatar da aikin nan su rabu kowa ya kama gabansa.
Gaba daya shima ya shiga rashin walwala, haka idan ya fita aiki ze kirata yanda ya saba dukda bazata dauka ba har lokacin dawowa ya rage ya zamana yana dawowa gidan da wuri kuma idan ya dawo sallah kadai take qara fitar dashi sedai ya zauna zuru a palour ko yayi ta yan tabe tabe a Laptop dan wayar kanta baya so ya dauka balle tayi zargin Chatting yake da wata.

A hankali da kanta kuma se gashi ta fara sakkowa tana kulashi, tun yana dari dari har ya fahimci dagske ta sauka daga fushin nata ya saki jiki suka koma sabgoginsu kamar da, yanda bata daga maganar Zahra ba shima beyi mata ba ya kuma qara toshe duk wata kafa da zata bata damar fahimtar wani abu dan wani sa'in ma daya dawo yake kashe layinsa da Zahran ta sank dan tunda ta fahimci bata samunsa idan ya koma gida ta chanza lamba, randa ta kira ya shiga kuwa yasha mitar Bala'i akan me yake blocking dinta yace saboda baya so ta kira a gaban matarsa, ta kuwa samu nayi har Dadynta seda ya shiga maganar yayi masa tatas yana kuma sake jadd??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ada masa yabi a sannu dole ya chanza taku a haka dai ake ta lallabawa.

UMAIMAH
Kallonsa kawai takeyi da yanda yake raina mata hankali yana daukar bata san abinda yakeyi ba amma ta zabi tayi shiru kamar yanda suka sake shawartawa da Safina tace ya nuna masa komai ba komai na ta shammace shi hakan kuwa akayi, dukda ya chanza password abinda ya qara baqanta mata rai zarginta ya tabbata akansa kenan amma seda tasan ta yanda ta gano sabon daya saka.

Ranakun Lahadi yana gida throughout be fiya fita ba seda kwakwkwaran dalili. Da rana suna yin lunch ita dashi, Bibi sun tafi gidan Jamila da Habiba kusan satinsu daya tunda Habiban ta samu Hutu Mu'ayyad yana islamiyya. Abinci sukeci suna yar hira jefi jefi wayarsa dake ajiye tayi qara yanda ya zabura seda ta zura masa ido kawai tana kallonsa ganin haka ya sakashi daidaita nutsuwarsa ya dauki wayar cikin borin kunya yake cewa
"Namanta shaf na qaro qarar wayar dazu yayi yawa har na firgita"
"Uhm" ta iya ce masa kafin ta mayar da kai taci gaba da tura abincin da gaba daya ya fita a ranta.

Be amsa kiran ba seda wani ya sake shigowa shima gudun zargi ya sakashi amsawa a gaggauce yace
"Abinci nake ci idan na gama zan kiraku please" bata san me aka ce masa ba daga can bangaren ya sake cewa
"Toh, naji" kafin ya kashe yana jan tsaki yace
"Anwar ne, haka kawai wai sun shirya mana walima akan kwangilar dana baki labari bayan ko gama kammaluwa batayi ba. Bayanda banyi dashi ba akan ya bari ba yanzu ba amma wai ya rigada ya sanarda duka Employees dinmu yau za'ayi qarfe hudu nidan bazanje ba se suyi abinsu su kadai"

"Aiko dai da kaje" ta fada tana kallonsa, yanda yayi maganar da bata san abinda yake shiryawa ba tsaf zata yarda amma ina ta gama rafko shi babu ta yanda ze layance mata.

"Gaskiya bazanje ba tunda yaqi jin maganata ya bari ba yanzu ba se suyi su kadai, ni yanzu ma so nakeyi mu shiga daga ciki na gaya miki wani abu" ya fada yana zagayowa ta bayanta yayi kissing wuyanta. Janye jikinta tayi ta miqe tana cewa
"Gara dai kai tafi dan ni nan me kitso nake jira kaina ya dameni gara tazo ta lallabe mun shi" ta qarasa tana tattare kwanukan da suka bata. Shiya tayata suka kwashe komai suka kai kitchen kafin suka fito ta wuce dakinta shima ya tafi nasa dan shiryawa ransa qal da ya samu damar fita ba tareda ta zargi wani abu ba.

Zahra ce ta addabeshi, tun farkon satin nan take gaya masa qawayenta zasu zo yau daga kuma tana so ya hadu dasu su gaisa dan duk ta basu labarinsa. Baya son su samu wata matsala a ritsin shiyasa ya amince yana ta lalubo abinda ze fitar dashi daga gidan ita kuma gata da shegen gajen haquri se kiransa take tana tambayar yaushe ze zo. Wanka ya shiga, Umaimah data biyo bayansa ta labe seda ta tabbatar ya shiga wankan kafin ta dauki wayarsa a gaggauce ta kwafi number Zahran daya chanzawa suna zuwa Engineer Z tsabar sa idonta yasa ta gano shi, har ta mayar da wayar saqo ya shigo daga Zahra. Budewa tayi ta karanta
"Dear kazo da wuri saboda su ganka a cikin hasken rana suga irin zaben mijin da nayi, Love you" abinda ta rubuta kenan. Goge saqon Umaimah tayi zuciya tazo mata wuya, a hasale ta qarasa jikin qofar bandakin cikin rashin Sa'a muqullin qofar ta ciki aka sakashi dan da so tayi ta kulle shi a ciki taga ta inda ze fita se kuma meta tuna ta fice daga dakin da sauri zuwa nata.

Khalil daya jiyo qarar rufe qofa cikin Sauri ya dauraye jikinsa ya fito ko gama daura towel din dakyau beyi ba ya tsaya yana dube dube bega kowa ba, ya qarasa inda wayarsa take ya duba tana nan yanda ya ajie dan haka yayi tunanin kunnensa ne yajiyo masa badaidai ba saboda ba a nutse yake ba.
Wankan yakoma ya qarasa. A gurguje ya shirya cikin Wani baqin Wandon Jeans da Farar Long sleeve shirt da aka rubuta 'I'm all yours' a jiki saboda garin akwai sanyi sanyi anyi ruwa da safe.

Tsaf ya feshe jikinsa da turarukansa masu qamshin gaske, ya gyara gashin kansa da Gemu shida kansa yasan yayi kyau ya fito kamar wani qaramin saurayi ba zaka ganshi kace yana da shekaru Talatin da takwas a duniya ba. Yana cikin daura Agogo Umaimah ta shigo dakin da sallama ya kalleta ganinta cikin shirin fita Ta saka Baqar Abaya tayi rolling da mayafinta ga qaramar Jaka da waya a hannunta. Kallonta yake harta qaraso gabansa yace
"Kinyi kyau, se ina haka kuma?"

Umaimah da wani hadarin kishi ke haduwa a zuciyarta tayi qarfin halin cewa
"Kaima kayi kyau, amma dai babu mata a gurin da zakaje ko?"
"No haba dai kema kinsani ai, iya mune babu mata kuma badan kin matsa bama ba zanje ba ni" ya fada yana janyota jikinsa ya rungumeta ta bata saboda cikin jikinta.

"Zakaci abu ta kazan ubanka ne" Umaimah ta raya a ranta tana kallo ya daga wayarsa yayi musu hoto yana ta doka uban murmushi ita dai fuska babu yabo babu fallasa ta kalle shi tace
"Na kira me kitson wai ba zata samu zuwa ba ko zaka saukeni a Salon idan yaso in kun gama se ka biyo ka daukeni"
"Ok, babu damuwa muje yama fi sauqi dan ni daman banaso ayi kitso a gida duk gashi ya bata ko ina kayi ta tsintarshi a abinci" ya bata amsa yana yin gaba ta bishi a baya.
Dakinta ta koma ta dakko Jakar data zuba kayan kitson, a palour qasa ta tarar dashi yana waya yana hangota ya kashe ya qarasa inda take ya riqe mata hannu Umaimah dai murmushi kawai tayi masa ita kadai tasan me take shiryawa a ranta. Seda suka shiga bangaren Hajiya suka gaidata, basu jima ba suka kama hanya suna tafe yana mata hira ita dai amsa biyu take bashi Eh ko Aa dan gaba daya hankalinta yayi gaba.

A wani guri da bata san me akeyi ba ya tsaya yace mata minti biyu yana zuwa, wayarta tayi saurin dauka bayan ya fita ta shiga kiran Harun, wani yaro ne dan unguwarsu yana jan Adaidaita Sahu yawanci idan zata fita bada mota ba shi take kira ya kaita ko ya dakkota daga inda zataje. A taqaice tace zata turo masa da Address yanzun, idan yana kusa da gurin kuma ze iya qarasawa a wasa da minti goma yayi mata Reply kawai karya kirata. Address din Salon din da zataje ta tura masa, yana gani yace mata ai yana ma kusa da gurin yanzu ya ajiye customer ya tafi se tayi saurin kiransa tace ya koma ya jirata gata nan zuwa daidai sannan Khalil ya dawo motar ya bude Sit

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login