Showing 27001 words to 30000 words out of 512766 words
Chapter 10 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1536
gwuiwowinta wanda da ba haka take ba, kiran sunanta Fatuu tay shiru bata amsa ba hakan yasa tay tunanin ko bacci ne ya kwashe ta daga karatu, d'aga murya tay tace "Fauzyyy tashi baki ga ta yin bacci ba a wannan lokacin in ba munyi passing Intro ba" shiru bata tanka mata ba bata kuma d'ago ba ta sake kiran sunan ta da d'an k'arfi k'asa k'asa taji muryar ta tace "ba bacci nike ba" yadda Fatuu taji sautin muryar ta sai taji kaman tana kuka da alamun mamaki tace "to mi kike, naji kaman ma kuka kike ko" daga yadda take ta girgiza mata kai Fatun tace to ta d'ago ta gani, a hankali ta sak'a hannunta ta cinyoyinta Fatuu na ganin haka ta gane so take ta goge kwalla ne da sauri ta saukko daga kan gadon tana sanye da Vest da dogon skirt kan ta ba d'an kwali, gadon da Fauzyn take ta haye tasa hannu ta d'ago da face d'inta, Har saida gabanta ya fad'i ganin fuskar ta jage jage da hawaye sai kace ba ita bace suke karatu suna magana ba a d'an rud'e Fatuu ta shiga tambayarta abunda ya faru take kuka shiru bata ce mata komae ba sai faman sheshsheka take hakan yasa Fatuu cewa "Saboda Exam d'in da zamuyi kike kuka?" Girgiza kai tay da yar damuwa Fatuu tace "To don Allah Fauzy miye?" cikin muryar kuka tace "Mujaheed........" Sai kuma ta Sake fashewa da kukan kan Fatuu ne ya d'aure jin sunan da ta ambata ta rasa gane wanene shi sannan kuma miya faru da shi, ganin wayarta a gefenta yasa Fatun cewa "Rasuwa yayi ne?" Da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a, d'an yarfa hannu Fatuu tay tace "to don Allah ki fad'a man waye shi kuma miya faru kinsa ni na rud'e fa" shanye kukan Fauzy tay tasa hannu tana goge k'wallan kafin ta fara magana "Mujaheed shine silar zuwa na wannan Makarantar Zarah na kasa man cewa da abunda yay man duk yadda naso na manta" cikin d'aurewar kai Fatuu ta tambayi waye shi kuma miya mata, goge kwalla ta k'ara yi taci gaba "Tsohon saurayi nane kusan in ce ma shine saurayi na farko kuma na k'arshe kusan shekararmu hud'u tare...." Dakatawa tay ganin hakan yasa Fatuu sake tambayar ta abunda ya faru tsakanin su, cigaba tay "Mun had'u dashi ne lokacin da na dawo gida nayi Jsce da yake Boarding nayi lokacin na raka wata Yayata wadda muke uba d'aya don Matan babanmu biyu mamarmu da tasu dinner party d'in k'awarta to lokacin da muka je sun tashi su da k'awayen su suna rawa an bar ni ni kadae zaune sai gashi ya zo inda nike da murmushi ya tambayeni ya na zauna ni kadai bazan je nima in yi rawar ba na d'an yi mashi murmushi kawae a tunani zai tafi ne sai kawai naga ya zauna kujerar kusa dani yaci gaba da latsa wayar shi lokaci bayan lokaci yake d'agowa ya kalle ni da murmushi nima sai in d'an yi mashi can ya k'ara d'agowa ya tambaye ni sunana na fad'a mashi Fauziyya da bud'ar bakin shi sai cewa yay sunan ya dace da mai shi ina dae ta dariya daga baya ya mik'e ya bar wurin har yana ce man wai ya zo ya tayani fira ne dama kyauta nace mashi Nagode, ba'a kaiga tashi ba muka fito don tafiya Saboda in muka kai har lokacin da za'a gama to zamu ja ma kan mu ne wurin Abban mu dama da K'yar aka bar mu muka zo ba tare da ya sani ba, muna fitowa sai ga mutumin ya biyo bayanmu yace man tafiya zamuyi na d'aga mashi kai sai yace to bari yay dropping namu muka bishi inda ya parker Motar shi,lokacin da muka isa layin gidan mu bamu k'arasa ba muka ce ya ajiye mu anan Farko farko ya tambayi ina ne gidan namu muka ce yana a d'an can gaba yana murmushi yace to ya k'arasa damu mana da sauri muka ce a'a Ya tambayi dalili anan Yayata Fareeda tace mashi bamu son baban mu ya gan mune yace Ok, dama ni ce a seat d'in gefen shi kafin mu fita yace na bashi no d'ina nace ai ni ban fara rike waya ba ya tambayi dalili nace Saboda nayi k'arama kuma Makarantar kwana nike yi yana yar dariya yace shi bai ga wata k'aranta tawa ba anan ya tambayi ajina nawa nace mashi Jsce nayi zan tafi s.s 1 ganin ita Fareeda nada waya ne yasa yace to ko tata ce a bashi sai mu rink'a gaisawa ya zama yayana harda tambayata ko ban so ina dariya nace mashi ina so aka bashi ta Fareeda d'in, tun daga wannan lokacin muka fara yin waya dashi daga baya watarana har yazo gidan mu da yake ba'a hana mu tsayawa da samari Saboda da mun gama Secondary Matan gidan mu ake mana aure maza ne ke cigaba da karatu, yan gidan mu suka fara tsokanata nayi saurayi don sun san ban saurarar samari ko zancen su ma ban so ay man inta faman rantse masu shi ba saurayi na bane don bai ce yana so na ba sai su ce wai ai in aka ga kare na Sunsuna takalmi to d'auka zai, lokacin dana tashi komawa S.s One sosae yay man hidima kinga uban provisions d'in da ya siya man muka raba ni da K'anwata da muke makaranta d'aya ko Fareeda ma boarding tay amman ita lokacin da nayi Jsce ta gama, bayan mun koma Makaranta Zaria saida nay yadda mukae muka rink'a waya da shi da wayar wani malami mai shago da muke siyayya har lokacin kuma bai furta man so ba kuma har Visiting yake zuwa man in dae yana Funtua...." D'an dakatawa tay tana maida numfashi Fatuu dae ta zuba mata ido duk ta k'agu taji abunda yay matan can taci gaba "Saida muka shiga Ss 2 wato aji biyar sannan ya furta man yana so na bayan mun dawo wani hutu, Sosae naji dad'in hakan don dama tuni ni na Kamu da son shi Saboda Mujaheed Namiji ne wanda da wuya mace tay rejecting soyayyarshi yana da kyau sosae duk da ba fari bane bak'i ne amman bak'in nashi mai kyau ne ba kamar da Yake hutu ya zauna mashi da yake Family d'in su sanannu ne a garin suna da Kud'i, lokacin da ya furta man so na sanar da shi mu gidan mu da an gama Secondary ake yin aure saidae mutum yaci gaba da karatu a d'akin mijin shi in yana so yace man lafiya lou ai shima ya kusa kammala Karatun shi da yake a K'asar Malaysia ranar da farinciki na kwana Zarah, koda yan gidan mu suka ji suma duk sunyi murna ba kamar mahaifiyata, tunda ya furta man so ban sake kula wani Namiji ba don ya nuna man zai aure ni duk da kuwa lokacin sosae ake cewa ana sona,tunda nike da Mujaheed a wannan lokacin bai ta6a nuna yana son ta6a jikina ba hakan ne ma yasa nike k'ara bala'en son shi don a gani na mutumin kirki ne sai Bayan da na gama Secondary ne ya fara kaman man hannu haka in muna zance wani lokacin har d'an kiss yake man a bayan hannu, sam hakan bai canza daga kallon da nike mashi ba a ganina bai wuce iyaka ba, Bayan mun gama Secondary da kamar wata d'aya watarana da yazo duk sai na ganshi a cikin damuwa na fara tambayar shi mi ke damun shi farko ce man yay ba komae sai dana matsa mashi ne yace zai fad'a man don Allah in fahimce shi kar in tada hankali na tunda naji hakan gabana ya fara fad'uwa amman sai nace mashi to kawai ya kama hannuwana ya fara fad'a man wai a gidan su ne ake son had'a shi aure da wata Cousin d'in shi an matsa mashi sai ya aure ta shi kuma baison ta ni yake so, wllh tunkan ya rufe baki jikina ya fara rawa nan da nan sai kuka ban san lokacin da na fara rok'on shi kan ya fad'a man gaskiyar Magana in ita zai aura amman sai ya nuna man shi fa ba wanda zai masa dole don haka in kwantar da hankali na dama kawai ya fad'a man ne, sosae ya kwantar man da hankali lokacin har da hugging d'ina yay saida yaga hankali na ya kwanta sosae sannan muka rabu...." K'ara dakatawa tay tana share kwallan da suke zubo mata kafin taci gaba "bayan kaman sati biyu da yin hakan Mahaifina yasa in yazo in ce yana son ganinshi akayi hakan bayan sun gama naje wurin shi yana murmushi yake fad'i man cewa akai ya turo sosae nai murna har na kasa boyewa anan yake ce man amman yaba Dad d'ina hak'uri sai after 1 Month don Dad d'in shi bai K'asar nace Allah ya maido shi lafiya, tun bayan wannan Maganar sai ya rage zuwa sai dae muyi waya har tambayar shi nayi sai ya nuna man ba ya fad'i man Dad d'in shi bai nan ba to ai shike kula da harkokin kasuwan cin shi nace na Fahimta, ina ganin acikin watan da yace a bashi bai fi sau biyu ko ukku ya zo ba aka shiga wani watan to shi kwata kwata ma bai zo ba saidai waya har dae na k'ara mashi Maganar turowa sai yake ce man tafiya ce ta kama shi in fad'a a gida ayi hak'uri sai ya dawo lokacin jikina ya fara yin sanyi amman sanin yana tafiye tafiye yasa ban kawo komae ba nayi mashi fatan ya dawo lafiya, tun daga wannan ranar inaga sau d'aya na k'ara yin waya da shi kullum wayarshi bata shiga haka in nayi mashi Magana ta chat itama bata shiga a haka har akayi 1 month aka shiga wata na biyu tun ban damuwa sosae hardai na fara ganin haka yasa Momynmu ta tambayeni kodae wani abu ya faru ne ko munyi fad'a nace mata nidai nasan ba muyi fad'a ba kuma ban masa komae ba na fad'a mata Maganar da yay Mun kafin ace ya turo ta auren Cousin d'in shi tunda naga yanayin fuskar ta a lokacin na fara sarewa tace man kar in damu in ci gaba da Addu'a nace to, abu sai gashi har anyi wata ukku ba Mujaheed babu dalilin shi a lokacin harna fara tunanin ko in je gidan su in duba in lafiya duk da bansan ta ina zan fara ba don gidan su Babban gida ne, ban kaiga zuwa gidan ba bayan kwana biyu an aike mu bakin kasuwa nida sister d'ina da muke boarding tare lokacin ta dawo Hutu muna tsaye bakin titi zamu tsallaka kaman ance in juya sai na hango wani abokin Mujaheed mai suna Usman wanda sun sha zuwa wurina tare da shi har da ina Makaranta ya ta6a zuwa dashi kusan sau biyu ya fito daga Motar shi ya nufi wani shagon Pos aikuwa da sauri nace ma Ummi muje wurin shi, lokacin da ya ganni har saida naga kaman ya d'an razana bayan Mun gaisa nace mashi ina Mujaheed ne farko shiru yay yanayin shi ya canja lokaci guda na rud'e cikin rawar murya na tambaye shi kodae ya mutu ne da sauri ya girgiza man kai yace yana nan raye na hau rok'on shi kan ya fad'a man yana ina da k'yar ya iya bud'e baki ya gaya man Maganar da tunda nike a rayuwata ban ta6a jin abunda ya razanar da ni ba irin ta wai Mujaheed yayi aure kusan wata ukku....." K'ara dakatawa tay tasa kuka sosae Fatuu da itama idanunta har sun cika da kwalla ta jawota jikinta tana bata hakuri, bayan ta d'an tsagaita ne ta d'ago taci gaba ".....nidae tunda ya fad'a man hakan ban san miya faru ba kawai dae na farka na ganni a gadon Asibiti ake sanar dani kwanana biyu anan, Zaraah ko ban fad'a maki ba kema kinsan dole na shiga wani hali na samu Heartbreak, nayi kuka har na gode Allah saida nayi sati biyu a Asibiti koda muka koma gida ma bai lafa ba sai sambatu da koke koke ganin abun yay yawa yasa aka k'ara maida ni Asibiti anan likita ya tabbatar kwakwalwata ta d'an ta6u a maida ni psychiatric muga likitan can a tak'aice dae can ma d'in nayi wani watan har Doctor yace yakamata a nemo man abunda nike so amman da yake ran Abbanmu ya 6aci sosae yace ko da wasa kar wani yace zai nemo Mujaheed har ya kira shi inyi hak'uri kawae don ko dawowa yayi wllh bazai bashi aure na ba, sam banga laifin shi ba Saboda ya matuk'ar yarda dashi bashi kad'ai bama duk yan gidanmu saboda yardar da Abbanmu yay dashi yasa har yake barin mu muna yin zance a cikin Mota wanda ba wanda ya ta6a ma hakan dole saidae aje sitting room d'in shi ko kuma a tsaya a waje amman badai a shiga cikin Mota ba, haka naci gaba da jinya a gida duk da yadda kowa ke kokarin ganin ya faranta man kaman yadda likita ya bada shawara amman abun gaba yake k'arawa don na kasa mantawa ga zuciya tay ta tunzura ni akwae ranar da har na d'aga maganin kwari zan sha k'arfin imani ne ya hana, na dau tsawon lokaci ina cikin hali hardae na fara rarrashin zuciyata da kaina kaman yadda kullum Mahaifiya ke nuna man in yi hakuri kar in ma kaina illa don shi yana can da matarshi bai san ina yi ba, akai akai Usman ke zuwa duba ni dana fara warwarewa ne watarana nike ce mashi Mujaheed ya zalunce ni da yayi man hakan don mi bazai gaya man zancen auren ba kamar yadda da farko ya gaya man gidansu an matsa ya aure ta ai ni da zan fahimce shi ko mu biyu ne sai ya aura banda matsala da hakan cike da tausayawa Usman yace bari ya fad'i man gaskiya ba wani matsa mashi da akai dama can yana tare da ita cousin d'in tashi don tare ma sukayi karatu a Malaysia kawai ni yace ina bala'en burge shi ne, yace man tun kafin mu dad'e tare dashi saida ya bashi shawarar indae yasan ba Aure na zaiyi ba ya rabu dani Amman sai yace wai yasani ko Allah yasa ya aure nin ko da zai yi auren saida yace mashi ya had'a mu ya aura sai yace wai gidan su baza'a bari ba, Saboda haka har d'an sa6ani suka samu lokacin dashi har yana ce mashi wai to shi ya aure ni mana yace ba don sa rana dake a kan shi ba wllh da ya Aure ni, wannan bayanin da Usman yay man yasa raina ya 6aci sosae wani irin haushin shi yakamani don na fahimci shi d'in mugu ne macuci kuma Azzalumi in ba haka ba yasan akan shi nasan miye so kuma Ba wanda nike tare dashi sai shi ko da wasa ban ta6a tunanin ba wani dama ba sai shi amman bai ji komae ba ya iya rabuwa dani, ba abunda ya k'ara bani haushi irin cewa da yay wai burge shi nike...., amman ba komae ai akwae Allah shi mai ji ne kuma mai gani ban mashi ko Allah ya isa ba amman nasan sai Allah ya saka man wllh....." Fashewa tay da matsanancin kuka ta fad'a jikin Fatuu da ta kumbura baki tamkar zata fashe wani irin takaici had'i da haushin Mujaheed d'in ne suka turnuk'e ta a yadda take ji da yana a kusa da ita ba abunda zai hana ta d'udd'ura mashi ashar har bugu ma in tasamu dama Wannan zalunci har ina kuma ita bata ga aibun Fauzy ba indae kyau ne Tubarkallah tana da shi don su rumawa ne harda tsagar 11 gareta a gefen fuskarta ga farinta mai kyau ga gashi duk da bata kai Fatuu ba amman tafi Fatuu tsawo sannan tana da d'an dirinta daidai gwargwado ko a hostel d'in ce ma d'akin su ake d'akin kyawawa, (Uhmm irin hakan na faruwa ko a zahiri don wani 6angare na labarin nan true life story ne, bansan miyasa wasu mazan ke yaudarar mata haka ba duk da a Matan ma ana samun masu yaudarar maza amman ba kamar Mazan ba wanda hakan tsagwaron zalunci ne ko ba'a fad'a ba, ka 6ata ma yar mutane lokaci kayi mata k'arya ta d'auki dukkan yardarta ta d'aura akanka amman kazo ka cuce ta wllh duk mai irin wannan yasani Allah bazai k'yale shi ba don kuwa ya haramta zalunci a tsakanin bayin shi ba yadda za'ai mutum yay haka kuma yaci bulus, duk da mun san wani bai auren matar wani haka wata bata auren mijin wata in ma rabuwar ta kama to ayi ta ba tare da an zalunci juna ba misali kana son ta tsakani da Allah itama haka sai kuma Allah yasa kaddaro dole a rabu amman bawai tun farko ayi tarraya ta k'arya ba kasan bazaka aureta ba initially don me zaka rufe, wasu Matan ta dalilin irin hakan sun samu ta6in hankali wasu sun Kamu da ciwon zuciya wasu ma d'ungurugum kashe Kawunan su suke Saboda an samu irin hakan ba sau d'aya ba ba sau biyu ba ko 6angaren labarin dana ta6o wanda ya danganci yaudarar da akai ma Fauzy ita yarinyar ma tasha maganin k'warin Allah ne yasa da sauran numfashinta gaba bata mutu ba amman ta shiga mawuyacin hali, anan nike son kira ga yan'uwana mata musamman wad'anda aka yaudara da su rungumi hak'uri su d'auki hakan matsayin jarabawa suna zaune Allah zai saka masu kar ki kuskura ki halaka Saboda wani k'ato wanda ba lalle ko gaisuwa yaje gidan ku ba in kin mutu, nasan abun da rad'ad'i da ciwo dole zuciya ta girgiza amman in akayi hakuri duk na d'an lokaci ne a yak'i zuciya kar a biye mata azo ai dana sani mara amfani yin hak'uri shine mafi Alkhairi domin Allah yana