Showing 333001 words to 336000 words out of 512766 words

Chapter 112 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1663

sai ke kina d'auke da yaron ciki zaki ce wani a koya maki Mota" Kukan taci gaba da yi idonta akan Hajiyar itama kallonta take ta kwa6e fuska yadda sukai har saida yaba Mino da Tk dariya, ganin tana son a koya matan yasa Tk ce ma Hajiyar ko ya fara koya mata anan cikin gidan tunda akwae space lafiya lou tun kafin ta bashi amsa Fatuu tace "Eh don Allah Hajiya ki bari ya koya man d'in anan cikin gidan kinsan bai tuk'in ganganci zai koya man lafiya lou" fuska a kwa6e take kallonta Fatun ta shiga motsa baki, k'arshe dai dole hajiya ta amince da hakan ganin yadda Fatun ta k'wallafa rai kuma tasan duk aikin cikin jikinta ne amman tace ba ruwanta.

Washe gari da safe lokacin su Fatuu sun tafi Makaranta Haisam ya kira Hajiya bayan sun gaisa ta tambayi yadda suke da aikin shi yace mata dama Maganar fara zuwan Fatuu awo zai mata sun yi magana da ita tace lafiya lou yanzu ma zata iya fara zuwa, ruk'e ha6a Hajiyar tay jin Maganar da yay mata tace wato shi ga mai d'a ita bata san abunda ya dace ba kenan yay yar dariya yace No ba haka bane, ce mashi tay to tana sane bari tay ya cike wata hud'u sannan ta fara zuwa tunda dai lafiyar ta lou duk abunda ya dace ana mata yace Ok, yar hira sukai ta tambayi lokacin da zai zo ya fad'i mata tay fatan Allah ya kaimu ya kawo shi lafiya daga baya sukai sallama.

Kamar yadda sukai anan cikin gidan aka fara koya ma Fatun Motar da yake tana so sosae take ganewa, lokacin da cikin ya kai wata hud'u daidai ranar Laraba da yamma suka shirya zuwa yin booking d'in awon da yake a private hospital d'in da suke zuwa ne zata rink'a zuwa awon, tare da Hajiya suka tafi a Motar Fatun Tk yaja su, bayan sun isa Asibitin suna shiga Opd suka had'u da Nurse bilki tana ganin Fatuu ta ganeta ta nufo su, Fatuu na ganinta itama ta gane ta suka gaisa ta tambayi wani ne ba lafiya Hajiya tay mata bayanin abunda suka zo yi da sauri tace to suzo suje 6angaren Mama ne, a bakin d'akin da ake awon suka tsaya ta shiga ciki bada jimawa ba ta fito tace su shigo, lokacin da suka shiga Mama na zaune kan kujera idanunta sanye da glass ganin Hajiya yasa ta mik'ewa tana masu sannu da zuwa ta nuna mata kujerar data tashi tace ta zauna Hajiyar tace Fatuu ta fita buk'ata ita ta zauna, jin haka yasa tace ma nurse bilki taje ta kawo wasu kujerun tace to ta juya ta fita, gaisawa sukai a mutunce kai kace dama sun san juna Fatuu ma ta gaishe da ita ta maido idonta akanta bayan ta amsa tace ashe har an maida rabo abu har yama fara girma ita dai murmushi kawai tayi Hajiya ce ta bata amsa, nan mama ta hau fad'i mata ai kwanaki data yi 6ari taje ta dubata a Amenity Hajiya tace Allah sarki gashi ai har an samu wani Mama tace ai wuyar abun ace dama ba auren, bayan nurse bilki ta kawo kujerun duk suka zazzauna nan Hajiya tay mata bayanin abunda suka zo yi tace Ok, katin awo aka yankar ma Fatun daga baya Mama d'in tace ai bari ma a fara mata tun yanzu Hajiya tace aikuwa sun gode, Bp d'inta aka fara dubawa ya nuna normal sai aka auna tsawonta da kuma nauyin ta, bayan duk an gama Mama ta had'a ta da nurse bilki tace suje lab ta tura awon fitsari da na jini da za'a mata suka tafi nan fa suka hau yin hira da Hajiya, ba'a d'au wani dogon lokaci ba duk akayi mata awon har an turo result mama ta duba tace Alhamdulillah komai lafiya lou, gado tasa Fatun ta hau ta fara mata scanning gaba d'aya idanunsu ita da Hajiya da nurse bilki na akan computer d'in dake gwado cikin Fatun, tana cikin yin Scanning d'in tace "ni wannan cikin ma yadda nike gani kamar ba d'a d'aya bane" tai Maganar tana d'age idanunta dake a cikin glass Hajiya tace "ko?" mama ta amsa da "eh Allah, amman dai sai d'an nan gaba za'a tabbatar haka dai nike gani" jinjina kai Hajiya tay "ba mamaki ba d'ayan bane tunda shi Mijin nata suna da gadon abun Mahaifiyarshi yan biyu ne kuma cikin K'annan shi ma akwae yan biyu ni dama tunda naga yadda take d'irkar Abinci na yanke hukuncin da k'yar in ba yan biyun bane" dariya duk sukai Mama tace ai ko cikin d'ayan ma akwae mai saka cin Abincin Hajiya na dariya tace dama itama ta dai yanke hukuncin ne kawai tasan haka, bayan an gama komai aka rubuta mata date da zata dawo, a tare harda Mama suka fito tayo masu rakiya Fatuu dai ta kasa gane farinciki take ko fargaba jin zancen ana tunanin ba yaro d'aya bane a cikin nata, har harabar asibitin inda suka parker Motar su Mama ta raka su Hajiya nata mata godiya saida taga tafiyar su sannan ta nufi komawa cikin Asibitin.

A kwana a tashi ba wuya har sati ukkun da Haisam yace zai dawo sun yi, tun ana gobe zai dawo Fatuu ke ta farinciki har Fuskarta ta kasa boyewa ranar ta kasance Juma'a Tk na d'aukko ta daga makaranta ita da Mino suka wuce kasuwa siyayyar kayan da zata mashi Abinci, Washe gari da wuri ta tashi ta hau shirin tarbar mai gida, anan part d'inta ta fad'i ma Hajiya za'ai abinci gaba d'aya hakan yasa Saude zuwa nan suka shiga Kitchen tare Mino kuma ta hau gyaran part d'in Tk kuma aka sa ya gyara harabar part d'in, zuwa sallar Azahar sun gama komai sai uban k'amshin girkin da sukai kala ukku ke tashi drinks ma kala ukku sukai harda lafiyayyen kunun Aya sannan sunyi had'addan tsiren hanta da grilled lamp daya gasu ya sha vegetables nad'e a cikin foil paper, bayan sun gama komai aka zuba na su Hajiya Saude ta tafi dashi Mino ma ta zuba mata wanda zata kai ma gwaggo tace ta shiryo daga nan zasu je d'aukko shi Airport a d'okance tace to ta tafi, tana shiga Bedroom ta fad'a toilet bata d'au lokaci ba ta fito don tafi son jirginsu yay landing suna a Airport d'in, shiryawa ta shiga yi tayi make up wadda rabon data yi irinta ta manta saidai ko wadda akayi mata da bikin ta, tana cikin yin shafar Haisam d'in ya kirata ya sanar mata gasu zasu taso daga Kano cike da zumud'i tace to tay mashi fatan isowa lafiya, shaf shaf ta k'arasa don tasan bada jimawa ba zasu iso, wata rantsattsar marron d'in shadda sabuwa dal a cikin kayan lefenta take tasha ubansun aiki ta fiddo, ba 6ata lokaci ta saka ta tayi d'aurin kallabi mai kyau ta fiddo jewellery da suka hau da kayan ta saka harda hannunta tasa Agogo da zobuna ita kanta taga kyaun da tayi data kalli Madubin, jaka da takalma da gyale ta fiddo wanda suka hau da aikin shaddar ta saka sosae tay kyau ga cikinta ya fito, tana gamawa ta kira Tk tace mashi sun kusa k'arasowa yace Ok su a had'u a parking space, lokacin data fito har ya fiddo Motar cikin harabar yana hangota ya tunkarota da Motar bayan ya tsaya ta bud'e baya ta shiga yaja suka tafi, a kan hanya suka had'u da Mino itama tayi wanka tayi kwalliya tana sanye da riga da skirt na blue lace ta yafa blue d'in gyale bakinta yasha jan jambaki sosae itama tayi kyau, gaban Motar ta bud'e ta shiga suka tafi. Basu fi minti biyu ba da zuwa jirgin su Haisam d'in ya sauka gaba d'aya Fatuu a k'agare take data gan shi don ba K'aramin missing d'in shi tay ba, gaba d'aya sun baza ido suna kallon masu shigowa can sai gashi ya shigo yana janye da trolley d'ayan hannun shi ruk'e da jakar laptop jikin shi sanye da bak'ak'en riga da wando ya d'aura jar coat, Fatuu na hango shi ta tafi da gudu har saida tasa hankalin shi ya d'an tashi ganin yadda ta nufo shi gashi takalman k'afarta half cover ne masu d'an tsini, da sauri ya saki akwatin itama jakar laptop d'in ya ajeta k'asa ya nufota da sauri yana fad'in ta tsaya tare da yi mata nuni da hannu amman ina ai saida ta k'araso tana niyyar fad'a mashi ya ruk'eta yana murmushi ita kuma ta washe baki gaba d'aya k'amshin jikin shi ya karad'e wurin, ce mata yay miyasa tasan halin da take ciki zatai gudu haka bata ce mashi komai ba sai faman dariyar farinciki take duk hankalin mutane ya dawo kan su, k'arasowa wurin su Mino da Tk sukai suna murmushi sukai mashi sannu da zuwa fuskar shi a sake ya amsa masu, kama trolley d'in Tk yay Mino kuma ta d'auki jakar laptop d'in ya tallabo kafad'ar Fatun gwanin sha'awa suka nufi barin wurin idonta akan shi sai faffad'an murmushi take shima haka, sosae yaga ta canza mashi kan yadda yake ganinta a Vedio call, inda Motar su take suka nufa ita dashi suka shiga baya Mino ta zauna a gaba suka tafi, kwantar da kanta tayi a saman shoulder d'in shi tana ta bashi labarai harda koya mata Motar da ake yana ta jinjina kai fuskar shi d'auke da Murmushi a haka har suka k'araso Unguwar su, a gida Mino tasa aka ajeta tayi ma Haisam Allah ya huta gajiya sukai sallama da Fatuu sannan suka wuce.

Kwana ukku da dawowar shi ya tafi Abuja hidimar bikin Saleem Fatuu ji tay kamar ta bishi saidai Saboda makaranta ta hak'ura Saboda yanzu karatun suke da zafi zafi Saboda shekarar k'arshe ce. Ranar Friday aka d'aura ma Saleem aure da amaryar shi Saleema wadda d'iyar Minister of Health ce sai fatan Allah ya sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya da zuria dayyiba, Ranar Sunday Haisam ya dawo Katsina.

Bayan sati biyu.......

Ranar Friday Fauzy ta dawo Weekend gidan Aunty Mareeya kamar yadda ta saba, da yamma tana kwance akan gadonta cikin d'akinta tana lallatsa wayar ta, jin an turo k'opa yasa ta juyo taga Aunty Mareeya ce ta shigo tana sanye da riga da skirt na jan lace kanta ta d'aura kallabi daga baya ta lankwasa igiyoyin kitson ta Sosae kayan suka amshi jikinta sun bayyanar da k'irarta ta dirarrar giant d'in mace, gadon ta nufo hannunta ruk'e da wayarta ta zauna a baki idon ta akan Fauzy, ganin irin kallon da take mata ga yanayin fuskarta kamar da alamun tashin hankali ko kuma ace Al'ajabi yasa Fauzy tashi zaune itama riga da skirt d'in atamfa ne a jikinta kanta ba kallabi anyi mata kitso shuku jelar ta sauka k'asa,
"Aunty lafiya?" Fauzy ta tambaya ta d'an waro ido da alamun fargaba akan fuskar ta, ajiyar zuciya Aunty ta sauke ta d'an motsa baki tama rasa ta ina zata fara, hakan da tayi yasa hankalin Fauzy tashi tace "Aunty don Allah minene, ki fad'i man kin ji" wata ajiyar zuciyar ta sake saukewa ta yarfa hannu tace "to ai Fauziyya nama rasa ta ina ne zan fara tsabar mamaki wllh" da sauri tace mata mi akai,

"Dama kun fara soyayya ke da Sameer ne baki fad'i man ba?" da mamaki Fauzy ta furta
"Soyayya!" Kai Aunty Mareeya ta d'aga mata, girgiza kai ta hau yi "a'a wllh, ni ba wata soyayya da muke yi duk yadda muke da shi ai kin sani ko daga haka ba wani abu" shiru Aunty tay duk tayi zuru zuru,

"Amman Aunty miyasa kika ce haka?" Hannu ta kai ta ruk'e ha6a tace "Wai kinsan yanzu Baba ya kira ni da alamun tashin hankali yake tambayata wai wane yaro ne kike tare dashi basu sani ba kuma Sameer ne yake magana akai"

zaro ido Fauzy tay ba shiri ta gyara zama Aunty taci gaba "Wai kiran shi akai daga gidan gwamnatin Nasarawa kan ya bada rana za'a zo neman Auren ki kuma harda rana za'a saka" tun kafin ta k'arasa Fauzy ta k'ara zaro ido ta bud'e baki Aunty tace "Wllh, ke duk yadda nike fatan hakan baki ji yadda hankali na ya tashi ba don ban tsammaci abun haka ba" gaba d'aya bakin Fauzy ya mutu sai ido kawai sosae taji Al'ajabin Maganar don ita an fi sati ma ko ta WhatsApp basu yi magana da Sameer d'in ba, da k'yar ta iya cewa "Yanzu shi baban miya ce masu??" Aunty tace "wai ce masu yay don Allah su bashi lokaci zai kira su ya sanar masu don farko ma gardama masu yay kan bake bace saida aka tabbatar mashi ta hanyar yi mashi bayanin ki ya gasgata tabbas ke d'in shi shine ya kira ni yaji yadda abun yake baki ji yadda hankalin shi ya tashi ba bayan nayi mashi bayanin tsakanin ki da shi sosae yay mamaki" Fauzy ba baki sai ido kawai wani irin bugu k'irjinta yake mata sosae Al'amarin ya d'aure mata kai,

"Yanzu shi Baba so yake wai aji ta bakin ki don yama rasa yadda zai tafi da Al'amarin" shiru Fauzy tay idonta acikin na Aunty can ta fara girgiza mata kai "Aunty kice mashi kada ya amince su zo ban son Auren shi" waro ido Aunty tay "amman Saboda me Fauziyya, ba abunda dama muke fata ba kenan??" Idanun Fauzy ne suka ciko da k'walla cikin karyayyar murya tace "Haba Aunty ina ake haka fisabilillahi, ko don mu talakawa ne shine zai nuna mana iko haka, bafa soyayya muke dashi ba hasalima bai ta6a nuna man wani alamu na yana so na ba kawai kuma sai ace wai zai aure ni to wane irin aure ne haka zamu yi dashi don Allah?" Shiru Aunty tay tana kallonta k'wallan suka fara zubo mata, ajiyar zuciya Aunty tay tace "amman Fauziyya ba kina son shi ba?" Da sauri tace "ko ina son shi Aunty ni bazan yarda ya nuna man iko haka ba, don ina talaka ai nima inada daraja ba yadda za'ai yayi man wannan ikon, a tunanin shi komai ne ake iya nuna iko, to bazan Aure shi ba gaskiya" ta k'arasa tana girgiza kai harda d'an huci ta kumbura baki, hannu Aunty ta kai ta kama hannunta cikin kwantar da murya ta fara magana "ni ina ganin tunda kinsan halin shi Fauziyya bai kamata ki tada hankalin ki haka ba, k'ilan shi ba da niyyar nuna iko yayi hakan ba...." Katseta tay "iko ne mana Aunty tunda ai yasan ba Soyayya muke da shi ba" d'an cize le6enta na k'asa Aunty tayi kafin tace "watak'il fa shi a wurin shi a hakan soyayya yake dake kinsan Mutane irin shi suna da wuyar fahimta wllh, kiyi tunani tun farko da kuka san juna laifi fa kikai mashi amman kuma ya cigaba da kula ki yana maki abubuwan Alheri kinga ta yuwu kamar yadda nace a wurin shi soyayya yake dake, kuma tabbas yana son ki shiyasa har yasa a zo nema mashi auren ki, tunda kinsan halin shi Fauziyya hakan bai kamata ya dame ki ba har ki fatali da wannan babbar damar da kika samu wadda ko a film da wuya kiga wata ta samu irin damar ace dai d'an Governor zai auri d'iyar talaka " shiru Fauzy tay har lokacin da k'walla a cikin idanunta, still hannun Aunty na a ruk'e da nata,

"Tunda kina son shi ki amince kawai mu taru muyi fatan Allah yasa hakan Alkhairi ne kuma watak'il sakayyar abunda Mujaheed yay maki ne Allah yayi maki dama in dai aka cuci mutum yayi hak'uri ya bar ma Allah tabbas sai ya saka mashi" shiru tay tana ta bin ta da ido Auntyn tace mata tayi magana mana, motsa baki ta fara tana yamutsa fuska tace "to ni Aunty mi kike so in ce, wai ina aka ta6a Aure haka don Allah mutumin nan fa ko halin shi bamu sani ba shin yana da kyakkyawan hali ko mummuna ba wanda ya sani sannan kuma ni wllh ina zargin shi ma, akan ido na fa yasha giya kuma yaje Club taya mutum mai kyaun hali zai aikata hakan, ni dai gaskiya Aunty ina ganin gara mu hak'ura da shi kawai kar azo ayi abunda za'a dawo ana dana sani kema kinsan irin yaran masu kud'i da Mulkin nan sai a Hankali wllh" ta k'arasa tana girgiza kai,

"Amman mijin Zarah haka yake? Kuma ai baki da tabbas din giya d'in ce kika ga yasha ko tunda ai ke ba saninta kikai ba, kuma da ya sha kinga ya bugu ne tunda ai kun d'an jima tare sannan yayi maki wani abu na kaucewar hankali? In da ya bugu kema kinsan yadda kuka kasance ku biyu kawai wllh sai dai Allah ya k'wace ki kuma ko da bai bugu ba inda d'an iska ne na tabbatar da sai ya nuna maki halin shi a wurin, sannan Maganar zuwa Club tare kuka shiga ne? Ina ce a cikin Mota ya bar ki kinga kenan baki da ikon zargin shi tunda ai baki san miya shiga yayi ba duk da ansan ba wurin Arziki bane amma ba kyau ki munana mashi zato" kallonta kawai Fauzy take fuska a kwabe,

"Yanzu in don sanin halin shi ne ai Mijin Zarah na nan ko zan kirata in sa ta tambayar mana shi komai da muke son sani na tabbatar bazai 6oye mana komai ba, ni kuma na maki Alkawarin indai aka tabbatar yana da wani mugun hali da ya kamata a guje ma auran shi to zan goya maki bayan hakan" ganin bata ce komai ba yasa tace mata hakan yayi mata, d'an yamutsa fuska tay a raunane tace "to amman Aunty yanzu misali ace baida wata illa haka zan aure shi ko fa sona bai ta6a cewa yana yi ba, ni nafi tunanin ma Saboda labarin dana bashi na Mujaheed ne yasa ya yanke aure na

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login