Showing 111001 words to 114000 words out of 512766 words

Chapter 38 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1616

Wuraren k'arfe sha d'aya Fatuu ta farka taga d'akin wayam ba kowa tana kwance aka turo k'opar sai ga Fauzy ta shigo da yar sallama da sauri Fatuu ta yunk'ura ta tashi zaune tana kallonta itama Fauzy da sauri ta nufi gadon ta zaune a gefe fuskarta d'auke da matsananciyar damuwa tayi mata sannu ta d'aga mata kai d'an shiru sukai sunata kallon juna fuskar Fatuu a yamutse kaman zata saka kuka can Fauzy tace "ashe haka abu ya faru harda kwanciya Asibiti tun bayan da muka rabu inata so in kira ki zullumi da fargaba suka hana ganin har dare yayi baki kirani ba kin sanar da ni halin da ake ciki yasa nai k'arfin halin kiran ki saidae kusan sau ukku ba'a d'aga ba tsoro ya kama ni sosae na shiga tunanin to ko lpy gashi na kasa kiran ko Kawu Amadu, sai can dare wurin karfe 11 nace bari in k'ara jarabawa k'ilan ki d'aga tunda lokacin kwanciya ne ina kira sai gwaggo ta d'auka nan take sanar dani wai an kwantar dake Asibiti wayar na gida aka barta wllh sosae hankali na ya tashi bazan 6oye maki ba ko bacci ban yi ba saboda fargabar abunda ya faru har aka kwantar da ke, Aunty Mareeya har ta gane ina cikin damuwa tanata tambayata Mike damuna saidae in ce mata ban jin dad'i kawai don ban san taya zan mata bayani ba" dakatawa tay ta kai idonta kan ledar Karin jinin dake rataye cike da damuwa tace "harda k'arin jini ma akai maki kenan, cikin ne ya fita kika zubda jini sosae?" Kai Fatuu ta d'aga mata alamar eh, girgiza kai Fauzy tay "Sannu, wllh irin abunda nake ta gudu kenan kinga ko a Makarantar hakan ta faru sai an san dalili, to yanzu da su gwaggon suka sani miya faru?" Shiru kaman bazata ce komae idanunta suka ciko da k'walla a hankali suka fara gangaro mata cikin muryar kuka tace "Fauzy na aikata babban kuskure wllh ashe cikin nan na halak ne ba yadda na zata ba" waro ido Fauzy tay with mouth agape a rud'e tace "cikin halak! Kenan kina son kice man Ya Haisam Mijin ki ne???" Cikin kuka ta d'aga mata kai k'ara zaro idon tay ta kai hannu ta rufe baki kafin ta cire cike da Al'ajabi ta tambayeta yadda hakan ta faru nan ta shiga fad'i mata komae da ya faru bayan ta dawo gidan har zuwa yanzu, salati Fauzy ta shiga yi tana yi tana kai hannu tana dafa gaban kanta da kuma bakin ta cikin tsananin tashin hankali ta hau fad'in "ni wllh dama raina saida ya bani anya ba wani abu a k'asa kwata kwata na kasa yadda Ya Haisam zai aikata maki hakan Saboda son zuciya kawae dai bani da wata hujja ne, innalillahi abu dae bai yi dad'i ba wllh aka ce rashin sani yafi dare duhu" sosae ta shiga damuwa har fuskar ta ta nuna idanun ta sun sauya kwalla ta kwanta cikin su sosae Fatuu ke kuka tana fad'in "nayi danasani Fauzy duk da na d'aga wayar Ya Haisam bayan dana je na sanar mashi da hakan bata faru ba, saida yay ta kira na harda message ya turo man yace kar in yi komae in picking kiran nashi amman na k'iya k'in Fad'a maki nay don kar ki hana a zubar na nuna maki sau d'aya ya kira, wllh ban yi zaton na halak bane tunda ni bansan komae ba ai gashi naga kaman ma yayi fushi Saboda hakan " itama Fauzy k'wallan ne suka fara zubo mata suna cikin haka suka ji karar bud'e kopa duk suka kai idon su kan kopar toilet sai ga gwaggo ta fito idon ta a kan su suma suka bita da ido cike da rashin gaskiya...............





_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2055*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


......Kauda idon ta tay daga kallon su ta nufo cikin d'akin cikin kame kai Fauzy ta gaishe da ita ta amsa tare da d'an kallon ta tay mata ya mai jiki nan ma ta amsa kafin ta nufi kujera, a jikinta ta janyo Hijab d'inta ta nufi hanyar fita daga d'akin tana kokarin sakawa, bayan ta fita Fauzy ta kalli Fatuu da yar damuwa tace "ta san kin yi wani abu ne don zubar da cikin?" d'an shiru Fatun tay fuskar ta duk hawaye tace bata sani ba ko likita ya gane ya sanar masu tunda ta dad'e bata farfad'o ba amman in ma ta sanin to bata nuna mata ba, ajiyar zuciya Fauzy tay tace "to k'ilan bata sani ba amman yanzu kaman ma taji abunda muke cewa" shiru kawae Fatun tay idon Fauzy akan ta wani irin tausayin ta ne ya kamata tasan dole ta shiga matsananciyar damuwa yadda take son Ya Haisam bazata ji dad'i ba ace ta samu cikin shi na halak kuma ta zubar da hannun ta gashi tace yayi Fushi, hannu Fauzy ta kai ta kamo nata ta fara lallashin ta "ki kwantar da hankalin ki Zarah nasan dole Kiji ba dad'i amman kada kisa damuwa a ranki ki d'auka komae rubutacce ne dama haka Allah ya k'addaro kuma shima Ya Haisam d'in na tabbatar zai fahimce ki kawae dae dama dole ne ya nuna maki 6acin ran shi Saboda zai ga kin k'i jin Maganar shine har hakan ta faru wanda nasan bai yi zaton hakan daga wurin ki ba a yadda kuke da shi amman dae komai zai daidaita in sha Allahu, ki daina damuwa ko don halin da kike ciki kada ki samu wata matsalar kuma" tana kai Maganar ta kai hannu tana goge mata kwalla daga baya tace bari ta sanar ma Aunty Mareeya, bayan ta kirata ta sanar mata zancen kwantar da Fatun Asibiti salati ta saka hankali a tashe ta hau tambayar Fauzy abunda ya samu Zarah nan ta kwashe komai ta fad'i mata tana jin yadda take zabga salati a rud'e tace tana nan zuwa wane Asibitin take ta sanar mata, bayan sun gama wayar yar hira Fauzy ta shiga yima Fatun duk don ta daina damuwa harda zancen irin shagalin da zasu yi in komae ya daidaita da kalar su ankon da za'ai daga baya kuma yanayin fuskar ta ne ya canza tace tasan ma d'auke Fatun zai yi su bar K'asar amman dae gaskiya a bari sai sun gama karatu lokacin tasan ta k'ara samun wani cikin harma ta haihu, harda Addu'ar Allah yasa next cikin da zata samu na twins ne, tun dai Fatuu na d'an murmushi sai gata harda su dariya, Bayan sallar Azahar sai ga su Feenah Abbas ya kawo su lokacin da suka shigo su Fatun na Zaune akan gadon Fauzy na gefen ta Abdul na hango ta ya nufi gadon da gudu ya fara k'ok'arin hawa Fauzy ta taimaka mashi yana hayewa ya fad'a jikin ta Feenah na fad'in bai ganin mara lpy ce, a gefen gadon Feenah ta tsaya bayan ta aje basket d'in kayan Abincin data shigo da shi tana sanye da doguwar rigar Atamfa tayi d'aurin kallabi mai steps ga gyale mahad'in kayan ta yafa a kafad'a hannun ta na dama ruk'e da hannun Nasreen da itama tasha yan kanti, da alamun damuwa Abdul dake kallon face d'in Fatuu yace "Aunty Fatuu ashe baki lpy" itama kallon shi take da d'an murmushi ta d'aga mashi kai alamar eh ya juya ya kalli ledar K'arin jini fuskar shi kaman zai kuka idanun shi har sun kawo kwalla yace mata sannu ta rungume shi ta gefe Feenah ma tayi mata ya jiki ta amsa mata kafin ta gaishe da ita Nasreen ta fara rigimar itama a d'aurata kan gadon Feenah tace ya duk zasu haye gadon mara lafiya Fatuu ta mik'o hannu tace ba wani abu ta d'auro ta Fauzy ta kai hannu ta d'aukko ta, ganin Feenah nata tsayuwa yasa Fatuu ce mata "Aunty Feenah ga kujera can ki zauna" d'an murmushi tay tace "bari in gama ganin ki to, ashe abu kuma haka ya faru jiya Dear ke fad'a man banji dad'i ba wllh nace da an sani ai da an tari abun da wuri duk da hakan bai faru ba, shima yace man bai san abunda ke faruwa ba sai jiyan" idanun Fatuu ne suka ciko da k'walla bata dae ce komae ba sai kikkafta idanu take don kada su zubo suna haka Abbas ya shigo dama yana waje wurin gwaggo suna gaisawa, bakin gadon shima ya tsaya Fauzy ta gaishe dashi ya amsa yay mata ya karatu ya maida kallon kan Fatuu cike da kulawa yace "Mom Zarah ya jikin?" Kallon shi tay a sanyaye tace da Sauk'i,

"Allah ya baki lafiya ashe haka abu kuma ya faru?" Aikuwa kaman tana jira ta fashe masu da kuka dama daurewa kawae take, girgiza kai Abbas ya shiga yi cike da tausayi Feenah ma Fuskarta kaman zata sa kukan Fauzy kuwa tuni kwalla sun ciko mata, sosae Abdul ya rud'e ya d'ago yana fad'in "Aunty Fatuu don Allah kibar kuka zaki samu lafiya in baki yi shiru ba nima zan yi kukan" k'ok'arin shanye kukan ta fara tana girgiza ma Abdul kai alamar kada yayi ya kai hannu yana goge mata kowa jikin shi yayi sanyi Abbas ne yace "Kiyi hakuri Mom Zarah nasan an maki ba daidai ba don da kin sani hakan ba zai faru ba to amman komai ki ka ga ya faru dama rubutacce ne" kallon shi tay cikin muryar kuka tace "Amman Ya Abbas Saboda mi aka 6oye man ko kai ba sai ka fad'i man ba tunda ni ban 6oye maka komai" da alamun Damuwa kan face d'in shi yace "kiyi hak'uri don Allah haka aka tsara ne ba za'a sanar maki ba shiyasa..." Katse shi tay "to Saboda mi?" Shiru yay don bai son yace mata auran tsarawa akai don a taimake ta ba don ya d'ore ba, ba kamar kuma yanzu da abu ya shiga tsakanin su, Feenah ta fahimci Abbas bai son sanar da ita game da auren hakan yasa ta kai hannu tana share mata hawayen dake zubowa tana fad'in "Haba Mom Zarah d'in mu kefa nasan mai k'arfin hali ce kiyi hak'uri komae ya wuce ko ma samu ki warke da wuri a k'ara samo mana cikin wani Baby d'in in sha Allahu ma twins za'a maida mana tunda da yawa wani rabon ke kore wani" d'an murmushi Fauzy tay ta sadda kan ta haka ma Fatuu d'an juyar da fuskar ta tay Abdul kuwa k'ura ma Feenah da tayi Maganar ido yay can ya kasa jurewa ya d'ago daga jikin Fatuu yace "Momy Aunty Fatuu tayi aure ne?"

D'an shiru tay sai kuma tace mashi "Mi yasa ka tambaya?" yace "naji kin ce ta Warke ta haifo babies?" shiru Feenah tay sham ta manta dashi a wurin tay Maganar tasan shi bai ji ya k'yale Abbas kuwa d'an d'age gira yay yana kallon Feenah da murmushi alamar jiran yaji amsar da zata ba Abdul don ya kafeta da ido can ta d'aga mashi kai tace eh tayi aure, waro ido yay alamun mamaki ya juya ya kalli Fatun ya sake juyowa ya kalli Mom d'in tashi yace "Yaushe tay auren ni ban sani ba kuma waye ta aura?" ta biyun ta amsa mashi tana d'an murmushi tace "Baban ka Zakee" har saida yay wata yar zabura ya tsuke fuska cikin fushi yace "Kamm shine sukai auran ban sani ba kuma bani nace ma ya aure ta ba" a hak'ik'an ce yay Maganar sai bin su yake da kallo ya kumburo baki sigh Abbas yay yace mashi "ai ba'a yi bikin ba tukun an dai d'aura masu aure ne....." Katse shi yay kaman zai kuka "to ni miyasa ba'a je dani d'aurin auren ba ba inada babban riga ba" har saida ya basu dariya su duka Fatun ma saida tay d'an murmushi wato shi a tunanin shi saida babban riga ake zuwa d'aurin aure, kafin wani ya bashi amsa aka turo k'opar da yar sallama k'asa k'asa ya shigo, Wow Tubarkallah Angon Fatuu shine abunda na fad'a, wankan bak'in Voile yay ana d'an hango hasken vest d'in shi kad'an hannun shi d'aure da Agogo ta bak'ar fata haka k'afafun shi dakakkun half cover ne masu kyau da tsada Sumar nan tasha gyara ta k'ara bak'i sai salk'i take, sosae yay kyau tun ma kafin ya k'arasa shigowa k'amshin turaren shi ya baza d'akin kai kace shi kadai kamfanonin turaren suke ma irin nashi don koda yaushe k'amshin shi na daban ne, tunda Fatuu tay arba da Fuskar shi gaban ta ya fara wani irin bugu gaba d'ayan su idanun su na akan shi yayin da Fauzy acikin ranta ta hau fad'in Tubarkallah sam bata ganin laifin Fatuu da take son shi ita a yadda take ji ma da itace abu ya shiga tsakanin su har ta samu ciki wllh bazata zubar da shi ba bari zatai har ta haife tunda tasan bazai ta6a wofintar da ita ba duk surutun da za'ai aje ai ta yi, Abdul na ganin shi ya saukko daga kan gadon ya nufe shi da sauri lokacin har ya zo tsakiyar d'akin a gaban shi ya tsaya yana kallon shi fuska a d'aure hakan yasa Haisam d'in tsayawa yana kallon shi Fuska a sake su Abbas nata murmushi daga inda yake yace ma Haisam "Baba Zakee yau fa ka ta6o d'an gidan ka kay mashi laifi" d'an kallon Abbas da yay Maganar yay sai kuma ya maido idon kan Abdul daya kumbura kamar zai fashe cikin cool voice d'in shi yace "What's happening?" Ya kai hannu zai dafa kan Abdul d'in da sauri ya janye kan yasa hannuwan shi duka ya ruk'e k'ugun shi alamar dai abun yau baram baram za'ai Abbas kau mi zai yi in ba dariya ba haka ma su Fauzy still Haisam murmushi yake calmly ya furta "kaga dariya suke mana tell me laifin mi nayi?" Yana tura baki yace "ashe dana ce ka auri Aunty Fatuu ka aureta ban sani ba kuma ko d'aurin auren ba'a je dani ba!" Abbas ya amshe da fad'in "kuma dae yana da babban riga ato" duk sukai dariya shima Haisam d'in yar dariyar yay ya kamo hannun shi yana fad'in yayi hak'uri to ya fara bubbuga k'afa k'arshe Haisam d'in ya sunkuce shi ya d'aura shi a bayan shi sai k'unk'uni yake cike da shagwaba, yana zuwa bakin gadon Fatuu ta sunkuyar da kanta Fauzy dake kallon shi ta gaida shi ya amsa tay mashi ya mai jiki haka Feenah ma duk ya amsa Fauzy ta sauka daga kan gadon ta nufi Kujera Feenah ma ta bi bayan ta ya rage daga shi sai Abbas tsaye a bakin gadon, kai idon shi yay kan ta kaman ance ta d'ago suka had'a ido Slowly ya furta "Ya jiki?" a sanyaye tace da Sauk'i ya jinjina kai kawae still da canjin da take gani akan Fuskar tashi, mai da kallon yay kan Abbas dake mashi wani kallo irin na wanda yay abu ba daidai ba shi kuma ya maida mashi martani da nashi mai kaman harara suna haka Dr Habeeb ya shigo cikin d'akin da sallama su Feenah suka amsa had'i da gaishe dashi yay masu ya mai jiki ya nufi su Abbas, hannu ya basu suka gaisa gaba d'aya ya kalli Haisam yay mashi ya mai jiki k'asa k'asa yace da Sauk'i kafin ya d'an matsa gaban gadon da murmushi yace ma Fatuu ya jiki tace da Sauk'i ta gaishe dashi ya amsa, tambayarta yay tana jin wani ciwo ko a marar ta haka tace a'a bata jin komae ya k'ara tambayar yanayin jinin da ke zuba da yanayin yawan shi a kunyance take bashi amsa tana yi tana d'an sadda kai don duk su Abbas na ji,

"To ya kike jin yanayin jikin ki?" tace "kawae ba k'arfi ne sosae" jinjina kai yay "Ok sai a hankali k'arfin zai dawo zuwa anjima sai a ida saka maki sauran jinin" kai ta d'aga ya juya kan Haisam yace "Yanzu ina ganin muje ai mata Scanning d'in mu ga" kai Haisam ya d'aga ya juya ya kalleta suka had'a ido sai taga kaman ma harararta yake da sauri ta sunkuyar da kan ta, Abbas ya yi ma Feenah magana kan tazo ta taimaka mata suje wurin scanning tace to ta mik'e su kuma suka wuce tare da Dr d'in, bayan ta saukko daga kan gadon Fauzy ma ta taso lokacin gwaggo ta shigo tazo wurin su tana fad'in bari a bata abunda zata yafa ta wuce wurin jaka ta ciro mata d'an gyalen ta dama kan ta da hula suka tafi Feenah ta tallabo Shoulders d'in ta, a kan hanyar su ne Fauzy ke yin Addu'ar Allah yasa aga cikin na nan Feenah tace ai gaskiya da wuya ne Saboda Dear ya fad'a mata ta zubar da jini sosae gashi cikin dama d'an k'arami ne zai wuya ya tsaya kuma already Dr ma yace masu ya fita, lokacin da suka isa a bakin wurin suka iske su Haisam tunda ta kalle shi sau d'aya ta kauda idon ta Abbas ne yace mata ta shiga Dr d'in na ciki ta d'aga kai ta shiga suma su Feenah suka tsaya a bakin kopar don su jirata daga baya Dr ya fito yace ma su Abbas suje Office, sai bayan wasu mintuna Fatun ta fito Feenah ta tambayi an gama tace mata eh ance za'a tura ma Dr tace Ok ta k'ara kamata suka tafi, Suna zaune a Office suna yar hira aka turo result d'in ya fad'a masu gashi an turo ya fara dubawa bayan wani lokaci ya d'ago ya kalli Haisam yace "ya nuna ba sauran wani abu mahaifar ta is empty so ina ganin kawae taci gaba da shan magungunan tunda tace jinin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login