Showing 102001 words to 105000 words out of 512766 words
Chapter 35 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1594
ruk'e da basket d'in Warmers suka nufi Mota, yana shiga ciki sai ga kiran gwaggo tace ya wuce ne yace mata a'a yanzu dae zai tafi tace to don Allah ya d'an tsaya zata bashi kayan Fatuu akai mata in ta farka sai ta canza yace to, lokacin da ya tsaya horn yay Amadu ya fito ruk'e da yar jaka mai d'auke da kayan Fatuu harda undies da pad bayan ya saka a back seat yay mashi saida safe ya juya shi kuma yaja Motar ya tafi, lokacin da isa Asibitin k'arfe goma ta wuce bayan ya Parker ya fito ya bud'e back door ya fiddo basket d'in kayan Abincin da jakar ya rufe ya nufi ciki, Haisam na zaune kan kujeran ya d'an kishingid'a had'i da lumshe ido Abbas d'in ya shigo da yar sallama ya bud'e idon a hankali ya kalle shi Abbas d'in ya d'an yi mashi murmushi ya nufi inda yake, a gaban kujeran ya aje kayan hannun shi ya zauna gefe idon shi akan Haisam yace mashi sannu ya jinjina mashi kai nuna mashi kayan yay yace ga Abinci nan da kayan matar shi an ce inta tashi ya bata ya kuma taimaka mata tay wanka ta canza kaya wani kallo yay mashi Abbas d'in yay dariya kafin ya juya ya kalli Fatuu ya d'an girgiza kai ya juyo yace ma Haisam wai har yanzu bata farka ba ya d'aga mashi kai yace "Allah sarki Mom Zarah wllh na tausaya mata sosae Allah ya bata lafiya" shiru Haisam d'in yay Abbas yace "bazaka amsa ba ko baka so tay saurin samun sauk'i ka maida bugu nan da nan asamo mana twins" still banza yay mashi fuska a d'aure Abbas ya tuntsire da dariya yace "Serious kasan wani rabon na kore wani fa gashi Mom Zarah na fahimci ba ta wasa bace da an bata take amsa" d'an k'ank'ance ido yay yana kallon shi Abbas d'in sai dariya yake can slowly yace ya tashi ya tafi gida dare yayi Abbas d'in yace wato ya ishe shi kenan daga yana taya shi hira ya rage kad'aici yace mashi ya gode bacci yake ji ne Abbas d'in ya fara kokarin mik'ewa yana fad'in ai shikenan, tare suka fito saida ya raka shi har bakin Mota Abbas ya bud'e ya shige driver seat yay mashi saida safe ya juya ya koma ciki, yana shiga d'akin ya k'ulle kopar ya nufi kujerar ya zauna idon shi akan Fatuu can kuma ya kai hannu ya dauki wayar shi ya fara lallatsawa bayan wani lokaci ya ajeta don bacci yake ji daurewa kawae yake mik'ewa yay ya d'auki bargo ya shimfid'a a saman kujerar kafin ya kwanta saidae bata d'auke tsawon shi ba gaba d'aya a hankali ya fara lumshe ido yana yi yana bud'ewa har baccin ya d'auke shi, Misalin k'arfe sha d'aya da yan mintuna ta fara mutsu mutsun farkawa slowly ta fara bud'e idanuwan ta tana yi tana sake lumshe su a haka har ta bud'e su gaba d'aya akan ceiling d'in d'akin ta k'ura ma Fanka ido tana kokarin gano a ina take, d'ago hannuwanta tay duka jin su kaman ba daidai ba nan idonta ya sauka akan kanular dake a jikin kowanne nan take ta gane inda take, sauke su tay ta fara juya kan ta a hankali tana bin d'akin da kallo har idanunta suka sauka akan Haisam da idanun shi ke a rufe wani irin bugu kirjinta yay ta k'ura mashi ido lokaci guda abubuwan da suka faru suka fara dawo mata har zuwa lokacin data san shi Mijinta ne ta shiga tunanin ashe duk abubuwan da yake mata Saboda wannan dalilin ne ita bata sani ba tay wani tunani na daban a hankali ta saki d'an murmushi tana cigaba da kallon shi zuciyar ta na raya mata yanzun nan shi Mijinta ne wani irin dad'i take ji a cikin ranta can kuma ta tuno da Maganganun da ta gaggaya mashi a G.r.a nan take yanayin fuskar ta ya sauya damuwa ta bayyana tamkar yaji ajikin shi tana kallon shi ya fara motsi yana kokarin bud'e ido sam ta kasa janye idanunta kirjinta sai bugu yake da sauri da sauri a hankali ya bud'e idanun suka sauka akan ta ya bita da kallo suka zuba ma juna ido...........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2053*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
...........kasa jurewa tay a hankali ta maida idonta k'asa shima maida nashi yay ya lumshe bayan wani lokaci ta d'ago ta sake kallon shi har lokacin bai bud'e idanun nashi ba hakanan sai taji wani iri don kallon da ta ga yana yi mata ba kalan wanda yake mata bane a kwanakin baya kafin hakan ta faru, maida idon tay tana kallon gaban ta cikin ran ta tana k'ara tariyo abubuwan da suka faru gaban ta ne ya fad'i tunowa da jinin data gani nan ta fara kokonton anya cikin bai fita ba kuwa lokaci guda ta yanke ta san ma zai yi wuya in yana nan, wani iri taji damuwa ta bayyana kan fuskar ta sai kuma ta hau yin tunanin halin da gwaggo da Hajiya suke ciki tana haka taji fitsari ya matseta ta fara kokarin yunk'urawa ta tashi dama an riga an cire mata k'arin jinin da aka saka mata na farko a can gefe ta hango gyalenta dama yana jikinta aka zo da ita Saboda rolling d'in shi tay sai bayan an kawo ta d'akin ya kwance, bayan ta yafa gyalen saman kanta zuro k'afafun ta tay a hankali ta saukko daga saman gadon wani irin fayau taji ta kwata kwata ba k'arfi a jikinta ga juwa na niyyar kwasar ta ba shiri ta koma ta zauna tasa tafin hannun ta guda ta dafe forehead d'inta duk Haisam na kallonta don tunda ta fara k'ok'arin saukkowa ya bud'e ido jin mutsu mutsun da take, bin ta yay da kallo ba tare da ta sani ba can ya yunk'ura ya tashi tsaye walking slowly ya nufe ta duk bata sani ba har saida taji k'amshin shi jikin shi ya cika mata hanci sannan ta d'ago da fuskar ta da d'an sauri idanunta suka sauka a cikin nashi wani irin bugu kirjinta yay ta kafe shi da ido had'i da d'an motsa baki kamar zata ce wani abu amman ta kasa furta komae Slowly taji cool voice d'in shi ya furta "Let me Help" ya mik'a mata hannu duk tayi tsuru tsuru kamar mara gaskiya ta kai hannu a d'arare ta kama santalelen hannun nashi jajir dashi ga taushi kai kace ba hannun babban namiji ba don kuwa banda yanayin halittar fata shi kan shi hannun yana shan tsadaddun mayukan gyara masu saka taushi, bayan ta mik'e tsaye zame hannun na shi yay ya zagaya dashi ya tallabo Shoulders d'in ta suka fara tafiya fuskarta a k'asa gaban ta naci gaba bugawa har suka isa bakin kopar toilet d'in sannan ya dakata ya zame hannun nashi ta d'an kalle shi sai taji yace "Can u....or I should call Nurse?" d'an girgiza kai tay a hankali tace zata iya shiru bai ce komae ba ta juyar da fuskarta ta tura ta shige ta maido k'opar, toilet d'in tsaf kai kace bana asibiti ba duk da ba bathtub amman har heater ta ruwan zafi akwai da shower, butar data gani wadda gwaggo tasa Amadu ya kawo ta d'auka ta tari ruwan zafi daidai yadda zafin zai mata, lokacin data tattare rigarta gabanta ne ya fad'i ganin cinyoyinta jage jage da jini bata yi mamakin rashin ganin pant d'in data sa ba don tasan a ina take zai yuwu an cire shi ne, jiki a mace ta duk'a ta fara yin fitsarin bayan ta gama tay amfani da ruwan wurin wanke k'asan nata sosae bayan ta gama ta mik'e tsaye da k'yar, tunanin yakamata tay wanka ta shiga yi don tasan duk jini ne a jikin rigar don ma tana bak'a saidae bata san kuma ko akwai wasu kayan da zata canza ba, matsawa tay ta jingina da bango tay shiru sam ta kasa karantar yanayin da ta ga fuskar Haisam don sai take ganin kaman yana d'aure fuska, tana ta tsaye ta rasa mike mata dad'i gashi bata san ya zata yi ba tana son yin wanka amman bata san ko akwae kaya ba kuma sai take ta jin fargabar fita tana haka taji an yi knocking kopar har saida kirjinta ya d'an buga damm da sauri ta kai ido kan kopar k'ara knocking d'in akai ta nufi kopar cikin rashin k'arfin jiki tasa hannu a hankali ta bud'e tay arba da Fuskar shi, bin shi tay da ido ya mik'o mata abun hannun shi wanda towel ne da soap dish ta kai hannu ta amsa murya k'asa k'asa tace mashi ta gode bai ce komai ba ya juya itama ta koma ciki, yana bata kayan waje ya nufa yaje yay ma Nurse Magana kan azo a gyara mata bed har ya dawo bata fito ba ya zauna kan kujera yana nan aka zo aka gyara gadon aka canza Bedsheet can ya tuna da Magungunan da Dr Habeeb ya tura pharmacy don yace akwae yuwuwar ba sai an yi mata wankin ciki ba don yana tunanin komae ya fito sakamakon jinin da ya zuba sosae zuwa washe gari za'ai mata scanning don a tabbatar mik'ewa yay ya tafi ya amso, bayan ta gama wankan tsaye tay ta kasa fita da towel d'in jikinta wanda iyakar shi tsakiyar cinyoyin ta, tana ta tsayuwa gashi jiki ba kwari can dae ta nufi kopar saida tay d'an jimm kafin hannu na rawa ta kama handle d'in ta bud'e sai dae tana sa kai taga d'akin wayam ba kowa wani sanyi taji ta shiga ta nufi gadon da taga an gyara mata shi zaunawa tay tana ta yan kalle kalle ta hango jakar kayanta a gaban drawer d'in gadon ta tashi ta d'aukko ta a gefen gadon ta d'aurata ta bud'e, hannu ta kai tana d'an d'aga kayan kafin ta fiddo wata doguwar rigar material ta aje gefe ta ciro pant da pad data gani suma ta aje tunanin ko ta koma toilet tasa kayan ta shiga yi wata zuciyar ta raya mata tunda ita kadae ce ta sa anan mana k'ilan har ta gama bai shigo ba, yin wannan tunanin yasa da sauri ta bud'e pad d'in ta ciro wadda zatai amfani da ita tasa a jikin pant d'in bayan ta gama ta saukko daga saman gadon ta zura pant d'in tana kokarin sanyawa taji an turo kopar aikuwa da sauri ta d'ago ta kalli kopar ba tare da ta ankare ba kuma towel d'in ya kwance Saboda d'agowar da tayi ba shiri nan take boobs d'in ta suka bayyana duk ta dabarbarce don kuwa idon shi na akanta ganin haka yasa da sauri ya koma yaja mata kopar, ta d'ago da towel d'in da sauri had'i da dafe k'irji tana kallon kopar kafin a kasalance ta duk'a taci gaba da sakawa bayan ta gama ta zura doguwar rigar ta fiddo hula ta saka ta zuge jakar har ta koma ta zauna sai kuma ta mik'e ta d'auki towel d'in da ledar da ta ciro pad da yan takardun ta nufi toilet da ganin yadda take tafiyar jikinta sam ba kwari, bayan ta dawo still bai shigo ba ta koma bakin gadon ta zauna tana facing kopar tama rasa tunanin da zatayi tay zuru sai kikkafta ido take tana haka ya turo kopar da yar sallama ya shigo suka had'a ido a hankali ta amsa kafin ta maida idonta k'asa da sauri ta fara d'an wasa da yatsun ta, wurin gadon ya nufa a saman yar drawer d'in gefe ya d'aura ledar drugs d'in ya juyo ya d'an kalle ta kan ta a k'asa kaman yana son cewa wani abu ji tay a jikinta ita yake kallo ta d'an d'ago a hankali suka had'a ido taji yace "How are u feeling?" a sanyaye tace "Alhamdulillah da Sauk'i" shiru bai ce komae ba can taji yace "are u done with this?" jin tambayar yasa ta kai idon ta kan jakar kayan da ke gefen ta kafin ta kalle shi ta d'aga kai alamar eh ta gama amfani da ita hannu ya kai ya d'auke ta ya maida ita inda take da, duk'awa yay wurin kayan Abincin ya d'auki plate da spoon sai bottle water ya mik'e ya nufi window d'in d'akin bayan ya zuge net d'in jiki ya fara d'auraye su Fatuu nata kallon shi har ya gama ya rufe ruwan tana ganin zai juyo ta maida idonta k'asa ya dawo ya tsugunna gaban basket d'in Warmers masu d'auke da abincin ya fara bud'ewa, Faten dankalin ya zuba ya saka spoon d'in kafin ya mik'e ya kai mata ta mik'a hannu ta amsa nan ma saida ta furta mashi ta gode bai ce komae ba ya juya tabi shi da kallo, rufe warmer d'in yay ya koma kan kujerar ya zauna had'i da jingina bayan shi ya d'an d'age kan shi, gaba d'aya jikinta ya mutu Saboda canjin da ta gani a tattare da shi da k'yar ta d'auki spoon d'in ta fara ci duk yadda Abincin yay mata kyau a fuska sam ta kasa jin dad'in shi a baki hakanan dae take ci kad'an kad'an saida taci kaman rabi sannan ta tashi zata maida wurin kayan Abincin lokacin ya sauke fuskar idanun shi suka sauka a kan ta wani kallo ya jefa mata ta sadda kanta k'asa cike da bada umarni taji yace mata ta cinye shi duka d'agowa tay ta kalle shi still kallon dae yake mata jiki a sa6ule ta koma ta zauna don sai taga kaman ma hararar ta yake, ba yadda ta iya haka ta dingi turawa ba don tana jin dad'in shi ba har ta samu ta cinye tana niyyar mik'ewa taga ya taso yazo gabanta, amsar plate d'in yay ya maida ya k'ara d'aukar wani yaje ya wanko shi bayan ya dawo ya zuba mata farfesun yan cikin shima ya mik'a mata ta amsa yanzu bata ce mashi ta goden ba saidae ta d'an kalle shi, bayan ya juya plate d'in da ta 6ata ya d'aukka yaje ya wanko shi ya maido, kujerar ya koma ya zauna ya k'ara d'age kan kaman d'azu, sosae farfesun yay mata dad'i saidae damuwa ta hana taci shi sosae don gani take kaman dai da gaske fushin yake, bayan ta d'an sha kawai sai ta aje spoon d'in tsam ta mik'e zata aje shima sai gashi ya sake juyowa ya kalleta nan take tay pause tana kallon shi fuska a yamutse daga inda yake taji yace "Eat it up!" d'an yamutsa fuska tay cikin rawar murya tace "na k'oshi" shiru bai ce komae ba idon shi akanta itama ta kasa motsawa balle ta aje can ya mik'e ya nufo ta yazo daga gabanta ya tsaya suna facing juna abu ta rink'a had'iya ta sak'a d'ayan hannun da bada shi ta ruk'e plate d'in ba gefen wuyanta tana d'an sosa wurin kasa jure kallon shi tay ta maida idon t k'asa, hannu taga ya mik'o ya amshi plate d'in ta kalle shi da kai yay mata alamar ta zauna ta koma gefen gadon kawae sai gani tay shima ya zauna a gefenta ya fara d'ibowa zai bata ta yamutsa fuska idanunta har sun ciko tace mashi ta k'oshi wani kallo ya wurga mata ba shiri ta bud'e bakin ya zuba mata ta fara taunawa tana kikkafta ido, haka yaci gaba da bata har ta dai ta saki Fuska taci gaba da ci tana yi tana satar kallon shi wani lokacin su had'a ido sai tay saurin janye idon ga k'amshin shi da ya gama cikata, saida ta cinye shi duka sannan ya mik'e ya maida plate d'in ya d'aukko mata ruwa bayan ya bud'e mata ya mik'a mata ta amsa tasha da d'an yawa sannan ta cire robar daga bakinta ta mik'a mashi ya amsa ya rufe, ledar fruit ya bud'e suma ya zuba a plate d'in ya mik'a mata k'in amsa tay ya wani d'aure fuska kawae sai ta saka mashi kuka still yay yana kallon ta komi yay mata na kuka shida ko tanka mata bai yi ba cike da shagwa6a duk da ita ba da niyyar shagwabar take yi ba nature d'in ta ne haka taci gaba da yamutsa fuska tana d'an ta6e baki kalan yadda take kuka tun yarinta tana ta faman kikkafta ido kwalla na gangaro mata shi dai kallon ta kawai yake ga abu ta barshi dashi a hannu sigh yay ya d'age gira yace mata "na buge ki ne?" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a ya sake cewa "to wannan d'in na miye?" yay mata nuni da k'wallan dake zubawa da ido shiru tay ta sadda kanta k'asa har saida yace ba magana yake mata bane sannan ta d'ago tana d'an share kwallan cikin muryar kuka tace "ba komae" shiru bai ce komae ba sai ya koma gefen ta inda ya tashi ya sake zaunawa ya d'aukko 6ararrar ayaba zai bata tana ta goge kwalla ba tare data kalle shi ba hakan yasa bata san yana mik'o mata ba saida taji yace "FATUU" damm k'irjinta ya buga a ranta ta maimaita sunan daya kira ta dashi don tunda yasan sunanta bai ta6a kiran ta da hakan ba sai yau nan take jikinta yay lakwas tamkar an watsa ma kaza gishiri a sa6ule ta kai idon ta gare shi taga ayabar da yake mik'o mata a hankali ta bud'e baki ta d'an gutsira ta fara taunawa, haka yaci gaba da bata har saida ta shanye komae ya maida plate d'in ya d'aukko ledan magungunan daya aje da ruwa ya sake zaunawa suma ya shiga 6aro mata yana