Showing 282001 words to 285000 words out of 512766 words

Chapter 95 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1653

bashi hak'uri na tashin shi da tayi don tasan in ba bacci yake ba wayar bazata dad'e tana ringing ba batare da ya d'auka ba, ce mata yay ba komai Allah yasa dai lafiya cikin yar rawar murya ta sanar dashi abunda ke faruwa cikin daidaita natsuwa don kada ta tada mashi hankali, salati shima yayi ya tambayi asibitin da suka tafi ta fad'i mashi yadda Lailan tace yace Ok bari ya kira Son d'in, kiran Nameer Laila tayi a tunaninta ko basu kai gida ba don basu dad'e da rabuwa ba, ya tsayar da Motar kenan gaban Entry Hall kiran ya shigo, yana yin picking ta sanar dashi abunda ya faru cike da Al'ajabi ya maimata abunda tace su Fauzy dake niyyar fita daga cikin Motar cak suka tsaya suna sauraren shi, bayan ya gama wayar har suna had'a baki wurin tambayar shi abunda ke faruwa ya sanar masu, gaba d'ayan su razana sukai kar ma Mino taji gaba d'aya ta zaro ido kirjinta na mata wani irin bugu jin Adda Fatuu d'inta ta fad'i, Jidderh ce ta rok'e shi suje Hospital d'in yace Ok duk suka rufe kopopin Motar yaja suka tafi, tuni Mino ta fara kuka tana fad'in Allah yasa Adda Fatuu ba mutuwa tayi ba irin na mamanta, duk da su Fauzy na cikin tashin hankali haka suka shiga rarrashinta harda Nameer yace mata ta kwantar da hankalinta in sha Allah ba abunda zai sameta suyi mata Addu'a duk suka jinjina kai, nan fa Mino ta shiga yin Addu'oin a bayyane suna amsawa da Amin can ta kai hannu cikin jakarta ta fiddo wayarta ta shiga kiran gwaggo, lokacin da kiran ya shiga su gwaggon duk sunyi bacci, saida ya kusa katsewa ta farka lokacin data d'auki wayar kiran ya yanke, ganin mai kiran nata ta ambaci Mino to lafiya kira a wannan lokacin, tana niyyar kira saiga wani kiran ya shigo da sauri ta d'aga tun bata ji mi zata ce ba saida gabanta ya fad'i, cikin kuka ta sanar mata Gwaggon ta saka salati hakan ne ya tada Hajiya ta bud'e ido, bayan gwaggo ta gama wayar Hajiya dake kallonta ta hasken bedside lamps tace "Ya ya Mike faruwa ne miya samu Fateemar ne?" Cikin tashin hankali Gwaggo ta sanar mata ai ba shiri ta idasa tashi zaune, hannu ta kai ta d'aukko wayarta ta shiga kiran Haisam lokacin da kiran ya shigo mashi ya kife fuskar shi data Fatuu idanun shi a rufe sai Addu'oi yake mata, yana jin wayar na ringing amman a halin da yake ciki bai jin zai iya d'aukar waya, k'in d'aga wayar da yayi ya k'ara tada ma Hajiya da gwaggo dake kallon ta hankali, kiran layin Senator tayi tana fara yin ringing ya d'aga Hajiya tace mashi yaji abunda ke faruwa yace eh gashi nan ma zasu je Asibitin tace to bari su fito yace a'a ta yi baccinta in sha Allah ba abunda zai faru tace "taya wani bacci zai yuwu hankula duk sun tashi kaga uwar ta nan cikin tashin hankali gara dai muje da mu zauna zaman jiran tsammani" amsa mata yay da to,

Gaba d'aya Haisam ya rasa inda zai tsoma ran shi, fargaba ta cika shi zuciyar shi sai raya mashi abubuwa take, bawan Allah in ta raya mashi wani abun sai ya girgiza kai da sauri ya k'ara k'ank'ame Fatun, wani iri yake jin zuciyar shi gaba d'aya rayuwar shi da ita sai dawo mashi take ba abunda yake gani sai fuskar ta d'auke da Murmushinta mai burgewa, "ko dai dama Allah bai yi zaku rayu tare tsawon lokaci ba" zuciyar shi ce ke raya mashi hakan da sauri ya hau girgiza kai kawai sai jin kwalla yay suna zubo mashi bai ko yi yunkurin gogewa ba, gaba d'aya gani yake tafiyar tayi tsawo har saida yayi ma Na'eem magana yace sun kusa, bada jimawa ba suka k'araso Asibitin a Jere motocin nasu suka shigo cikin harabar, Laila ko inda aka tanada don parking motoci bata k'arasa ba ta parker Motar, da sauri ta bud'e k'opar ta fito lokacin cikin security guards d'in dake bakin gate da ya biyo bayan Motocinsu yace mata pls ta gyara fakin ba'a yi anan bata ko kalleshi ba ta furta mashi it's an emergency daga haka ta nufi cikin Asibitin ko rufe Motar ma bata yi ba, Na'eem na fakawa da sauri Haisam ya kai hannu ya bud'e kopar ya fara k'ok'arin fitowa da ita Na'eem ya zo wurin ya taimaka mashi su Najeeb ma da sauri suka k'araso, yana d'auke da ita suka nufi cikin Asibitin a bakin main entrance suka had'e da Laila ta taho da nurses sun turo gado, d'aurata akai nurses d'in suka turata ciki suma suka rufa masu baya, Amenity suka nufa da ita Lokacin Doctor da wata nurse taje tayi ma magana ya nufo su, yana zuwa wurin ya gaidasu su Abbas ne suka amsa mashi ya shiga tambayar su abunda ya faru da ita suna tafiya suke bashi amsa, bayan sun iso aka shiga da ita d'aki Dr yace su jira shi ya shige,

Shiru shiru tun bayan da likita ya shige bai fito ba sai nurses dake ta shige da fice cikin d'akin, can bayan kaman minti goma sai gashi ya fito nurse na biye dashi d'auke da sample na jini da gani na Fatun ne, tarar shi su Najeeb sukai suna tambayar ya ake ciki shi Haisam ido kawai ya bishi da shi don zuciyar shi tuni ta karye, ce masu yay in sha Allah she will be alright su d'an jira kad'an suna kan binciken dalilin sumar nata ne don da ran ta in sha Allah, har saida su Najeeb d'in sukai d'an murmushi tare da jinjina mashi kai ya wuce nurse d'in ta bi bayan shi, kallon Haisam daya jingina da bango Abbas yay fuskar shi tayi jajir haka idanun shi, dafa Shoulder d'in shi yay yace ya kwantar da hankalin shi in sha Allah ba wata babbar matsala bace da alama haka take suman ta don da ta yi miscarriage ma ai ta dad'e bata farfad'o ba duk da shi harda firgici yanzu kuma k'ilan gajiya ce tayi yawa,

Na'eem ne ya matso shima yace "ni ina ma tunanin k'ilan harda smoke d'in nan duk da ance baida illa amman kasan kowa da kalan yadda jikin shi ke karbar bak'on abu" jinjina kai sukai cike da gamsuwa ba laifi Haisam d'in ya d'an ji fargabar shi ta ragu, after some minutes Likitan ya dawo saida ya d'an d'aga masu hannu sannan ya tura k'opar d'akin ya shige, su Nameer ne suka k'araso bayan Laila ta yi masu kwatancen inda Asibitin yake, gaida su Abbas sukai Mino dai ta kasa cewa komai sai bin su da ido take Fuskar ta sharkaf da hawaye Abbas ne ya shiga kwantar mata da hankali tana jinjina mashi kai, bada jimawa ba Laila ta dawo wurin tare dasu Dad da Mom sai Hajiya da gwaggo, gaidasu su Najeeb suka shiga yi gwaggo dai kai kawai take d'agawa don hankalinta in yayi dubu to ya tashi gaba d'aya jinin ta akan akaifa yake, Dad ne ya tambayi ya ake ciki Abbas ya fad'i mashi bayanin da likitan yayi yace "Ok sai mu jira shi Allah yasa muji Alkhairi" duk suka amsa da Amin, kallon Haisam yay da tunda suka zo bai tanka ma su ba sai ido kawae yake bin su dashi, ganin yanayin fuskar shi yasa shi kai hannu ya dafa Shoulder d'in shi da d'an murmushi yace "Don't worry Son, she will be fine in sha Allah muyi mata Addu'a" jinjina mashi kai yay Dad d'in ya kai hannu ya fara k'ok'arin cire mashi babban rigar yana fad'in bari a cire yasha iska don duk yayi zufa duk da yanayin wurin ba zafi, bayan d'an lokaci da zuwan su Hajiya tace ko dai a yi ma likitan magana aji halin da ake ciki an bar mutane da zullumi Gwaggo tace mata in ba ya gama binciken ba ba abunda zai iya fad'i tunda bai samu sakamako ba Hajiyar ta d'aga kai, Senator ne ya nuna masu waiting seat yace ma su Hajiya su zauna, Mino ma da duk hankalinta a tashe yake yace mata ta zauna ta d'aga mashi kai, basu jima sosae da zuwa ba Doctor d'in ya fito da sauri su Mom suka mik'e haka Hajiya ma da gwaggo, yana ganin Dad ya d'an sunkuyar da kai ya gaishe dashi bayan ya amsa yace ashe patient d'in su ce yace eh matar d'an shi ce, jinjina kai Doctor yay ya d'an yi shiru with confusion on his face Hajiya tace "Dr kai muke saurare, mi binciken naku ya gano yayi silar fad'uwar ta" nannauyar ajiyar zuciya yay idon shi akanta yace "pls zan iya ganin wani daga cikin danginta?" kan kowa ne ya d'aure duk suka zuba mashi ido, Dad ne yay saurin cewa "da wani abu ne?" d'an girgiza kai yay yace "No, kada ku damu yalla6ai inaso zamu d'an yi wata magana ne da d'aya daga cikin danginta wanda suke da kusanci sosae" kwa6e fuska Hajiya tayi tace "to ai nan duk danginta ne tunda alak'ar Aure ta shiga tsakani ai duk an zama d'aya, in ma mafi kusancinta ne ai Mijinta ne gashi sai kuyi Maganar" ajiyar zuciya doctor ya k'ara yi ya kai hannu ya gyara zaman glass d'in shi gaba d'aya jikin kowa yayi sanyi don sun fahimci bai son fad'i masu halin da ake ciki, sosae Doctor ya shiga rud'ani kawai sai ya yanke ya sanar da Mijinta abunda suka gano k'ilan shi yana da masaniya kan ciwon nata, tambayar ina Mijinta yay aka nuna mashi Haisam yace "pls let me see you in my Office" mik'a ma Abbas rigar shi yay wani irin Fad'uwa gaban shi ke yi ya juyo yay ma Dr alamar suje da hannu,

"Shin wai Fateemar ko juna biyu ne da ita??" har likitan ya juya Hajiya ta furta hakan da sauri ya juyo ya kalleta, komawa yay wurinta a d'an fad'ace tace ya fad'i masu abunda ke faruwa duk miye na wani 6oye 6oye, d'an gyaran murya yay ya fara kora mata bayanin cewa abunda suka gano shine stress ne yay mata yawa ta yuwu tayi zurga zurga da yawa ta gaji sosae hakan yasa ta suma sai dai kuma abunda ya assasa suman nata shine sun gano tana d'auke da juna biyu na tsawon wata guda, ai tun kafin ya rufe baki suka hau washe baki su Jidderh da Mino harda sakin k'arar murna gwaggo ma bakinta a washe yake haka Mom dasu Abbas kowa ka gani sai washe bakin murna yake Senator ma fuskar shi d'auke da fara'a yanata fad'in Alhamdulillah nan aka kama anata fad'in Alhamdulillah, bawan Allah ango ai shi gaba d'aya ma ya kasa magana sai murmushi yake kawai sai gani akai ya duk'a yayi sujjadar godiya ga Allah duk aka kalle shi kowa fuskar shi da fara'a, bayan ya mik'e Senator ya dafa Shoulder d'inshi yace "Hankali sai ya kwanta ko Son" kawae sai Haisam d'in ya fad'a jikin shi Dad d'in yasa hannu ya rungume shi anata dariya shima Haisam d'in dariyar farinciki yake don kwata kwata ba abunda yake zato ba Kenan, sosae hakan da suke ya ba Dr mamaki har Fuskar shi ta kasa 6oyewa Dad ne da ya lura still Haisam na jikinshi yace ma likitan kada ya damu ba sabon Aure bane an kwana biyu da yi kawae yanzu ne ake shagalin bikin, wata ajiyar zuciyar samun relieve Dr d'in yayi don da he was completely confused ace ana cikin shagalin biki kuma ga Amarya da ciki hakan ba K'aramin Al'amari bane, shima sai ya shiga taya su murnar yanata murmushi,

D'ago Haisam Dad yay suka had'a ido ya d'an bud'a ido yace "Son da alama ma har kuka kayi ko, halan kana tsoron kada Amarya ta tafi ana tsaka da shan Amarci ne" Yar dariya Haisam d'in yay sauran ma duk aka sa dariya, hannu ya kai suka gaisa ya furta "Congratulations my man, soon you will become a Father" cikin cool voice d'in shi ya furta mashi "Thank you Dad" Laila ce itama ta matso tana washe baki ta taya shi murna yay mata side hug ya amsa Jidderh ma ta matso tana washe baki tace "Congrats bro" jinjina mata kai yayi haka ma su Fauzy duk suka matso suna taya shi murna Nameer ma wurin shi yazo yana murmushi ya rungume shi yana taya shi murna, Abbas na tsaye tare da su Najeeb suma duk farinciki ne akan fuskokin su don ba K'aramin tashi hankulan su sukai ba, Abbas na dariya idon shi akan Najeeb da yake yasan da zancen wanccan cikin ya furta mashi "gaskiya Mom Zarah Sharp shooter ce ta gaske kaga fa har ta maida wani" kafin Najeeb d'in yace wani abu kaman daga sama suka ji ance "Shi kuma abokin naku jarababbe ko" gaba d'aya waro ido sukai suka sauke su akan Hajiya data yi Maganar kuma ko kallon su bata yi ba gwaggo dake gefenta sadda kai tay cike da jin kunya, gumtse dariya su Abbas d'in sukai ba wanda yace wani abu, Hajiya ce tace ma likitan zasu iya shiga su ganta da sauri yay mata alama da hannu ya furta "Yes you can" nufar d'akin sukai gaba d'aya harda Mom da Dad da gwaggo dasu Fauzy, su Haisam d'in suka tsaya jiran su gama shiga Najeeb da Na'eem suka matso wurin shi suna taya shi murna, Abbas na zuwa ya kamo hannun shi guda yay mashi side hug yace "Mom Zarah ta biya mu bashi da wuri kuma da alama dai a G.r.a d'in aka sake samo mana" washe baki Haisam d'in yay wanda shi rabon da yayi irin dariyar ma ya manta, tabbas a yadda aka fad'i lokacin shi da alama a G.r.a d'in ta same shi nan ya gane k'ilan harda shi yasa ta jin jiri da suka sauka Abuja Allah yasa ma bata samu wata matsala ba, daga baya suka shiga cikin d'akin, duk a tsattsaye suka iske su an zagaye gadon da take kwance har lokacin head dinta na a saman kanta fuskar ta sanye da Oxygen mask haka hannunta guda na sanye da drip, Addu'oin Allah ya bata lafiya aka shiga yi daga baya Doctor yace masu akwae buk'atar a d'aura ta kan Bed rest don akwai chance na zata iya miscarrying cikin in ta cika zirga zirga dole ta samu hutu sosae har ya zauna duk aka jinjina kai, Dad ne yace yakamata su tafi don dare yayi sosae sai wasu su tsaya, Aunty Laila ce tace a barta Hajiya tace a'a shi Mijin nata ya tsaya gwaggo dake murmushi tace a'a abar shi yaje ya huta ai an sha hidima Abbas yace kada shima ya fad'i duk aka sa dariya, shi da za'a barshin ma daya fi son hakan don zai so ace yana a kusa da ita ta farka, sallama Dad yayi masu ya juya Mom ma haka Nameer yayi ma su Mino magana suma suka tafi Fauzy sai faman sakin murmushi take ji take inama tana nan Fatun zata farka, kallon gwaggo Hajiya tayi tace suje ko tana d'an murmushi tace ba komai Laila taje don itama tasha hidima da yawa ita ta zauna, murmushi Hajiya tayi tace kawai dai K'aunar ta motsa bata son barin autar tata, kunya ce ta kama gwaggo tay yar dariya Hajiya tace ma Laila d'in suje kawai, har zasu juya Hajiya ta dakata tana kallon gwaggo tace bari suje sai a kawo mata abun shimfid'a da na lullu6a an taho hankali ba kwance ba, da sauri tace a'a tunda ga Hijab d'inta kuma doguwa ce lafiya lau zata yi mata ba sai an kawo komai ba abari sai zuwa gobe tunda ma dare yayi sosae tace to Shikenan suka juya suka tafi,

Bayan fitowar su ganin Laila yasa Mom tambayar ya akai ta taho Hajiya ta fad'i masu yadda sukai da gwaggon Dad yace amman dai Laila din yakamata ta kwana Hajiyar tace mashi su je kawae ko gwaggon ta koma gidan ba bacci zata iya yi ba yar lelen ta na kwance a gadon Asibiti, yar dariya Dad yay yace ai ba ita kad'ai ce yau bazata iya yin baccin ba tana da d'an uwa yay Maganar idon shi akan Haisam duk akayi dariya, sallama su Najeeb da Na'eem sukai masu don wucewa zasu yi duk akayi masu godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci sukai ma Haisam Allah ya bata lafiya shima yayi masu godiya bayan sun shige Motocin su Senator yace ma Haisam suje shida Abbas su samo masu Abinci don tana iya tashi da yunwa yace Ok, a tare duk suka shiga cikin Motoci suka tafi.

Lokacin da suka isa gidan tuni wanda suke cikin gidan sunyi nisa a baccin su, a gaban Entry Hall duk suka parker Motocin aka firfito, bayan sun shiga main parlor anan sukai ma juna sai da Safe Senator ya nufi part d'in shi haka ma Mom da Hajiya da Laila, Fauzy tare da Mino suka nufi hanyar baya har sun d'an yi nisa Nameer dake tsaye yana jiran su Mom d'in shi su shige ya kira sunan ta, juyowa tay yayi mata alamar ta zo ta juyo ta nufo shi, daga gaban shi ta tsaya suka sakar ma juna murmushi yace "Hankali ya kwanta ko Adda d'inki bata mutu ba" dariya tayi tasa hannu ta rufe fuska kafin ta cire, wani irin kallon love yake mata sai murmushi take a hankali ya furta "in muka yi aure I don't want you to get pregnant da wuri sai mun gama shan love sosae tukun" da sauri ta kai hannu ta rufe fuskarta ta juyar da fuskar wata irin kunya ce ta kama ta, ce mata yay miye abun wani kunya tunda auren zasu yi kuma ma bai son a d'auki time don ya yanke zai sanar da Hajiya sai ayi magana da parents d'in ta kafin su tafi, jin haka yasa ta juyo a sanyaye

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login