Showing 510001 words to 512766 words out of 512766 words

Chapter 171 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1574

don Haisam ya bashi kuɗi masu yawa Fatuu ma ta ƙara mashi an gyara part ɗin nasu ya koma babban Flat saida aka ƙara faɗaɗa shi, sauran bangarorin ma anyi gyare gyare don yanzu gaba ɗayan tsakar gidan siminti ne ko ina sannan an zagaye gidan da katangar bulon siminti haka gaban gidan ma ya koma irin na yan birni harda gate, fadar da Baffa ke zama itama ta koma irin ta zamani, bayan sun zauna anyi gaishe gaishe shiru Yaya tayi ta rasa ta ina zata fara sai Mairo ce ta fara magana tace mashi dama Yaya ce tazo neman yafiya a wurinshi kan abubuwan da suka faru a baya ta juya kan Yaya tace tayi magana, cikin karyayyar murya ta shiga roƙonshi akan abubuwan data yi masu a baya ta bayyana mashi ta zalunci mahaifiyarshi don ita tayi mata asiri duk gidan aka tsaneta harda arɗo wannan ne yay silar ta kamu da ciwon zuciya har ta mutu haka shima tay ta zaluntar shi bayan rasuwarta ganin arɗo ya damu dashi shima tayi mashi asiri ya daina ji da shi sai bayan daya girma ne da yake shi mai yawan ibada ne sosae sai ya zama ko tayi asirin bai kamashi hakan yasa soyyyarshi ta dawo ma arɗo sai kuma ta rinƙa yi mashi makirci haka iyalinshi ma ta ɗauki karan tsana ta ɗaura masu, shiru Baffa yayi kan shi a ƙasa yayinda ƙwaƙwalwarshi ta shiga dawo mashi da lokacin don bazai ta6a mantawa da irin rayuwar ƙuncin da mahaifiyarshi tayi ba a gidan lokacin yanada ƙuruciya har zuwa mutuwarta lokacin haka ya rinƙa kuka yana roƙon shima Allah yasa ya mutu ya bita, kawai saboda yana da haƙuri sosae da kuma kawaici irin na fulani yasa bai nuna masu komai amman ba wai don ya manta ba, saukkowa Yaya tayi kan carpet ta duƙa cikin kuka ta shiga bashi haƙuri tana mashi magiyar ya yafe mata, Mairo ce da idanunta suka ciko da ƙwalla cikin kwantar da murya ta shiga roƙonshi ya yafe mata Don Allah duk irin abunda tayi mashi gashi nan bai hana rayuwarshi yin albarka ba ƙarshe ma gaba ɗayansu sun koma karkashin kulawarshi yayi koyi da mai sunan shi wato manzon Allah (S.A.W) wanda haƙuri da yafiya halin shi ne, ɗagowa yay idanunshi sun yi ja sun cika da ƙwalla cikin karyayyar murya yace shikenan ya yafe mata sai taita istigfari ta roƙi Allah ya yafe mata abunda tayi ma Mahaifiyar shi, godiya sosae ta shiga yi mashi fuska jage jage harda su majina ta shiga yi ma Mahaifiyar tashi Addu'o'i a hankali yake amsawa daga baya suka tafi, bayan tafiyarsu kuka sosae ya shiga yi yana tunawa da mahaifiyarshi tare da yi mata Addu'a, bayan Yaya ta koma ɗaki saida ta kira Fatuu a waya itama ta roƙeta yafiya kan abubuwan da tayi mata na tsanarta da tayi tana murmushi tace mata ba komai ai ya riga ya wuce ta yafe mata taita mata godiya da Addu'oi, sai lokacin Yaya taji hankalinta ya ɗan kwanta da tafiya Hajjin da zatayi tun daga ranar kullum da cazhaba zaka ganta tana ta istigfari.

Ta dalilin Fatuu yanzu yan ƙauyansu suna karatun boko sosae, a gidansu ma an daina yi ma mata auren wuri sai sunyi boko har Abuja yan'uwan nasu suke zuwa hutu wurinsu inda rabo ƙilan wasu su ƙara samun mazaje a can. A can Katsina yanzu Foundation ɗin su Fatuu ya ha6aka sosae anata taimakon mutane yanzu a unguwarsu Gwaggo ita ta koma matsayin Hajiyar Sanata sosae take taimakon Makwabtanta, rayuwa dai ta inganta ga dukkan bangarorin. Ta dalilin Addu'oin da wanda Haisam ke kaiwa Hajji ke mashi sosae hakan yake ƙara ha6aka arzukin shi wanda yanzu shi kanshi Haisam ɗin bai sai iya adadin dukiyarshi ba har gida ya gina ma Abbas ya kuma kaishi Makka harda Feenah sannan ya ɗauki nauyin karatun Abdul wanda yanzu ya girma, a bangaren Aunty Mareeya itama Sameer ya gina masu babban gida har sun koma kuma duk sunje Hajji suma. Bayan wani lokaci Haisam yasa aka fara gina ma su Fatuu Asibiti anan Abuja wato private Hospital ita da Fanan wanda aka yanke saka mashi HAIFAT SPECIALISTS HOSPITAL sai fatan Allah yasa a gama lafiya a kuma buɗeshi lafiya yasa kuma mutane su amfana, Amin.


Fatuu zaune a gaban madubi da daddare tana yin shafa bayan ta fito daga wanka yayin da Haisam ke zaune a saman gadonta ya ɗaura Laptop a saman table ɗin gaban gado yana daddanawa da alama wani aikin yake jikinshi sanye da robe haka idanunshi na sanye cikin glass ya ƙara manyanta saidai duk da haka ba sosae jikinshi ya nuna ba saboda har yanzu yana motsa jiki sosae, kamar an jefo Esha ta faɗo cikin ɗakin tana ƙwala ma Fatuu kira tana faɗin "Auntyyy!" itama yanzu ta ƙara girma don tana shekara ta sha huɗu duk da bata da tsawo sosae sak irin jikin Fatuu tana yarinya gareta,

"Esha! Wai sai yaushe zaki hankali ne, didn't i warn you to always say salaam before entering into a place???" a fusace Fatuu tay mata Maganar ta ɗaure fuska, tura baki Esha ɗin tayi tana ɗan murmushi tare da noƙe kai tace "to Sorry Aunty mantawa nike bari inje inyi salaam ɗin" tayi maganar tare da juyawa ta nufi kopa, bayan ta fita daddagewa tayi ta kwaɗa wata uwar sallama har saida Haisam ya ɗan yamutsa fuska Fatuu kuma ta girgiza kai kafin tace wani abu Esha ɗin ta ƙara kware baki ta rafko wato sallamar tare da faɗin "Aunty in shigo???" ba arzuƙi gudun ta sake yin wata da sauri Fatun tace mata ta shigo, shigowa tayi tana dariya Fatuu ta wurga mata harara, bayan tazo gabanta tace mata miya kawota ɗakinta yanzu cikin zazzaƙar muryarta tace "Momy ce tace ki bata charger ɗin phone en ki in baki using dashi mun shanye mata caji zata saka nata ya ƙiya kafin tomorrow Dad ya kawo mata wani" yadda kasan abun faɗa yadda tayi Maganar, maida kanta tayi kan madubi tana cigaba da shafar ta tace mata gata can jikin socket wurin bedside drawer taje ta ɗauka, maimakon taje ta ɗaukan sai ta tsaya tana kallon fuskar Fatun ta cikin madubi tana wani murmushi tace "Aunty Daddy kike ma makeup?" dakatawa Fatuu tay ta watsa mata harara, dariya Esha ɗin tayi tace "ai nasan Dad kike mawa don ke Babynshi ce....." tsawa Fatun ta daka mata "Esha! Will you go and take the charger ko zaki tsaya kina surutun banza ne!!" da sauri ta wuce tana dariya, tana zuwa saitin Haisam ta furta "My lovely Dad" dagowa yay ya kalleta yay mata murmushi tare da miƙa mata hannu suka kashe yace taje ta ɗauki charger din ana jiranta tace to, bayan ta ɗauko cazar ta nufi hanyar fita, har ta kusa fita ta tsaya da ƙarfi ta furta "Babyn Daddy kin yi kyau...." robar mai Fatuu ta wawuro Esha na ganin haka ta fice da gudu tana dariya, tsoki Fatuu tayi tare da girgiza kai idonta akan madubi ta furta "i think Aisha needs to see a psychiatrist gaskiya" murmushi Haisam yay ba tare daya kalleta ba can idonshi akan screen ɗin kwamfuta yace mata saboda mi, juyawa tay da sauri ta kalleshi tace "baka ga yadda take behaving abnormal bane, wataƙil in aka kaita aka binciki ƙwalwarta aga tana da problem",

"An yi maki hakan ne?" Haisam daya ɗago yana kallonta ya furta, da alamun rashin fahimta tace to ita akan mi za'a kaita wurin likitan kwakwalwa, yana murmushi yace saboda da tana kamarta itama tana buƙatar hakan amman ba'a kaita ba to don haka itama ba sai an kaita ba zata bari ne kuma in ma tana tunanin tana da matsalar kwakwalwa to ita tata matsalar da tana yarinya ta linka tata tunda ita Esha har yanzu bata fasa ma wani glass ɗin Mota ba, waro ido Fatuu tay jin abunda yace ta bishi da kallon mamaki bakinta a ɗan buɗe shi kuma sai murmushi yake, da alamun mamaki ta furta "kana son kace nayi hauka lokacin?" ɗan ƙanƙance ido yay cike da tsokana ya furta kusan hakane, ƙara zaro ido tay ya shiga yi mata faffaɗan murmushi can ta miƙe a fusace ta nufe shi, lokacin data tashi har saida alƙalamina ya kusa su6ucewa ganin irin haɗaɗɗar rigar baccin dake jikinta gaba ɗaya ta fito da dirinta na babbar mace yar 30s tana tafiya ko ina na jikinta na amsawa abun saidai ace tubarkalla, tana zuwa gaba ɗaya ta faɗa jikinshi har saida yay ɗan sautin zafi batai wata wata ba ta hau bugunshi saidai bugun yafi kama da a kirashi dana soyayya, haƙuri ya fara bata yanata dariya har haƙuranshi sun bayyana cike da shagwa6a data riga ta zame mata jiki ta shiga faɗin Allah bata yin haƙurin tunda ya kirata da mahaukaciya yana ta dariya yace shifa bai ce mata haka ba itace ta kira kanta da haka, cigaba da bugun nashi tayi tana faɗin ai haka yake nufi ko yace to tayi haƙuri taga ƙopa a buɗe take amman taƙi bari aikuwa ya nuna mata ƙarfi ya burkice da ita ta yadda ko ƙwaƙkwaran motsi bata iya yi, ɗaure mata fuska yay yace tunda abun yar haka ce ya bata haƙuri taƙi to shima ya warware yarjejeniyar dake tsakaninsu ta glass, tana ɗan nishin nauyi tayi murmushi tace ai yanzu ba wannan yarjejeniyar tunda tayi abunda yace a lokacin, fuskarshi a daure yace shi ba ruwan shi sai ta biya shi, ɗage mashi gira tayi tace in don dai miliyan goma yanzun nan zata biya shi ya ɗaga ta, girgiza mata kai yay yace ba kuɗi yake so ba ta kanne mashi ido tace to mi yake so, ce mata yay yara zata haifa mashi yawan hakan yanzu tayi biyar saura biyar kuma a lokaci ɗaya yake son ta haiho mashi yan biyar, bata san lokacin data ƙyalƙyace da dariya ba tace kawai yace mata ya gaji da ita so yake ta mutu in ba haka ba taya zata haifi yara har biyar, still fuskar shi a ɗaure take yace ai ana haihuwan har ma fin hakan tana dariya tace ta sani amman ita dai bata iyawa yayi haƙuri yace bazai yi ba sai ta ƙara mashi yara biyar lokaci guda, lumshe mashi ido tay tace yafi ƙarfin hakan a wurinta don haka indai ya bata yara biyar ɗin to zatayi ƙoƙari ta haifa mashi, jin abunda tace yasashi sakin murmushi itama shi take mashi ya mirgina gefenta suka shiga bin juna da wani irin azababben kallo mai cike da tsagwaron ƙauna can Fatun ta saki yar ajiyar zuciya ta fara magana,

"Thank you Hubby, Thank you for your support and guidance. You didn't just change my life, you became a part of it and loved me unconditionally. You have shown me what true is.Thank you for choosing me to be your life partner. You are truly my best friend and my soulmate, and I couldn't imagine my life without you. Thank you from the bottom of my heart for everything that you have done for me......"

( Nagode Hubby, Nagode da taimakon ka da jagorancinka a gare ni, ba wai kawai ka canza rayuwata ba, ka zama wani bangare a cikinta kuma ka so ni so mara iyaka, ka nuna man mene ne soyayya ta gaskiya. Na gode da za6ata a matsayin abokiyar rayuwarka. Haƙika kai ne babban abokina kuma abokin ruhina sannan bana iya tunanin rayuwa ba
tare da kai ba, Ina mai matuƙar godiya a gareka daga can ƙasan zuciyata akan duk abin da ka yi min....." muryarta ce ta karye hawaye suka shiga gangaro mata, matsar da fuskarshi yay saitin tata ya shiga kissing hawayen kafin can ƙasan maƙoshi yace shima yana godiya a gareta sosae data saka shi yake jin yafi kowane namiji sa'ar mata a duniya, haɗe fuskokinsu yay inhaling each others breathe, ganin yana ƙoƙarin hade lips ɗinsu da sauri ta ankarar dashi ƙopa a buɗe take hakan ya sashi dakatawa, saukkowa yay don yaje ya rufe a lokacin nima naga ya dace na bar masu cikin ɗakin.





*Alhamdulillah!* *Alhamdulillah!!* *Alhamdulillah!!!💃💃💃💃💃💃💃*


*A nan na kawo karshen littafin A Sanadin Makwabtaka wanda na ɗau lokaci ina rubutawa😍*

_Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala, the Most Compassionate, the Most Omnipotent and the Most Omniscient da ya bani ikon kammalawa cikin ƙoshin lpy kamar yadda na fara, to him be all the glory🙏, tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi muhammad(S.A.W) da Ahalinsa da Sahabbansa baki ɗaya😍, Darussan dake ciki Allah ubangiji yasa mu amfana dasu🙏 ya sadar da ladan gareni da mahaifana da zuri'ata, yan'uwana da malamai na, kura kuren ciki ina roƙon Allah ubangiji ya yafe man Alfamar Annabin rahama (S.A.W)🙏_

_Gaisuwar ban girma ga Mahaifiyata Hajiya Rabi'atu Yahaya, she is my first luv and my everything💘,Allah ya ja da rai ya ƙara maki lafiya my sweetheart😘, My beloved Siblings💞waɗanda littafin nan Sadaukarwa ne a garesu, Nafisat, Aisha, Khadija, Maimunatu, Hafsat, Abdul'azeez, Fatima, Maryam, Ameenatu, I luv you so so much, kune ni, in baku bani, I really appreaciate ur Encouragement💪,prayers and all-round support👍, Allah ya kara haɗa kawunanmu ya jiƙan Mahaifinmu, Ameen_


_Gratitude To my Sweetheart😍, who is ever glad at every inch of my progress, I really appreaciate ur Support, Encouragement and prayers, Allah ya bar mu tare ya ƙara daukaka, Amin_.

_Special thanks to My lovely Sis Hafsat Bature Writer Of Abban Sojoji and Kurkukun Ƙaddara na gode da ƙarfafa man Gwuiwa Allah ya baki ikon Kammala naki cikin ƙoshin Lafiya yasa ya amfani al'umma Amin, Abubakar Sadeeq AlQuramy, Uncle Isma'il ina matuƙar godiya a gareku da taimakon da kuka bani Allah ya ƙara taimakon ku a dukkan Al'amuran rayuwar ku🙏, My P.A Munah Bature sannu da ƙokari Allah ya ƙara ma rayuwar ki Albarka ya kawo miji nagari Amin, ina matuƙar godiya agareki😘_

*To My Novel's Fans*

*Ina matuƙar godiya a gareku musamman waɗanda suka saka kuɗin su suka sayi littafin nan ina roƙon Allah ya ƙara arzuƙi yasa ku amfana da littafin, Members Of Comment Section na gode da ƙaunarku da uzurinku a gareni kamar su, Asma'u sani, Asma'u Kebbi, Bajatu, Bahillot, Dr Hamida Gandi, Mrs Mu'utassim, Sofix, Minat Sgy, Shafa Adill, Zeefakhad Collecion, MaryamSalisu, Rababs222, Angel love, A'isha Abdurrahman, Fadeelamande, Queen, Shafar Dauran, Aunty wasee, Amina Sulaiman, Habibty, Aunty Hadiza, Aunty Sa'adatu, Salma Nijar, Fatima Fannami, Hauwaabubakar, First Lady, Maman Amir, Ummulkhairi Nijar, Satheyer, Maman Naeem, Deejarh da sauran waɗanda bansamu na lissafo sunayensu ba, ina sane daku, ina matuƙar godiya a gareku ur comment means a lot to me, bansan da wane kalmomi zanyi amfani wurin gode maku ba, sai dae ince Allah ya barmu tare don ku ɗin kun wuce fans kun zama yan'uwa agareni,*

*Ina Gwanar wata ga tawa💃😍 Jinjina a gareki Hajiya Kubrah (Momy) Mace mai irin halin Hajiyar Sanata, Allah ya ƙaro mana irin ku acikin al'umma, har bansan da wane irin kalmomi zanyi godiya a gareki ba sai dai kawai ince Allah ya ƙara girma da ɗaukaka ya raya maki zuriya ya ƙara danƙon kauna keda Oga yasa afi haka ya kuma sa a gama da Duniyar nan lafiya, ya bar mana zumunci daga nan har Aljanna, Amin ya Hayyu ya Ƙayyum🙏*


*Ban mance da irin gudunmawar da kika bani ba Miss Walida Ɗanwaire Fulanin Yola ina matuƙar Godiya a gareki Allah ya barki da Oga ya raya Baby Maryam, Maman Afra kema ban mance da irin taki gudunmawar ba ina miƙo godiya lodi lodi Allah ya raya zuri'a ya bar ƙauna keda Oga, ya jiƙan Habiba (Ummy), Amin ya Rabbi, haka ban mance da taki gudunmawar ba wato Nabila Yar Gata Fulanin Daura kema Allah ya bar ƙauna keda Oga ya baku zuriya ɗayyiba*



*Allah Ya bar mana zumunci daga nan har Gidan Aljanna, Allah Yabiya maku dukkan buƙatunku, Allah ya baku ikon Yin amfani da darussan dake acikin Labarin nan, Ina matuƙar godiya Da irin haƙurin da kuka yi da kuma uzirin da kukayi mun har Allah ya bani Ikon Kammala Littafin nan, Yanzu gashi komai Ya wuce no more kiran ayi man uzuri, lols😂*

*Littafin nan Ya ƙunshi darussa daban daban Na rayuwa,Ya ilmantar,Ya faɗakar,Ya kuma nishaɗantar, Manyan darussan cikin shi sune Muhimmacin Haƙuri da kuma Taimako wanda gaba ɗaya labarin ya ginu ne akan hakan💃💃💃*

  
*Taku Mai ƙaunarku da zuciya ɗaya, ZAINAB BATURE (Zee Laluh/Oum Imam).*

*Ga mai buƙatar wannan littafin Complete tun daga na ɗaya har zuwa na ukku sai ya tuntu6i ɗaya daga cikin waɗannan lambobin wayar, 09013804524 ko 08169856268.



 



 


  


  






 





  























































































Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login