Showing 201001 words to 204000 words out of 512766 words
Chapter 68 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1608
ce mashi tay ita gaskiya bazata zauna da Zarah matsayin kishiya ba in dai basu rabu ba to ita ta hak'ura da auren kuma yaci Amanarta, jin yayi shiru yasa tace mashi kawai ya tura mata sakin kaman yadda ta turo mashi sak'on, sai da ya nisa sannan ya d'an girgiza mata kai yace tunda Hajiya bata so bazai iya yin hakan ba tasan yadda take a wurin su, hakan ya k'ara 6ata mata rai tana d'an huci tay shiru tana d'an kallon gefe can ta jinjina kai ta kalle shi tace mashi suje Nigeria d'in tare ita zata ma Hajiya Magana shiru yay kawae yana kallonta ganin haka yasa da alamun zargi tace kodai dama shima yana son ta, d'an guntun murmushi yay yace mata kawai bai son a samu matsala ne dalilin hakan cike da tabbaci tace mashi ba wata matsalar da za'a samu tasan Hajiya zata goyi bayan abunda take so tunda dai duk basu son Auren, jinjina mata kai yay yace Shikenan ta tambayi yaushe zasu tafi yace nan da 2 weeks da sauri ta girgiza mashi kai tace mashi gaskiya yayi tsawo cikin satin nan zasu je yace Shikenan, sai gashi ta saki ranta harda d'an murmushi ta fad'a jikin shi cike da shagwaba take cewa an kusa asa zuciyarta tayi bursting yanzu haka da bai cire mata bak'in cikin da take ji ba tasan da wuya bata samu Heart attack ba, shidai murmushi kawai yake can ya d'agata yace suje tayi breakfast tace ya fara mata wanka bata jin dad'in jikinta, bayan an yo wankan ya taimaka mata ta shirya sannan suka fita don yin Breakfast, sai gashi ta sake sosae kamar ba ita ba suka cigaba da gudanar da rayuwar su yadda suka saba.
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:29] +234 901 700 4868: *ASM070*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
........bayan sallar isha gwaggo ta nufi gidan Hajiya, lokacin data isa a parlor ta isketa ta yi mata maraba, ganin tayi tsaye ta nuna mata kujerar gefen ta tace ta zauna mana, bayan ta zauna ta gaishe da ita ta amsa tay mata ya aiki ta tambayeta Amadu kwana biyu bata gan shi ba tace yana nan, shiru sukai gwaggo ta d'an sunkuyar da kanta tama rasa ta ina zata fara, jin shirun nata yayi yawa yasa Hajiya cewa "Ya ya Dije, koda wani abu ne?" kallon ta tayi tay d'an murmushi kawai ba tare data ce komai, lokaci guda Hajiya ta fahimci abunda ya kawota tana murmushi tace mata ko itama Maryam d'in taje ta firgita ta, sai lokacin ta fara magana cikin sanyin murya tace "Hajiya dama zuwa nayi in rok'i Alfarma, don Allah tunda basu son auren ina ganin a hak'ura kawai don hankalin kowa ya kwanta, ban so silar hakan asamu rashin fahimta" d'an murmushi Hajiya tay ta d'an kya6e baki tace "to dawa dawa ye basu san Auren? Duka fa ita kad'ai ce ta nuna k'in amincewa kuma itama ba wani abu yasa ba face kishi da take taya yarta" shiru gwaggo tayi ita dai har cikin ranta tafi son a raba Auran kawae saidae bata iya yin jayayya da Hajiyar, ganin yanayin ta yasa Hajiya cigaba "ki kwantar da hankalin ki Dije ba abunda zai faru sai Alkhairi Fateema kuma tana nan Lafiya kuma ba abunda zai sameta in sha Allah, duk maganganun da taje ta fad'a maki barazana ce kawai ba wani abu ba" gyad'a kai gwaggo tayi tay shiru, can tace ma Hajiyar bari ta tafi tayi mata godiya Hajiya tace ta bari ta ci Abinci tana d'an murmushi tace mata a k'oshe bata jima da ci ba tace to bari a zubo mata ta kaima Amadu tace mashi tunda ya manta da matar ta shi gashi nan tana biko duk suka d'an yi dariya, Saude ta kira ta bata Umarnin zubo ma gwaggo Abinci, bayan ta kawo har zata bata Hajiya tace ta rakata part d'in Fateema ta ganta ko hankalin ta ya k'ara kwanciya ita dai gwaggo murmushi kawai take sukai sallama suka tafi Saude na ruk'e da Warmer d'in Abincin, Fatuu na cikin Bedroom ta fito daga wanka tana shiryawa da kayan bacci don tafiya part d'in Hajiya akai kopa ta nufeta ta bud'e, Saude ta gani sukai ma juna murmushi ta gaida ita tace mata ta zo ga bak'uwa ta kawo mata, d'an jimm Fatuu tay a ranta tana tunanin wace bak'uwa ce don rabonta da wani yazo tun cikin wanccan satin da Haulat tazo har take fad'i mata ta kusa komawa, juyawa tay ta d'aukko hula tasa ta fito, tana zuwa bakin corridor ta d'an wara ido tana son ganin wacece bak'uwar, gwaggo ta hango zaune akan armchair Saude na tsaye gefe aikuwa ta watso da gudu tana zuwa ta fad'a kanta cike da Farinciki take fad'in gwaggo dama ke ce bak'uwar, gaba d'aya dariya suke yi Saude na fad'in Fateema sai kace kin shekara baki ganta ba, ita dai gwaggo sai dariya take, sallama Saude tayi ma gwaggo tace ma Fatuu sai ta shigo ta juya ta nufi kopa, d'ago kai Fatuu tay suna kallon juna ita da gwaggo sai sakin murmushi suke, ganin gwaggon tak'i cewa komai yasa Fatuu tura baki a shagwa6e tace don Allah tayi magana mana, tana dariya tace taya zata yi Magana ta sakar mata nauyi jin haka yasa ta tashi maimakon ta zauna akan d'ayar armchair d'in sai ta haye saman hannun kujerar ta kama hannun gwaggon sai kace zata gudu, tambayar ta tana lafiya tayi tace mata eh sai lokacin ta tuna da bata gaishe da ita ba, shiru suka d'an yi Fatuu ta tambayeta Kawu Amadu tace ta wuto shi a shago yana gaishe da ita, shiru suka k'ara yi Fatuu nata wasi wasin ko ta fad'i mata abunda Hajiya Maryam tazo tayi mata, itama gwaggon tana son ta tambayeta ta rasa ta ina zata fara bata son Fatun ta fahimci taje gida kar ta tashi hankalin ta,
"Daga wurin Hajiya nike, naji tace Mahaifin d'ana Haisam da Hajiya Maryam sun zo har sun koma" yanayin fuskar Fatuu ne ya sauya a hankali tace mata eh, "Yanzu sun san da Maganar auren kenan?" Kai Fatuu ta d'aga tace mata eh, amfani tay da canzawar fuskar Fatun tace mata ya taga Fuskar ta ta sauya ko da matsala ne, shiru tay tana d'an kikkafta ido tana son fad'i mata amman bata son hankalin ta ya tashi gwaggo ta fahimci da wani abu hakan yasa ta kwantar da murya tace inda wani abu ta fad'i mata in ba ita ba wa zata fad'i mawa, labarin abunda ya faru ta bata harda yadda Senator ya kar6eta, Fuskar gwaggon da murmushi tace mata ta kwantar da hankalin ta komai zai daidaita in sha Allahu itama kar ta k'ullace ta tana gudun abunda ka iya faruwa da d'iyarta ne tunda bata san da Maganar ba sai suyi ta Addu'ar Allah ya kawo komai cikin sauk'i, tambayar Fatun tay koda wani abu tace mata a'a ta mik'e Fatuu ma ta saukko tana fad'in don Allah ta bari su tafi tare ta kwana a can ta d'an harareta tace to bari ta d'aukko mayafi su fita tare ta rakata ita kuma ta wuce part d'in Hajiya tace to ta juya da sauri sauri gudu gudu ta nufi hanyar corridor gwaggo ta bita da kallo tana Murmushi.
Bayan sati guda da zuwan su Senator Fatuu na a parlon Hajiya bayan la'asar suna yin kallo tana sanye da riga da skirt na atampa, akai akai Hajiya ke mata magana akan film d'in da suke kallo wani wurin ta bata amsa wani wurin kuma tay dariya kawai don Hajiya bata iya in tana kallo tayi shiru, Sallama akai daga can bakin kopar duk suka juya suka kallo mai sallamar, Kawu Amadu ne daga bayan shi kuma wata ce tana sanye da doguwar rigar Atamfa da Hijab Fatuu na ta son ta gane ko wacece ta kasa don sun d'an masu nisa gashi Kawu Amadu ya d'an kare ta, Hajiya ce ta d'aga murya tace su shigo mana sun yi tsaye sai kace parlon bak'on shi ne ya nufo ciki yana murmushi wadda suka shigo tare na biye dashi, suna zuwa bakin kujerun Fatuu tay zumbur ta mik'e da alamun Al'ajabi idon ta akan wadda yazo da ita, ganin murmushin da take mata yasa da k'arfi ta furta "MINO" dariya minon tayi aikuwa Fatuu ta watsa da gudu tana zuwa ta kankame ta Amadu nata dariya Hajiya ma kallon nasu take ta cikin glasses tana murmushi, zama Kawu Amadu yay ya gaishe da ita ta amsa tace kace da babbar bak'uwa kake tafe yace aikuwa,
"To wai ni ba za'a bari in gaisa da k'awar tawa da ban sani ba sai a hoto" Hajiya tay Maganar idonta akan su Fatuu da suka saki juna suna ta ma juna dariya, kamo hannunta tayi suka nufo wurin Hajiya Mino na niyyar duk'awa ta gaishe da ita Hajiya ta mik'o mata hannu ta kama ta zaunar da ita a gefen ta, cikin hausar ta dake bayyana ita bafullatana ce sosae ta gaishe da Hajiyar tana fara'a ta amsa tay mata an zo lafiya da tambayar sauran yan'uwanta ta amsa Fatuu na tsaye gefe farinciki shimfid'e akan Fuskar tata, Hajiya ce tace mata ta zauna mana sannan ta zauna a kujerar kusa da su,
"Ita Dije wannan shine Fateema ta tafi ga wata Fateemar ta zo" ta fad'a idon ta akan Mino da ke ta washe baki in ka ganta baka ce daga k'auye take ba tsaf tsaf da ita ba irin kwalliyar yan k'auyen nan iya jan baki kawae ta shafa ko jagira batayi ba don tana da gashin gira sosae kaman Fatuu gashi sai d'an k'amshin turare take, "kusan ma tsawon su d'aya da Fateema kawai yanayin jiki ne ba d'aya ba" Hajiya ta fad'a tare da kallon Amadu yana dariya yace eh ita da gani ma sai tafi Fatuu tsawo tace ba shakka, Fatuu dai sai murmushi take saki farinciki fal ranta yar uwa tazo, hannu ta kai ta dafo Shoulder d'in mino ta juya ta kalleta, tambayar ta tayi su Yadikko tace mata zasu zo amman ba yanzu ba sai daga baya Baffa ne dai suka zo tare da shi,
"Kai haba! da Baffa kuka zo yana ina?" ce mata tay yana nan waje, kallon kopar shigowa Fatuu tayi ta nuna ta da yatsa tace bakin kopar nan ta d'aga mata kai alamar eh aikuwa zumbur ta mik'e ta nufi kopar da gudu, Kallon Amadu Hajiya tayi tace ya zai bar Mutum a waje yace mata shine yace ya fad'a tukun a bada izini, dariya Hajiya tay "wannan parlon na mutane har sai an nemi wani izini kaima Amadu ai da ka shigo dashi", ce mashi tayi yaje ya shigo dashi yace to, Fatuu na fita ta ganshi a gefe yana sanye da manyan kaya riga da wando na shadda brown kusan sun saje da kalar fatar shi kanshi sanye da hula saidai karin ta bai fita da kyau ba shima tsaf dashi harda su Agogo anzo gidansu suruki, da sassarfa ta nufe shi tana fad'in sunan shi tana zuwa ta kankame shi sai kace zata shige cikin jikinshi, yana ta dariya yasa hannu guda ya dafa ta, d'agowa tay da tsantsar farinciki tana kallon shi sai washe baki take ta kasa yin Magana shima idon shi na a cikin nata suna ta yi ma juna murmushi, suna haka Amadu ya fito yace mashi ance su shigo yace to, Fatuu na ruk'e dashi tayi mashi side hug suka shiga, suna isa cikin parlon ya fara k'ok'arin duk'awa ya gaishe da Hajiya ta dakatar dashi tace don Allah ga wuri ya zauna sai a gaisa, bayan sun gaisa tayi mashi ya aka baro mutan gidan yana ta murmushi ya amsa, kallon Fatuu dake gefen shi har lokacin tana a jikin shi Hajiya tay tace su Fateema an ga Baba an hana mashi sakat tasa dariya Amadu ya kai hannu alamar zai bugeta yace ta sake shi ya huta ta mak'e mashi kafad'a shi dae sai murmushi yake, godiya Baffan ya shiga yi ma Hajiya kan abubuwan Alkhairi da aketa yi masu da Addu'oi tana murmushi tace mashi ai ba komai an zama d'aya,
kallon Fatuu tay tace "to mage sai a tashi aje a had'a masu Abinci ko" tana dariya ta d'ago a kunyace baffan yace a bashshi sun ci Abinci Hajiya tace eh ai tasan sun ci shima na nan d'in sai aci duka sukai murmushi ta kai hannu ta dafa jikin Mino tace ita ai ta samu k'awa minon nata mata murmushi, cikin parlon ta kawo masu Abincin tare da Aunty Saude da bata san da zuwan nasu ba saida Fatun taje Kitchen take sanar mata, gaisawa tayi dasu tayi masu an zo lafiya, daga baya bayan sun gama cin Abincin suka yi ma Hajiya sallama ta tambayi yaushe Baffan zai koma yace mata gobe in Allah ya kaimu, tambayar Hajiya Fatuu tay wai ta bisu can gidan ta d'an ta6e baki ta girgiza mata kai alamar a'a, marairaice mata tayi tace mata don Allah tayi yar dariya tace taje in ma kwana zata yi ta kwana, zo kaga murna harda d'an tsallen murna. Bayan sun fito ne Fatuu tace ma Baffan suje yaga inda take yace mata ba sai yaje ba ta marairaice mashi ta kama hannun shi guda tana mashi magiya, Amadu ne yace mashi ai ba wani abu suje sannan suka nufi part d'in nasu, sosae yay farincikin ganin inda yar tashi take rayuwa har fuskar shi ta kasa 6oye farinciki nashi, Mino ma sai washe baki take tana fad'in yanzu Adda Fatuu nan gidan ki ne tana ta kalle kalle, matsa mashi Fatuu tay wai yazo yaga sauran wurare ya k'i yace ba sai yaje ba tunda yaga nan Mino ko ai tuni ta nufi ciki.
Bayan sun je can gidan mino tasa Fatuu ta kira mata Abbas tace ashe bata manta dashi ba tace ai suna waya dashi ta wayar yadikko, d'an waro ido Fatuu tay da d'an mamaki tace kodai wani abu ke tsakanin su ne da sauri Minon tace mata a'a wllh kawai yana kira yaji ya suke sai suyi hira wani lokacin har yasa tayi mashi magana da fulatanci har ma yace inta dawo nan zai siya mata waya kuma zata rink'a koya mashi fullanci jinjina kai kawae Fatuu tay, bayan ta kira shi sun gaisa taba Mino wayar ta sanar dashi game da zuwan su da alamun jin dad'i yace mata to yana nan zuwa, da daddare bayan sallar isha yazo a parlor suka zauna aka kira mashi Baffan Fatuu suka gaisa shima yayi mashi godiya sosae da Addu'oi yana ta fad'in ba komai, hira suka shiga yi gaba d'ayan su harda Kawu Amadu da gwaggo da Baffan Fatun Mino dai na a gefen Abbas, abun gwanin burgewa yadda suke yin hirar in akayi hausa wani lokacin sai a juye a koma fullanci Abbas yay ta murmushi har Mino nace mashi tunda tazo zata koya mashi ai, anan yake ma Gwaggo Maganar cigaba da karatun ta tace eh inda Fatuu tayi take son taci gaba in ta huta sai Amadu yayi mata cuku cukun samu Abbas d'in yace abar mashi komai, bayan Abbas ya tafi gwaggo tace ma Fatuu ita sai yaushe zata tafi dare yayi fa sosae tace ai anan zata kwana Hajiya ta amince tace a'a miya kai na wani kwana ta tashi ta koma ta marairaice kaman zata saka kuka gwaggon tace ko na jini zata yi sai ta tafi tace su tafi tare da Mino su kwana, jin hakan yasa ta washe ta basu tsarabar Hajiya da ta Fatun suka tafi, Bayan sun koma gida sun kaima Hajiya tsarabar suka dawo part d'in su, Bedroom suka nufa Mino sai faman washe baki take tana fad'in "Adda Fatuu wllh gidan ki Aljannar duniya ne" ita dai Fatuu sai dariya take, toilet ta jata don tayi wanka, a Laundary suka tsaya tasa ta cire kayanta ta d'aukko mata towel kanta yasha kitson fulani gwanin sha'awa, bud'e injin wanki tayi ta saka kayan data ciren nan fa Mino ta fara k'auyanci tana tatta6a shi cike da mamaki take fad'in ta ta6a ganin irin shi a kallo ashe tana da rabon ganin shi a fili har ta ta6a, gaba d'aya ta bi ta rurruk'e saman towel d'in da Fatuu ta bata ta d'aura, tana dariya tace mata in aka d'aure saki ake tace ai ji take kaman zai kwance ne, tare suka shiga toilet d'in ta fara nuna mata yadda zata yi amfani da komae ta waro ido tana bin shi da kallo, had'a mata ruwa tayi cikin bathtub ta fara nuna mata yadda zata shiga tayi wanka tana cikin mata bayani Minon tace wai ko kaman yadda ake yi a tafki ta d'an harareta, bayan ta gama nuna mata tace zata tsaya a cikin d'akin waje in akwae abunda bata gane ba tayi mata Magana tace toh, da yake tana da fahimta kuma k'auyancin nata da Sauk'i bai yawa ba sai gashi tayi wankan lafiya lou ta fito sai shinshina jikinta take yi tana washe baki tana fad'in yau tayi wanka da ruwan turare, Fatuu dai saidae tay dariya ta girgiza kai, bayan sun koma cikin Bedroom tasata ta shafa mai ta daukko mata rigar bacci, saida ta gama shiryata ta nuna mata gado tace ta kwanta a d'arare ta hau gadon tana yi tana tatta6a jikin shi sai kace tana jin tsoron shi, bayan ta kwanta Fatuu ta wuce don tayo wankan itama, bayan ta fito a takure ta iske Mino sai faman rawar sanyi take ita tama d'auka tayi bacci, rage mata Ac d'in tayi ta nuna mata duvet tace da shi ake lullubewa tace ai ta d'aukka kwalliyan gado akai Fatun tay d'an guntun