Showing 12001 words to 15000 words out of 512766 words

Chapter 5 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1533

kasan ranar ake bikin don kuwa musamman Baffa ya yanka masu k'atuwar tunkiya su gwaggo aka hau suya wad'anda suka ga zasu yi ma kan su buk'ulu ba Arzik'i suka shigo akai aikin da su aka yi Abinci mai uban yawa Yaya dai na can zazza6in bak'in ciki ya rufeta, da rana kowa yaci gayun Juma'a aka ci aka sha harda lemuna da Abbas ya kawo daga Jimeta da ya je Salla tare dasu Kamalu, a ranar da yamma sai ga akwatuna guda biyu da kit d'in su daga wurin Chairman yace akai ma Fatuu harda kud'i dubu d'ari kowa yayi tsananin mamakin hakan duk d'inkakkun kayan da akai mata ne a ciki da wasu abubuwan su Cosmetics takalma komae saida aka d'ebo gwaggo murna kamar ta zuba ruwa a k'asa tasha wai akace hassada ga mai rabo taki ranar dae ta shiga tarihin su, sosae Kamalu ya zagaya da Abbas yaga rugan ya kuma yi hotuna da daddare suka fara shirye shiryen tafiya don dasu Yadikko za'a tafi kamar yadda suka buk'ata Baffa ma na zaune a parlon Abbas kuma basu kaiga dawowa shida su Amadu ba anan yake ma Gwaggo Maganar kayan kitchen d'in Fatun yace daga baya zai sawo su a Mota a maido tace hakan yayi tay mashi Maganar yadda za'ai da kayan d'aki da aka riga aka siya yace wannan ba matsala bane tunda kayan amfani ne yasan za'a samu yadda za'ai dasu zai tuntu6i wad'anda suka yisu ko zasu fanshe su tace to duk yadda ake ciki sai ya sanar mata sai kuma kayan gara nan tace kowanne su d'auki d'ai d'ai suyi amfani dashi buhun shinkafa, taliya, macaroni, aka fiddo su man shanu da su dublan aka zuzzuba su Mino suka hau rabo sauran gidajen har 6angaren Yaya saida aka kai.

Washe gari ana gama sallar Asuba aka fara shirin tafiya aka zuba kayan da za'a tafi dasu su shinkafa da akwatunan da aka ba Fatuu a booth bayan duk sun yi sallama da yan gidan suka hau Mota, gwaggo da yadikko sai su Mino a baya gaba kuma Amadu da Kamalu shi Baffa banda shi sai zai maida kaya yana tsaye yana murmushi had'i da d'aga masu hannu suka tafi Katsina za tay di6a su Mino sun kasa 6oye farincikin su yau dae Allah ya kira su zasu je Katsina Yadikko ma bata ta6a zuwa ba haka Kamalu sai fatan Allah ubangiji yasa su isa lafiya Amin.


KATSINA TA DIKKO DAKIN KARA KUNYA GARE SU BA DAI TSORO BA.

Tun suna kan hanya Fatuu keta faman kira tana tambayar gwaggo sun kawo ina sam bata san da su Yadikko aka taho ba kuma bata san an fasa Auran nata ba don duk inta kira don jin halin da ake ciki sai gwaggo tace mata tay ta Addu'a dai ko jiya da ta kira kaman zatayi kuka ta hau rok'on Gwaggo kan ta fad'i mata wai gabanta sai fad'uwa yake Saboda zullumi nan ma cewa dai tay taci gaba da Addu'a gobe zasu dawo zata ji komi ake ciki, yau da Asuba bayan sun tashi ne gwaggo ta kirata tace mata su koma gida ita da Haulat suyi Abinci mai d'an yawa. Kaman dae lokacin da suka je yau ma cikin ikon Allah kafin la'asar suka iso zo kuga su Mino yan kauye an zo birni sam sun kasa tsaida idanun su a wuri d'aya sai zuba k'auyanci suke su gwaggo da Abbas na masu dariya yadikko ce kadae bata k'auyanci ita da tay zaman Abuja amman har Kamalu kasa rufe baki yay, tun suna shigowa gari Amadu ya kira Fatuu ya sanar mata lokacin da suka isa Unguwar tun kafin su k'arasa kopar gidan suka hangota a tsaye tana sanye da doguwar rigar atampa ta yafa d'an mayafi a kanta ai koda ta gane sune tun kafin Motar ma ta tsaya ta nufo ta da sauri, lokacin da tay arba da su Mino da yadikko kuwa wata uwar k'ara ta fasa ta hau tsalle tana kwad'a ma Haulat kira gaba d'aya gyalenta ma ya fad'i k'asa sai tulin gashinta dake a fake, suma sai murnar ganinta suke kowa baki yak'i rufuwa sai gwaggo ce ta d'aukko gyalenta dake yashe a k'asa ta yafa mata a kan, tana cikin murnar take tambayar yadikko an fasa Auren da sauri Mino tace mata eh, tafin hannuwanta tasa ta rufe baki cike da tsantsar farinciki, gwaggo ce tace to su shiga ciki sai ai murnar da kyau duk suka juya gwaggo ta kalli Abbas dake jingine da Mota tace ya shigo ya ci Abinci amman sai yace mata a'a zai k'arasa gida duk yadda tay dashi yak'i yace kada ta damu, sosae tay mashi godiya da fatan Alkhairi tace sai tazo har gida yanata dae dariya har ta juya sai kuma tace ya d'an jira zata aiko da sak'o a kai ma su Abdul yace to, har Fatuu zata shige gidan sai kuma ta dawo ta tsaya gaban Abbas d'in tana ta washe baki kamar gonar auduga da tsananin mamaki tace "Wai ya Abbas da gaske an fasa Auran?" K'ura mata ido yay da d'an murmushi kaman bazai ce komae ba can yace "Eh an fasa amman an d'aura maki da ni" waro ido tay baki bud'e ganin hakan yasa shi sakin dariya itama sai tay dariyar don ta fahimci wasa yake ta sake tambayar shi wai ya akai aka fasan yace mata ikon Allah sun dogara da shi shiyasa aka samu mafita ta jinjina kai cike da gamsuwa kafin tace "Alhamdulillah" yar dariya Abbas d'in yay ya jinjina mata kai suka d'an yi shiru sai faman kallonta yake har ta kula ta d'an yamutsa fuska sai ya fad'ad'a murmushin shi suna haka Haulat ta fito ruk'e da babbar leda ta ba Abbas tace inji gwaggo ya amsa yay godiya harda tsokanarta wai mai rako Amarya ta gudo ta saki dariya haka Yadikko ma tace mata da ta ganta, juyawa yay ya bud'e back door ya saka bayan ya rufe ya d'ago suka had'a ido da Fatuu yana murmushi yace "Wai Mom Zarah ban ji kin yi Maganar Mutumin naki ba" tace "Wa?" d'age gira yay yace "Wa kike tunanin zan maki Maganar shi ko na Jimetan?" Tura mashi baki tay yasa dariya tace "Wai Ya Haisam ai ya manta da ni" ta d'an d'aure fuska Abbas dake dariya yace "Haba shi ya isa ya manta da Mom Zaraah d'in shi kawae nasan k'ilan aiki ne yay mashi yawa" tace "tun fa da na tafi sau d'aya mukai waya" Abbas yace "kingane bai nan ne Company d'in su sun tura shi wata seminar ina tunani bai samun isasshen time ne" d'an ta6e baki tay yace "shi kike tura ma bakin?" Yar dariya tay tace a'a, sigh yay yace bari ya wuce sai sunyi Magana ta d'aga mashi kai tace ya gaida su Abdul sai tazo ya d'aga mata kai ta wuce gida shi kuma ya shige Mota ya tafi.

Koda ta koma cikin gidan farin cikin suka ci gaba da yi anata murna bakin kowannan su yak'i rufuwa su Mino sai santin gidan suke basu kad'ai ba har Yadikko da Kamalu gidan ya burge su a d'aki Fatuu ke tambayar Mino yadda akai aka fasa Auranta tace ita bata sani ba gaskiya, sai bayan da suka huta gwaggo ta k'wala mata kira anan ta nuna mata Akwatunan da aka bata Fatuu was completely speechless tayi matuk'ar mamakin jin an bata su a rud'e ta shiga tambayar gwaggon yadda akai aka fasa har aka bata wannan uban kayan ta kwashe komae ta fad'i mata Yadikko nata yabon kirkin Chairman gwaggon ma tace wllh ita kanta ta matuk'ar yabawa da karamcin da yay masu ta hau yi mashi Addu'oi tana Allah ya shirya mashi yaron nashi da sauran yara ita dae Fatuu shiru tay tana bin ta da ido tunowa da Khalid, gwaggo tace ta kwashe su ta kai d'akinta ta k'wala ma Haulat kira tace su zo ita da Mino, bayan sun maida su d'akinta ne ta fara k'ok'arin gwada kayan wanda ada ta k'i sosae kowanne ya amsheta su Haulat nata santin yadda kayan su kai mata kyau tana fad'in ita gaba ta kaita gobarar titi a Jos Fatuu na dariya tace amman dae ai anyi asarar k'walla galan galan duk suka sa dariya, sai dare Haulat tace zata tafi gwaggo ta bata su dublan tace ta kai ma innarta tay ma Yadikko sallama tana sai tazo gidan su, Fatuu da su Mino ne suka rakata har gida, sosae innar su Haulat tay farinciki da jin zancen an fasa tay ma su Mino an zo lafiya daga baya Haulat ta rako su bakin lungu suka tafi. Washe gari da safe bayan sun yi Breakfast sai ga kiran Abbas bayan sun gaisa yace mata tace ma su Mino su shirya zai zo ya kaisu su ga gari, zo kaga murna ba tare da 6ata lokaci ba suka hau shiri Fatuu ta taimaka masu sukai kwalliyar yan birni Mino ma ita ta bata kaya ta saka koda Kamalu yaji cewa yay aikuwa ba za'a bar shi ba shima ya fara shiri gwaggo tace ma Yadikko itama to ta shirya tace abun yara ta bisu kuwa tace eh mana ba ganin gari bane tace to daman tana so, Wurin k'arfe sha biyu na rana yazo d'aukar su duk sun shirya har Fatuu ma ta d'auki ado da wata fitinannan fitted gown ta Atamfa acikin kayan da aka kawo mata koda ta fito yadikko taga shigar da tayi ga d'an mayafi da bai rufe ta ba sosae kasa hak'uri tay tace mata gaskiya kayan sun kamata kuma ga mayafin ba babba ba gwaggo ta k'arasa fitowa daga cikin d'akinta cikin fad'a take fad'in haka take fama da ita da son saka matsattsun kaya kuma tasan ba kyau, k'arshe cewa tay kodae taje ta saka babban mayafi ko kuma ta cire kayan ba sai an je da ita ba tana tura baki ta koma cikin d'aki, yadda Rigar tay mata sai taji data saka babban mayafi gwara ta cireta ta saka wasu riga da skirt na lace bayan ta d'aura kallabi ta laga mayafin kayan sannan ta fito, koda suka fito waje Abbas na ganin ta yace ta koma ba da ita za'a ba tunda ita ba bak'uwa bace tasan ko ina, cikin sigar shagwa6a tace Allah sai an je da ita Yadikko nata dariya yace su shiga Mota yana ta yaba Kwalliyar su Mino da Aysha suna dariya, Sosae ya zaga gari da su ko ina da yakamata haka ya rink'a siya masu abubuwan ciye ciye har park and zoo ya kai su da Fatuu taga zasu yi k'auyanci sai ta taka masu burki Abbas ya rink'a masu hotuna da wayarshi sai yamma ya wuce da su gidan shi sosae Feenah tay murnar ganin su ta tarbe su hannu bibbiyu bayan sun zazzauna aka shiga gaisawa ta kalli Fatuu cike da zolaya tace "Amarya Sai kika gudo munata shirin zuwa mu sha biki" duk akai dariya daga baya ta tayata murna tace Allah yasa hakan yafi zama Alkhairi suka amsa da Amin, bada dad'ewa ba Abdul ya dawo daga Tahfiz yana ganin Fatuu ya ruga suka rungume juna bayan ya d'ago yace "Aunty Fatuu Daddy yace man an fasa Auran ki ko" kai ta d'aga mashi ya k'ara cewa "gara da aka fasa dama ban son ki tafi yanzu kin ga sai ki zaman ki anan in ma zaki Auren sai kawae ki auri Baba Zakee kin ga shi Babana ke kuma Mamana" gaba d'aya aka sa dariya Fatun tace to shikenan hakan za'ayi, sai bayan Magrib Abbas yazo maida su Feenah na fad'in kamar kar su tafi sunata dariya harda kayan shafa taba su Mino, Washe gari Monday wurin k'arfe sha d'aya da wani abu Yadikko da Fatuu suna aikin Abincin rana Yadikko na cikin kitchen Fatuu na daga waje tana yanka Alayyahu suna fira taji wayarta ta fara ringing Aysha ta kwad'a mata kira tana fad'in "Adda Fatuu an bugo maki waya" d'an d'aga murya tay tace ta kawo mata, Koda ta kawo mata ta duba screen d'in taga mai kiran nata har saida ta d'an bud'a ido ta d'ago ta kalli yadikko dake kallonta a bakin Kitchen ganin yadda ta kame kanta yasa yadikko yin yar dariya tace halan Ya Handsome ne itama yar dariyar tay ta jinjina mata kai ganin tana niyyar d'auka yasa tace mata ta d'an ke6e mana murmushi kawae tay ta mik'e tana tunanin inda zata can ta nufi d'akin Kawu Amadu Saboda bai nan suna shago shida Kamalu, a bakin mattress d'in shi ta zauna bayan tay picking ta karata a kunne, shiru ba wanda yay Magana har bayan wasu sakannai sannan taji yace "Zaraah" wani yammm taji jikinta yayi harda d'an runtse ido tunda take a rayuwarta bata taba ganin Namijin dake da murya mai sanyin dad'i ba irin ta Haisam, a hankali tace "uhyum" sigh yay kafin ya k'ara cewa "kin picking and u can't talk" d'an tura baki tay kaman yana kallon ta tace "Fushi nike da kai" har saida ta d'an ji sautin murmushin da yay,

"Did I offended you?" can taji ya tambaya tana tura baki tace eh sigh ya k'ara yi kafin ya tambayeta tana cikin Mutane ne tace a'a ita kadae ce yace Ok bari ya maida Video Call yaga angry face din tay d'an murmushi, bayan ya maida zaune yake kan Sofa jikin shi sanye da silky sleeping dress riga da wando farare ya zuba mata ido suna kallon juna tana sanye da yar riga v-neck ta mata cib burst d'inta ya fito sosae kanta d'aure da d'an bak'in gyale daya d'an zame bak'in gashinta ya d'an bayyana bai hango skirt d'in dake jikinta ba wanda iya gwuiwa ne don a zaune take, ita shamm tama manta a yadda take Fuskar shi a sake kaman zai murmushi ya tambayeta suna lafiya tace mashi lafiya lou sai kuma taji yace "So tell me laifin mi na maki?" d'an yamutsa fuska tay a d'an shagwa6e wanda hakan yama zame mata jiki tace "ba ka manta dani ba" still yay yanata kallonta kaman bazai tanka ba har saida ta d'an tsargu da kallon ta d'an kauda idonta can taji yace "am sorry it wasn't intentionally, naje wani wuri ne and I have been trying to call but u'r out of reach kinsan k'auyen ku ba Network mai kyau" wani kallon k'asan ido tay mashi kawae sai taga yay dariya har jerarrun fararen hak'oran sa suka d'an bayyana, idasa d'agowa tay tana ta kallon shi ya d'age mata gira ya tambayi ta yi hak'uri bata san ma ta d'aga mashi kai ba alamar eh, ya furta mata "thanks" tay yar dariya, shiru ta d'an biyo baya kafin ta tambaye shi ina Aunty Fanan yace mata tana wurin aiki da d'an alamun mamaki tace amman ba taga kaman dare bane yace eh acan zata kwana ne ta jinjina kai,

"Sai kika gudo ko" tura mashi baki tay tana kikkafta ido tace "to ai ni ban son Auren fa" d'an d'age gira yay da d'an murmushi kawae tana dai ta kallon shi ta lura kaman yanayin face d'in shi ya canza yana nan yadda yake saima wani fresh daya k'ara yi gashi ya d'an tara suma a sajen shi ba kaman da ba duk yana lura da kallon da take mashi duk da sai kace ba kallonta yake ba can taji yace ya akai take k'are mashi kallo haka, yar dariya tay dama tasanshi da rashin son kallo tace "naga fuskar ka kaman ta canza" fuska sake yace mi face d'in nashi tay tace kaman ta d'an fad'a ko bai lafiya ne, hannu yasa ya shafi forehead d'in shi slowly yace "Yea but na samu sauk'i" tace Allah ya k'ara sauk'i ya amsa da Amin ta sake cewa "Amman a haka kana ciwon ka tafi wurin da ka ce ka je?" idon shi a kanta yace eh, cikin nuna damuwa tace "ai da sai kace baka lafiya kai zaman ka gida" d'an ta6e baki yay yace "ai ni ba lazy bane kaman ke" waro ido tay tace itace lazy d'in yace "yeah komae kuka" aikuwa a shagwa6e ta fara yarfa hannu tana fad'in wllh ita ba raguwa bace shima ai ya sani still yay yanata kallonta da d'an murmushi komae nata burge shi yake ba kaman in tana shagwa6a duk da ba ita kadai ke mashi hakan ba Fanan ma na yi mashi sosae amman sai yafi ganin kyaun abun in Zaraah tayi, har saida yace wasa yake sannan ta daina mitar, cigaba da firar sukae har yana ce mata daga yanzu in tasan tana cikin Matsala ta rink'a sanar dashi in ma bata same shi ba ko Abbas ne ta kira ta fad'a mashi Koda wani abu ne take so ta amsa mashi da toh, fira tayi fira saiga su Fatuu harda kwanciya kan Katifar shima can ya mik'e ya d'auki laptop d'in ya koma Bedroom d'in shi, gado ya hau ya jingina da headboard ya d'aura laptop d'in akan laps d'in shi, Hira da Masoyi dad'i😍 sai ga Fatuu da fara yin gyangyad'i tun tana yi tana bud'e idon har takai baccin ya kwashe ta dai abun sai ma ya bashi dariya kamar ba ita bace ta tada jijiyar wuya ba don an ce mata lazy, sam ya kasa disconnecting ya kafeta da ido sai kallon face d'in ta yake ba kamar eyelashes d'inta da lips d'inta da tun ba yanzu ba yake ganin kyawun shape d'in su yadda na k'asan yake da d'an fad'i sosae, slowly ya mik'a hannunshi kan screen d'in ya sauke dogon yatsan shi manuni daidai lips d'inta ya fara zagaye su tamkar mai tracing ya d'an d'auki lokaci yana hakan can kuma ya janye hannun ya katse kiran ya maida laptop d'in saman bedside drawer bayan ya rufeta, idasa kwanciya yay idon shi na kallon sama tamkar mai tunanin wani abu a hankali kuma ya lumshe su...........



_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login