Showing 75001 words to 78000 words out of 512766 words

Chapter 26 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1604

kira ta shigo itama ta ga kayan tay godiya sosae tana fad'in lalle Mama Fatima ta fito da d'iyarta wannan kaya haka k'arshe tay Addu'ar Allah yasa suma su ga yaran su kowa ta sunnar da kai suna d'an murmushi Haulat na fad'in su Fatuu ashe yanzu an san kunya innarsu dake dariya tace ai daman can da kunyarta daga baya ta fita, har akai la'asar suna gidan bayan an gama salla gwaggo tazo itama harda kayan ta kawo masu sosae suka ji dad'i sai bayan Magrib sukai masu sallama Haulat na tambayar Fatun yanzu Makarantar zata koma tace eh amman zata dawo cikin satin ta k'ara ganin Baby tace to Allah ya bada sa'a suka amsa da Amin kafin su tafi aka basu naman suna mai uban yawa har gwaggo na fad'in kar su kwashe ma mai jego fa innar su tace a'a bakomae godiya sukai suka tafi.

Washe gari da safe sukai shirin tafiya bayan sun gama yin breakfast suka je d'akin gwaggo sukai mata sallama tay ma Fauzy godiyar ziyara harda kud'i ta basu ta rako su har bakin zaure Kawu Amadu ma ya fito sukai sallama, Lokacin da suka isa Class kawae suka wuce don duk suna tare da jakunkunan su da akayi break suka fita, tun bayan da suka dawo zuciyar Fatuu ta fara tashi ga wani ciwon kai daya far mata lokaci guda daurewa kawai take bayan da malamin su ya shigo yana cikin yi masu bayani yau ma kamar rannan amai ya taso mata ta fita da gudu Fauzy ta d'auki excuse ta bi bayanta, saida ta gama ta kamata suka je bakin famfo ta wanke fuskarta da bakinta bayan ta gama Fauzy dake kallonta cike da damuwa tace gaskiya suje taga likita ciwon ya fara yin yawa Fatun ta d'aga mata kai don itama abun ya fara damunta class Fauzy ta koma ta fad'i ma malamin zata kaita taga likita ya bata izini ta d'aukar masu jakun kunan su, lokacin da suka isa Opd office d'in wani Doctor Madugu suka nufa don sun san shi son Fatuu yake ita kuma tak'i saurarar shi ba kamar da yake tasan halin shi ya cika son mata, saida suka jira patient d'in dake ciki ta fito sannan suka shiga yana ganin su ya sakar masu murmushi suka zauna a kan kujerun gaban table d'in shi yabi Fatuu da wani kallo yana sakin k'ayataccen murmushi ta d'an d'aure fuska Fauzy ce ta fara gaishe dashi sannan Fatun kaman an mata dole yace ba zai amsa ba in bazata saki face en ta ba k'ara tamke fuskar tay Fauzy ce tace mashi bata lafiya ne d'age gira yay ya tambayi abunda ke damunta har Fauzy zata bashi amsa yace ita yake son yaji daga bakinta d'an shiru fatun tay kafin ta fara mashi bayanin abunda ke damunta bayan ta gama yana d'an murmushi yace "kinga da mun yi aure sai in yi tunanin ko mun samu rabo ne" a d'an harzuk'e ta kalle shi bata dae ce komai ba ya fara rubutu a Computer d'in gabanshi can ya d'ago yace suje lab ya tura test ayi mata suka mik'e yabi bayanta da kallo har suka fice, suna zuwa lab d'in ba 6ata lokaci akai mata awon don sun san masu yi awon Malaria da typhoid ne aka mata bayan an tura ma likitan suka koma Opd d'in lokacin daya duba result d'in akwae malaria d'in amman ba typhoid ya fad'i masu kafin ya tura masu magunguna yace suje pharmacy bayan sun mik'e ya kira Fauzy ya bata kud'i yace su biya tay mashi godiya suka tafi, bayan sun amshi magungunan suka tafi ganin an kusa tashi Fauzy tace su wuce hostel kawae sai ta sha magungunan ta d'aga mata kai, bayan ta fara shan magungunan sosae ta samu sauk'i ta daina yin aman saidae bata da appetite ba komae take iya ci ba tafi shan youghort sai kuma lemu Fanta sai abu mai d'an tsami ko yaji a haka har Friday tayi suka tafi weekend, lokacin data koma gidan gwaggo bata nan bata dawo ba sai dare Fatun ta fito tsakar gida ta tareta tay mata sannu da zuwa tana niyyar zuwa kitchen don ta kawo mata Abinci tace mata ta barshi in tayi wanka zata ci ta ce to ta koma d'aki, washe gari bayan ta gama gyara gidan tay wanka ta shirya cikin doguwar rigar material tay rolling veil d'in ta shiga d'akin gwaggo lokacin tana kishingid'e saman gado amman ba bacci take ba a bakin gadon Fatuu ta zauna suna kallon juna da gwaggon da ta d'ago kanta tana kallon Fatun sosae tana murmushi ta gaishe da ita ta amsa tace mata zatace gidan su Haulat shiru gwaggon tayi tana ta kallonta saida Fatun ta maimaita mata sannan ta d'aga mata kai alamar to har ta mik'e ta nufi kopa tana fad'in sai ta dawo taji gwaggon ta kirata ta dakata ta juya da kai tay mata alamar ta zo ta koma ta tsaya daga d'an gabanta tace gata gwaggon ta yunk'ura ta tashi zaune sosae tana kallonta tace "wani abu na damun ki ne??" Cikin rashin fahimta Fatuu ta tambayeta wani abu tace tana nufin bata lafiya ne d'an murmushi Fatuu tay tace "Eh ciwo nayi har ma naje naga likita ya tura ni aka man test aka ga malaria ce ke damuna sosae ya rubuta man magunguna yanzu haka cikin shan su nike amman na samu sauk'i ai sosae" shiru gwaggo tay kafin tace mata basu saka net ne in zasu wanta tace suna sawa wllh kawae ciwon ya kamata ne kuma kafin su shiga net d'in saurayen na cizon su ko in sun fita class da daddare,jinjina kai gwaggon tay tace taje Allah ya sawak'e amman dole su k'ara kulawa tace to ta tafi, tunda tazo gidan wani ikon Allah lafiya lou take cin Abinci washe gari lahadi harda cin cin tayi masu ranar Monday da safe ta tafi.

tun bayan da ta koma sai ciwon ya k'ara dawowa sosae ga yawan amai da take yi kusan kullum sai tayi amai a class wani lokaci in Malam na ciki ko kuma da break haka a Hostel ma in ya taso mata ta window take zura kanta tai tayi ga magani tana ta sha amman abun yak'i lafawa har fuskarta ta d'an rame tayi wani fayau da ita ranar laraba Fauzy tace mata kodae ta rakata gida amman sai tace tunda har anzo ranar ta bari Friday ta je tace to kodae ta saka mata drip ko taji k'arfin jikinta Fatun tace eh, da kanta ta fita taje ta siyo drip d'in bayan ta dawo ta saka mata shi lokacin daya k'are sosae ta samu k'arfin jikinta washe gari Alhamis taje class lpy lou har aka tashi, da yamma Fauzy taje siyo abu a shop bayan ta dawo ta nufo Hostel hannunta ruk'e da leda taji ana k'wala mata kira ta bayanta ta tsaya da ta juya sai taga wata yar class d'in su ce mai suna Zainab Muhammadu wadda ake ce ma suda (sarkin labari) tana ta sauri ta k'araso ta tsaya gaban Fauzy tace "dama tambayar ki nike son yi ya jikin Fatima Ard'o?" Wani kallo Fauzy tay mata tace bata ganta bane yau a class da sauri tace ta ganta taga ma duk ta rame Fauzy tace eh ai ciwo take ko daga haka ta fara kokarin wucewa Zainab d'in tace "wai kinsan abunda ake fad'a kuwa game da ciwon da take?" Cakk Fauzy ta tsaya tana kallonta tace mi ake fad'an yar in ina ta fara tace "j....ji nayi ana cewa wai kamar ciki ne da ita don ciwon da take yayi kama da laulayin ciki" rassss gaban Fauzy ya fad'i ta zaro ido waje gaba d'aya hannunta guda dafe da bakinta can ta cire cikin bacin rai tace "uban wa yace ciki gareta dama mara aure na samun ciki ne ko kuwa ana sha a ruwa ne ban sani ba???" Yarfa hannu Zainab d'in tay tace "nima fa bani nace ba abunda aketa fad'a ne nagaya maki don ku sani" daga haka ta wuce tay tafiyarta Fauzy tabi bayanta da kallo fuska a matuk'ar d'aure can ta wuce fuuu itama ta shige cikin hostel d'in idonta har rufewa yake Saboda tsabar bacin rai da bibbiyu ta rink'a hawa staircases d'in ta nufi d'akin su, lokacin data shiga Fatuu na kwance saman gado tana jiranta ta kawo mata Fanta gado ta nufa ta aje ledar hannunta gefe ta zauna fuska a d'aure ta kumbura baki ganin yanayinta yasa Fatuu yunk'urawa ta tashi zaune ta fara tambayarta lafiya bin ta da ido kawae tay kaman bazata tanka ba can cikin bacin rai tace "wllh magulmaci bai ji dad'i ba yaji haushin asara!!" A d'an rud'e Fatuu ta hau cewa ta fad'i mata gulamar mi akayi don Allah tace "wai shikenan mutum bazai yi ciwon Allah da Annabi ba sai an ja mashi sharri yanzun nan da zan shigo wai Zainab Muhammadu ta tsaida ni take fad'a man maganar da ake tayi game da ciwon ki.." a rud'e Fatuu tace mi ciwon nata yayi kaman bazata fad'i mata ba ganin yadda take mata Magiya yasa tace "ke wai ciwon da kike wai kaman ciki gare ki don ciwon yayi kama da laulayi Kiji jan sharri don Allah kawae don aja maki, ta ina zaki samu ciki tunda ba aure gare ki ba!!" Zaro ido waje Fatuu tay tasa hannu guda ta dafe kirjinta a kidi'me ta maimaita "ciki kuma!" Wani uban tsoki Fauzy taja jikin Fatuu har ya fara rawa kaman zata yi kuka tace "ni a ina zan samu ciki bacin kowa yasan ba aure gare ni ba!" Wani tsokin Fauzy taja tace "dalla rabu dasu magulmantan banza kawae an fad'a ne tunda kika ji Zainab Muhammadu ta fad'a don in dae tace abu to tabbas an yi ne ki k'yale su ta Allah ba tasu ba duk mai neman ki da sharri saidae ya koma mashi wllh" tana k'arasa Maganar ta fiddo mata Fanta d'in ta mik'a mata hannun Fatuu sai rawa yake ta amsa sai ta aje ta a gefenta kawae tsananin tsoro da fargaba ne suka kamata jin abunda zuciyarta ke ayyana mata na kada ace daga abunda Ya Haisam yayi mata ta samu ciki sosae kirjinta ke bugawa tunanin yaushe yakamata tayi period ta shiga yi a lissafin ta gobe Juma'a wata guda kenan da abun ya faru kuma tayi wanka da kwana d'aya hakan ta faru kenan yanzu kusan kwananta talatin da yin wanccan tasan kuma bayan kwana ishirin da d'aya wato sati ukku koda biyu take yin sabon period yanzu kenan lokacin ya wuce kuma ko alamun zata yi bata fara ji ba wani abu ta had'iya Kutt lokaci guda zufa ta fara tsattsafo mata ta koma tamkar an dasa ta a wurin ko kwakkwaran motsi ta kasa yi kallonta Fauzy tay ganin halin da take ciki da alama ta rude yasa tace mata wllh kada ta sake ta wani damu da zancen munafurcin su tunda ita dae ai tasan ba shi gare ta ba ko, zuru da ido kawae tay ma Fauzy k'arshe Fanta d'in ma kasa sha tay don ko kallonta ma bata k'ara yi ba Fauzy ta hau lallashin ta tana don Allah ta d'auka tasha kada ta tada hankalin ta a banza ita data san haka zata shiga damuwa da bata fad'a mata bama, a wannan daren yadda Fatuu taga rana haka ta ganshi sam bacci ya k'aurace ma idanunta sai juyi take tana zullumin kada ace da gaske ciki ne da ita don duk alamu sun nuna kaman laulayi take yin da gaske yin wannan tunanin har saida tasa hannu ta rufe bakinta, akan kunnanta aka kira sallar Asuba da k'yar ta iya yin salla tana gamawa ko Addu'a kasa yi tay ta koma gado ta kudundune lokacin da gari ya waye Fauzy ta d'an bubbuga ta tace ta tashi ta shirya kada su makara tana a kudundunen tace mata ta shirya ta tafi ita bazata je ba jin hakan yasa Fauzy zama a gefen gadon da take tace "kamar ya bazaki class ba kuma, ko don Maganar jiya to ke miye abun wai damuwa har haka ne tunda kin san kina da gaskiya ki tashi kawae ki shirya mu tafi in mutum ya isa ya tunkare mu yayi mana Maganar mu mana" duk yadda tayi da ita ta kafe kan bazata je class ba har ran Fauzyn ya 6aci tace "to ko dae Zarah da gaske cikin ne da ke???" shiru Fatun tay bata bud'e fuskarta ba kirjinta na wani irin bugu can Fauzy ta kai hannu ta yakice bargon data lullu6a Fatun ta kalleta da sauri suka zuba ma juna ido baiwar Allah duk ta firgice sai numfashi take da k'arfi wani irin kallon tuhuma Fauzy ta fara yi mata ganin haka yasa Fatun sunkuyar da kai cikin d'aurewar kai Fauzy tace "Zarah na tambaye ki baki ban amsa ba ki fad'a man gaskiya ko dae Maganar da ake gaskiya ce??" Girgiza kai ta fara yi da k'yar ta d'ago ta kalleta idanunta sun ciko da Kwalla tace "Fauzy ya zaki fad'i hakan kema bacin kin fi kowa sanin wacece ni kuma kin san ba aure ke gare ni ba" sauke Ajiyar zuciya tay tace "to don mi zaki k'i zuwa class??" Cikin rawar murya tace "h.... hakanan kawae, hankali na ya tashi sosae da jin Maganar ban so inje class haka su k'ara tabbatar da Maganar su gara in tafi gida kawae in fad'i ma gwaggo halin ciwon da nike ciki a nema man maganin hausa" da k'yar ta kai Maganar, shiru Fauzy tay tana nazarin Maganar can tace mata shikenan ta fahimta amman ta bari a tashi sai ta rakata gidan tace mata to kawai, saida ta matsa mata sosae sannan ta d'an sha ruwan tea da yar wainar kwae, tun bayan da Fauzy ta shirya ta tafi class take ta faman kai da kawowa a cikin d'akin gaba d'aya ta gama firgicewa kanta ko kallabi babu ta rasa tunanin da zata yi tsoron ta ace da gaske tana da ciki duk in tayi wannan tunanin sai yan hanjinta sun juya can wata Zuciyar ta raya mata taje ta siyo Pt strip ta auna in shine tun wuri ta d'auki matakin daya dace, yin wannan tunanin yasa da sauri ta nufi kayan su ta d'auki hijab ta bud'e jakarta ta d'auki kud'i har zata fita tay tunanin ta saka nikab d'in Fauzy ta tafi dashi ta juya ta d'aukko shi ko sakawa daidai bata yi ba a haka ta tafi.......





_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2048*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*



...........Tafiya take bata san inda take wurga k'afafunta ba don sam bata cikin hayyacin ta a haka har Allah yasa ta fito cikin Asibitin tasan in taje pharmacy d'in asibitin ba za'a bata ba tunda ba Doctor ya turo ba hakan yasa ta yanke zuwa d'aya daga cikin pharmacies d'in dake wajen Asibitin tana ta tafiya gani take tafiyar ma bata sauri tamkar maidota baya ake hakan yasa ta yanke hawa Napep duk da ba wani nesa bane tama kusa isa, bayan ta tsaida ta fad'i mashi inda zai kaita shima mai Napep d'in har saida ya d'anyi mamaki yace mata nan wajen gate tace eh amman zai jira zata siyo abu ne sai ya maido ta makaranta yace nan school of nursing tace mashi eh yace to ta hau, bayan sun tsaya ta nufi cikin pharmacy d'in gabanta sai fad'uwa yake har ta kusa rubzawa k'atuwar kwalbatin dake wurin batare da ta ankare da slab din ya fashe ba mai Napep d'in ne ya d'an d'aga murya yace tabi a hankali don ya lura duk a firgice take ta d'aga mashi kai kawae, bayan ta shiga ta fad'i abunda za'a bata ba 6ata lokaci aka d'aukko mata ta je wurin biya ta bada d'ari biyar ta juyo saida cashier d'in yace mata canjin ta fa sannan ta juya ya bata ta amsa ta fito bayan ta hau Napep d'in suka komo Asibitin, a bakin gate ya aje ta ta mik'a mashi duka sauran canjin dake hannunta ta juya, ganin a rud'e take yasa yay tunanin ko bata san nawa ta bashi ba ya tsaidata yace kud'in sun yi yawa tazo ta amshi canji hannu kawae ta d'an girgiza mashi alamar ya bassu ta nufi ciki yana ta kallonta gashi dai baisan wacece ba don ta rufe face d'inta amman dae ta bashi tausayi don tabbas da gani akwai abunda ke damunta k'arshe yay mata Addu'a yaja napep din ya tafi, nan da nan ta iso d'akin su ta shige bayan ta cire nik'ab d'in zaune tay a gefen gado tana ta zare ido wani irin tashin hankali take ciki tsoronta ta gwada taga cikin ne can wata Zuciyar ta bata shawarar ta daure ta gwadan in ma shine tunda wuri ba sai taje ta siyo allurar zubda ciki ba tay ma kanta, sosae hakan yay mata ba tare da tayi tunanin wata matsala ba ta mik'e saida ta samu wani d'an murfi sannan ta fita zuwa toilet d'in su bada jimawa ba ta fito ko kallabi babu a kanta haka taje tayo fitsarin, a bakin windown d'akin ta tsaya ta d'aura robar fitsarin ta koma bakin gado ta d'aukko ledar pt d'in ta dawo, tsaye tay cike da fargaba take kallon fitsarin ba don komai sai Allah ya k'addara ba da iya tashin hankalin da take ciki ya isa yasa in ma cikin ne ya zube, can zuciyarta ta raya mata time fa na tafiya gashi yau Friday tayi abunda yakamata da sauri tasa hannu ta cizge ledan hannu na rawa ta fiddo tsinken gwajin ta tsoma shi a cikin fitsarin kaman

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login