Showing 228001 words to 231000 words out of 512766 words
Chapter 77 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1552
gira yace to shine mi, k'arshe ba yadda zata yi dole ta zauna idanun shi a lumshe yace tay kissing nashi iya yadda take so a kuma duk inda take so........
Bayan ta koma parlor duk ta bi ta kama kanta Hajiya tace ya tafi ta ce eh, bata dad'e da komawa ba Mino tazo jikinta sanye da Uniform d'in islamiyya taje can part d'in bata isketa ba, tana murmushi ta gaishe da Hajiya itama da fara'a ta amsa tace mata an dawo tace mata eh Fatuu ta nuna mata gefen ta alamar tazo ta zauna, bayan ta zauna Hajiya tace jiya bata zo tayin kwana ba maigida ya dawo, ita dai Minon murmushi kawae take yi cike da wasa ta sake ce mata ai da tazo ta taya ta ita duk suka d'an yi dariya, bata dad'e ba sosae ta mik'e zata tafi, bayan ta masu sallama Fatuu tace ta gaida mata da gwaggo, daga baya itama Fatun mik'ewa tay tace bari taje ta taya Aunty Saude aiki a Kitchen, Lokacin da akai Azahar sun gama komai ta wuce d'akin Aunty Sauden don tayi salla, bayan ta gama sallar ne ta fito ta nufi d'akin da Fanan take, da sallama ta tura kopar ta shiga, a saman abun salla ta hangota daga gaban gado tana jingine dashi ta juyo tana amsa mata sallamar da d'an murmushi, sosae gaban Fatuu ya fad'i da ta k'arasa wurinta taga idanunta a haka ma wai don ta samu bacci sun rage, gabanta ne ya shiga fad'uwa Fanan d'in ta nuna mata gefen gado tace ta zauna mana tayi tsaye, bayan ta zauna a sanyaye ta gaida ita ta amsa kafin tace taso taje ai can part d'in nata su gaisa bata tashi da wuri bane, cikin kama kai Fatuu ta d'an yi murmushin yak'e tace mata ai tun d'azu itama tazo ta shigo ta gaida ita ta iske tana bacci, sama sama suke d'an yin hira yawanci ma Fanan d'in ce ke kawo zance anan har take tambayar ta gwaggo tace zata shiga su gaisa in sha Allah, suna haka Haisam ya shigo duk suka yi mashi sannu da zuwa fuskar shi a sake ya amsa ya nufi mirror ya d'aukko stool ya dawo daga gefen gadon ya zauna, gaba d'aya Fatuu ta takura Saboda yawon kallon da yake mata har fakar idon Fanan tay ta d'an mashi alamar ya daina sai kawai taga yayi d'an murmushi, gaba d'aya su biyu ke yin hiran sama sama sai ta kama sannan Fatuu ta saka masu baki, daga baya Saude tazo tayi masu Maganar an shirya table bayan ta fita Fatuu ce ta fara mik'ewa dama duk a takure take cikin wasa Haisam d'in yace mata acici bazata jira su tafi tare ba sai kuma kunya ta kamata tana niyyar komawa ta zauna ya mik'e yana yar dariya Fanan ma yar dariyar tay ganin bata tashi ba yayi mata magana ta d'an yamutsa fuska tace gaba d'aya bata da appetite ne yace ta dai daure kar ta zauna da yunwa, mik'a mashi hannu tayi alamar ya taimaka mata ya kama hannun ya mik'ar da ita, bayan ta mik'e ta fara k'ok'arin cire Hijab din jikinta Haisam ya kai idon shi kan Fatuu dake kallon su suna had'a ido da sauri ta maida kan ta gefe, moving yay zuwa inda take yace su je ba tare data kalle shi ba ta wuce yana biye da ita Fanan kuma na gefen shi. Bayan sun fara cin Abincin Haisam na lura da Fanan bata wani ci kaman dai jiya can ya d'ebo ya kai spoon d'in bakinta da yake tana a gefen shi, kallon shi tay da murmushi yay mata alamun ta ci ta bud'e bakin ya bata, ci gaba yay da bata tunda Fatuu taga haka ta daina kallon su, sai gashi taci sosae, gaba d'aya Fatuu jin ta take wani iri hakan yasa taji Abincin ma ya fitar mata a rai hakanan take d'an tsakura gudun kada ta tashi ai tunanin wani abu, can bayan an k'ara lokaci ta mik'e duk suka kalleta da k'yar ta k'ak'alo murmushi tace ta k'oshi, Fanan ce tace mata amman ai kaman fa bata ci da yawa ba still da murmushin tace ai bata dad'e da yin Breakfast ba tazo ta d'aga mata kai alamar gamsuwa, idon Haisam a kanta ita dai Hajiya d'an murmushi kawae take a ranta ta raya aiki ya ga Haisam don tasan dama dole Fateema bata rasa jin wani abu a ranta a kan Abincin da yake ba Fanan d'in a baki, d'akin Saude ta wuce don acan ta aje gyalen ta, lokacin da ta shiga ba kowa a d'akin don Sauden na can baya ta nufi katifa ta Zauna tay shiru tana kallon wuri guda kaman mai tunanin wani abu, daga baya ma sai ta kwanta kawae,
Bayan su Fanan sun gama cin Abincin Parlor suka wuce Suna kallo saidae gaba d'aya hankalin Haisam na a wurin Fatuu tunani abunda take a cikin d'aki yake ta yi, ana fara kiran sallar la'asar ya mik'e yace zai je Masallaci, bayan ya fito tsayawa yay cikin harabar yana kiran Fatuu a waya saida ya kira har sau biyu amman bata yi picking ba ya juya ya nufi part d'in su a ranshi yana wani tunani, bayan ya shiga Bedroom ne yaga wayar ajiye akan bedside ashe bada ita ta tafi ba ya wuce toilet don yin Alwala, bayan fitar shi Hajiya ma ta tashi itama Fanan d'in ta mik'e suka tafi suma su yi sallar, har Hajiya zata shiga d'aki tayi tunanin Fatuu tace ma Fanan ta duba Fateema a d'akin Saude watak'il bacci take tace to, bayan ta shiga taje ta tasheta tace lokacin salla yayi Fatun tay mata godiya ta mik'e ita kuma ta juyo ta fito, d'aukar gyalenta tayi ta fito daga cikin d'akin lokacin data shigo parlon ba kowa ta nufi hanyar fita ta wuce part d'in su, tana shiga Bedroom ta cire gyalenta a gefen gado ta wuce laundry, bayan ta fito ta yo Alwala ta shimfid'a prayer mat ta kabbara salla.
Tun bayan data gama tayi zaune a wurin tay shiru k'arshe ma sai ta jingina da gado ta kwantar da kanta, Fauzy ce ta fad'o mata a rai ta raya yakamata ta kira ta sanar da ita Ya Haisam ya dawo bata samu ta hau online bane shiyasa data fad'a mata tuni, tana ta zaune can taji an turo k'opar ta kai idon ta, shine ya shigo suka had'a ido bayan ya rufe kopar ya nufota ta d'ago tana kallon shi, tayi tunanin saman gadon zai zauna amman ga mamakinta sai gani tayi ya zauna k'asa a gaban ta ya d'age kafa d'aya d'ayar kuma ya mik'ar da ita tana dai ta kallon shi fuskar ta a d'an sake, kallon ta yake shima saidai yanayin kallon kaman na mai nazarinta ganin haka yasa ta sunkuyar da Fuskar ta ta koma kallon k'asa, tana haka taji Muryar shi calmly yana fad'in "I want to try my possible best to be equitable to you, but I understand it would not be as easy as I think" jin abunda yace yasa a hankali ta d'ago ta kalle shi yanayin damuwa ya bayyana akan fuskar shi, bin shi tay da ido ta fahimci dalilin da ya sa yayi Maganar k'ilan yayi tunanin ko tayi fushi ne Saboda abubuwan da suka faru tsakanin shi da Fanan d'azun, d'an murmushi yaga tayi ta kai hannu ta ta6a gefen fuskar shi da turanci itama tace mashi kar ya damu zata taimaka mashi ya cimma hakan a tsakanin su, d'age gira yay ya tambayi da gaske ta d'aga mashi kai yace kenan bata yi fushi ba, tana yar dariya ta girgiza mashi kai tace fushin mi zatayi ya d'an kashe mata ido guda ya furta kishi, sosae ya bata dariya yadda taga yayi ta fad'a jikin shi a shagwa6e tace to yau ta fara gani ya ba Aunty Fanan Abinci a baki ai tasan yana bata dama, d'age mata gira yay ya tambayi a yaushe tasan hakan tace "a can baya mana lokacin ranar nazo nan gidan har na kawo mata wainar fulawa daga baya da aka ce an shirya table ta matsa man sai munje an ci Abincin da ni, koda naje ma kasa wani ci nayi na taso na dawo parlor, dama ranar da k'yar nazo sai da gwaggo ta ce ya kamata in zo ita ta damu dani tana ta zuwa" a shagwa6e take Maganar gaba d'aya ya zuba ma bakinta ido har ta gama sannan ya k'ara d'age mata gira yace "lokacin kina ciwon so na?" wani kallo tay mashi ta d'an tura baki ya ce ta bashi amsa kawae sai tasa hijab ta rufe fuskarta tana dariya, k'ok'arin bud'e Fuskar ya fara ta bi ta k'ank'ame ta, wani abu ya fara mata yana cigaba da k'ok'arin bud'e Fuskar sai ta ji yanayin yadda take jin abunda yake matan yayi mata kaman cakulkulo ai kuwa cikin d'an k'araji ta fara fad'in "Ya Haisam!....don Allah ka bari.... Wayyo Allah zan bud'e wllh, ka bari don Allah......" ba Arzik'i ta bud'e Fuskar tana haki da dariya, shima dariyar abunda ta rink'a yi yake, ce mata yay to ta fad'i mashi still tana a jikin shi saidai ta zame ta kwanta sosae, d'aga mashi gira tay irin yadda yake mata yace ta bud'e baki a shagwa6e tace "Ehhhhh" d'an bud'a mata ido yay yace "Eh What?" tura baki tay "kai Ya Haisam ba ka gane ba" d'an girgiza mata kai yay alamar bai gane ba ta tura baki, kawai taga ya d'ago hannu aikuwa da sauri ta tare hannun tana dariya tace "Ehh lokacin ina ciwon son ka" sosae yadda tayi Maganar ya bashi dariya sukai tayi a tare saidae ita tafi shi yi,
bayan ya tsagaita yin dariyar yace "ni yaushe za'a canza man suna ne" d'age mashi gira tay "kana so ne?" da murmushi ya d'aga mata kai, tace "to wane suna kake so?" wani kallo yay mata mai kaman harara yace shi zai fad'i mata shi da ya canza mata ita ta fad'i mashi, d'an jimm tay ta kanne ido guda alamar tunani can tace "To Sweetheart?" shiru ya d'an yi sai kuma ya girgiza mata kai yace bai son shi ai dama tana ce mashi haka tace to ai da hakanan take ce mashi ko yanzu kuma da dalili yace to ai shiyasa yake son a canza, jimm ta k'ara yi tace to tunda shi yana da jinin larabawa bari ta rink'a ce mashi Habiby waro ido yay jin irin sunan da Mom d'in shi ke fad'a mashi ne ya girgiza mata kai yace a canza wani tace to Honey, wannan karon yar dariya yay yace to ai duk kusan d'aya ne da Sweetheart d'in, d'an yamutsa fuska tay ta d'an Jujjuya jiki cike da shagwaba tace to ita ta rud'e ta rasa wanda zata za6o yay shiru dae yana bin ta da ido da murmushi can tace "Yauwa to Hubby" Dariya yay kawai bata san shi yadda take mashi Maganar bane yake burgeshi shiyasa yake ta jan abun, tambayar shi tay yayi ya d'aga mata kai harda d'an d'aga hannuwa ta jinjina su alamar jin dad'i, shiru sukai suna ta kallon juna kowanne face d'in shi d'auke da Murmushi can yace mata mi ta zauna yi k'asa ne bata je Parlor ba ko ta hau gado tace mashi Sallah tayi da ta gama Addu'a sai kuma tayi zaune, tambayar ta yay Addu'ar mi tayi tace da yawa, hannu ya kai ya kama hannunta ya d'agata ta zauna sosae suna kallon juna yace to ta fad'a mashi Addu'o'in da ta yi,
"Nayi ma mamana na rok'i Allah ya jaddada rahama a gare ta da sauran wanda suka rasu...." jinjina kai yay Slowly ya furta "Ameen" cigaba tayi "Sai Baffana da gwaggo harda Hajiya na rok'i Allah ya k'ara masu lafiya da nisan kwana mai Albarka" lumshe ido yay, ta sake cewa "Aunty Fanan ma nayi mata Allah ya bata lafiya ya kuma had'a kan mu, sai su Kawu Amadu da sauran yan'uwa harda k'awaye na su Fauzy na rok'i Allah itama ya bata Miji na gari wanda zai sota tsakani da Allah ya riketa da Amana harda su Mino ma" jinjina mata kai yay a hankali yace Allah ya amsa, shiru tay yace Shikenan ta d'aga mashi kai, wani kallo yay mata mai kaman harara tana ganin haka tasa dariya tace "to ai kai fa na fara yi mawa Allah, na rok'i Allah ya k'ara ma rayuwar ka Albarka yasa ka gama da iyayen ka lafiya ya k'ara maka lafiya da Arziki mai Albarka ya biya maka dukkan bukatunka na Alkhairi yasa ka dawwama a cikin farinciki ya kuma bani ikon yi maka biyayya" lumshe ido yay ya saki k'ayataccen murmushi sosae yaji dadin Addu'oin ya amsa mata da Amin, ce mata yay ita bata ma kanta bane tace tayi yace to ta fad'i mashi wacce tayi ma kanta wani kallo tay mashi tana dariya da alamun kunyar fad'i take ji yace yana jin ta, cikin jin kunya tace "Na rok'i Allah yasa....in samu ciki in haiho yaro mai kama da kai sak" da k'yar ta k'arasa Maganar tana rufe fuskarta da hannunta d'aya, yana murmushi yace bata son mai kama da ita ta d'aga mashi kai, tambayar ta yay miyasa take son mai kama da shi tace "Saboda nasan ba kowane lokaci zamu kasan ce a tare ba kaga in na haifi mai kama da kai ko baka nan zan rage kewar ka in ta kallon fuskar shi" tana yar dariya ta k'arasa Maganar, jinjina kai yay ya d'an kalli gefe alamar tunani kafin ya juyo yace mata to taji wani alama, ta d'an bud'a ido tace alamar mi, wani kallo yay mata da sauri ta maida fuskarta gefe, ce mata yay ta bashi amsa ba tare data kalle shi ba a shagwabe tace ita ya za'ai ta gane,
"But, did you feel anything last time?" Yay tambayar ya kafeta da ido, d'an jimm tay sai kuma ta yarfa hannu cike da kunya tace itafa bata fahimci komai ba lokacin, yace "Ok I forgot, u were in severe pain lokacin ba zaki fahimta ba" ita dai shiru tayi taga ya mik'e, Hijab d'in jikinta ya cire da kan shi ya kaita wardrobe tana ta kallon bayan shi, dawowa yayi ya duk'a a gabanta yasa hannu ya duk'o da kanta saman chest din shi ya kai hannu ya cire mata necklace d'inta bayan ya dagota ya had'a da earrings d'in gaba d'aya jewellery d'in ya cire ya kai saman dressing mirror, saida yaje ya sa ma kopar Bedroom d'in key sannan ya dawo wurinta gaba d'aya ya ciccibo ta yana fad'in Let them try their luck now.........
*ASM 076*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........Gab da kiran sallar Magrib Haisam tsaye a gaban mirror ya gama shiryawa cikin jallabiya, bai dad'e da ya fito daga wanka ba bayan ya tashi bacci, gado ya nufa ya hau ya matsa kusa da Fatuu dake lullu6e da duvet tana ta shan bacci, hannu ya kai ya shafi fuskarta tare da kiran sunanta, ganin tak'i tashi yasa shi d'an bubbuga fuskar a hankali yadda bazata ji zafi ba, motsi ta fara yi kafin ta fara bud'e idanun tana yi tana lumshe su har ta bud'e su gaba d'aya sun d'an yi ja, bin juna sukai da kallo Haisam na d'an murmushi yace "My Lazy Wife" jin haka yasa ta tura mashi baki a shagwabe tace itace lazy d'in ya d'aga mata gira alamar eh, k'ok'arin rufe fuskarta da duvet ta shiga yi ta d'an d'aure ta ita ala dole tayi fushi, da sauri ya ruk'e Duvet d'in yace mata wasa yake mata ita ba lazy bace shi shaida ne, ganin irin kallon da yake mata yasa ta d'an juyar da fuskar ta tana yar dariya, ce mata yay ta tashi taje tayi wanka lokacin salla ya yi ta d'aga mashi kai, hannu ya kai zai d'ago da ita da sauri ta k'ank'ame duvet d'in tace yaje zata tashi yanzu, murmushi kawai yay ya juya ya saukko daga kan gadon, tanata kallon bayan shi har ya bud'e k'opa ya fita, lumshe ido tay tana ta sakin k'ayataccen murmushi da alama itama ta zaucen, daga baya ta saukko ta nufi toilet.
Bayan ta gama sallar Magrib mik'ewa tay ta d'aukko wayarta ta dawo kan prayer mat d'in ta zauna ta shiga kiran Fauzy, tana fara ringing ta d'auka suka gaisa tace mata ya School Fauzyn tace ta manta Weekend ne tana gida ai, d'an shiru Fatun tayi jin haka yasa Fauzy tambayar ta lafiya, tace "kin san Fauzy Ya Haisam fa ya dawo" da alamun mamaki tace mata da gaske Fatun tace mata "Eh, kuma harda Aunty Fanan ma, ashe wannan sak'on da kika tura sun gani kuma lokacin daya shiga ma ita ta fara gani wayar na a hannunta" wani uban salati Fauzy ta buga har saida ta kusa sa Fatuu fashewa da dariya don a matuk'ar razane ta yi shi, a rud'e ta shiga tambayar ta yanzu ya akai, mi ya faru, da alamun damuwa Fatun tace mata bata yarda ba rigima tasa wai sai an sake ta shine suka taho, wani salatin Fauzy ta k'ara saki, a iya muryarta zaka shaida ba K'aramin tashi hankalinta yay ba, a kid'ime tace ma Fatun to shi ya Haisam d'in miya ce, don kada taci gaba da tada mata da hankali tasan hakan bashi da kyau yasa ta saki dariya tace "sorry k'awata ina tsokanar ki ne amman da gaske ya dawo kuma taren suka zo sannan da gaske ita ta fara ganin sak'on" da sauri Fauzy tace "to yanzu miya faru don Allah??" Fatuu na murmushi tace mata Alkhairi, nan ta kwashe yadda komai ya faru harda bayyana mata da ya Haisam yayi yana son ta shima, wata uwar k'arar murna Fauzy ta saki Fatuu nata dariya tana jiyo ta tana k'wala ma Aunty Mareeya kira tana fad'in the long expected day has come, d'akin Aunty