Showing 141001 words to 144000 words out of 512766 words

Chapter 48 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1640

ta tuno da ran da tazo kawo mashi takardar list d'in littattafan da yace taje ta d'aukko bata gan shi a parlon ba ta zo bakin corridor ta tsaya tana yin sallama tace ga takardan, jin shiru bai amsa ba yasa tace ko ta shigo ne ta kawo mashi ya bata amsa da tunda d'akin ta ne ai sai ta shiga daga bayanta ashe bai a cikin d'akin, wani irin murmushi ta saki har fararen hak'oran ta suka d'an bayyana a ranta ta ayyana yanzu gashi ya zama nawa d'in gani ma zaune a saman gadon ka, k'ara tunano lokacin da zai kaita makaranta tay da tace don dai ita k'arama ce da sun yi soyayya kuma in ta gama Secondary School cigaba zatai da karatu yace to ko ya jirata ne tace ai lokacin ita ta zama babbar budurwa shi ya kuma ya tsufa, tace in yana so zata had'a shi da yar ajin su sofiya moussa yace bai sata ba daga baya kuma ta hau yi ma safiyar sharri har tana ba ma lalle ya so ta ba don k'aton baki gare ta hak'oranta kuma sun d'an turo kuma bata da jiki kamar sandar suluka take, tunano hakan har saida tay dariya mai d'an sauti, ita kanta tasan tayi ma Haisam hauka iri iri kafin ta girma amman bai ta6a yin fushi da ita ba ko ya canza mata, in ma tayi abunda ya nuna ta 6ata mashi rai da ta bashi hak'uri yake hak'ura, tabbas dole ne ka ra6i Haisam sai ya burge ka don komai nashi na musamman ne samun irin shi wanda ya had'a abubuwan da ya had'a zai matuk'ar wahala, ga tsantsar kyau, ga kud'i, ga kirki, ga hali mai kyau, ga ilimi, ita kam ko iya haka ta gode ma Allah don ya gama mata komai samun Haisam a matsayin miji ba k'aramar baiwa bace wllh, wata zuciyar ce ta raya mata in kuma bai son ta fa kuma dangin shi suka k'i amincewa da ita, sosae jikinta yay sanyi lakwas yin wannan tunanin, tasan koda bai son ta bazai cutar da ita ba tana da tabbacin hakan inda za'a samu matsala wurin dangin nashi ne in basu amince da ita ba ga kuma matar shi Fanan, sosae Fatuu ke jin zullumin abunda zai je ya dawo in ta samu labarin auren nasu don ita shaida ta kan irin son da take ma Ya Haisam ga hirar da ta ta6a ji yana yi da Abbas da ta tabbatar da cewa Fanan d'in ce ta fara son shi da ya nuna baiso shine har ta kwanta gadon Asibiti, tsayawa tay da yin tunane tunanen Saboda gaba d'aya jikinta ya mutu ta zuba ma bangon da take facing ido a ranta ta shiga ayyana ita bazata so Ya Haisam ya shiga matsala Saboda ita ba, in dae bai son ta da bai cigaba da zama da ita ba, wata zuciyar tace ki ka sani ko yana son ki kaman yadda ake hasashe tunda har abu ya shiga tsakani kuma ya nuna rashin jin dad'i da kika zubar da cikin, shiru tay don a wannan ga6ar baza ta iya yanke hukunci ba duk da a yanzu tasan gaba d'aya abunda ya farun bada niyya bane kuma da ya nuna yayi fushi kan abunda tay k'ilan don aikata hakan laifi ne kaman yadda ya fad'a mata da taje bashi hak'uri da kuma gudun kar wani abu ya faru da ita ba wai don yana son cikin ba ko ita, haka tay ta sak'e sak'e, jin Abdul yay tsit yasa ta kai idonta kan shi taga ashe yayi bacci ta fara k'ok'arin gyara mashi kwanciya a gefen ta tana cikin haka taji an turo kopar Bedroom d'in ta kai idonta da sauri, Kawu Amadu ne ya shigo yana sanye da sabuwar shadda light blue da ya d'inka musamman Saboda ranar, suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi ya iso bakin gadon ya zauna sai faman murmushi take mashi ta kasa yi mashi magana,

"Amarya, Allah dai ya amince Romeo ya zama naki" ya fad'a yanata murmushi still itama murmushin take ta k'i cewa komae,

"Ko duk Farin ciki ne ya hana ki magana?" Ya fad'a yana murmushi da sauri tasa tafukan hannuwanta da suka sha k'unshi ta rufe fuskar ta, bayan ta cire tana kallon shi yace "kinga ikon Allah ko?" Kai ta d'aga mashi alamar eh, "zaki iya tuna abunda na fad'a maki a can baya lokacin dana iske ki a d'aki cikin mawuyacin hali har kika fad'a man Saboda Ya Haisam ne?" Shiru bata ce mashi komae ba ta maida idanun ta k'asa, yaci gaba "lokacin na fad'i maki in Ya Haisam rabon ki ne kina zaune ba tare da wata wahala ba za ki ga yazo ya Aure ki har kita mamakin yadda akai hakan, kin tuna?" d'agowa tay ta kalle shi tare da d'aga mashi kai, yaci gaba "kin ga maganata ta tabbata, Wannan kad'an ne daga cikin ikon Allah, in dae zaka dogara gare shi to tabbas zaka samu biyan buk'ata ba kamar in ka had'a da hakuri da kuma Addu'a, in kika ga duk kin yi wannan amman bukatan ki bata biya ba to abun ba Alkhairi bane gare ki sai ya musanya maki da wanda yake Alkhairin, shi yasa ake son bawa ya kasance mai yawan godiya ga Allah, in ka samu ka gode mashi haka in ka rasa, a koda yaushe in zaka yi Addu'a to ka rok'i abunda yafi zama Alkhairi a gare ka, duk abunda kaga kasamu to shine yafi Alkhairi, Allah ubangiji da kan shi acikin suratul baqara yace zaku so wani Al'amari alhali ba Alkhairi bane a gare ku, haka zaku K'i wani Al'amari alhali Alkhairi ne a gare ku, Allah ne mafi sani ko baku sani ba, to kinga ba buk'atan ka matsa ma kan ka akan dole sai ka samu wani abu tunda ga mai badawa wanda ya san abun Alkhairi ne a tare da kai ko sharri sai ka mik'a komai a Wurin shi ka dage da Addu'a, a k'arshe ina taya ki murnar samun abunda ran ki ke so ina fatan kuma ku zame ma juna Alkhairi, Allah ubangiji ya bashi ikon ruk'e ki da Amana ya kauda dukkan wata fitina, kema Allah ya baki ikon yi mashi biyayya ya albarkace ku da zuria d'ayyiba Amin" idon shi a Kanta ya k'arasa fuskar ta da d'an murmushi take kallon shi ba tare da ta ce komae ba, d'an tsuke fuska yay yace "ba zaki ce Amin ba" d'an yamutsa fuska tay ta d'an sa hannu ta rufe wurin idanun ta alamar kunya, yace "ke ni zaki wani nuna ma ke mai kunya ce, miye abun kunya an roka maka abun Alkhairi ba sai ka amsa ba" jin haka yasa ta ce Amin a hankali tare da d'an kallon k'asa, kafin ya kara cewa wani abu aka turo k'opar bedroom d'in gaba d'aya suka kai idanun su wurin Tk ne ya shigo shima yana sanye da irin shaddar Amadun da alama anko su kai suna had'a ido da Fatuu ya washe baki ya tunkaro su yana fad'in "Amaryar mu, amaryar mu" yadda ya furta sautin kaman Wak'a Fatun tana ta murmushi ya k'araso bakin gadon shima ya zauna kusa da Amadu ya k'ara ce ma Fatuu dake kallon shi Amaryar su ta gaida shi, da sauri yace "ah ai yanzu ni ne yakamata in rink'a gaishe dake tunda kin koma Aunty na" bata ce komae ba tana dae ta murmushi ya juya kan Amadu yace "kaga ikon Allah ko, yanzu fa dole in rink'a girmama ta tunda ta zama Matar Yayana kuma uban gidana" yar dariya Amadu yayi Tk d'in ya juya kan Fatuu yace "Aunty Amarya Allah yasa dae a rink'a rangwanta man, a da daba k'ark'ashin ikon ki nike ba ma baki d'aga man k'afa ba balle kuma yanzu da kike da cikakken iko dani...." Maida kallon shi yay kan Amadu yace "AA (Ahmad Abdullahi) ka tuna can baya lokacin da aka sa in kaita yawon salla ta maida ni kaman yaron ta tay ta wahalar dani?"

"na tuna mana har saida kay ciwon k'arya" ya k'arasa yana dariya shima Tk tuntsirewa yay da dariya tunowa da lokacin, Fatuu ma dariyar take dama lokacin daga baya ta gane ciwon k'arya ne har ta fad'i ma Haisam bayan ya dawo tace bata gama yawon ba har ta rok'e shi ya idasa kai ta hakan ne silar farkon zuwan ta gidan Abbas, Amadu dake kallon shi yace "har ka kai Yayar Fauziyyar ta d'aukko sauran kayan?" d'an girgiza kai Tk yay "No tace in bata makullin Motar ta iya sai
su d'aukko ni in huta shine na bata" kai Amadu ya d'aga Tk ya juya kan Fatuu dake kallon su, da murmushi yace "na taya ki murna yar k'anwar mu yanzu kuma Auntyn mu, Allah ubangiji yasa Alkhairi ya baku zaman lpy, wllh baki ji dad'in dana ji maki ba lokacin dana samu labarin auren, Ya Haisam cikakken mutum ne harda ma rabi, samun shi matsayin abokin rayuwa abun a taya mutum murna ne sam bani da shakku a kan shi don yayi 100% kuma kun bala'en dacewa wllh, zaku ji dad'in yin rayuwa tare don kun riga da kun gama fahimtar juna, shine zai iya maki don ma yanzu naga kin natsu....au tuba nike Hajiya tah su6ul da baka ne" gaba d'aya suka sa dariya ya k'ara cewa "dama ni ne mai kula da part d'in nan wurin gyara shi, to yanzu Aunty zan ci gaba da aiki na ne ko yaya?" Yay tambayar idon shi akan Fatuu dake ta faman sakin murmushi ta kasa ce mashi komae,

Amadu ne yace "ah dama ai don ba mata ne, yanzu kuma tunda gata na me kaci gaba ita zata rink'a gyarawa" da sauri Tk yace "No ka bar Hajiyata ta yanke hukunci don itama tana da iko dani yanzu" ya juya kan Fatuu yana fad'in ta yanke yadda za'ai sai Faman dariya take, da k'yar tace mashi ai ba ita zata yanke hukunci ba Ya Haisam ne yace shikenan, ya juya kan Amadu yace "gaskiya AA yakamata muma fa mu fara haramar shigewa daga ciki, ko da yake k'ilan ma sai na riga ka kai da ko budurwa nasan baka da ita, ko kayi ta Yanzu?" Amadu dake murmushi ya girgiza mashi kai alamar a'a,

"Gaskiya yakamata ace by now kana da budurwa ko kuma ka tsaida wadda zaka aura tunda nasan ba'a rasa masu son ka kaine kawae baka basu dama" Amadu dake yar dariya yace "No k'yale budurwar nan bari dae in nemi kud'i su taru tukunna in lokacin auren yayi zaka ga bazan sha wahalan samu ba tunda na gama had'uwa" dariya sosae Tk yasa bayan ya tsagaita yace "kuma wllh in dae kana da kud'i bazaka sha wata wahalan samun irin Matar da kake so ba, wai ni yanzu yan mata na soyayya tsakani da Allah kuwa? Ni kaina nan wai d'an ganin da ake ina fantamawa da motoci aka kuma ji gidan da nike kar kaso kaga yadda yan mata suke lik'e man, nan basu san Almajiri bane" gaba d'aya sukai dariya Amadu yace ai yanzu yafi k'arfin a ce mashi Almajiri shima ya zama dangin Senator d'in, suna haka aka turo k'opar duk suka kai idanun su kan masu shigowar, Abbas ne da Saleem da k'yar Abbas ya matsa mashi suka shigo don ya k'iya yace mi zai shigo ya yi, su Amadu na ganin su suka mik'e suna gaishe dasu kafin suka nufi kopar fita su kuma suka k'arasa shigowa ciki idanun su akan Fatuu da itama kallon su take da d'an murmushi haka Abbas ma murmushin yake mata, a gaban gadon suka tsaya yana kallon ta yace "Mom Zarah Amaryar mu, an daina kukan ko?" Kai ta d'an d'aga mashi alamar eh kafin a Sanyaye ta gaishe dasu suka amsa,

"haka yakamata ai kar ya haddasa maki wani ciwon muda muke so a biya mu abunda muka rasa a yau......", bai rufe baki ba daga bayan shi yaji an ce "mi kake ci na baka na zuba ai kunsan dai ita d'in bata wasa bace da kun bata zata biya ku" Aunty Mareeya ce da ta shigo ruk'e da kwalin kwalaben kayan k'amshi tay Maganar duk suka juya har da Saleem suka kalleta Fatuu kuwa wata irin kunya ce ta rufe ta da sauri ta sadda kan ta k'asa, shigowa tay cikin d'akin ta nufi wurin dressing mirror Abbas ya bita da murmushi don sai ya d'an ji kunya duk da tun a Mota wurin kawo Fatuu ya fahimci bakin ta a sake yake itama, Saleem ne ya kalli Fatuu cikin cool voice d'in shi yace mata Allah yasa Alkhairi bata amsa ba sai d'an murmushi kawae tay mashi Aunty Mareeya ce ta amsa tare da juyowa ta kalle shi kafin ta maida idon kan Abbas dake ta murmushi itama ta yi had'i da d'an girgiza kai tana a gaban dressing mirror, ta fiddo wasu had'add'un kwalaben humra da turaren wuta tana jerawa a wurin a parlor ma ta jera wasu a cikin gidajen da su tv suke sosae suka k'ara k'awata wurin, Saleem ne ya juya zai tafi Abbas dake kallon Fatuu yace mata bari su je sai ya kawo mata Angonta Aunty Mareeya tay carab tace suna jiran shi yazo ya siya bakin Amarya a wurin su tay Maganar tana dariya shima Abbas d'in dariyar yake ya juya suka fita,

bayan fitar su Fauzy ta shigo ruk'e da burner data gama turara parlor ta jona ta anan aka zuba turare Bedroom d'in ya fara turaruwa shima Aunty Mareeya da ta gama ta shiga yi ma Fatuu bayanin yadda zatay amfani da wasu daga cikin kayan kamshin ita dae kai kawai take d'aga mata, bayan an gama turara d'akin Fauzy ta hau gyara bedroom d'in duk da ba wani 6aci yay ba tana cikin gyaran Aunty Mareeya ta sake shigowa hannunta ruk'e da cup ta nufi side d'in da Fatuu take ta zauna a bakin gadon ta bata tace ta shanye abun ciki, ba musu ta amsa ta kafa baki saida ta shanyen ta mik'a mata Cup d'in tace ta taso zata nuna mata abu a kitchen tace mata to ta zuro da k'afafun ta ta mik'e suka nufi hanyar fita Fauzy nata sakin wani kalan murmushi wanda da gani da biyu take yin shi, bayan sun je kitchen d'in bin d'akin Fatuu tay da kallo an tsara shi ya koma babban Kitchen a ranta ta shiga tuna lokacin da ta fara shigowa cikin shi yin fitsari da ta zo ba Haisam hak'uri da kuma lokacin da yay mata Assignment d'in maths tuna lokacin har saida ta saki murmushi, waya ta6a tunanin wai d'akin zai zama kitchen d'inta gaba d'aya part d'in ma, wata drawer Aunty Mareeya ta jawo ta ce ta matso, nuna mata abubuwan dake ciki tay wanda sauran magungunan ta ne da aka siya mata a wurin Aunty Bee ta shiga yi mata bayanin yadda zata rinka amfani da kowanne Fatun na d'aga mata kai har ta gama, tambayarta tay ko a cikin kitchen d'in akwae abunda bata iya amfani da shi ba ta gwada mata, a sanyaye tace duk ta iya tana ganin yadda Aunty Saude mai aikin nan gidan ke amfani da su Aunty Mareeyar tace da kyau daga haka suka fito suka koma Bedroom d'in, suna komawa Feenah ta shigo tace ma Aunty Mareeya ance su fito za'a maida kowa gida tace to dama sun gama mata komae ai, ta kalli Fatuu da tay zuru jin zancen zasu tafin ta tambaye ta akwai wani abu ta girgiza mata kai sukuku da ita ta juya ta nufi wurin k'atuwar wardrobe d'in d'akin, a gefenta ta d'aukko jakar ta ta dawo bakin gadon Feenah na tsaye, zuge zip d'in jakar tay ta kai hannu ta ciro wata farar shopping bag mai d'auke da tambari ta d'aura ta akan cinyoyin Fatuu tace "Yar k'anwata Amarya ga tawa gudunmawar nan saura kuma kice zaki k'i yin amfani dasu Saboda wai kunya, ke da shi yanzu ba sauran wata kunya don kun riga kun zama abu d'aya, an san kunya abu ce mai kyau amman yanzu a wani wurin in kika ce zaki saka kunya to zaki k'wari kan ki ne da kuma shi Mijin naki don haka ba a komai zaki rink'a nuna kunya ba....." Katse ta Feenah tay da fad'in "ba kamar yadda take da kishiya kuma ma baturiya, gaskiya dole sai kin zage wllh don su ba wata kunya gare su ba don ma ita tana ruwa biyu....." Aunty Mareeya ta kar6e "kin ji dai ko, wannan nasan har yawo daga ita sai d'an pant in ma tasa kenan tana iya yi a gaban shi, don haka ki zage wllh balle ke da ma kike da surar jan hankali Tubarkallah, ki kuma dage da gyara jikin ki ciki da waje, duk magungunan da nayi maki bayani kada ki wasa da shan su sannan kuma kada ki k'asa a guiwa wurin faranta mashi irin su ta nan wajan aka fi kama su, ki sashi ya susuce ta yadda duk in zaiyi Magana sai ya ambaci sunan ki alamar kece a ran shi koda yaushe" gaba d'aya suka sa dariya harda Fauzy dake can d'ayan side d'in gadon raku6e,

Feenah ta d'aura da fad'in "Bayan wad'annan kuma sai a had'a da biyayya don itace zata k'ara taimakawa wurin siye zuciyar shi duk da nasan ke mai biyayya ce a gare shi tun ba yanzu ba, to ki k'ara akan wadda kike mashi don yanzu ne zata fi yin aiki kuma zaki fi cin ribar yin ta, a k'arshe ina Addu'ar Allah yasa Alkhairi a zaman ku ya had'a kawunan ku gaba d'aya da abokiyar zaman taki ya kauda fitina ya bashi ikon yin Adalci a tsakanin ku, ya albarkace ku da zuria d'ayyiba" su Aunty Mareeya ne suka amsa ita kuma Fatun kan ta na a k'asa, lokacin Abbas ya lek'o cikin d'akin yace su suke

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login