Showing 126001 words to 129000 words out of 512766 words

Chapter 43 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1569

rage, tun bayan da gwaggo ta fita tay zaune zugudum ta rasa Mike mata dad'i ita dai har ga Allah zallumin zama part d'in nashi take ba tare da dangin su sun san da auren ba sam hankalinta bai kwanta da hakan ba, tana haka Gwaggo ta k'ara shigowa hannunta ruk'e da cup mai d'an girma a bakin gadon ta tsaya ta mik'a mata ta ce ta shanye abun ciki maganin sanyi ne ba tare data ce komai ba ta amsa ta kafa baki nan da nan ta shanye shi tass don dama ta saba bata tun kwanakin baya harda itatuwan tsarki da na sha duk ce mata take na sanyi ne, bayan ta shanye ta mik'a mata Cup d'in ta amsa ta juya Fatun ta bita da kallo don a yanzu ta gane ko magungunan miye take bata da sunan na sanyi, can wata zuciyar ta raya mata ko shiyasa ma lokacin da abun ya faru Ya Haisam d'in ya rikice mata tamkar bashi ba duk da rok'on shi da ta rink'a yi amman a banza, tuno lokacin yasa ta saki d'an murmushi tasa tafin hannunta ta rufe idanunta alamar kunya tana haka ta tuno da magungunan da Fauzy ta kawo mata na yar kwalbar inserting d'in shi ake bayan wasu mintuna sai a wanke da ruwan d'umi wata zuciyar ta raya mata tay amfani dashi yanzu sai kuma ta tuna da jinin da take hakan yasa ta bari sai ya d'auke sai wanda ake ci da nama gashi yanzu ta gama cin naman saidae ba dama ta sa a gaban gwaggo d'ayan kuma da peak milk tunanin ko taje shagon Kawu Amadu ta amso Madarar tay amman kuma ta k'oshi sosae gashi yanzu gwaggo ta bata wani k'arshe ta yanke gobe tayi amfani dasu kawae ta sauka don taje ta wanko hannu ta sha ruwa, tun bayan da ta kwanta bacci ya k'aurace ma idanunta sai juye juye take tana tunanin wane irin zama za tay da Ya Haisam matsayin miji kuma ta koma part d'in shi ganin abun take kaman wasa wllh, can kuma ta koma tunanin ya Aunty Fanan zata ji in taji Maganar auran na su ita da yan gidansu har saida gabanta ya fad'i tunowa da Mahaifiyar Fanan d'in wato Hajiya Maryam jikinta ne yay wani mugun sanyi don ta santa tana da kirki amman fa jarababbiya ce ta gaske a hankali tunanin ta ya koma kan yan gidan su Haisam su wannan bazata iya yanke hukunci a kan su ba kawai dae tasan suna da kirki sosae kuma tana Mutunci da wasu daga cikin yan gidan kaman Nameer, Jidderh dasu twins wannan sun ma maidata tamkar yar'uwar su haka Mahaifiyar Haisam d'in ta san ta sosae kuma duk in tazo tana zuwa ta gaishe da ita cikin sakin fuska take amsa mata bata san in suka ji zancen auren ko zasu amince ba, damuwa ce kwance akan fuskar ta haka taci gaba da tunane tunane har bata san lokacin da bacci ya kwashe ta ba, Washe gari da niyyar zuwa Makaranta ta tashi ta hau shiri ba 6ata lokaci gwaggo na cikin Kitchen ta iske ta bayan ta amsa mata gaisuwar ta ta bita da kallo ganin ta sanye da Uniform yasa tace mata ba dai Makaranta wai zata je ba tace eh ai ta samu sauk'i, girgiza kai gwaggo tay "koda kin samu sauk'i bazaki je ba gaskiya har sai shi Mijin naki ya baki izini tukun kar ai rashin hankali" yamutsa fuska tay kaman za tai kuka tace "amman gwaggo ko da ai da auren nike zuwa ko har ma in zauna a can" gwaggo dake kallon ta ta d'an d'aure fuska tace "da kika ce lokacin baki san da auren ba yanzu kuma kin sani don haka duk abunda zaki sai da izinin shi" idanunta cike da k'walla tace "to gwaggo in kika ce sai ya bada izini har sai yaushe kenan zan ci gaba da zuwa kina gani fa ko jiya bai shigo ba Kawu Amadu ya ba sak'o" tace "ba kina da waya ba ki kira shi mana ki fad'i mashi" tura baki tay tana cigaba da yamutsa fuska had'i da kikkafta idanu gwaggon ta mik'o mata abun breakfast tace taje tayi yadda sukai da shi to ta amsa ta juya, tana komawa d'aki ta aje kayan Breakfast d'in akan Carpet ta koma bakin gado ta zauna sai k'unci take ita sam bata son ta kira shi don bata san mi zata ce mashi ba da sunan neman wani izini shi da ko kiranta bai yi ba tun bayan da suka dawo har yanzu sai ita ce zata kira shi, tana ta zaune cikin 6acin rai can dubara ta fad'o mata da sauri ta kai hannu ta d'aukko jakar goyonta ta bud'e wayarta ta fiddo ta fara kiran Abbas tana fara yin ringing ya d'auka bayan ta gaishe da shi yay mata ya jikin ta amsa daga nan tay shiru jin haka yasa shi tambayar ta da wani abu ne murya kaman zata yi kuka ta fad'i mashi makaranta take son zuwa amman gwaggo ta hana wai har sai Ya Haisam ya bada izini kuma tun jiya daya maido su ma ita bata k'ara ganin shi ba tambayar ta yay har ta samu sauk'in da zata iya cigaba da zuwa School tace mashi eh har yana cewa kodae ta bari ta k'ara warwarewa amman ta kafe kan ta samu sauk'i ko ta zauna ba abunda take sai kwanciya kuma can ana ta wuce ta, sigh yay jin haka yace ta bashi wasu mintuna zai sake kira tace to, bayan sun gama wayar ta saukko ta fara yin breakfast don ranta ya bata zata je Makarantar tana cikin yi sai gashi ya sake kira bayan tayi picking yace ta zama cikin shiri ga Mijin nata nan zai zo ya kaita ya k'arasa yana yar dariya tace ta gode, cire wayar tay ta bita da kallo jikinta ne yay sanyi jin shi zai kaita aje wayar tay taci gaba da yin Breakfast d'in, tana gamawa ta jiyo horn d'in shi har saida gabanta ya fad'i ta d'an yi jimm lokacin taji ya k'ara yin wani ta yunk'ura ta mik'e, gado ta nufa ta goya jakar ta ta sa hijab dake aje saman gadon bayan tasa fararen takalman ta na makaranta ta d'auki tray d'in kayan breakfast d'in ta fita, kitchen taje ta aje su ganin gwaggo bata ciki yasa ta fito ta nufi d'akinta tana zaune kan carpet itama tana yin breakfast d'in ta shiga ta d'aura idonta a kanta Fatun tace mata gashi nan yazo zata tafi gwaggon tace "to a dawo lafiya kinga ai hakan yafi da ai abu kai tsaye" bata ce komai ba tana shirin juyawa gwaggo ta sake cewa "amman fa gida zaki dawo don zama a Makaranta ya k'are in ma kina da kaya ki kwaso su yau kin ji ni?" Kai ta d'aga mata kawai ta juya ta fita, bayan ta fito ta nufi d'ayan side d'in Motar ta kai hannu ta bud'e lokacin da ta shiga idonta ya sauka akan shi har saida gaban ta ya d'an fad'i tay saurin d'auke idon ta ta rufo kopar, juyawa tay ta d'an kalle shi yana sanye da jallabiya ta gaishe dashi ya amsa ba tare da ya kalleta ba yaja Motar suka fara tafiya ta juyar da fuskar ta gefe wani abu taji ya tokare mata k'irji wai ita Ya Haisam ke sharewa haka idanunta ne suka ciko da k'walla da sauri ta fara K'ok'arin maida su don bata son su zubo mata, har suka isa fuskar ta na gefe ya parker inda ya saba aje ta tace mashi an gode ba tare da ta kalle shi ba tana niyyar juyawa don ta bud'e kopar taji yace mata "Wait" dakatawa tay still bata kalle shi ba saida taji yace mata ta amsa sannan ta juya ta kalli kud'in da yake mik'o mata yan dubu duba bin kud'in tay da ido kafin ta d'ago a raunane ta kalle shi suka had'a ido da sauri ta kawar da nata ta furta "ka bar su" shiru bai tanka mata ba bai kuma janye kud'in ba yamutsa fuska ta fara yi tana d'an kikkafta ido a K'ok'arin ta na kada tay kuka ta sake juyawa still kallonta yake fuskar shi ba yabo ba fallasa ta sake ce mashi tana da kud'i nan ma bai tanka ba bai kuma janye kud'in ba bata da yadda zatay ba don ta so ba tasa hannu ta kar6a wani irin bak'in ciki ne ya turnuk'e ta ta shiga ayyana wato ita ga mayyar kud'i, ko tambayar ta ya jiki bai yi ba sai wasu kud'i zai bata, can k'asan mak'oshi ta furta mashi ta gode tana shirin juyawa ta bud'e taji yace mata ya jikinta har bata san lokacin data juya ta kalle shi ba kaman mai jin zancen zuci, d'auke idon tay ta ce mashi ta samu sauk'i daga haka ta juya ta bud'e Motar ta fice, saida taji ya juya Motar ya tafi sannan ta tsaya da tafiya ta juyo tana kallon Motar idanun ta cike da k'walla sharr suka fara zubowa tasa hannu tana gogewa kafin ta juya ta nufi aji, tana shiga suka had'a ido da Fauzy aikuwa ta taso da gudu ta nufo ta tana fad'in Oyoyo Bestie nah, tana zuwa ta kankame ta gaba d'aya hankalin yan ajin ya dawo kan su, sakin ta tay tana kallonta da murmushi da alamun mamaki tace mata wai har ta warke ta d'aga mata kai, kama hannuta tay suka nufo cikin ajin ana ta mata sannu da jiki tana amsawa, koda suka zauna akan seat d'in su haka a kaita tasowa ana zuwa yi mata ya jiki harda Zainab Muhammadu nan ta hau ce ma Mutane wllh su zo su nemi yafiyar ta zargin ta da sukai na tana da ciki bada aure ba aikuwa wasu sukai ta ce mata ta yafe masu su basu san ita matar aure bace tace ta yafe suna haka malamin su ya shigo kowa ya koma seat d'in shi, gaba d'aya damuwa tay mata yawa har ta kasa tsaida hankalin ta kan abunda ake koya masu saidae ta sunkuyar da kai kota kai hannu ta dafe goshi ko ta d'an cije baki Fauzy duk tana lura da ita saidae ba damar tayi mata magana, basu samu damar yin Magana ba don malamin na fita wani na shigowa har saida akai break sannan Fauzy ta tambaye ta wai mi yake damunta ne ta lura tana cikin damuwa nan ta kwashe zancen tarewar ta ta fad'a mata har Fauzy bata san lokacin data saka yar k'arar murna ba cike da farinciki tace "to keda zaki farinciki ma Allah ya cika maki burin ki Aure ya d'ore Ya Haisam ya zama naki sai kita damuwa" d'an yarfa hannu tay ta cije baki tace "Fauzy bazaki gane ba ne ina hango gagarumar matsala a tattare da hakan dangin shi fa basu sani ba haka ma Matar shi Hajiya ce kadae ta sani yanzu in suka zo daga baya suka ce basu amince da auren bafa?" Da sauri Fauzy tace "ni wllh ban ganin za'a samu wata matsala, karfa ki manta gaba dayan su Hajiya na iko dasu tunda kuma ta amince ai ta zauna na tabbatar bazata bari a raba auren ba kawae muci gaba da Addu'a" shiru kawae tay idanunta sun cika da k'walla can suka zubo sharr da sauri Fauzy ta dafa Shoulder d'in ta ta shiga bata hak'uri cikin kuka tace "Fauzy abunda yafi damu na Ya Haisam ya canza man yanzu da nike ganin ya zama mallaki na, in don laifin dana yi mashi ne na bashi hak'uri duk da in zai man Adalci ai bani kadae keda laifi ba ko, ni ina ganin gaskiya kaman gara in hak'ura da auren shi tunda na fahimci bai sona kawae nasan zai amince ya zauna da ni ne k'ilan don Hajiya tay mashi dole kinga to wane irin zaman aure zamu yi haka, koda nike son shi nafi son shima ace yana sona ko d'an yaya ne" yar ajiyar zuciya Fauzy ta sauke tace "ni gaskiya ina tunanin k'ilan akwae wani dalili da ya sa ya canza maki amman ba wannan ba kuma da dukkan alamu yana son ki shiyasa tun farko bai sake ki ba kaman yadda aka tsara, kuma in ma fushin yake Saboda rasa cikin kinga hakan ya tabbatar da yana son kine shiyasa yake son cikin har yay fushi da kika zubar, kuma da bai son ki gaskiya a ganina bazai amince yaci gaba da zama da ke ba tunda shi fa namiji ba'ai mashi dole irin wannan" shiru tay kaman mai nazarin wani abu can tace "ina ganin kaman hakurin da kika bashi bai isa ba mi zai hana ki same shi ki bashi hak'uri sosae, da kaman ki k'ara iske shi can G.r.a d'in nike gani" d'an waro ido Fatuu tay tace "in je in k'ara bashi hak'uri kuma, gaskiya ni bazan je ba Fauzy hakanan ya wulakanta ni ai na bashi hakurin ko" hannu Fauzy ta kai ta dafa Shoulder d'inta tace "k'ilan abun yay mashi ciwo ne sosae, kinsan su irin su gane masu yana da wuya amman tunda har kika ga ya nuna to tabbas bai ji dad'in abun bane kije ki same shi ki bashi hak'uri sosae ba fad'uwa bane wllh karki manta shi Mijin ki Aljannar ki na a tafin kafar shi kuskurene ace yana fushi dake haka indae fushin yake da gaske Saboda abunda kika aikata don haka nidai a gani na kije ki bashi hak'uri tun kafin ranar Juma'ar tayi" shiru Fatuu tay tana juya zancen zuwa bashi hakurin a cikin ranta can wata zuciyar ta tuno mata da lokacin data fasa mashi glass har Haulat ta bata shawarar taje ta bashi hak'uri kuma shawarar tayi mata amfani wanda itace silar komae a tsakanin su, yin wannan tunanin yasa ta kalli Fauzy tace "shikenan zan je d'in amman bansan lokacin da yake can ba gashi in na koma gida bansan yadda zan ce ma Gwaggo ba har ta barni in fito" Fauzyn ta tambaye ta yana zuwa aiki ne tace mata a'a ya bar aiki nan tunda ya bar K'asar, sake tambayar ta tay yaushe rabon data gan shi tace mata shi ya kawo ta tace "kinga da ace can ya tafi sai kiyi sauri tunda anyi break duk da ma an kusa dawowa sai kije ki dawo mai Napep d'in da ya kai ki sai ya jira ki ku dawo" d'an jimm Fatun tay kaman mai yin tunani can tace bari ta gwada zuwa k'ilan can ya wuce in kuma bai can sai ta dawo ta mik'e Fauzy ma ta mik'e tace bari ta rakata, suna fitowa waje suka samu Keke Napep Fatuu har zata shiga ta dakata takai hannu cikin aljihun rigarta ta fiddo kud'i cikin wanda ya bata ta mik'a mata tace tay break ta shige cikin Napep d'in Fauzy ta d'aga hannu tana mata sai ta dawo da fatan Allah yasa ta iske shi ta amsa da Amin yaja suka tafi ita kuma ta juya...............




_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2058*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


.........Tunda suka taho take ta faman zullumin abunda zai biyo baya in ta iske shi, wannan karon bata wani sha Wahalar gano gidan ba da suka iso don ta rik'e sunan Road d'in, a bakin tangamemen gate d'in tace ma mai Napep d'in ya tsaya bayan ta fito tace zai jirata ne su koma yace to ba matsala ta juya ta nufi k'aramar kopar a d'arare, Officer dake zaune shi kadae yana ganin ta ya hau washe baki harda mik'ewa yana mata sannu da zuwa abun har saida ya bata mamaki a hankali ta amsa mashi ta tambaye shi ko Ya Haisam na ciki da sauri ya d'aga mata kai yace eh yana nan tace zata gan shi ne yace mata ba Komai ta fito lafiya ta wuce, tunda ta shiga harabar gidan gabanta ke ta fad'uwa tana tafiya tana yan waige waige har ta isa bakin mai entrance na gidan ta turo kopar ta shige, ba kowa a cikin parlon farko ta wuce Corridor d'in da zata kaita d'akin nashi cike da fargaba har ta iso bakin dakakkar kopar dake a rufe, tsaye tay ta kasa kwankwasawa sai faman wasi wasi take a cikin ranta ta had'e hannawun ta tana cakud'a su, can dae ta kai hannu yana d'an rawa ta fara knocking a hankali, kusan sau biyar ta kwankwasa amman shiru bata ji an yi magana ba, dakatawa tay da knocking d'in tay jimm tana tunanin ko dae bai nan wata zuciyar ta ayyana mata amman ai Officer yace yana nan kuma da ya fita bazai ce mata haka ba ta raya to ko bacci yake yin Wannan tunanin yasa ta yanke ko dae ta tafi, har zata juya sai kuma ta dakata tay tunanin k'ara d'an kwankwasawa k'ilan tay sa'a yay Magana, can cikin bacci yaji knocking d'in sama sama har dai yaji shi sosae ya fara motsa idanuwan shi kafin slowly ya bud'e su dai dai lokacin ya k'ara jin anyi knocking d'in cikin disasshiyar murya irin ta wanda ya tashi daga bacci ya tambayi wanene shiru ba'a amsa ba saima k'ara yin knocking d'in da akai ya k'ara tambaya nan ma shiru, tunani yay k'ilan Officer ne ko ya kira landline bai ji ba hakan yasa ya yaye lallausan duvet d'in daya rufe rabin jikin shi da shi ya saukko da k'afafun shi kafin ya idasa mik'ewa daga shi sai farar singlet fara kal sai short da iyakar shi rabin cinyoyin shi, saida ya zura takalman da ke a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login