Showing 132001 words to 135000 words out of 512766 words

Chapter 45 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1603

iske bata nan ko ta tafi aiki ne tace a'a taje inda zata kai aikin su dublan ne, ta tambayi taci Abinci ko tace mata taci a Makaranta bata jin yunwa amman duk da haka saida tace mata ta k'ara taci ta k'oshi tace to, daga baya ta sanar da ita zancen zuwa gyaran jikin da zasu yi da Fauzy a kunyace gwaggon tace mata to amman ta kira shi ta sanar da shi har saida ta d'an yi murmushi dama saida ranta ya bata ta fad'i mata ta tambaye shi daya kawo ta harma da kud'in daya turo da wanccan daya fara turowa itama gwaggo saida ta jinjina yawan kud'in tace saidae ta dawo tay amfani dasu suyi duk abunda zasu yi tace to, bayan sun gama wayar ta mik'e ta nufi kitchen ba laifi taji damuwar da take game da yanayin Ya Haisam ta ragu,


Saida Fauzy tay wanka ta shirya sannan ta fito don tafiya gida, bayan ta isa bata iske kowa a parlor ba yaran Aunty Mareeyar basu kaiga dawowa daga School ba don suna tsayawa extra lesson, Bedroom d'in ta ta nufa tay knocking ta jiyo Muryar ta tana a shigo sannan ta tura kopar da sallama ta shiga, tana kwance saman gado tayi wanka jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa kallabin ta aje a gefe kanta yasha kitso yar yar Tubarkallah dama akwae gashin kitson ya zubo gefe da gefen wuyanta tana ruk'e da wayar ta, tana ganin Fauzy tace lafiya dai ko ta dawo don jiya ta tafi, a bakin gadon Fauzy ta zauna tana kallon ta da murmushi tace mata lafiya lau, Aunty Mareeyar tace "kenan hakanan kika dawo, ko missing d'ina kike shine kika zo ki gan ni?" Yar dariya tay tace mata eh amman harda Albishir tazo yi mata, tana jin hakan ta aje wayar ta maido hankalin ta gaba d'aya kan Fauzy tana fad'in ta bata ta sha, cike da tsokana Fauzy tace "Dama Daddyn su Hanif ne na gani ya kai wata Makarantar mu amman shi bai ganni ba saida ya sauketa ya tafi naje muka gaisa nike tambayarta inda ta san shi take ce man wanda zata Aura ne har an sa masu rana shine nace bari in zo in fad'i maki kin kusa yin k'anwa mu kuma zamu yi sabuwar Aunt......" bata k'arasa ba Aunty Mareeya ta kai hannu ta janyo ta ta daddage ta d'uma mata dundu tana fad'in bari ta fara ta kanta ita yar zuwa ta fad'i, wata irin gantsarewa Fauzy tay sosae taji zafin dundun har saida ta saki k'ara tana fad'in "Aunty Mareeya so kike ki kashe ni kika buga man wannan k'aton hannun naki tubarkallah" sakin ta tay tana dariya tace gobe ma ta k'ara fad'i mata irin wannan mummunan labarin Fauzyn ta tashi zaune tana yamutsa fuska kaman zatai kuka har kallabinta ya cire Aunty Mareeya dake ta dariya tace mata tana jin ta wane Albishir ne zata mata, tana tura baki tace ta fasa fad'i mata ta fara k'ok'arin mik'ewa da sauri ta janyo ta ta fad'a saman gadon ta rungume ta tana bata hak'uri sannan ta shiga fad'i mata zancen tarewar Fatuu, har saida Aunty Mareeya ta rangad'a gud'a ta shiga washe baki tana fad'in Alhamdulillah an zo daidai inda take so, ta bata labarin zuwa da tayi d'azun bashi hak'uri da yadda sukai dashi, yamutsa baki Auntyn tay tace "in ma bai hak'uran ba ta lalama zai hak'ura ne don dole, wllh ni dama fatana auren dai ya d'ore duk wannan miskilancin sai an sauke mashi shi sai ya rasa sukuni duk in bai ji Zarah a gefen shi ba, shiri za'ai mata na musamman ba boka ba Malam amman fa sai ya susuce a kanta mu da muke da AUNTY BEE KAYAN MATA AND SUPPLEMENTS ai zance kuma ya k'are, mu mata da Allah yay mu masu daraja ai duk kika ga mace bata da k'ima da daraja a wurin mijinta wllh ita taso, macen data san kanta wllh bata zama ba tare da gyara kan ta ba musamman da kaya masu tsananin inganci na Aunty Bee, ai ance ko kana da kyau to ka k'ara da wanka" Fauzy da tay sototo tana sauraren ta tace "Aunty su kayan Aunty Bee d'in nada kyau sosae kenan" hannu Aunty Mareeya tasa ta ruk'e ha6a tace "Uhmm bazaki gane ba yarinya tunda baki san yadda karatun yake ba, amman wllh kin ji na rantse kayan ta Kat ne ingancin su ba'a magana sai mutum yayi amfani dasu zai shaida don sha yanzu ne magani yanzu, gashi abun burgewa abubuwan mune na gargajiya ake sarrafawa ayi magungunan sam basu da wata illa sa6anin wasu magungunan ke da kinji kin san harda surkulle" Fauzy ta tambayeta a ina Aunty Bee d'in take tace "a Kano take nima yadda akai na santa nan Neighbor d'ina Maman taufiq taji ina complain kan sai aita zuzuta magani amman in na siya sai inji ba haka ba k'arshe ma na daina siya nace gwara in cigaba da shan su Fruit dasu Fresh milk shine fa tace ai in jaraba kayan Aunty Bee d'in, farko k'iyawa nay nace kowane Magani haka ake cewa amman ta matsa man ta bani wasu in gwada....."

Hannu tasa ta ruk'e ha6a tace "Fauziyya...." Itama Fauzyn ruk'e ha6ar tay tana gumtse dariya tace "Aunty..." ajiyar zuciya Aunty Mareeya ta sauke tace "naga abun Al'ajabi wllh, amman mu bar Maganar daga nan bari in kira ta in mata zancen Zarah" tana rufe baki Fauzy ta kyalkyace da dariya itama Aunty Mareeyar dariyar take ta fara k'ok'arin kiran layin Aunty Bee kamar haka, 08144224934 wayar na fara yin ringing Aunty Mareeya ta d'aga ma Fauzy gira tace "yanzu zata d'auka ta bala'in iya haba haba da customer da kin kirata ko kika tura mata sak'o ta WhatsApp ba 6ata lokaci zaki ji ta d'auka saidae in wani babban uzurin ya hanata d'agawa da wuri amman data gani ko daga baya ne zatay ma mutum magana..." Jin Aunty Bee d'in ta d'aga kiran yasa tay shiru suka shiga gaisawa cike da mutunta juna daga baya ta shiga yi mata bayanin K'anwarta take so a gyare mata sosae kaman yadda aka saba harda cewa mijin miskili ne na gaske so take asa ya magantu ba tare daya shirya ba Aunty Bee d'in tay dariya irin ta mata da suka amsa sunan su tace mata karta damu wannan ba matsala bane saidae in bata yi amfani da magungunan ba amman tabbas zai magantu, gaba d'aya suka saka dariya Aunty Mareeya tace tana son ta turo mata hotunan packages na magungunan zata tura ma Mamar Amaryar tace ba matsala ta duba WhatsApp yanzu zata turo mata in sha Allahu sukai sallama, suna gama wayar ta shiga WhatsApp d'in dama anan take Fauzy ta shigo, ba 6ata lokaci sai ga hotunan ta turo Aunty Mareeya tay ma Fauzy alamar ta matso ta gani ta k'arasa hayewa kan gadon, baki bud'e take ganin hotunan magunguna ba kamar package na Amaren ya burge Fauzy sosae tun ma a ido, magunguna ne sosae Aunty ta shiga fad'i mata sunayen su, su Zakaran mak'alemata, kazar gadali, zabuwa, cicci6i, tsumi kala kala masu wanke mara suyi maganin sanyi, gumba ma kala kala ga garirrrika wato daka akwae d'akan yar gata, k'orama, green emergency, bata gaban kishiya , a ciji kunne....." Aunty bata k'arasa fad'in sauran ba Fauzy ta kwashe da dariya harda tuntsirawa ta d'ago tana fad'in Aunty badai kunnan Zarah za'a cije ba da sauri Aunty Mareeya ta kai mata bugu tana fad'in mara kunya kawae ita tana nuna mata ne don in za'a ma k'awayen ta aure ta taimake su ta tallata masu don su gyara kansu, k'arshe sai ta fita daga cikin hotunan Fauzy nata rok'on ta taci gaba da mata bayani tace bata yi,

"To amman Aunty kince a Kano take yanzu yaushe har aka kawo su Zarah tai amfani dasu saura fa kwana ukku ta taren" murmushi Aunty Mareeya tay tace "ai wannan ba matsala bane Aunty Bee bata da wasa a kasuwarta in yanzu nace duk ana son wannan kayan a gobe insha Allahu zaki ga ta turo su ke ko Lagos kike kika ce kina son kayanta cikin kwana biyu zasu iso maki kuma abun mamakin kayanta basu lalacewa yadda ta turo su haka zaki amshe su ba cuta ba cutarwa, kuma koda yan kud'i k'alilan zaki samu kayanta, kai ai Allah yaba Aunty Bee gaskiya ba k'aramin taimakon mata take ba shiyasa a koda yaushe Allah ke k'ara ma kasuwarta Albarka wllh" Fauzy tace "to yanzu tura ma Zarah za'ai ta gani in mata bayani?" Yar harara Aunty ta wurga mata "wata Zarah can, kenan ita zata gyara kanta sai kace mara gata gwaggon zaki kira man in mata bayani kina da no d'inta?" tace mata ba'a rasawa ta ciro wayarta a cikin jaka ta fara dubawa cikin sa'a akwae lambar tace ta kirata, tana fara ringing ta d'auka Aunty ta amsa cikin girmamawa ta gaishe da ita tay mata Allah yasa alheri Fauzy ta fad'i mata zancen tarewar Zarah, daga baya ta shiga yi mata bayanin magungunan sosae gwaggo taji dad'i tay ta godiya tana shi Albarka tace duk kud'in da ake buk'ata tay ma Fatun Magana zata turo sai a kawo tace to, daga baya sukai sallama suna gama wayar gwaggo ta kira Fatuu tace mata Auntyn Fauziyya zata kira inta fad'i mata kud'i ta tura mata tace to, ba tare da 6ata lokaci ba bayan ta kira Fatuu ta tura mata kud'in ita kuma nan take ta tura account d'in Aunty Bee daga baya ta kirata tace ta tura mata receipt ta duba, bayan ta gani ta tabbatar mata gobe in Allah ya kaimu wurin k'arfe 10 na safe magungunan zasu iso tace harda gudummawarta ta k'ara aba Amarya, dama haka take da wuya kai siyayya bata k'ara maka ba Aunty tay mata godiya sosae sukai sallama har Fauzy na yamutsa fuska tana ita baza'a siyar mata koda kazar bace Aunty tace asarar kud'i kenan, ana yin sallar la'asar Fauzy tay ma Aunty Mareeya sallama ta tafi gidan su Fatuu don zuwa gyaran jikin...........

(Aunty Bee Kayan Mata And Supplements TESTED AND TRUSTED duk abunda Aunty Mareeya ta fad'a game da kayanta gaskiya ne ni shaida ce don haka kar ki bari a barki a baya wllh ki zama tauraruwa a idon oga ta hanyar amfani da kayan Aunty Bee, Mace mai gyara bata boranci)




_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2060*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*



......... Lokacin da su Hajiya suka fito Abbas na tsaye bakin Jeep d'in da ya zo da ita har an shiga da Fatuu, Aunty Mareeya da Feenah da inna Zaliha da Matar Baba shehu duk suka shiga ya juya kan sauran k'awayen Fatuu da suka rage don wasu sun tafi ya nuna masu Jeep d'in Saleem yace su je su shiga harda Fauzy ita ta shiga gaba sai Haulat, sauran wad'anda suka rage Abokan aikin gwaggo Hajiya ta nuna masu Motar da Tk ya zo da ita suka shiga Amadu na a Front seat, kowa ya samu wuri sai wasu daga cikin Makwabta ne basu samu ba Hajiya tace su taka a k'asa itama a k'asan zata duk akai dariya ta kira Abbas yazo gaban su tace mashi su d'an zagayo da su Fateemar ita ma ta shaida an yi mata d'aukar Amare yana murmushi yace to ya juya, Motar Saleem ya nufa ya zagaya driver side ya bud'e yana zauna ya d'an d'age kan shi jikin headrest ya sanar dashi zasu d'an zagayo dasu roundabout ya jinjina mashi kai ya rufe mashi kopar, saida yaje ya sanar ma Tk shima sannan ya dawo Motar tashi, lokaci guda gaba d'aya suka kunna motacin sai lokacin gwaggo dake tsaye ta tuna da kayan Fatuu ta yi ma Hajiya Maganar ko a d'aukko kafin su tafi tace ta bari in suka dawo sai Tukur yazo ya d'auka tace to, Tk ne ya fara jan tashi dama shine a gaba lokacin da suka baro gidan Hajiya da zasu zo ya mik'i hanya Abbas ne a tsakiya sai ta Saleem k'arshe suka tafi,

Bayan tafiyar su Hajiya tace masu su tafi su jira su acan gidan, har zasu tafi ganin an bar gidan a bud'e yasa Hajiya cema gwaggo akwai sauran mutane ne a gidan za a bar shi a bud'e, sai lokacin ta ankare da sauri ta juya tana fad'in ta manta Hajiya na cewa ko duk tafiyar Fateemar ce tasa ta rikicewa, bayan ta shiga ta d'aukko wayar ta da makulli ta fito ta rufe gidan suka tafi, ta k'aramar kopa suka shiga suka nufi part d'in Haisam, lokacin da suka shiga a gyare harabar take tsaf an gyare shukokin flowers d'in wurin gwanin sha'awa suka nufi kopar shiga parlon, suna shiga makwabtan da aka je da su suka saki baki galala suna bin parlon da kallo ga wani ni'imtaccen sanyin Ac had'i da fitinannan k'amshi da ya karad'e cikin parlon, gwaggo dae sai d'an murmushi take itama tana k'are ma parlon kallo, parlon yana nan yadda yake amman an k'ara wasu abubuwa kaman daga bayan L-shape ansa dining table mai kujeru hud'u suma leather ne bak'ak'e sai daga gaba bangon dake kallon su an sa wani jigunannan console mai jan hankali golden haka saman kujera L-shape an canza throw pillows an sake wasu masu design mai kyau da d'aukar hankali, Carpet d'in k'asa ma an canza wani sabo wanda ke akwae da an maida shi wurin dining table, haka flowers d'in dake a angles d'in parlon an k'ara wasu, d'an madaidaicin Fridge d'in dake parlon an maida shi cikin kitchen sai sabon freezer da aka siya mata a cikin kayan kitchen aka aje shi a parlon daga can wurin dining table, a jikin bangon parlon an manna manyan Frames harda mai Ayatul kursiyyu, blinds d'in jikin Windows ma an canza su zuwa manyan labulaye wanda daka kalla ba sai an fad'a maka ba zaka shaida masu kud'i ne Saboda had'uwar da sukai kuma sun hau da parlon sosae, komae ya hau daidai nan aka shiga yabawa ana sa Albarka tare da Addu'oi, Hajiya tace masu su shiga suga sauran d'akunan suka ce to suka nufi hanyar corridor, Bedroom d'in ma tsab dashi sai k'amshi ke tashi nan ma an canza labulayen ciki haka gadon ma yasha babban bedsheet mai pillows da yawa ko a ido ka kalle shi kasan zai yi mugun taushi, nan ma sosae suka yaba daga baya Hajiya tace suje su ga Kitchen ta juya gaba suka bi bayanta, d'ayan d'akin da yake matsayin Lab d'in shi a da shine aka maida mata kitchen d'in, bayan sun shiga ciki sosae shima suka yaba komae an tsara shi har a sama anyi cabinet haka k'asan ma cikin kankanin lokaci an maida d'akin Kitchen na yan gayu, bayan sun gama gani suka nufi Parlor sai faman yabo da san barka ake, duk suka zazzauna suna dakon isowar su Fatuu farinciki Fal cikin zuciyar gwaggo har fuskar ta ta kasa 6oyewa sai d'an murmushi take ganin wai autar ta ce zata rayu a cikin wurin, sai godiya take ga Allah acikin ran ta,

Tun da suka tafi Fatuu ke ta faman kuka har Abbas saida yay mata Magana yace gidan fa Ya Handsome d'inta za'a kaita ba wani wurin ba ai farinciki yakamata tayi ba tay ta yin kuka ba sai kace za'a kaita inda za'a cuta mata, Aunty Mareeya itama tace abun ya bata mamaki wannan kuka haka sai kace za'a kaita gidan makiyinta Feenah ce tace "ai dole duk da hakan sai taji ba dad'i barin gidan da ka saba rayuwa a ciki ka koma wani wuri ba abu bane da ba za'a ji komai ba", inna Zaliha tace gaskiya ne ba kamar yadda suka shak'u da gwaggon ta,
Aunty Mareeya tace "hakane, amman dae kukan yayi yawa bai kamata ta sama kanta damuwa ba tunda dai ga baki ga hanci ba nisa tayi da gida ba, muda aka d'aukko daga wani gari sai an dad'e kafin muje gida ita kuwa data fito fa zata ga gidan koda bata shiga ba zata ji dad'i, gani ma zatayi tamkar ba ta bar gidan ba tunda duk unguwa d'aya ne kuma in taso ma kullum taje nasan ba zai hana ba" inna Zaliha dake d'an murmushi tace "hakane amman dai kar ace kullum sai anje d'in hakan bai kamata ba, ita mace ta zauna a d'akinta shi yafi mutunci ba kullum ai ta ganinta tana sunturi a waje ba hakan bai dace ba" gaba d'aya suka ce gaskiya ne harda Abbas, saida suka shawo roundabout na Barhim sannan suka koma. A cikin kwanar gate suka parker Motocin bayan sun iso duk aka firfito Aunty Mareeya na ruk'e da Fatun gefenta Abdul ne ruk'e da hannunta guda suka shiga ta k'aramar k'opa da sauran Mutane, lokacin da suka k'araso bakin kopar shiga parlon Aunty Mareeya ta tsaya da ita tace tayi Addu'a sannan ta shiga da k'afar dama wad'anda ke a bayan su duk suka tsaya saida ta gama sannan suka shige sauran suka bi bayan su, suna shiga d'aya daga cikin makwabtan dake zaune suna jiran isowar su ta mik'e ta rangad'a gud'a mai sautin gaske su Hajiya suka shiga sakin murmushi itama ta mik'e ta nuna masu inda zasu shiga da ita kowa ya baza ido yana k'are ma parlon kallo, hardae Aunty Mareeya da Feenah bin parlon suke da kallo don ba k'aramin had'uwa yay ba ya matuk'ar burge kowa ga wani irin k'amshi mai had'e da sanyin Ac da ya baza ko ina na parlon, Fauzy ma ta jinjina had'uwar wurin har d'an jinjina kai take haka sauran k'awayen su Zainab Muhammadu ma baki bud'e take k'are mashi kallo,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login