Showing 489001 words to 492000 words out of 512766 words
Chapter 164 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1580
gaske Hajiya tafiya zata yi, cikin sanyin jiki yace mata eh yasani nan da sati guda ya shiga bata haƙuri yana nuna mata ai ba an rabu ba kenan za'a cigaba da zumunci yanzu ma daga wurinta yake tace ma zasu iya cigaba da zama a gidan, haƙuri yaci gaba da bata can ta ɗago idanunta sunyi jajir ta saukko daga saman gadon a tunanin shi wani wuri zata ko toilet kawai sai gani yay ta duƙa a gabanshi cikin kuka a marairaice tace mashi don Allah tana neman alfarma a wurin shi tana rokon ya dubi girman Allah yayi mata, gaban shi ne ya fara faɗuwa yace mata in sha Allah in bata fi ƙarfin shi ba zai yi mata, a marairaice tace mashi tunda dama a nan gidan suka haɗu har sukai aure kuma Allah bai sa sun samu rabon haihuwa ba don Allah tana roƙon shi ya sawaƙe mata Allah ne shaidarta tana jin Hajiya har cikin ranta bata jin zata iya cigaba da zama a gidan nan ba tare da ita ba, shiru yay yana kallonta duk da yaji ba daɗi data yi Maganar amman ta bashi tausayi yace mata yanzu in ya sawaƙe matan garinsu zata koma kenan tace a'a zata roƙi Hajiyar ne ta tafi da ita, shiru yay yana kallonta ta langa6ar da kai tana mashi magiya can yay yar ajiyar zuciya yace mata shikenan ta bari sai da safe zasu yi Maganar tunda yanzu dare yayi ya kama hannunta ya miƙar da ita yace suje ta wanke fuskarta. A wannan daren baccin su gaba ɗaya harda Tk ragagge ne, Washe gari Officer na dawowa daga sallar Asuba part ɗin Hajiya ya wuce, bayan ya ƙwankwasa ƙopar daga ciki ya jiyo muryarta tana bashi izinin ya shigo, zaune take kan darduma hannunta ruƙe da cazbaha, da hannu tayi mashi alamar ya shigo ya nufi inda take ya duƙa a kan carpet, bayan ta shafa Addu'a ta kalleshi da ɗan murmushi da sauri ya gaishe da ita ta amsa tayi mashi ya suka tashi ya amsa da Alhamdulillah daga haka yay shiru idon shi akan carpet, daga yanayin shi ta fahimci da wani abu tana ɗan murmushi tace mashi tana fatan dai lafiya ko da wani abu, dagowa yay a nutse yace mata dama Saudatu ce jiya da daddare ta roƙeshi kan yay mata wata alfarma to yace ta bari sai zuwa da safe shine yaga ya dace ya fara tuntu6arta gudun yay mata ba daidai ba, kai Hajiya ta jinjina ta tambayi wace alfarma take son ya yi mata ne nan ya faɗi mata duk yadda sukai da Sauden,
"Humm, Saudatu Kenan, to yanzu kai ka amince zaka sawaƙe matan ne?" Hajiya ta faɗa tana ɗan murmushi idonta akan shi, ɗan shiru yay farko kafin yace tunda ta nuna hakan take so zai mata Hajiyar tace bai son auren ne ko kuwa, da sauri da alamun damuwa yace wllh yana son zamanshi da ita Allah ya sani kawai dai ya fahimci in bai yi mata yadda take so ba ba lalle zaman nasu yaci gaba da yin daɗi ba don ta nuna bazata iya cigaba da zama ba tare da ita ba, yar ajiyar zuciya Hajiya ta sauke ta juya ta kai hannu ta ɗaukko wayarta ta shiga kiran layin Saude bayan ta ɗaga tace mata tazo dakinta tana son ganinta, ba'a ɗau lokaci ba Sauden ta shigo cikin ɗakin da sallama tana sanye da doguwar Hijabi duk suka amsa mata ta nufo ciki, gefen Officer Hajiya ta nuna mata alamar ta zauna, bayan ta zauna ta gaishe da Hajiyar tare da yi mata an tashi lafiya da tambayar ƙarfin jikinta duk ta amsa mata daga haka Sauden ta sunkuyar da kanta idon Hajiya a kanta tana ɗan murmushi, a nutse cikin dattako ta fara magana tace taji yadda sukai da maigidanta saidai sam bata jin daɗin jin hakan ya fito daga bakinta ba a matsayinta na wadda take gani mai hankali taya zata tunkari mijinta da zancen ya saketa kenan ta za6i bauta a ƙarƙashin wani fiye da ubangijinta, da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a,
"Aure shine mutuncin kowace mace Saudatu, nasan saboda kauna da sabo yasa kika za6i hakan saidai ni a wurina zaman ki a ɗakin mijinki shine abun alfaharina ba kamar in na tuna a gidana kuka haɗu har akai auren, kiyi haƙuri don na tafi ba yana nufin shikenan an rabu ba in sha Allahu za'a cigaba da yin zumunci in dai da rayuwar" ɗagowa Sauden tayi idanunta sharkaf da ƙwalla ta ɗaga mata kai kafin cikin disashshiyar murya tace mata to zata koma Daura,
"To auren fa Saudatu, taya zaki koma can bacin ga mijin ki anan?", shiru ta ɗan yi idonta a ƙasa kafin tace "Hajiya don Allah ki bari in koma Allah ne shaidata bazan iya cigaba da zama ba a gidan nan in baki nan" shiru Hajiya tayi tana ɗan murmushi idonta a kan ta, cikin sigar rarrashi tace mata ta dai yi haƙuri ta zauna saboda aurenta Sauden tayi shiru tana matsar kwalla can Officer yace in hakan take so lafiya lou shi ya amince ta koma Daura din Hajiya tace to ya za'ai hakan yace ba komai indai hankalinta zai fi kwanciya sai ya rinƙa zuwa, ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tace shikenan bari ta gani in zata iya neman alfarma sai a maida shi Daura da aiki dama tuntuni abunda yasa ya daɗe anan gidan ita ta roƙi alfarmar abar mata shi yanzu abunda za'ayi tunda dama zata siya ma Sauden gida in ta amince sai a siya mata acan Daurar sai su zauna a cikin shi, da sauri Sauden ta ɗaga kai alamar ta amince Hajiyar tayi murmushi tace to wurin ina take son a siya mata gidan tasa a bincika mata Sauden ta ɗago ta faɗi mata tace shikenan, kallon Officer tay tace ya jirata Maganar canjin wurin aiki ya yi kuma Addu'a Allah yasa a maida shi can yace Amin ta ƙara ce mashi zata turo mashi saƙon kuɗi sai ya juya ya haɗa da aikin nashi Allah ya ƙara rufa asiri ya amsa da Amin tare da yi mata godiya da addu'o'i ta amsa tare da cewa shikenan zasu iya tafiya.
Tun bayan da Hajiya tayi magana dasu Tk game da tafiyarta gaba ɗaya duk sun shiga damuwa gidan ya koma shiru sam basu da wata walwala a haka har ranar tafiyar tata tazo, ranar ta kama Juma'a da safe jirgin Hajiya Maryam ya iso tazo tafiya da ita, bayan zuwan nata nan da nan gidan Hajiyar ya cika da manyan mutane musamman yan siyasa sun zo yi ma Minister sannu da zuwa da kuma yin sallama da Hajiya, da lokacin sallar Juma'a yayi gaba ɗaya a Masallacin gidan duk sukai salla, misalin ƙarfe huɗu na yamma ana gama sallar La'asar aka firfito don raka Hajiya Airport tuni an fito da akwatunan kayanta an saka a Mota don iya su kawai zata tafi dasu ba'a dauki komai na gidan ba, a gaban entrance aka jere motocin lokacin da Hajiya ta fito sanye da rantsatstsiyar lifaya tana dogara sandarta ta alfarma Tk na daga can gefe a tsaye idanunshi sunyi ja don tun da safe yake matsar ƙwalla, har su Gwaggo sun zo suma zasuyi rakiya Amadu ne zai kai su a Motar Fatuu, bayan an fara shiga cikin motoci Amadu ya nufi wurin Tk ya dafa kafaɗarshi yana bashi haƙuri yace mashi yazo suje suyi mata rakiya idanunshi cike da ƙwalla ya girgiza mashi kai yace su je kawai, ganin yanayin shi yana cikin matsananciyar damuwa yasa Amadun ƙyale shi ya juya, a tare Convoy ɗin motocin suka tashi gaba da baya motocin security ne idanun Hajiya na akan Tk dake tsaye har suka isa gate suka ta ɗan girgiza kai tare da rufe idonta, lokacin da suka fito kopar gidan cike yake da mutane yan unguwa tun dazu suke son shiga yin bankwana da Hajiya amman Security sun hana, motocin na fitowa suka shiga daga masu hannu suna faɗin sunan Hajiyar Sanata ganin haka yasa Hajiya tasa a dakata, bayan Jeep ɗin da take ciki ta tsaya ta sauke glass aikuwa mutane na ganinta suka nufo ta da sauri nan fa aka shiga tutsetseniyar kama hannun nata ana kiran sunanta harda masu yin kuka daga baya ma sai ta buɗe Motar ta fito aikuwa matan unguwa da yara aka shiga rungumeta ana kuka cike da ƙarfin hali take basu haƙuri tana kwantar masu da hankali tace ai ba an rabu ba kenan in sha Allahu za'a cigaba da zumunci kuma duk abunda take yi baza'a bari ba tunda ga Tk nan, ganin suna 6ata lokaci yasa Hajiya Maryam tayi ma security magana suka sallami mutanen Hajiyar ta koma cikin Mota, duk yadda ta daure saida ta matse ƙwalla motocin suka tafi anata cigaba da ɗaga ma Hajiyar hannu, mutane rahama ko iya haka za'a iya cewa Hajiya ta dace. Hajiya ta tafi ta bar mutane da kewa ba kamar su Tk don tun bayan tafiyarta yake ta zazza6i bawan Allah don ma Allah yasa yana da mata tanata aikin rarrashin shi duk da itama sosae take kewar Hajiya don ba ƙaramin shaƙuwa sukai ba ita kanta ɗiyar su Hauwa'u duk ta damu ko yaushe cikin tambayar yaushe Hajiyarsu zata dawo take sai an kira mata ita ta waya sunyi magana ko Vedio call take kwantar da hankalinta, ta bangaren Saude ma taso tafiya Daura bayan tafiyar Hajiya Officer ya rarrasheta kan tayi haƙuri tunda Hajiya tace zata nema mashi transfer sai su koma can baki ɗaya da haka ya samu ta haƙura, su Gwaggo ma duk sun yi kewar Hajiyar duk da su bama gida daya suke da ita ba amman da sun zauna suna hira sai sun yi maganarta, sai bayan wani lokaci Tk ya warware amman ko yaushe cikin jin kewar Hajiyar shi yake.
Bayan komawar Hajiya Abuja da yan watanni Allah ya sauki Farha ta haiho san6aleliyar ɗiyarta mace kai kace ɗiyar aljanu ce don kyau gaba ɗaya mamanta da babanta ta biyo, a fuska da Kamalu take kama amman farinta na Farha ne sannan ƙwayar idonta ma ta Farha ce gashin kanta kuma baƙi ne wuluk kalar na babanta, cikin sa'a lokacin da akai haihuwar su Fatuu na hutu hakan ba ƙaramin daɗi yay masu ba, kowa ya ga Babyn sai ya furta ma sha Allah ana ta farinciki Hajiya Maryam ma lokacin data ga Babyn sam kasa rufe bakinta tay sai farin ciki take, bayan sun koma gida daga asibiti da daddare Lokacin da Kamal ya shiga wurin maijegon yana ruƙe da babyn yake sanar mata da sunan da yake son sakamata wato sunan Hajiya Maryam Farhar tace mashi ba gara yasa sunan late Mom ɗin shi ba yace mata tunda Fatuu tasa su bari in ta ƙara haihuwa sai su saka sunan Mom ɗin nashi, harda yar harararshi tayi tace ita wannan wahalar da tasha ta gama haihuwa yana murmushi tare da yi mata kallo mai cike da tsantsar ƙauna yace tayi haƙuri pls ta ƙara mashi yana son su haifi yara tare, itama murmushin tayi ta kai idonta kanshi tana mashi kallon love tace indai irin yaran nan zata rinƙa haifa tare dashi to zata ƙara wasu Amman sai ta huta sosae yay murmushin shi mai burgewa tare da jinjina mata kai alamar amincewa da zancenta tana murmushi ta kwantar da kanta a kan shoulder dinshi tana kallon Kyakkyawar Babyn su tana haka taji ya furta "Thank you my lovely wife for loving me for who i am" ɗago kai tayi ta kalle shi ta kashe mashi ido tare da furta "i will always love u Babe" yadda tayi maganar har sai da ɗumin bakin ta ya bugi fuskarshi saboda kusancin da fuskokin nasu suke dashi, shiru sukai suna kallon juna wani lokacin har mamaki Kamal yake a cikin ranshi irin yadda take nuna mashi ƙauna bata ƙi a ce koda yaushe suna manne da juna ba, a iya zaman da sukai matsayin ma'aurata ba ƙaramar zazzafar soyayya ta nuna mashi ba hakan yasa shima yake ƙokari wurin faranta mata a koda yaushe bai ta6a yin wani abu da zai nuna ta takura mashi ba zaman su suke lafiya sam baida matsala da ita kawai dai tana da zafin kishi wannan kuma tun kafin suyi auren ya sani shiyasa yake taka tsantsan da duk abunda yasan zai haifar masu da matsala, lokacin da Hajiya Maryam taji sunanta aka saka ma jaririyar murnarta ninkuwa tayi jin anyi mata takwara, bayan kwana biyar da yin haihuwar aka maida maijegon Villa don acan za'ayi suna, saida Hajiya Maryam tayi ma jaririyar saitin akwatuna ukku masu guda huɗu haɗaɗɗun gaske shaƙe da kayan jarirai na gani na faɗa da sauran kuma abubuwan da suka danganci jarirai ita kanta mai jegon ita tayi mata kayan da zata fita suna harda shi ma Baban jaririyar tayi mashi ɗinkuna na alfarma abun dai gwanin daɗi, ranar suna ta kama Juma'a suna na gani na faɗa akayi a Villa maijego ta samu iyayen kaya ita da Baby, mai girma shugaban ƙasa kyautar ƙaton fili yay ma jaririyar haka dai aka cika su da abubuwan arzuƙi kowa yayi bajinta su Gwaggo da Haulat harda Kawu Amadu da Tk da matarshi duk sun zo suna, zo kaga farincikin ganin juna wurin Hajiya da Tk harda rungume shi tayi, suna yayi suna abun sai son barka bayan gama sunan anan Villa apartment ɗin da Hajiya Maryam take Farha ta zauna sai ta gama wanka zata koma.
A kwana a tashi ba wuya a wurin ubangiji gashi President Ali har yayi shekara biyu da komawa kujerar mulki lokacin yaran Fatuu duk sun girma su Twins nada shekara takwas Esha kuma nada shekara bakwai, tun bayan da Esha ta fara girma gaba ɗaya halayenta sak na Fatuu da tana da ƙuruciya ne don sam bata jin magana ga masifa sannan tana da ƙarfi sosae don abu kaɗan sai ta kai bugu ko su twins bata ƙyalesu ba da ɗan abu ya haɗa su sai ta kama bugun su duk da suna maza bugunsu take har ta saka su kuka kuma duk sun fita tsawo amman tana da jiki bulbul take, kullum cikin rabata faɗa ake da yara a gida da kuma makaranta
gashi saboda ansan ko ita wacece yasa ba'a ta6a kai ƙorafin halinta ba ga iyayenta har sai watarana data fasa ma wata yar ajin su baki daga ta taka mata colour bata gani ba ta karye tana bata haƙuri amman duk da haka saida ta kai mata bugu saitin bakinta aikuwa bakin ya fashe yay ta jini lokacin Class Aunty ɗin su ta yanke yin magana da Dad ɗinta don ai mata faɗa ta rage faɗa da yara da yake suna da lambobin wayoyin iyayensu, bayan ta kira Haisam cike da girmamawa tayi mashi bayanin dalilin kiran nashi harda bashi haƙuri kan hakan da tayi tace taga abun yana yin yawa ne kada wata rana ta illata wani student sosae, Haisam ɗin yace mata ba wani abu ya gode da sanar mashi da tayi, a ranar da daddare bayan ya dawo daga sallar isha ya zauna a main parlor dama duk dare in ya dawo daga salla nan yake zama su Twins da Esha din su kawo mashi Assignment ɗin su ya taya su bayan sun gama sai ya rakasu ɗakunansu su kwanta, su Twins ɗakin su ɗaya sai ita kuma Esha a Bedroom ɗin Fanan take kwana, bai daɗe da zama ba sai gasu sun fito duk suna sanye da ƙananun kaya su Twins Jeans da t-shirt sai Esha tana sanye da blouse da ɗan gajeran skirt duka kalar pink gashinta na fake a tsakiya ya sauka har kusan tsakiyar bayanta dama kusan koda yaushe sai dai ka ganta da gyaran gashi don bata son kitso, kowannensu ya ɗaukko ƙatuwar jakar Makarantarshi, suna ƙarasowa inda Haisam yake zaune Esha ta saki jakarta ƙasa ta washe baki duk gefen kumatunta suka lotsa sosae ta nufi Haisam da yar sassarfa tana faɗin "My Daddy.." dama ita yar gidan Daddy ce sosae suke shiri kowa ma ya sani daddie's pet ma ake ce mata ko rashin ji take da ance in ya dawo sai an faɗi mashi take cewa ta bari kada a faɗi mashi don Allah, haka in ya dawo gidan in suna nan haka zata nufeshi da gudu tana mashi welcome ya ɗagata sama yana faɗin His little Angel tun bata girma ba yake mata haka har kuma yanzu data girman a haka suke tarbar juna, haka in yana zaune ma tana zuwa zata faɗa jikinshi tana mashi dariya shima yayi mata har gyaran gashi yake mata da wanka cikin Weekend da yake yana ƙoƙarin basu lokaci sosae a ƙarshen sati har fita yake dasu outing wani lokacin kuma anan cikin gidan zaije dasu Field suyi wasanni harda Fanan in Fatuu ma tazo Weekend da ita ake yi, Esha ɗin na zuwa zata faɗa jikin Daddy ɗin nata yay saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu fuskarshi a ɗan ɗaure hakan yasa ta ja ta tsaya a gaban shi tana kallon shi da manyan idanunta masu ɗauke da zarazaran gashin ido, da alamun ɗan mamaki take kallonshi don ta gane ya ɗaure mata fuska su Twins ma tsaye sukai suna kallonshi can yace masu su zauna dukansu suka zauna akan carpet dama anan suke zama in za'ayi Assignment ɗin shima Haisam ɗin sai ya saukko ya zauna akan carpet ya fara nuna masu yadda zasuyi koda sun iya ƙa'ida sai tare da Haisam ɗin zasu yi don haka suka saba, yawanci ma duk Assignment ɗin da aka basu suna iya fiddawa dama gasu da ƙoƙarin tsiya sune gaba gaba a cikin ɗalibai masu ƙwazo a Makarantarsu, bayan duk sun zauna harda Esha ɗin zuru sukai suna kallonshi duk sun fahimci ya canza masu fuska, Adam ne cikin shan jinin jiki ya gaishe dashi da turanci Haisam din ya jinjina mashi kai ganin haka yasa Abie ma gaishe