Showing 9001 words to 12000 words out of 512766 words

Chapter 4 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1538

d'in ya dakatar da shi ta hanyar fad'in "No Dad ba sai ka d'aukko ba it's true na saka mata saidae bada niyya bane sharrin shaidan ne kuma ban cutar da ita ba" komawa yay ya zauna cike da takaici yace "ka bata maganin bacci ka gane mata jiki har ka ta6ata shine baka cutar da ita ba! Idan aka ma k'anwarka Sadeeya haka zaka ji dad'i???" cije lower lip d'in shi yay remorsefully yace "am so sorry dad wllh sharrin zuciya ne tasa naga ai ni zan Aureta amman nasan nayi kuskure don Allah ka yafe man" banza Dad d'in yay mashi ya juya ya kalli Mom d'in shi da ido tay mashi alamar ya duk'a ya bashi hakuri slowly ya sauka on his knees ya shiga bashi hakuri can ya d'ago idanun shi sun yi ja yace ba shi zai ba hakuri ba ga dangin ta nan su suka cancanci ya ba hakuri don su yay ma laifi har suka tako suka zo garin Saboda hakan, juyawa yay ya kalli Gwaggo ya fara bata hak'uri yana yasan yayi ba daidai ba don Allah su yafe mashi Abbas dae sadda kan shi yay yana jinjina shi gwaggo ma rasa abun cewa tay can taji muryar Dad yana fad'in "Don Allah Hajiya ku yi hakuri kaman yadda kika ce yaro ne ka haife shi baka haifi halin shi ba amman ina mai tabbatar maki zan d'auki kwakkwaran mataki kan abun da ya aikata ai man Alfarmar hakan" yana rufe baki Mom ma ta d'auka ta hau bata Hakuri can gwaggo ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace "Hakuri ya zama dole Alhaji tunda aikin gama ya riga da ya gama" gaba d'ayansu murmushi suka saki suna mata godiya ta sake cewa "Amman Alhaji nima ina son in rok'e ka wata Alfarmar kuma ina fatan za'a yi man" jinjina kai Dad yay yace in sha Allahu ta fad'i yana ji, gyara zama gwaggo tay taci gaba "Ina son ka dubi girman Allah ka janye batun auren nan....." Zaro ido sukae shi kam Khalid wani kallo ya bita dashi cikin yar in ina Dad yace "a... amma Hajiya yanzun nan kika ce fa kin hak'ura kuma na fad'a maki zan d'auki mataki to miya kawo Maganar a janye batun auren kuma ko baki hakuran bane?" Girgiza kai tay har idanun ta sun ciko da k'walla tace "dalili na na son a fasa auren shine saboda ba auran had'i bane auren dole ne za'a ma ita yarinyar kuma nasan duk kun san illolin da auren dole ke haifarwa ba kamar yanzu da ita yarinyar ta tsani auren har tana ikirarin mutuwa zatayi in aka mata" dakatawa tay tana goge kwallan da suka fara zubo mata gaba d'aya kan su ya gama d'aurewa ganin tana kuka yasa Chairman cewa "Hajiya ai abun duk bai kai na haka ba kuma ni nasan tun tsawon shekaru ukku na nemi auren ita yarinyar don da bakinta ta fad'a man lokacin tana aji ukku na matuk'ar yabawa da komae nata shiyasa nayi sha'awar ta shigo Family na saidae a lokacin tayi k'arama kuma sai ya kasance shima yaron nawa lokacin yana k'asar waje bai ida gama karatun shi ba shiyasa sai nace a bari ta k'arasa Secondary d'inta ala bashshi in sukae Auren sai taci gaba aka kuma amince man" yana rufe baki gwaggo ta d'auka "to mudai bamu san da Maganar an bada itan ba sai sati biyu zuwa ukku da suka wuce kawae aka kira mu wai za'a zo d'aukar yarinya an bayar da ita, wllh Alhaji bazan 6oye maka ba rabon da in shiga tashin hankali irin na jin wannan batun tun rasa Mahaifiyarta da nai bawai ina k'in ai mata aure bane saidae abu ne da ban ta6a zato ba don nayi tsammanin an bani ita kuma ko za'a raba ni da ita bai kamata a nuna man fin k'arfi ba, ban ta6a samun sa6anin da har nay fushi da ita ba sai akan auren nan, na zubar da kwalla har bansan adadin ta ba ba kuma don komai ba sai Saboda amincewa da tayi wanda ita kanta don bata da yadda zatayi ne Mahaifinta ya kira yana kuka ya sanar mata cewa shima bai son a mata auren amman mahaifin shi Ard'o yace in har bai amince ba zai yafe shi ne kuma dole ya bar mashi gida........." Nan gwaggo ta kwashe duk yadda akai har Fatuu ta taho don amata auren da niyyarta na k'in zuwa biki Saboda bacin ran da take ciki har halin ciwon da take ciki, lokacin da ta gama rufe fuskarta tay tana ta kuka, sam Chairman bai ji dad'in jin abubuwan da suka faru ba don shi ya d'auka tuni sun san da Maganar, sai lokacin Abbas ya fara Magana cikin natsuwa da nuna shi mai ilimi ne ya shiga kwatanta ma Alhajin illar da yin auren zai iya haifarwa tunda har yarinyar ta gudu yanzu to in aka matsa mata za'a iya ganin ba daidai ba don yanzu kwata kwata abun ya fitar mata a rai a k'arshe ya tabbatar ma da Chairman d'in tana da wanda take so kuma shima yana sonta bai k'asar don haka shi abunda yake gani a k'yale ta ta auri wanda take so kawae kar a mata dole don ko addininmu ba'a ce ai ma yarinya dole ba a aure, shiru Chairman yay hannunshi ruk'e da ha6arshi har Abbas ya gama cike da gamsuwa ya shiga jinjina kai kafin ya fara Magana "Duk na fahimci bayanan ku kuma har ga Allah ni dama ba wai son zuciya ne yasa zan had'a auren su ba kawae don yarinyar ta kwanta man ne kuma wllh da ina da wani yaron ba Khalid ba to da shi zan nema ma auren ta, amman yanzu daga abunda ya aikata mata na fahimci sam basu dace da juna ba sannan Hajiya ki sani duk abunda bazan so ya faru da yata ba to bazan so ya faru da yar wani ba tunda d'a ai na kowa ne kuma ta cika yar halak da har ta sadaukar da farin cikinta don mahaifinta ta k'ara burge ni sosae ta cancanci itama a faranta mata Saboda haka zan maki Alfarma kamar yadda kika buk'ata matuk'ar hakan zai saka ki farinciki, Hajiya a yanzu na Janye maganar auren su a barta ta auri wanda take so Allah yasa hakan yafi zama Alkhairi" ido waje Khalid ke kallon mahaifin nashi har ya rufe baki ita kuwa Hajiya Rabi'atu girgiza kai kawai take sam bata so hakan ya faru ba don tasan wata matsalar ce zata kunno kai tsakanin Khalid da Mahaifin na shi saidae har cikin ranta Gwaggon da Fatuu sun bata tausayi.................



_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2034*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*Wannan page kyauta ne a gareki Mommy Kubra ki yadda kika ga dama dashi🤩 Allah ubangiji ya bar mana zumunci Amin🤝😍*

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*





..........cike da farinciki gwaggo ta hau yi mashi godiya had'i da Addu'oi yana jinjina mata kai yana fad'in ba komae haka ma Abbas godiyar yay mashi daga baya gwaggo tace kar dai ya gaji don Allah tana k'ara neman Alfarmar yaje suyi Magana da Ard'o yace ba komae yanzu dae yamma tayi amman zuwa da safe yana nan zuwa karta damu duk abunda ya kamata za'a yi sosae suka k'ara yi mashi godiya suka Mik'e zasu tafi Mom ma ta mik'e jikinta duk ya mutu a sanyaye tace su bari su ci Abinci mana Gwaggo tace sun gode wllh saida suka ci Abinci suka taho, ita ta rakosu bayan fitar su Khalid ma ya mik'e zai tafi Dad ya ce bai sallame shi ba ya koma ya zauna, bayan tafiyarsu d'aki Momy ta koma duk ta rasa mi ke mata dad'i ta d'auki wayarta ta kira su Sadeeya suna can suna shirin Bridal shower da zasu yi gobe ta sanar mata da su dakata da komai su dawo gida matsa mata tay da tambayar abunda ya faru nan ta kwashe komae ta fad'i mata ba k'aramin tashi hankalin Sadeeya yay ba Mom na jiyo yadda take ta sakin salati. Tsitt kake ji sai Ac da tv dake ta aiki Chairman nata d'an jinjina kai da k'afa Khalid kuma ya sadda kan shi k'asa sai da aka d'an d'auki lokaci sannan Dad yay ajiyar zuciya cikin karyayyar murya ya fara fad'in "Ka kyauta mun Khalid ka nuna man irin muhimmancin da nike dashi a wurin ka....,amman ka sani ba ni kai mawa ba kan ka kai mawa, kanka ka zubar ma da k'ima da daraja koda yake dama baka da su don duk mai su bazai rungumi sa6on Allah ba....." Dakatawa yay har saida Khalid d'in ya d'an d'ago ya kalle shi kafin yaci gaba "Allah ne shaida ta na fita hakkin ka a matsayi na na uba duk wani hakki na sauke kuma nasan ban yi maka tarbiyar da zata sa ka rink'a sa6a ma Allah ba hasali ma har Al'qur'ani ka sauke ba sau d'aya ba sannan kuma ka haddace wasu bangarori nashi masu yawa amman duk da haka ka za6i take sanin da ke gare ka kake aikata manyan laifukan da Allah ne shaida ta ban aikata su balle in ce abun da nike yi ne nima ake man...." Kwalla ne suka ciko idanun shi ya sa hannu yana gogewa sosae hankalin Khalid ya tashi sai zare ido yake kallonshi Dad yay yace "Khalid ka rasa abun da zaka rink'a aikatawa sai Zina!! duk da ka sani ka karanta kasan illolinta k'asan hukuncin mai aikata ta, mina rage ka dashi ne a rayuwar nan? Duk wata ni'ima Allah ubangiji yayi maka ita ya baka lafiya ya wadata ka ta yadda idan mata hud'u kake so ka aura a rana guda zaka iya amman shine ka za6i sa6a ma wanda yay maka wannan baiwar, Ya Allah! d'ana na ciki na shi ke neman mata shi ke shaye shaye....." Muryar shi ce ta karye ya fashe da kuka a gigice Khalid ya saukko ya durk'ushe a gaban shi ya fara fad'in "billahi Dad kaji na rantse maka na daina tun last Maganar da mukae da kai akan yarinyar nan Danejo ban k'ara aikata hakan da kowa ba, Yes nasan in na 6oye maka bazan 6oye ma Mahallici na ba ina ta6a mata kuma nasan hakan baida kyau kawae son zuciya ne amman nayi maka alk'awarin na daina daga yau Dad kuma ko shaye shaye da kace shima nasan ina yi amman wllh na rage kaji na rantse, don Allah Dad ka daina man kuka kar abun ya k'ara man yawa" dakatawa yay yana goge k'wallan dake zubo mashi duk wannan abun akan idon Mom da tun d'azun ta shigo tana tsaye gefe itama kukan take jin sheshshekar ta yasa Khalid juyowa ya hau rokonta kan ta taya shi rok'on Dad kar ya k'ara yin fushi da shi girgiza kai kawae take dama dalilin auren Fatuu suka k'ulla yarjejeniya har ya amince yasa suka shirya da Mahaifin nashi yanzu kuma ga wannan, matsawa Mom tay itama ta duk'a suka taru suna ta bashi hak'uri, sosae fasa Auren ya ta6a mashi zuciya don yarinyar ta shiga ran shi kuma yana tunanin ta silar ta Khalid d'in zai natsu to amman duk da da laifin Khalid d'in yasan haka Allah ya k'addara yarinyar ba Matar shi bace, can ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya d'ago ya kalle su d'an murmushin takaici yay yace ma Khalid "Ka tashi kaje komi kai don kan ka kuma kowa yay da kyau zaiga da kyau sannan ka sani kayi ma kanka don ban tunanin zaka k'ara samun nagartacciyar Matar aure kaman Yarinyar nan kuma ba baki nay maka ba wllh I assure u sai kayi da na sani u should mark my words" daga haka ya mik'e yay hanyar Bedroom d'in shi ya shige, yana shigewa Mom ma ta mik'e ta bi bayan shi idon Khalid a kan ta, ya rage saura shi kadae tunanin rayuwarshi ya shiga yi tabbas yasan bai kyauta ma kan shi ba abubuwan da yake yi daga zuwa karatu ya biye ma gur6atattun abokai ya canza daga halayar shi mai kyau zuwa maras kyau tabbas yasan ya cuci kan shi, a hankali tunanin shi ya gangaro kan Maganar Dad d'in shi ta k'arshe da ya ce sai yay dana sanin rashin Auren Fatuu ko bai fad'a mashi ba shi yasan yayi asarar mace har mace yarinya ce mai tarin baiwa lokaci guda suffarta ta fara mashi gizo ya dingi tariyo lukkuttan da suka kasance a tare yanzu shikenan ya rasata! Wani Sarawa kan shi yay mashi da k'yar ya yunk'ura ya mik'e hannunshi guda dafe da gaban kan shi ya nufi hanyar fita daga parlon, Uhmmmm dama ance rashin hakuri na rana guda kan iya ja ma mutum dana sani na har Abada Bature kuma yace Once Opportunity lost would never be regain, Allah ya kiyashe mu aikin dana sani ya k'ara shirya mu ya shirya mana zuri'a Amin ya hayyu ya kayyum.


Cike da farinciki Gwaggo ke sanar ma dasu yadikko da Baffa lokacin da suka koma kowa yay murnar jin hakan don abu ne da basu tsammaci fasuwar shi cikin sauk'i ba saidae kuma a d'ayan bangaren na zuciyoyin su suna fargabar abunda zaije ya dawo in Ard'o ya sani gwaggo ce ta nuna su kwantar da hankalin su in sha Allahu komae zai zo cikin sauk'i kaman yadda ya faru yanzu. Washe gari Misalin k'arfe 11 na Safe sai ga Chairman Alhaji Lawal harda Hajiya Rabi'atu a Fadar Ard'o suka sauka yasa aka kira kowa manyan gidan harda mata su Yaya da Gwaggo da Baffan Fatuu Abbas da dai sauran su bayan an gaggaisa a nutse cikin Fahimta ya bayyana masu ya janye Maganar aure Saboda yarinyar bata so tana da wanda take son Aure aikuwa nan aka fara zantuttaka Ard'o yace sam baza'a fasa auren ba wllh Yaya ma a harzuk'e take fad'in ba'a fasa shi su za'a maida kananun mutane aja masu abun kunya, harda ce ma Alhaji Lawal duk wannan makarkashiya ce ba wani wanda yarinya ke so komae tsarawa akai don wata manufa ta daban, gwaggo bata tanka ba Abbas ne ya shiga nuna masu da gaske ne tana da wanda take so bai K'asar ne shi Amininsa ne kuma da ya dawo zai zo a d'aura masu auren, da k'yar Alhaji Lawal yasa kowa ya natsu nan ya shiga nuna masu illar dake tattare da yi ma yaro auren dole tunda har bata so to a kyaleta shi bai ji komae ba don yasan komae mukaddari ne daga Allah, Allah ya k'addaro ba Matar yaron shi bace tun bai rufe baki ba Ard'o yace sam fa yana raye hakan bazai faru ba dole abi Maganar shi ai ba itace ta farko da aka fara za6a ma miji ba kuma suma sauran ai basu rasa wad'anda suke so d'in Yaya sai k'ara tunzurashi take tana Kumfar baki haka wasu daga cikin yan uwan Baffan Fatuun ma k'arshe dae da k'yar Alhaji Lawal ya shawo kan Ard'o ta hanyar nuna mashi ita yarinyar a birni ta taso ba za'a had'ata da sauran yara na nan ba kuma a birni in hukuma taji za'a ma yaro auren dole baiso to kuwa d'aukar kwakkwaran mataki suke don har kotu ake zuwa don haka gwara su kyaleta, abun ka da mutumin k'auye da tsoron hukuma ta haka ya samu suka sassauto k'arshe Ardon yace yaji za'a fasan amman sai dae a d'aura da wanda aka ce suna son juna don tayi girma da yawa ba aure kuma shi karatun nasaran ai ana yin shi ko bayan anyi aure ko, har saida cikin Abbas ya Murd'a shi da ya tsara hakan suka d'an saci kallon juna da gwaggo, da k'yar cike da k'arfin hali yay masu bayanin bai nan ne yaje yin wani aiki ne shiyasa ayi hakuri ya dawo Ard'on yace ai ko miji bai kusa ana yin aure ganin yadda ya d'auki zafi sosae yasa Alhaji Lawal sa baki yace ayi hakuri ya dawon sai ita yarinyar ta fara ma karatun ta da k'yar dae aka tankwara kafaffen tsohon harda kukan shi Yaya kam kamar ta had'iya zuciya ta mutu sam Al'amarin bai mata dad'i ba duk da haka bata hak'ura ba saida ta kawo zancen wai to a maida auran kan Mino mana sosae hankalin Baffan su ya tashi bashi kad'ai ba har su gwaggo da Abbas saida hakan ya bayyana a fuskokin su, d'an murmushi Alhaji Lawal yay ya tambayi wacece ita aka ce mashi k'anwar ita Fatun ce still da murmushin yace ya gode amman ba sai anyi hakan ba a k'yaleta ta auri wanda take so itama sannan ya tambayi bata karatu ne Abbas ya bashi amsa da tana yi har ta kai J.s 3 ma, Chairman d'in ya shiga fad'i masu muhimmancin karatun ya'ya mata yace don haka a k'yaleta tay karatun ta, Jama'a zuciyar Yaya zata buga a fusace tace ma Baffa ai sai aje a kwaso masu kayan su tunda ba gadon su za'a ci ba Chairman na a barsu ai ko daga baya a turo a d'auka amman Yaya ta kafe sai an d'aukko, tsamm Gwaggo ta mik'e ta bita da wani mugun kallo bada jimawa ba suka dawo tare da Yadikko dasu Kamalu suka shigo da akwatunan duk da haka saida tasa aka bud'e kowanne wai kada a nemi wani abu a rasa anan aka ga kud'in da Fatuu ta saka Yadikko tace shi Khalid d'in ya bata su ranar da ya zo chairman ya jinjina kai, daga baya taro ya tashi wasu na farinciki yayin da Zuciyoyin wasu ke k'una aka fitar masu da akwatunan suka tafi. A hayye shagali zo kaga farinciki wurin su Gwaggo har bai 6oyuwa. Washe gari Juma'a yanda

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login