Showing 393001 words to 396000 words out of 512766 words
Chapter 132 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1619
zasu nufo su had'e ya mik'a ma driver wayar yaci gaba da mashi bayani, sai faman bin garin Sameer yake da kallo haka Haisam ba laifi Sameer yaga ba k'auye bane kamar yadda ya zata, lokacin da suka had'e da Yaya Mubarak yana ganin Motocin ya gane sune yay ma driver d'in alamun ya tsaya, nufar Motocin yay da sauri aka sauke mashi glass cikin girmamawa ya gaishe dasu tare da yi masu sannu da zuwa Haisam ne ke amsawa shi kuwa Sameer tunda ya d'aga mashi kai sau d'aya bai k'ara ba balle ya tanka, bayan sun gama gaisawar yace ma driver d'in ya biyo shi a baya ya koma Motar shi suka tafi, lokacin da suka k'arasa anata aikin gyaran gidan don Kusan ma an kusa gamawa don an d'aura bene komai dai ya kusa kammaluwa, a falon Baban su aka sauke su wanda tuni an canza mashi fasali don shi yace ko angama ginin bazai hau sama ba dama kuma da k'asan aka fara gyaran, sosae aka nuna farincikin zuwan nasu duk samarin gidan da yan'uwan mahaifin nasu harda shi mahaifin nasu sun zo sun gaisa dasu sai basu girma ake ba laifi Sameer d'in ya d'an saki fuska amman kowa daya gan su yake gane shine wanda Fauziyya zata aura don sun san labarin shi, Aunty Mareeya na a falon tana gabatar masu dasu da kuma dangantakar su haka suma su Haisam d'in tana gabatar masu da dangin nasu nan aka shiga yi masu godiya yawanci dai Haisam ne ke magana, koda Aunty tayi masu Maganar Abinci cewa sukai a k'oshe suke sai da ta matsa masu sannan suka d'an ci wanda ta kawo masu kan c-table dama tasan ana iya yin hakan shiyasa basu wani yi Abinci masu yawa ba, bayan sun gama zama tayi tana k'ara yi masu sannu da zuwa da godiya ta lura da yanayin Sameer duk da tasan halin shi tana murmushi tace "K'ani na ansha gajiyar Mota ko" kallon Sameer d'in Haisam yayi yana murmushi shima ya d'an yi kad'an ba tare daya ce komai ba, basu yi awa da zuwa ba suka ce zasu tafi lokacin iyayensu sun dawo cikin parlon aka ce basu bari su k'ara hutawa Haisam yace Saboda hanya kada yamma tayi masu, godiya Haisam ya shiga yi masu na auren da aka basu sai lokacin Sameer ya bud'e baki yay godiyar shima duk suka ce ba komai ai sune da Godiya anata faman dawainiya dasu, a tare gaba d'aya aka fito yi masu rakiya harda Aunty da k'annansu mata harda masu aure da suka zo su Fareeda Mahaifiyarsu ce kawai bata fito ba amman har gwaggo ma ta fito rako su, har zasu shiga Mota Sameer ya dakata ya kira Yaya Mubarak da sauri ya nufo shi, magana yayi mashi saidai ni kaina banji mi yace mashi ba kawai dai sunga Yaya Mubarak d'in nata d'aga kai daga baya ya juya ya shige security ya rufe mashi k'opar anata d'aga masu hannu suka tafi, bayan tafiyar su cikin parlon suka koma gaba daya aka dasa hirar su Haisam d'in sai faman yaba kyaun su ake ana fad'in Fauziyya tayi dace ta ko ina Mijinta yayi k'anin mahaifin su ne yace saidai yaga kaman magana na mashi wahala ga Fauziyya da surutu ya kenan zasu yi zaman auren duk akayi dariya Aunty Mareeya tace haka yake amman in yaso yana d'an yi, Yaya Mubarak ne yayi masu bayanin kiran shi da yayi yace Maganar aikin da ake ne ya tambaye shi ko da matsala sannan ya tambaye shi anan akwae furniture masu kyau yace mashi eh to yanzu yace in aka k'arasa aikin aje a za6i wanda ake su da za'a saka a ko ina sai yayi mashi magana nan fa aka shiga fad'in Ma sha Allah wannan hidima haka abu yayi kyau saidai iyayen Fauzy sun ma kasa magana don Al'amarin ya girmi tunanin su, bayan su Aunty Mareeya da sauran yan gidan mata sun koma part d'in da aka ware masu suke zaune Saboda aikin da ake nan suka dasa hirar su Haisam kowa na fad'in wanda yafi mata wasu suce Haisam yafi burge su wasu suce dukkan su sun yi don suna kama ai sosae,
"Ni wllh wannan farin yafi burge ni da yanzu zai ce yana sona da gudu zan yarda ni koma matsayin mai aikin shi ce in dai zai aure ni" wata k'anwar su ce Nusaiba tayi Maganar dama ga yanayin Maganar ta kamar ta sakarkaru aikuwa gaba d'aya aka saka dariya Aunty Mareeya tafi kowa 6a66aka dariyar ta kai hannu ta bugi shoulder d'in ta tana fad'in "Su an Nusi Nusi anga fari rainon Madara da carpet an rud'e ko, wato in zai aure ki to kima fidda rai don wanccan da kike gani ya auru zuciyar shi a gark'ame take da k'aton kwad'o da Zarah ta rufeta da shi kima fidda rai don ba samu zaki ba" tura mata baki Nusaibar tayi tace kaji Aunty Mareeya da mugun fata tasan abun Allah itama yace yana sonta kamar yadda ya faru da Yaya Fauziyya, Mahaifiyar su da tunda suke abun su bata saka masu baki ba sai murmushi kawai tace "aikuwa Nusaiba koda ace hakan ta faru bazaki aure shi ba, baki ji ana fad'in ana barin halak ko don kunya ba kar ki manta matar shi fa itace silar duk wannan Alkhairan dake samun mu" Gwaggo tace gaskiya kam, tura baki Nusaibar tayi ta juyar da kai sai kace Haisam d'in yace yana son ta yadda tayin ne duk ya k'ara basu dariya,
"Ni gaskiya na Fauziyya yafi burge ni yanayin kalar fatar shi ina son Namiji haka kawai dai na lura kamar miskili ne na bugawa a Jarida" Fareeda ce tayi Maganar Aunty Mareeya tace bari mijinta ya jita tana dariya tace yo yaji mana daga ta yabi mijin k'anwarta, Ummi ce tace ita gaskiya Haisam yafi tafiya da ita don shima da gani miskili ne ga shi yafi na Fauziyya sakin fuska, ganin abun na niyyar zama gardama yasa gwaggo tace bari ta bambanta masu shi na Fauziyya gaskiya kamar yana da izza ne shine kawai Aunty ta d'aga hannu tace yauwa gwaggo kin gane, lokacin da gwaggo ke magana Yaya Mubarak ya shigo jin abunda take cewa ya sashi yin dariya yana k'ok'arin zama yace ai shi ne zai basu labarin irin izzar Sameer tunda dashi suke Maganar aikin da ake yace "wllh ba K'aramin gasa ni yake ba yasa inta faman jiran ya bani amsa sai ya mula yasha iska sannan shiyasa har nafi son muyi chat duk da shima d'in wani lokacin zai duba amman fa ba lalle in samu amsa a lokacin ba haka dai nike ta bin shi sai kace ba Yayan matar da zai aura ba kuma ko a shekaru da gani na girme mashi sosae" gaba d'aya akai dariya Abubakar Yayan Fauziyya amman Kusan tsaran juna ne da ita yace tabb lalle aiki ya samu Fauziyya kafin ya bata amsa sai ta bushe, Gwaggo dake dariya tace ai bata anan tunda yana sonta ita zai iya sakar mata baki, haka dai sukai ta hira kan su Haisam d'in daga baya Yaya Mubarak yay masu sallama zai tafi su Aunty sukai mashi godiya, lokacin da mahaifin su Fauzy ya rako yan'uwan shi zasu tafi suka tsaya suna yin bankwana yana k'ara masu godiya wani makwabcin shi ya fito daga cikin gida ganin shi yasa shi nufo shi har zai juya ya koma ciki ya dakatar dashi ta hanyar kiran sunan shi "Barka Alhaji Rufa'i" dakatawa yay ya juyo ganin shi yasa shi yin murmushi yace "barka dai Alhaji Salisu" hannu ya bashi suka gaisa cikin yar in ina yaci gaba "dama Alhaji Rufa'i ina son tambayar ka ne amman ina gudun kaga kaman na saka maka ido shiyasa nayi shiru to yau dai naga ya dace in maka magana a matsayin mu na makwabta, yan kwanakin baya zuwa yanzu abubuwa na ta faruwa a gidan ka da suke ta jan hankalin mu muna ta ganin anayin bak'i wanda da gani manyan mutane ne tunda harda jami'an tsaro suke zuwa don ko na d'azun da suka zo suma naga haka ga kuma aiki da ya taso gadan gadan cikin d'an kankanin lokaci har an kusa kammalawa to gaskiya hakan yaja Hankulan mu sosae don bazan 6oye maka ba anata magana kan hakan shine na yanke in tambaya ko wani abun Alkhairin ne ya same ka bamu sani ba tunda ba alamun wani abun tashin hankali, amman dai kayi hakuri in nayi maka katsalandan don Allah" fad'ad'a murmushin shi Baban su Fauzy yayi yace mashi ko d'aya wllh dama yana niyyar ya sanar dasu to da rabon shi zai riga shi yin magana, nan ya fad'i mashi abunda ke faruwa tsabar mamaki bakin Alhaji Salisu kasa rufuwa yay yace yanzu Fauziyya dai yar wurin shi daya sani ce zata auri d'an gwamna yace mashi eh, "Yanzu Alhaji Rufa'i ana tare irin wannan abun Alkhairin ya same ka amman ace har tsawon wannan lokacin bamu sani ba, haba Alhaji ko dai baka d'auke mu yadda muka d'auke ka ba ko kuma munyi maka wani abun daya sa haka ne" ya fad'a cikin d'an kwantar da murya Baban su Fauzy nata Murmushi yace mashi ko d'aya kawai dai bai bari abun ya bayyana bane sai ya tabbata tukun tunda yasan sha'anin aure yadda yake, da sauri Alhaji Salisun yace kuma hakane hakan da yayi daidai ne saboda yan tsirku da mahassada to shidai wllh tllh ya taya shi murna sosae Allah ya tabbatar da Alkhairi ya nuna masu, Baban su Fauzy yace Amin shi bama don haka yasa ya 6oye ba kawai dai yafi son abun sai ya tabbata ne. Suna yin sallama Alhaji salisun ya nufi komawa cikin gidan shi wanda da fita ya fito zaiyi, tsaye matan shi sukai fuskar su d'auke da Al'ajabi da yana fad'a masu zancen haka ma yaran shi da suka ji zancen sai faman maimaita Fauziyya zata auri d'an gwamna suke, d'ayar matar shi ce ta buga hannu tace haba biri yayi kama da mutum ashe shiyasa abubuwa keta faruwa suke ganin dankara dankaran Motoci na zuwa gidan, d'ayar matar da bakinta ya gama mutuwa da tsananin mamaki ta tambayi maigidan nasu wai ya akai Fauziyyar ta had'u da yaron gwamna har yace yana sonta ya watsa hannu yace Allah nasani amman shima dai yaji mamakin abun ba kad'an ba, juyawa tayi zata nufi d'akinta tana fad'in bari taje gidan ya dakatar da ita yace ta bari ba yanzu ba don duk yan gidan na nan, d'aya daga cikin yaran shi ne yace ashe shiyasa d'azun yaga had'add'un motoci sun zo harda jami'ai mahaifin nasu yace eh wai shine yazo, kan kace mi matar shi daya hana zuwa har ta fita ta fara fad'a ma sauran makwabta kowa tsananin mamakin jin hakan ya yi. Bayan Yaya Mubarak ya fito saida ya biya wurin mahaifin su don yayi mashi sallama anan yasa shi ya zauna yace yana son zasu yi magana, bayan ya zauna ne a nutse ya fara mashi magana kan abunda suka tattauna da Sameer na furniture yace shi yana ganin da ya bar wad'annan tunda akwae kud'i a hannun su sai suyi kawai hidiman ta isa haka iya wannan ginin da ake masu ba K'aramin kud'i ake kashewa ba, nisawa Yaya Mubarak yayi shima a nutse yace to amman yana iya ganin ya nuna zai yi abu an hana shi don haka shi yana ganin ayi yadda yace d'in sai a fad'i mashi kud'i ba masu yawa ba in ya bada sai a had'a a zuba sababbin furniture d'in in ma ta kama sai a had'a da na gidan a sayar Alhajin nasu yar dariya yayi yace ko dai tsoron mijin Fauziyyar yake don yaga ba alamun wasa a tattare dashi shima dariyar yayi yace a'a kawai dai abunda ya sani su mutane irin su basu son a dakatar dasu kan abunda sukai niyya, mahaifin nasu ya jinjina kai yace Shikenan ayi yadda yace amman baza'a saida wasu kaya ba da niyyar a had'a in Sameer d'in ya turo shi ai mashi magana ya bada wasu sai a hada su kuma tsofaffin kayan sai a samu wasu a basu suma su dangwali arzuki ya k'are Maganar da murmushi shima Yaya Mubarak d'in murmushin yake yace to shikenan, addu'ar Allah ya k'ara mashi lafiya yayi ya amsa kafin yace mashi Shikenan zai iya tafiya sukai sallama, zuwa daren Ranar ai duk yan unguwa sun ji zancen auren Fauzyn anata mamaki wasu dai har sun zo jin kwakwaf da sunan fatan Alkhairi, Washe gari Aunty Mareeya zata baro funtuwar ta dawo Katsina.
Alhamdulillah su Haisam sun koma Abuja lafiya kwanan Haisam d'aya ya dawo Katsina, bayan dawowar shine shima yaje yayi ma Haulat gaisuwa tare da Fatuu anan ya tambayi Fatuu ta amsar mashi account no d'in Haulat bayan ya fito tace to, saida suka koma gida sannan ya tura mata kud'in dubu d'ari biyar nan ma dai Haulat kuka ta saka da taga sak'on innarsu tace rayuwa kenan Allah yana had'a ka da mutum baka san moriyar da zai maka ba ta shiga tuna ma Haulat lokacin da aka kawo Fatuu da yadda in ta k'ule ta take zuwa tace ma innar tasu ita dai ta gaji da abunda take mata tace mata tayi hak'uri, tana kallon Haulat da murmushi tace mata yau ga ranar hak'urin da tayi da ita nan Haulat d'in na d'an murmushi tana d'aga mata kai a cikin ranta tana ta tuna rayuwar ta da Fatuu ta baya. Daga baya har da kaya masu yawa Fatuu ta siya ma d'iyar Haulat kullum ne sai sunyi waya wani lokacin kuma taje Haulat har Magana tayi mata kan zaryar da take tace mata in bata yi mata ba wa zata mawa,
Watan Haisam guda anan sannan ya tafi lokacin Haulat har ta gama takaba su twins kuma watan su ukku amman in ka gansu sai kace sun yi wata biyar yaran Tubarkallah dasu sunyi girma duk inda aka gansu sai an tanka hakan yasa kullum Fatuu cikin yi masu Addu'oi take kamar yadda Hajiya da gwaggo ke yawan fad'i mata ta dage da yi masu Addu'a Saboda bakin mutane gwaggo har ruwan Addu'a da akayi da zam zam ta amso mata tana shafa masu, don ma yaran k'yuyar tsiya garesu iya wanda suke gani koda yaushe suke yarda dasu daga basu ba basu yadda da kowa Fauzy ma dakyar take samu suna yarda ta d'auke su.
Satin Haisam guda da tafiya suka fara yin School Final sosae suka dage don daga ita sai council Shikenan, suna cikin yin jarabawar ne Hajiya Zainab ta kira Aunty Mareeya a karo na farko don tun bayan da sukai exchanging number saidai ta gaishe da ita ta chat wani lokacin sai sak'on ma ya dad'e sannan take reply ta nuna mata uzuri yayi mata yawa ne, bayan sun gaisa ne tace mata dama suna son measurements na Fauzy sannan suna neman wata alfarma game da lefen Fauzyn tunda abu bana kusa bane akwae tafiya in akace a kawo kuma sannan in aka d'aura auren sai an kwaso an maido zai zama aiki don haka abunda suke tunanin ayi shine za'a kawo wanda zata yi amfani dasu in aka kaita sai su iske sauran, da sauri Aunty tace ai ba komai duk yadda sukai yayi wllh ta hau yin godiya da Addu'oi Hajiya Zainab d'in na amsawa daga baya sukai sallama, suna gama wayar ta kira can gidan su ta sanar masu Mamar su tace ita wllh hakan yayi mata dad'i ma Allah ya saka masu dai da Alkhairi,
Cikin sa'a suka gama sai kuma ta k'arshen wato council, bayan sati guda suka fara yin ta duka kwana ukku sukai suka gama, a ranar gaba d'ayansu cikin tsananin farinciki suke sun sha ankon atamfofi sun d'aura jacket mai d'auke da sunayen su a baya ta Fatuu an rubuta RN Zarah ta Fauzy kuma RN Fauzy abun gwanin k'ayatarwa nan suka shiga d'aukar hotuna mutane sai so suke suyi hoto da su twins amman sun k'i yarda, Zainab Muhammadu ce tace wllh basu isa ba ayi bikin uwar su tare da ita gari ya gari har Abuja taje amman Suk'i yarda da ita, dole da tsiya ta d'auke su suna ta kuka suna ta6e baki irin dai yadda Fatuu ke yi da k'uruciyarta in zata yi kuka suma haka suke yi don lokacin da Haisam yazo har Magana yayi akan hakan yace ita suka biyo in zasu yi kuka yadda take.
Alhamdulillah shine abunda su Fatuu keta fad'a da suka kammala karatun nasu lafiya, tare da Fauzy suka dawo gida saida suka fara tsayawa a gidan gwaggo akai ta taya su murna da Addu'ar samun sakamako mai kyau daga baya suka koma gida nan ma su Hajiya da Saude kowa dai ya taya su murna Haisam ma tun bayan da suka fito daga jarabawar ya kirata ya taya ta murna da fatan sakamako mai kyau haka ma Sameer shima ya kira Fauzy ya taya ta murna.
Kwana ukku da gama jarabawar su Sameer yazo Katsina Ranar ya kama Alhamis dama ya sanar ma Fauzyn zai zo ya tafi da ita Abuja can za'ai masu pre wedding pics, da yamma jirgin su ya tashi zuwa Abuja, duk da hawanta ne na farko ba laifi ta dake saidai itama taji juwa kamar yadda Fatuu tayi, gabda kiran Magrib suka sauka Aunty Laila ce taje d'aukko su don itama ta gama karatunta ta dawo dama komawar da tayi Final Exams zasu yi, gidansu suka wuce su Mom suka tarbeta hannu bibbiyu sosae Jidderh ta nuna farinciki da zuwanta shi dama Sameer ya wuce part d'in Haisam, d'akinta Aunty Laila ta wuce da ita tana zuwa salla ta fara yi bayan ta gama anan ta kawo mata Abinci da abun sha cikin fara'a tace mata ta taso taci d'an anjima zasu fita ne tace to, ba laifi ta saki jiki taci Abincin Jidderh na gefenta tana mata hira, ana gama