Showing 390001 words to 393000 words out of 512766 words
Chapter 131 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1617
ta fita, bayan ta gama cin Abincin an saka su Yasmeen sun gyara d'akin Aunty ta d'ago jakar ta mik'a ma Fatuu tace gashi nan tayi amfani dasu ta d'ago d'ayar itama m'ika ma Fanan tace d'ayar Momyn twins itama gashi a tare duk suka bud'e, wasu had'addun laces ne kowa guda d'aya sai kuma manyan atamfofi na Fatuu guda biyu ita kuma Fanan guda d'aya, nan fa aka shiga yi ma Aunty godiya sosae Fanan taji dad'in hakan da tayi mata itama tayi mata godiya ta mik'e da sauri tana ruk'e da jaririn ta nufi hanyar fita tana fad'in bari ta je ta gwado ma Hajiya anata mata dariya don kowa ya fahimci taji dad'in kyautar, bata dad'e sosae ba ta dawo tana ruk'e da ledar cikin washe baki tace Hajiya tace ayi mata godiya sai ta shigo zata k'ara mata Aunty dake dariya tace sai kace wani abu Fanan d'in tace aikuwa wani abu ne don babbar kyauta ce nan suka cigaba da yin fira har aka yi La'asar, bayan sallar ne Fatuu tace ma Aunty Laila don Allah ta tayata su duba kayan da aka samu tace to nan aka shiga fiddo kayayyakin kili guda harda Fanan aka shiga bubbud'awa ana shirya su, Kusan raba kayan Fatuu tay wanda nata ne taba Fanan wai ta bata aikuwa tace wllh bazata amsa ba sai kace ita tayi mata nak'udar, K'arshe da k'yar ta amshi wata doguwar riga cikin wanda kakar su Haisam ta kawo mata daga Qatar tare da kayan jarirai had'add'un gaske duk da haka saida Fatuu ta k'ara mata da wata babbar atamfa ta rok'e ta kan ta amsa sannan ta amsa tayi mata godiya sosae, wasu masu yawa ta k'ara warewa tace ma Aunty Laila gashi ta kai ma Mom suyi amfani da su itama harda rok'onta Laila d'in ta d'an waro ido tace don me zata basu kaya haka ta marairaice mata, yar dariya tayi ta gyad'a kai tace tunda sak'o ne ta bata bari ta kai ma Mom d'in amman ashawarce ma da ta bar kayanta Fatuun ta girgiza mata kai tace Don Allah ta saka Mom d'in ta amsa, Bayan sun gama shirya kayan ta d'aukko jakar da kud'i suke suma ta fara kokarin fiddo su Laila dake kallonta tace mi kuma za'ai dasu tace mata wai su k'irga wani kallo tay mata tace har tama saka zata harareta tana matsayin Yayarta to shima k'irga kud'in aiki ne da bazata k'irga abunta ba, dole Laila tayi mata ta maida kud'in data fiddo bayan sun gama komai ta d'auki wanda ta basu ta tafi.
Bayan Sallar la'asar Fatuu na cikin yin chat saman gado Fanan ma na daga gefenta ta tasa su twins gaba saiga Mom ta shigo Laila na biye da ita d'auke da kayan da ta kai mata tana yar dariya, a saman gado Mom ta sakata ta d'aura kayan kafin ta zauna a sanyaye Fatuu ta gaishe da ita ta masa kafin tace ga kayanta nan ta maido mata a ina ake haka kawai ta kwashi uban kaya ta basu sai kace su aka ba, marairaicewa Fatuu tay ta shiga yi mata Magiya Mom d'in tace bafa za'a amsa ba gara ma kar ta wahalar da kanta, suna haka Aunty ta shigo ganin drama d'in da suke yasa ta zauna tana dariya Mom na cema Fatuu ko tayi Kuka ba za'a amshi kayan ba, tambayar abunda ke faruwa Aunty tayi Mom ta fad'i mata tare da nuna mata kayan ta kalli Fatun tace "to daughter taya za'ai hakan ai kayan ki ne ko kiyi amfani da abun ki" murya kamar zata yi kuka tace to ai kayan da yawa ya zatayi da su Mom ce tace ba tana da yan'uwa ba sai ta babbasu suma suci albarkacin twins suyi masu Addu'a,
"Amman Mom kuma ai yan'uwan nawa ne ko",
tana yin Maganar k'walla suka zubo mata Mom ta d'an bud'e ido tace miye abun kuka anan, Aunty ce tace yanzu dai tunda hakane Shikenan a d'an d'auka suma suci albarkacin twins d'in tunda haka take so, ba wasu kaya masu yawa ba suka d'auka duk da haka Fatun taji dad'i hannu ta kai ta d'aukko jakar da kud'i suke Laila na ganin haka tace "Mom see, wai kud'in ma sai an gani" wani kallo mai kaman harara Mom d'in tayi mata Fatun ta marairaice fuska tana niyyar yin Magana Mom tace "Daughter yaushe muka fara wasa irin wannan ne?" abu Fatuu ta had'iya ta d'an girgiza mata kai kamar zatayi kuka ta bata hak'uri tace dama tana son nuna masu ne Mom d'in tace mata ba buk'ata komai ta gani nata ne tayi duk abunda take so da su ta d'aga mata kai, abunda Mom ta ruk'o a hannunta ta mik'a ma Fatun tace to itama ga nata tunda ta kar6i nata Fatuu tabi yan kunnan zinari da take Mik'o mata da kallo Mom tace mata ta amsa mana ta mik'a hannu ta amsa gudun kada ta k'ara cewa ta raina ta, kallon Fanan tayi itama ta mik'a mata zoben zinarin tace itama ga nata ta waro ido tare da d'an bud'e baki cike da mamaki tace itama harda ita ta d'aga mata kai kawai sai ta matso ta rungume Mom d'in tana mata godiya su Aunty ma da Fatuu sukai mata godiya, bayan Fanan ta saketa ta saukko daga saman gadon ta nufi hanyar fita tace shima bari ta nuno ma Hajiya.
A Ranar da daddare duk suna a part d'in Fatun harda Hajiya da Haisam da Nameer gaba d'aya yan gidan anata hira ana cin naman suna ana korawa da lemu Aunty na ta cema su Jidderh wllh su bi a hankali ganin yadda suke ta d'irka kamar sun samu Abinci wai naman dad'i yafi wanda aka saba soya masu Hajiya tace ai haka naman suna yake, suna anan Dad ya dawo shima ya nufo nan part d'in su twins suka mik'e da gudu suna mashi oyoyo ya ruk'e su ganin bakin su jage jage da mai yace miye suke ci haka a tare suka ce naman suna ne ya d'an waro ido yace shine ko a tuna dashi suka ce ai akwai da yawa sosae ya d'aga kai suka nufo ciki, sannu da zuwa aka shiga yi mashi yana amsawa bayan ya zauna ya gaishe da Hajiya tayi mashi an dawo lafiya ya amsa Jidderh tace a zubo mashi naman shima yace anya dare ne fa suma suci a hankali in mutum yaci ya kwanta yana iya samun matsala Aunty Laila dake taunar naman tace ai zasu sha flagyl kafin su kwanta duk aka saka dariya, shima d'an kad'an yasa aka bashi ya fara ci abun gwanin sha'awa k'arshe dai saida Aunty tasa aka d'auke naman daga falon, Bayan Dad ya gama ne aka bashi tissue ya goge hannun shi ya kai hannu cikin aljihun rigar yar cikin shi dama saida yaje part d'in shi ya cire babbar rigar sannan ya nufo nan, wasu takardu ya fiddo guda biyu ya mik'a ma Mom yace taba Daughter gashi nan takardun gidaje ne guda biyu a cikin na Estate d'in shi yaba Abokanshi su daga yanzu kud'in hayar su nasu ne a bud'a masu Account a rink'a saka masu, wata irin shewar farinciki su Aunty Laila da Jidderh sukai su Mom da Aunty ma sai dariyar farinciki suke suna yi ma Dad d'in godiya da Allah ya kara girma da Arzuki, bayan an mik'a ma Fatuu takardun a sanyaye tayi mashi godiya da Addu'ar Allah ya k'ara girma da daukaka yanata amsawa, Hajiya ce tace wato salon sabon Angonta yaga bata yi farinciki da shi ba shiyasa zai masu wannan babbar kyauta haka to itama baza'a barta a baya ba ta basu d'aya daga cikin filayenta na Katsina wannan karon ihun murna Aunty Laila ta saka tana fad'in kaga yara masu k'ashin arzuki daga zuwan su duniya har sun zama masu arzuki,
"Wai to sai ba yaran kyauta kuke ita Mom d'in tasu fa?" Jidderh ce ta fad'a tana tura baki idonta akan Dad d'in su yana yar dariya yace yana sane da ita in sha Allah ita da yar'uwarta zasu je Hajjin bana amman tunda da sauran lokaci zasu fara zuwa Umra gaba d'aya gidan zo kaga farinciki su twins harda rawa suna fad'in dama an dad'e ba'a je dasu ba, Mom ce tace Shikenan ma in suka je sai a biya Qatar a gaido Abie Dad yace ba matsala ya kalli Fatuu yafe ta fad'i daga nan in akwai wata k'asa da take son zuwa Albarkacin su twins sai a wuce tayi shiru tana ta murmushi tama rasa mi zata ce don gaba d'aya bakin ta ya mutu su Aunty Laila na ta fad'i don Allah, Haisam ne yace sun kusa fara Final Exams d'in su ne bai fi nan da 2 Months ba Dad na jin hakan yace to a tsaya daga Qatar d'in, kallon Hajiya Jidderh tayi tace to itama bata ba Aunty Fanan da Fatuu kyautar ba ta d'an kwa6e fuska tace dole sai ta basu suma Aunty Laila tace eh gaskiya tace to ta basu kowa kaza da zakara suyi kiwo gaba d'aya aka saka dariya Fanan tace ta gode zata tafi US dasu tayi kiwon acan Aunty Laila tace gaskiya kyautar tayi kad'an Hajiya ta d'an harareta tace to ina laifi tasan Arzikin da zasu iya janyo masu Jidderh tace duk da haka dai gaskiya sunyi kad'an,
"To tunda had'in kai za'a nuna man Shikenan na basu kowa tunkiya da rago daga haka bazan k'ara ba" dariya aka fashe da ita Dad yace ai wannan ma ta basu mai yawa don tushen garke ne gaba d'aya sukai godiya,
"to wai shi Angon jegon fa banga an bashi komai ba" Aunty ta fad'a Dad na dariya yace "k'yale wannan mai kud'i ne shi" tace duk da haka dai shima a bashi gaskiya Arzik'in su twins Dad d'in ya kalle shi yace yana son wani abu ne a hankali ya girgiza kai yana murmushi yace a'a an gode da wanda aka bada Allah ya k'ara lafiya da Arziki suka amsa da Amin, Dad ya kalli Aunty yace to taji dai bai son komai tana yar dariya tace to ai ba haka yakamata a yi mashi ba shima sai a bashi kawai ba ai mashi tayin rowa ba duk akayi dariya Hajiya tace to ai shima ba za'a je dashi Umra d'in ba Aunty Laila tace wannan to na Dad ne saura ita ta bashi kyautar tace Shikenan shi ta bashi kaza da zakaran da suka guda duk aka kwashe da dariya harda Haisam d'in abun gwanin nishad'i haka suka cigaba da yin firar su lokacin Dad ya tambayi Hajiya nan da 2 weeks lafiya lou za'a iya yin tafiya da yaran Saboda suje su dawo Daughter ta koma School tace mashi eh yace to sai su shirya duk aka k'ara yi mashi godiya.
Bayan sati guda da yin suna yan Ethiopia suka koma lokacin saura sati d'aya su Fatuu su tafi Umra, sosae take samun kulawa gaba d'aya ita da yaran sunyi 6ul6ul dasu gwanin sha'awa, ana saura kwana ukku su tafi Hajiya tace mata in akwae kayan da za'a tafin mata dasu Katsina ta bada tunda da sun dawo zasu wuce can tace to. Lokacin da suka je Umra Fatuu harda kukanta na farinciki ganin gata ga ka'aba, sosae tayi Addu'oi daga cikin wanda tafi yi ma Addu'a akwae Mahaifiyarta da Mahaifinta sai mijinta da gwaggo, Hajiyar Sanata da kuma iyalin Sanata d'in sai sauran yan'uwanta da Abokan Arzuki harda Haulat bata manta da ita ba tayi mata Addu'ar Allah ya bata miji wanda zai kula da rayuwar ta da yarinyar ta, Satin su guda suka wuce Qatar sosae aka karramasu ba kamar Fatuu da su twins sai faman nan nan ake dasu gidan Yaya Othman d'in da suka sauka shi kan shi abun kallo ne don duniya ce mai zaman kanta ko ina walwali ke tashi kai kace da zallar gold aka yi gidan Fatuu ta girgiza da ganin gidan don bata ta6a zaton a rayuwarta zata ganta a cikin gida ba irin wannan, sun zaga garin sun sha hotuna sosae garin da suka je ya had'u Over don shine babban birnin su wato Doha, Birni ne na zamani kuma na duniya mai kyawun sararin samaniya, akwae gidajen tarihi da abubuwan jan hankali na al'adu kuma babbar cibiya ce ta kasuwanci da yawon bude ido na duniya, nan ma sati guda sukai suka juyo Abuja Haisam da Fanan kuma suka wuce US, kwanan su biyu da dawowa suka dawo Katsina, Ranar da suka dawo da daddare Fatuu ta nufi gidan su Haulat tare da Mino ta goya mata yaro guda don tana nan ta dawo anan take takaba don tun bayan rasuwar mijin nata bata jin dad'i hakan yasa aka dawo da ita nan yanzu ma har ta kusa gama takabar, lokacin da suka ga juna ita da Fatuu kuka sukai ta yi innar su na basu hakuri tana ruk'e da yaran tayi ma Fatuu barka tace taso tazo Abuja suna to Saboda yanayin da haulat take ciki yasa bata zo ba Fatun tace mata ba komai itama tana ruk'e da d'iyar Haulat, sosae tausayin Haulat ya kamata ganin yadda ta rame tana kwalla ta shiga rarrashinta kan ta rage damuwa tayi hak'uri tay d'an murmushi tace wllh ta bari ta rungumi kaddararta kawai abun ne wani lokacin in ya taso mata sai taji damuwa, k'arfafa mata gwuiwa ta shiga yi tace in sha Allahu zata samu miji wanda zai kula da ita ya ruk'e Umma Salma tamkar d'iyar shi a sanyaye Haulat d'in tace Allah yasa amman ita yanzu ma gaba d'aya auren ya fitar mata a rai Fatuu tace ta daina cewa hakan don zai zama tamkar bata yarda da kaddarar ta ba ta mik'a komai ga Allah in sha Allahu zai ji6anci lamuranta tace Allah yasa, anan ta kira Haisam ta bashi Haulat d'in ya k'ara mata gaisuwa, sosae Haulat ta yaba da su twins haka ma innar su sai faman fad'in Tubarkallah take daga baya sukai masu sallama suka tafi, Bayan komawar su gida Fatuu ta kira Aunty Mareeya ta sanar mata jini ya d'auke mata tun kafin su tafi Umra Saboda tafiyar yasa bata sanar mata ba amman ta fara amfani da wasu magungunan da Yadikko ta kawo mata tace to zata ba Fauzy sak'o ta kawo mata, washe garin da suka dawo ne Hajiya tayi ma Saude Magana akan ko za'a samo ma Fateema mai raino da zata rink'a taimaka mata Saboda zuwa Makaranta tace to za'a samu zata yi magana can gidan su, a Ranar da yamma Fatuu ta had'a uban kaya su atamfofi da lace harda dogayen riguna wasu daga cikin nata da tasan zasu yi ma Haulat da kayan shafa harda naman suna da kuma kud'i dubu hamsin taba Mino tace ta kai mata tace mata ta fara amfani dasu, lokacin da takai kayan Haulat kuka ta saka a haka cikin kukan ta kira Fatun a waya tace ya zatai mata wannan uwar dawainiyar tace mata ba komai tana dasu ne ita dai fatanta ta kwantar da hankalinta ta daina damuwa tace in sha Allahu ta daina, har gida washe gari innar su tazo tayi mata godiya harda rigunan jarirai ta kawo ma su twins taje tayi ma Hajiya barka anan take ce ma innar tasu ashe Haulat d'in gida ta dawo ta fad'i mata bata jin dad'i ne gashi ta saka damuwa a rai cike da tausayawa Hajiya tace ai dole ne don rashin miji ba K'aramin rashi bane tace ayi mata gaisuwa sai tazo innar tayi mata godiya kafin ta tafi.
Kamar yadda Hajiya tace taje tayi ma Haulat d'in gaisuwa tare da Saude suka je bayan sun dawo ne tayi masu Aiken kayan abinci masu yawa, sosae Fatuu keta gyara kanta bayan Aunty ta aiko mata da magungunan Saude kuma ta samo mata mai tayata rainon su twins tare suke zuwa Makaranta da ita, sosae take missing d'in Haisam sai bayan wata d'aya da dawowar su sannan yazo suka shiga shan sabon Amarci lokacin ne yayi ma Sameer magana kan zuwa Funtua gaishe da iyayen Fauzy da yake yana a K'asar, ya amince zai je harda cewa jirgi zasu hau ko Haisam na dariya yace mashi ai ba Airport acan dole a Mota zasu anan suka tsaida Ranar da zasu Haisam ya fad'i ma Fatuu ita kuma ta kira Aunty Mareeya ta sanar mata aikuwa sosae taji dad'i tace dole zata je don a tarbesu yadda yakamata. Ana saura kwana biyu suje Haisam ya tafi Abuja don daga can zasu wuce Aunty kuma washe gari ta tafi Funtua, Ranar da zasu zo ta kama Asabar da wuri suka taho Mota biyu sukai d'aya wadda suke ciki driver na jan su sai kuma d'ayar ta security, gaba d'ayan su farar shadda ce a jikin su anyi masu kalar d'inkin da suka fi so sai baza k'amshi suke k'afafuwan su na sanye da dakakkun takalma haka agogunan hannunsu ba sai na fad'i masu tsada bane yau dai kawunan su sun samu Arzik'in huluna amman shi Sameer bai saka ba tana dai ajiye k'ilan sai sun isa zai saka, duk tafiyar ta fara gundurar Sameer don har Fuskar shi ta nuna tun yana yin shiru har takai ya fara tambayar driver ko sun kusa isa sai yace mashi da saura, Haisam daya lura ran shi ya fara 6aci yana murmushi yace mashi gara ya saba kafin Ranar d'aurin aure ai tun kafin ya rufe baki ya fara girgiza mashi kai yace bazai k'ara wannan tafiyar ba Haisam da still Murmushi yake yace to ya za'ai Ranar d'aurin auren fuska a tamke yace oho shidai bazai zo a Mota ba, lokacin da suka iso garin gaba d'aya ran Sameer ya gama 6aci Haisam ya fara bashi hak'uri yana nuna mashi ai sun iso ya yamutsa fuska yace to mi akai tunda zasu koma, Yaya Mubarak ya kira ya sanar da shi gasu sun shigo gari yace Ok yana fara mashi bayanin inda