Showing 42001 words to 45000 words out of 512766 words

Chapter 15 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1569

ya buga jin tambayar da ya jefo mata har saida ta had'iye miyau Kutt, taya zata fad'a mashi abunda Khalid yay mata wanda shine silar komae, lokaci guda taji bata ma iya yi mashi wannan bayanin jin tayi shiru yasa shi ce mata yana saurarenta cikin dabarbarcewa tace "Ya Abbas bai fad'a maka ba?" Yace ya d'an fad'a mashi yana son yaji komae ne daga wurinta, a rud'e don har wata yar zufa taji a fuskarta tace mashi to ai abunda ya fad'i mashi shi ya faru ya furta mata Ok har saida ta dafe k'irji irin tasha da k'yar d'in nan,

"Zaka dad'e ne anan?" ta tambaye shi d'an shiru yay kafin yace "Nah Next tomorrow zan wuce" d'an zaro ido tay tace ranar Monday kenan yace mata Yea shiru ta d'an yi duk sai taji wani iri jin tayi shiru yasa shi tambayar ta koda wani abu ne da sauri tace "a'a Allah ya kaimu" a hankali ya amsa da Amin sai kuma ta k'ara ce mashi sai Allah ya kaimu yace baccin yazo kenan tace eh yace "Ok gud nyt" tace to ta kashe wayar a hankali ya lumshe ido, to bansan dai ko bacci bane shima yazo mashi ba, aje wayar tay gefe ta koma ta kwanta tay lamo hakanan take jin wani iri tunda taji yace jibi zai tafi a haka da k'yar bacci ya kwashe ta.

Washe gari wurin k'arfe 11 lokacin ta gama gyaran gidan tana zaune a d'aki saman gado tana duba littafin ta idanunta sanye cikin glass sai ga kiran Haisam ya shigo d'an murmushi tay ta d'aga ta gaida shi yay mata ta tashi lpy ta amsa da Alhamdulillah d'an shiru yay daga baya kuma sai yace mata ta fad'a ma gwaggo zasu d'an fita around 3:00 tace mashi to suka yi sallama ta sauka daga gadon ta iske gwaggon a d'aki tana kwance, koda ta sanar mata d'an murmushi tay tace ba komai Allah ya kaimu Fatun ta amsa mata da Amin kafin ta fito ta dawo d'aki, kasa cigaba da karatun tay ta tattare books d'in ta mayar cikin bag ta nufi wardrobe don ta za6i kayan da zata za ba sai lokacin ba ta kasa za6a, wani dark purple material lace ta fiddo yana da kananun flowers light purple da tsabu tsabun ash mai kaman silver d'inkin straight gown ne yayi kyau sosae ta fiddo gyalen shi light purple da takalma sai yan kunne da sarka silver da yar please purse itama silver komae ta aje a gefen gado sauran jiran lokacin saka su, zuwa k'arfe biyu da rabi tayi wanka taci Abinci ta hau shiri ba 6ata lokaci ta gama lokacin ukku ta d'an gota da Minti biyar daidai ya kirata yace yana waje tace to, saida taje tay ma gwaggo sallama yau ma tana ta yabon gayun nata Fatun sai dariya take tace mata sai sun dawo ta fito, idon shi a kanta har ta zagayo ta bud'e gaban Motar ta shiga bayan ta rufe ta juya suka had'a ido tana murmushi ta gaishe shi shima fuskar shi a sake ya amsa yana sanye da complete bak'ak'en kananan kaya jeans da t-shirt haka agogon dake d'aure a hannunshi itama bak'a ce sumar nan tasha gyara sai salk'i take ga k'amshi da ya cika Motar abun ba'a Magana kasa d'aurewa Fatuu tay ta d'an juyar da kanta gefe ta lumshe ido ya Haisam naso ya ida kasheta da salon gayun shi, jan Motar yay suka tafi ba tare da wani ya k'ara cewa komae ba sai sanyin Ac dake ratsa sassan jikin kowannen su, a daidai wata k'atuwar plaza ya karya kan Motar ya shiga ciki lokaci guda Fatuu ta ga kaman tasan plaza d'in bayan ya parker a wurin da aka tanada ya kalleta yay mata alamar suje da kai ta bud'e ta fito ya nufi cikin plaza din tabi shi saida ta ga shagon da suka tunkara mai d'auke da sunan Zee Collections sannan ta gane wurin har saida tay d'an murmushi, shi ya fara shiga tabi bayanshi ba kowa a Parlon sai wata yarinya da gani ba ita bace wadda ke a shagon ba lokacin da suka ta6a zuwa wato Esther saidae itama yarinyar Christian ce k'ilan ko k'anwar waccan ce tana ganin su ta mik'e da sauri tana ce masu welcome kafin ta gaishe dasu cikin harshen turanci suka amsa Haisam ne ya tambayeta Ogar tata tace tana ciki bari ta kirata ta juya da sauri Fatuu tabi kanta da kallo da akai ma k'waryar molo kamar dae waccan Esther d'in a ranta take ayyana kawae a aske mata gashi ai sai tayi hauka wllh, zama Haisam yay kan doguwar Leather sofa d'in dake a wurin yay ma Fatuu alamar ta zauna ta nufi can gefen shi ta zauna lokacin Zee ta fito tana sanye da doguwar rigar Boubou ta Atamfa tana yin arba da Haisam ta waro ido alamar mamaki shi kuma yay mata d'an murmushi can daga gefensu ta zauna saman wata kujerar tace "Zakee Manyan gari ko in ce Manyan dawa kai ne a K'asar tamu saukar yaushe?" Fuska a sake ya fad'i mata lokacin da yazo tana ta murmushi tace mashi an zo lafiya ya amsa mata lokacin Fatuu ta gaishe da ita ta kai idonta gareta tana amsawa da fara'a can tace "Wai kaman Zarah ko?" Yar dariya Fatuu tay tace itace Zee ta bud'a ido had'i da ruk'e ha6a tace "Zarah kece kika girma haka halan kin gama Secondary ma?" Fatuu tace mata eh ta gama ta tambaye ta taci gaba da karatu tace mata eh,

"Wani School kike ne?" Zee d'in ta tambaya Fatuu ta bata amsa da "School of Nursing" jinjina kai zee tay tace "Gud, Allah ya bada sa'a" ta amsa mata da Amin, maida idonta tay kan Haisam dake latsa waya tace "H,Zakee ya Matan ka ta haihu kuwa ai ina jin kaman anyi 9 Months da auren ku ko?" Kai ya d'aga mata alamar eh, tace "halan ta haihun don nasan ba lalle ka fad'a ba koda yake da ta haihu ko a wurin su Jidderh na ji ai, ba da ita ka zo bane?" Kai ya sake d'aga mata alamar eh tace Allah sarki sai kuma ta kalli Fatuu dake ta murmushi itama tayi mata ta sake maido dubanta kan Haisam tace "Wai ni H,Zakee ko dae kai zaka mana Wuff da Zarah ne?" Kamar saukar aradu haka Fatuu taji Maganar ba shiri da sauri ta kalli Zee dake ta murmushi sai kuma ta juya kan Haisam suka had'a ido da sauri ta kauda idon nata ta sadda kanta k'asa wani kallo yay ma Zee tana ganin haka tasa dariya tace "Serious ka Aure ta kawai kaga kayi kiwon abun ka kenan?" d'an murmushin gefe kawae yay bai ce komai ba ta kai idonta kan Fatuu da har lokacin kanta ke sadde tace "Zaraah ko baki son Yayan naki?" Shiru bata ce mata komae ba bata kuma d'ago ba hakan yasa Zee cigaba da yin dariya Haisam yay sigh kafin yace mata zata za6i kaya ne Fatuu na jin haka ta d'ago da sauri ta kalle shi tana niyyar yin magana Zee tace "a'a Zarah kar muyi haka dake fa kaya aka ce zaki za6a ki tashi kawae muje dama Akwae d'ibar farko ta salla suna ciki ban kaiga fiddo su ba sai an fara Azumi kin ga rabon ke zaki fara za6a ne" shiru Fatuu tay don ta riga ta kashe mata baki tace suje tana kokarin mik'ewa itama Fatun ta mik'e har sun tafi Zee ta juyo tace ma Fatuu ta shiga ciki tana zuwa ta koma gun Haisam ta tambayeshi kaman kala nawa yace ta tambayeta tace Ok sai kuma ta d'an rankwafa yadda zai ji ta cikin kaman rad'a tace "Serious H,Zakee ka auree yarinyar nan kawae wllh don bata dace da kowa ba sai kai kaga kaci ribar rainonta da kai duk da nasan don Allah kai amman fa gida bai k'oshi ba ba akai ma dawa ba" ba shiri Haisam yay dariyar da har fararen hak'oransa suka bayyana Calmly ya furta "Zee Who told u gida bai k'oshi ba?" Kanne ido guda tay tace "a ina gidan ya k'oshi ai sai Mutum yayi hud'u sannan kuma yarinyar nan da kake gani mai zafi ce don haka da irin ka mai zafi ta dace willh" tana k'arasa Maganar ta mik'e ta juya tana dariya tana fad'in kar ya fad'i ma Matar shi fa ya girgiza kai kawae shima yana yar dariyar, duk yadda Fatuu taso kar ta d'auki kaya da yawa saida Zee tasa ta d'auki kala biyar da k'yar gashi duk masu tsada, laces kala biyu sai Atamfa ma biyu sai wani had'addan cotton material harda doguwar riga jallabiya saida ta lik'a mata sannan aka d'auki mahad'in kayan su gyale da takalma harda jaka dasu sarkoki don ma Fatun ta kafe kan ba kowanne zata d'aukar ma mahad'in ba wanda zai hau da kaman kala biyu take d'auka, koda tay mata Maganar English wears da Undies Fatun cewa tay duk tana da su, bayan sun fito Zee ta zauna ta kalli Haisam tana yar dariya tace "da alama har yanzu Zarah tana tausayin ka bata son kana kashe kud'i don yanzu ma da k'yar aka za6i kayan kaman dai other time" d'aga ido yay ya kalli Fatun ta d'an tura baki ta juyar da kanta gefe, card ya ciro ya ba Zee d'in ta fitar da kud'in yau ma saida yace ta k'ara 30k ta siya sugar Azumi tay ta godiya Fatuu kam shiru tay a ranta tana mamakin yadda yake kashe kud'i kamar baisan zafin su ba kai kace kawae umarni yake badawa ake buga mashi, har Mota Zee ta rako su da kayan aka saka booth tay wishing Haisam Safe flight tace ma Fatuu tana jiranta tazo mata yawon salla ta amsa da to suka shige Motar ita kuma ta juya ta koma, bayan sun bar plaza d'in ganin hanyar da yabi yasa ta tambaye shi shagon Kb zasu ne ya d'aga mata kai alamar eh tace mashi a bari ba yanzu ba ya tambayi dalili tace tana so sai ta samu styles sai ta kai mashi baki d'aya ya furta Ok suka canza hanya, Fatuu tay mamakin ganin sun tsaya gaban Shagon Maman Abdul mai saloon ganin tana kallon shi yace mata taje a wanke mata kai gudun kar tay mashi gardama ta 6ata mashi rai yasa ta juya ta fita, tun kafin ta shiga ciki Maman Abdul d'in ta fito ta tarbeta da alama hangota tay suka shiga ciki ta nuna mata kujera bayan Fatun ta zauna ta hau gaidata ta amsa sannan cikin washe baki anga customer ta tambayeta abunda za'a mata tace Wash and Set ta amsa da okey har zata juya sai kuma ta tsaya tana kallon fuskar Fatun da d'an alamun nazari can tace "Ma, ur face look familiar as if u ave came here before" d'an murmushi Fatuu tay ganin yadda dimples d'inta suka lotsa yasa maman Abdul d'in tabbatar da tasan face d'in ta koda ba anan ba ganin ta dage sai ta tuna inda tasan ta yasa Fatun yi mata bayani aikuwa da tsananin mamaki ta ruk'e haba tana fad'in itace wai ta girma haka miyasa ta dad'e bata zo ba Fatuu dai dariya kawae take can ta tambaye ta ina yayanta d'in nan da ya ta6a kawota tace mata yana nan waje shine ya kawota yanzu ma, da sauri tace "let me greet him I will come back now" tayi Maganar had'i da juyawa ti6i ti6i ta nufi hanyar fita Fatuu ko mi zatayi ba dariya ba ganin yadda duk ta rud'e su maman Abdul anji kud'i sun zo, tana isa driver side d'in ta d'an kwankwasa glass d'in slowly ya fara sauka tana ganin shi ta washe baki ta sunkuya tana fad'in "Good after....oh good Evening sir" duk ta rud'e sai washe baki take, d'an murmushi yay mata ya amsa yay mata ya kasuwa ta amsa da Alhamdulillah nan ta shiga fad'in taga Fatuu tay girma sosae shidae murmushi kawae yake tace amman ya akai suka d'auki tsawon lokaci basu k'ara zuwa bane ko aikin nata bai masu ba fuska a sake Yay mata bayanin tana gyarawa a gida ne Maman Abdul ta marairaice fuska tace ya kamata dae don Allah a rik'a kawota don za'a fi gyara mata anan yace Ok in sha Allahu tace bari tay sauri ta gyara mata kar ai keeping nashi yana jira ya jinjina mata kai ta juya da d'an sauri sauri gudu gudu ta koma, yana zaman jiran nata akai sallar la'asar ya fita yaje Masallaci dake gefen benen yay salla bayan ya dawo bada jimawa sosae ba aka gama ma Fatun Maman Abdul ta rakota har bakin Mota tana fad'in tana jiranta sai ta k'ara ganinta ta amsa da Ok ta kopar da Fatun ta bud'e ta d'an duk'a tace ma Haisam ashe yayi aure bai K'asar ma saida suna fira ne ta fad'i mata ya d'aga mata kai tayi mashi Allah yasa Alkhairi ya amsa da Amin ta koma kan Fatuu tace mata pls ko bai nan ta rink'a zuwa tace to, kud'i masu yawa ya fiddo yaba Fatuu ta mik'a mata zo kaga godiya tana yi tana sunkuyawa saida yaja Motar ta koma shagon, yana ta driving ita kuma tana ta kallon hanya can taji kamar yayi magana ta juya ta kalle shi tace Magana yake ne kaman bazai tanka mata ba idon shi akan hanya sai kuma taji yace "cewa nay ba za'a nuna man ba yau" dariya tay tasa hannu ta rufe baki tasan wasa yake mata don ya tuna mata da wanccan lokacin ne shima fuskar shi d'auke da d'an murmushi yake driving d'in, suna akan hanya ya kira Abbas ya tambaye shi yana gida yace eh yanzu da la'asar d'in nan ya dawo yace Ok gashi nan zuwa, lokacin da suka isa yay horn Abbas ne yazo ya bud'e mashi ya shigar da Motar bayan ya parker ta ya bud'e ya fita Abbas dake gefe yana mashi dariya ya bashi hannu sukai shaking yana niyyar yin magana Fatuu ta bud'e kopar ta fito da mamaki Abbas yace "Mom Zarah tare kuke kenan" d'aga mashi kai tay kafin ta gaishe da shi ya amsa yana murmushi yay mata ya School ta amsa da Alhamdulillah ya sake cewa "sai kika ga mutumin naki yazo ba ko notice?" Ita dai murmushi kawae take kafin ta tambaye shi Aunty Feenah yace ta na ciki tace to ta nufi cikin idon shi akanta yanata wani irin murmushi can ya juya suka had'a ido da Haisam dake jingine jikin Mota Abbas d'in ya furta "Perfect Match" wani kallo mai kaman harara yay mashi Abbas yasa dariya yace "Wllh kun matuk'ar dacewa am telling u d truth" dan ta6e baki Haisam d'in yay yace zai bar shi a tsaye ne da sauri yace tuba nike Angon Mom Zarah mu shiga ciki Haisam d'in ya d'an girgiza kai kawae suka wuce, lokacin da ta shiga ba kowa a Parlon hakan yasa ta wuce Bedroom d'in Feenah anan ta iske ta, tay matuk'ar jin dad'in ganinta tace halan ita da H,Zakee ne Fatun na murmushi tace mata eh ta mik'e tace suje su gaisa, anan Parlor suka suna hira bayan Feenah ta kawo masu abun ta6awa daga baya Haisam da Abbas suka ce zasu je su dawo suka ci gaba da hirarsu su biyu har Abdul ya dawo daga islamiyya, sai bayan Magrib suka dawo Haisam d'in bai shiga ba sai Abbas ne ya shiga ya kirata su Feenah suka rako ta da gudu Abdul ya nufi Haisam ya kankame shi yana dariya can ya d'ago ya kalli Haisam dake murmushi shima yace "Baba Zakee don Allah ka auri Aunty Fatuu" d'an d'age gira Haisam yay Feenah da Abbas suka sa dariya ita kuwa Fatuu sunkuyar da kai tay gabanta ya fara fad'uwa bata ta6a zaton zai mashi wannan Maganar ba, ganin yak'i cewa komae yasa Abdul jujjuya kai yace mashi "kaji Baba zakee kuyi aure kai da Aunty Fatuu don Allah" sigh Haisam yay slowly yace mashi Saboda mi yake son hakan yace "kaga kai babana ne ita kuma sai ta koma mamana" Haisam na murmushi cikin cool voice d'in shi yace "but kai kace ai tayi k'arama ta zama mom en ka" waro ido yay baki bud'e yana son tuna sadda yace hakan can yace "gaskiya baba zakee ni ban ce hakan ba fa" Abbas dake dariya yace ya dae manta ne a shagwa6e yace "to in ma nace haka ai yanzu ta zama babba zata iya zama mamana kaji kuyi Auren" gaba d'aya aka sa dariya Haisam yace "ai sister na ce ita..." Da sauri Abdul d'in ya katse shi yace "Amman dai ai ba gidan ku d'aya ba ko kai a Abuja gidan ku yake ita kuma anan kuma a islamiyya ance sai sister d'in da ake gida d'aya ne ba'a iya aure" nan ya shiga lissafo mashi wad'anda aka ce masu ba'a iya aure Abbas sai dariyar k'eta yake shi ma Haisam murmushi ne akan fuskar shi yasan yaron da shegen wayau duk yadda zai zame sai ya gane hakan yasa ya d'aga mashi kai yace to kawae nan fa ya hau tsallan murna ya tambaye shi to yaushe za'a yi bikin Haisam yace in an shirya zai ji a wurin Dad d'in shi cike da farinciki ya nufi Fatuu da ji take tamkar ta nutse don kunya ya kama hannunta yana dariya yace taji Baba Zakee zai aureta ko ta kasa ce mashi komae saida Abbas yace ya k'yaleta ai taji sannan ya bar Maganar Haisam yay masu sallama Abbas yace sai yazo kai shi Airport gobe Feenah ma tay mashi Allah ya kiyaye ya gaida Fanan yace Ok duk suka yi ma Fatuu sallama da k'yar ta iya d'agowa ta kalle su da yake wurin fayau yake da hasken fitilu ta amsa masu kafin jikinta sukuku ta zagaya ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login