Showing 30001 words to 33000 words out of 512766 words

Chapter 11 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

2272

tare da mai hakuri kuma bai barin zalunci).

"Yanzu ina Mujaheed d'in yake" Fatuu ta tambaya a zuciye, shanye kukan Fauzy tay tace "lokacin da Usman ya fad'a man yace basu K'asar tunda sukae Auren amman daga baya watarana Mun ta6a had'uwa a bakin hanya ya tsaya zai man Magana na k'i sauraren shi na tsallaka titi nay tafiyata, tun bayan lokacin na tsani zancen soyayya balle kuma ace ana sona bana saurarar Mutum har lokacin kuma ban daina jin son Mujaheed ba saidae kawae ina matuk'ar kokarin yakar zuciya ta kan ta manta shi, daga baya ne ganin na warware Mijin Yayata na nan yayi ma Abban mu Magana kan ya barni inzo in yi Karatu hakan zai sa in mance komae in ina shiga Mutane to shima din yana son in mance hakan yasa bai gardama ba ya barni wanda nice mace ta farko a gidan mu da ta cigaba da karatu ba tare da tayi Aure ba don ko ita Yayata Mareeya ta nan garin saida tayi aure tayi degree d'inta a nan" sauke ajiyar zuciya Fatuu tay cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri Fauzy nasan yadda kike ji don nima na shiga irin wannan halin nasan yadda rad'ad'in yake a zuciya duk da ba....." Da sauri Fauzy ta d'ago ta katseta "Zarah kema an yi breaking heart d'in ki kenan?" Girgiza mata kai Fatuu tay tace "kusan hakan saidae ni ba wani ne yayi man hakan ba nice na ja ma kaina don son maso wani nayi koma ince nike yi Saboda har yanzu nima abun na damuna acikin zuciya amman na samu sauk'i sosae don ma still ina tare dashi shiyasa na kasa cire shi a raina kwata kwata" idanunta ne itama suka ciko da k'walla cike da mamaki Fauzy ta tambaye ta wanene don ita kallon wadda bata kula samari take mata, ganin tayi shiru yasa ta k'ara ce mata don Allah ta fad'i mata mana ko bata yarda da ita bane kamar yadda ita ta yarda da ita Fatun tace a'a ta yarda da ita mana nan ta fad'i mata ko waye take so, da tsananin mamaki Fauzy tace "Ya Haisam dai da na san pictures d'inshi a wayanki wanda rannan ina maki wasa nace don Allah ki had'a ni da shi?" d'aga mata kai Fatun tay Fauzy ta sake cewa "Amma ba kince man Yayanki bane dama ba d'an gidan ku bane?" Ajiyar zuciya Fatun ta sauke kafin ta fara bata labarin tsakaninta da Haisam tun daga farkon haduwarsu har zuwa lokacin da ya tafi harda bayan tafiyar tashi da auranta da aka fasa har ta fara karatu, da tsananin mamaki Fauzy tace "Dama a gaske akwae irin wannan Mutanen da zasu rink'a yi ma mutum Alkhairi haka don Allah! Kai gaskiya koma akwae to da wuya a samu sai dace, gaskiya banga laifin k'awar ki Haulat ba don ko nice wllh irin tunaninta zanyi akan shi, ko bata fad'a bama irin wannan dole zuciyar mutum ta kamu da son shi don ita tana son mai kyautata mata ni kaina iya labarin nan da kika ban baki ji yadda ya k'ara burge ni ba sosae wllh, amman na matuk'ar tausaya maki Zarah irin wannan a kwae ciwo ace kana son mutun amman bai sani ba" d'an ta6e baki Fatuu tay tasa hannu tana goge sauran kwallan dake fuskarta can Fauzy tace "Amman fa da ace lokacin muna tare dake ni zan baki shawarar ki fad'a masa ne koma in je in fad'i mashin" d'an waro ido Fatuu tay Fauzy ta jinjina kai tace "am serious duk da ita Friend en ki da Uncle d'inki sun fad'a maki abunda yake daidai amman ni nayi la'akari da yanayin shi na Mutum ne da yasan darajar mutane mara wulakanci mai fahimta sannan mai son yaga farincikin wani don kin fad'a mashi bana tunanin zai k'i fahimtar ki tunda ai yasan yadda zuciya take kuma yana daga cikin wad'anda suka fi kowa sanin halin ki balle ace k'imar ki zata zube ko yaga baki da kunya" d'an murmushi Fatuu dake ta bin ta da ido tay kaman bazata ce komae ba sai kuma a sanyaye tace "to ko na fad'a mashin ai bashi da wani amfani kamar yadda kowa yace tunda yana da wanda yake so zai aura k'arshe hak'uri kawae zai bani" Fauzy tace "Yes he might do dat and he might not also kar ki manta yana son farincikin ki ina tunanin zai iya amincewa ko don farincikin ki ita kuma Matar tashi in har tana son shi da Gaske zata amince" d'an murmushi Fatuu ta sake yi tana girgiza kai tace "Don baki san yadda take son shi bane wannan ai dole tay tsananin kishin shi ma wllh ban tunanin zata iya amincewa ya aureta ita da wata ko dangin shi ba lalle su yarda ba tunda yar uwar shi ce" gyad'a kai Fauzy tai kafin tace "ina rok'on Allah yasa rabon ki ne shi ya cusa mashi tsananin son ki har ya kasa zama ya dawo yace a d'aura maku aure ko baki gama karatun ba" wani kallo Fatuu ta bita dashi Fauzyn tay yar dariya tace ko bata so ta d'an ta6e baki kawae kafin tace itama tana mata Addu'ar Allah ya bata
Wanda take so da sauri tace "Mujaheed ne kadae na so kuma a yanzu ko ya dawo wllh tllh bazan Aure shi ba duk da kuwa har yanzu da sauran son shi a zuciyata amman ko ke ai bazaki ban shawarar in Aure shi ba" jinjina kai Fatuu tay "hakane nima na fad'a ne kawae amman ban fatar wannan azzalumin ya zama mijin ki don baisan darajar dan'adam ba ki manta da shi kawae kina zaune Allah zai kawo maki wanda ya fi shi a komae yanzu mu dage da karatun dake gaban mu shi yafi ba tunanin wasu da basu san ma muna yi ba k'arshe Muzo muja ma kan mu matsala su sun riga sun gina rayuwarsu" sosae Fatuu ta shiga bata shawarwari kan ta daina damuwa da wani Mujaheed su maida hankali, mik'ewa Fatun tay tana fad'in itafa wllh yunwa ma take ji ta koma gadonta Fauzy da ke kallonta tace ko ta dafa masu indomie ne,

"Ni dae na gaji da cin wata indomie wllh" yar dariya Fauzy tay tace "to ai itace mai sauk'in dafawa a halin karatun nan da muke ciki yar gidan Ya Handsome, to ko in dafa mana Macaroni sai asa sardine nasan zata yi dad'i" d'an yamutsa baki Fatuu tai ta fara k'ok'arin saukkowa daga gadon tana fad'in ita dae bari ta fara shan Cornflakes gaskia bata iya jira har sai an dafa wani Abinci ta nufi inda Provisions d'in su suke idanun Fauzy a kanta can tace "Wai ashe Ya Handsome d'in ki ne yasa maki Zarah da kika ce man haka ake ce maki" daga inda take ta d'aga mata kai ta k'ara cewa "Allah sarki wllh k'awar nan taki ta burgeni tana ina?" tace mata tayi Aure tana Nijar

"Da wuya yanzu ka samu irin su don k'awance yanzu ya zama abunda ya zama shiyasa ni tsoron tara k'awaye ma nike ko da can, amman dae ke nasan nayi dace don tunda na gan ki kika burge ni kuma in sha Allahu nima zan zamar maki madad'in Haulat bazan ce fin ta ba don duk abunda ake so a k'awa tana dashi, tana son ki da Alkhairi bata maki bakin ciki da hassada farin cikin ki shine nata haka damuwar ki damuwarta ce bata maki kallon bare face Yar'uwa wad'annan abubuwan duk an rasa su a k'awancen yanzu da k'yar ake samun masu wasu daga ciki Allah yasa mudace mufi k'arfin zukatan mu dae" daga inda take ta amsa mata da Amin tana murmushi,

"Amman dae watarana yakamata mukai mata ziyara har Nijar d'in" Fauzy ta fad'a, da sauri Fatuu ta kalleta ta zaro ido tace "tabb ai saidae ko in ta haihu kin kuwa san yadda tafiyar take a kwana a wuni ana abu guda lokacin da muka je bikinta baki ga yadda kafafuwana suka sumbuk'e ba" dariya Fauzy tasa lokacin Fatun ta kawo mata cup d'in Cornflakes data had'a mata itama ta amsa tana murmushi tace mata thanks suka fara sha.

Sosae su Fatuu suka dage da karatu don tsallake ma had'arin dake tattare da jarabawar intro dake gabato su, Bayan wata ukku da yin pre intro suka yi ita intro d'in, cikin hukuncin ubangiji Fatuu ta tsallake don sunanta ma ne farko a list d'in haka Fauzy ma ta tsallake sai faman murna wad'anda suka ci suke suna kiran clean pass yayin da wad'anda basu samu ba ke a mawuyacin hali harda masu suma abun ba dad'i wllh to amman haka tsarin yake dole sai Mutum ya dage yanzu wata shiddan da suka 6ata ya tashi a banza sai dae hak'uri, bayan cin jarabawar ne akai masu clinical posting nan cikin Asibitin saidai ba'a kai Fatuu da Fauzy wuri d'aya ba Fatuu Gyne aka kaita ita kuma Fauzy tana a A&E (Accident & Emergency), su Fatuu an fara kama hanyar zama ma'aikaciyar lafiya hadda su farin glasses take sanyawa yanzu kuma ba k'aramin kyau yake mata ba sai tayi kaman cikakkiyar nurse ba Student ba patients da masu jinyarsu sai dae kaji anata Sister sosae Fatuu ke jin tausayin irin halin da Matan wurin ke ciki masu lalurar data danganci haihuwa da sauransu.

Ranar Friday bayan sallar Juma'a Fatuu ta dawo daga Makaranta don sun tsaya Hostel saida aka yi salla tana shiga gida ta aje Bagpack d'inta mai kyau mai manne da
Yar teddy jikinta sanye da sababbin uniform d'in data canza da suka zama cikakkun dali6ai, a gefen kitchen ta aje jakar ta nufi toilet abun ya riga ya zame mata jiki da wuya ta shigo gida bata wuce toilet ba, bayan ta fito ta d'auki jakar ta wuce ciki, d'akin gwaggo ta nufa ta d'aga labulan lokacin tana kwance akan gado saidae ba bacci take ba suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi Fatuu ta shiga ta zauna a bakin gadon Gwaggo tace "ai na ji shigowar ki halan saida akai abunda aka saba?" Dariya tayi tace "ni gwaggo banson yin fitsari a wani wuri wllh kyankyami nike ji ga toilet infection da ake kamuwa da shi in mai cutar yayi using wuri kaima kayi shiyasa ko a Makaranta in ina can indae zan yi amfani da toilet to sai na wanke shi fess sannan fitsari ma a tsaye nike yi sai in bi da ruwa aita ce man sarkin tsafta kuma ni infection d'in nike tsoro don muguwar cuta ce" jinjina kai gwaggo tay tace "tabbas kuwa don har haihuwa take hanawa, akwae wasu saiwowin magani ma da nasa a kawo sai ki rink'a amfani dasu har acan Makarantar na tsarki ne akwae kuma na sha don wani lokacin duk yadda kake kiyayewa sai kiga ka kamu baka sani ba gara kana yin riga kafi" d'aga kai Fatun tayi gwaggo ta tambayeta ya Makarantar tace Alhamdulillah nan ta shiga bata labarin maras lafiyan dake ward d'in da take gwaggon nata girgiza kai tana Addu'ar Allah ya basu lafiya can tace mata bata jin yunwa ne taga bata nemi Abinci ba tace eh da yake sun biya hostel sun ci abu gwaggo ta tambayeta Fauziyya tace itama ta tafi Weekend gidan Yayarta tace Allah sarki daga haka suka d'an yi shiru can tace "Na manta ban fad'a maki ba Hajiyar Sanata fa ta dawo d'azun bayan kin tafi Makaranta don har na ma shiga na gano ta" waro ido Fatuu tay sai kuma tay yar dariyar farinciki tace "Allah sarki Hajiyata ashe ta dawo wllh nayi missing d'inta" gwaggo na murmushi tace "itama haka don sai tambayarki take wllh ba kamar da ta ji abunda ya faru ta jajanta sosae har tace ta k'osa ta ganki" mik'ewa Fatuu tay da sauri tace bari taje to gwaggo ta d'aga mata kai ta nufi hanyar fita, bayan ta aje jakar goyon tata a d'aki ta fito ba tare da ta cire uniform d'in ba da glass d'inta manne a fuska ta nufi gidan Hajiyar Sanata.............



_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2038*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*






.......Da k'yar taja k'afafunta ta koma kan kujera ta fad'a da6as duk jikinta yay weak ta kasa gane wannan bak'in Abubuwan da yake mata na miye, bai jin komae yanzu yake ta6a ta ga wani irin kallo da yake mata wanda ada sam ba irin shi yake mata ba, shiru tay kamar mai nazari can wata zuciyar ta ayyana mata kodai son ta yake tunda ada da bai mata hakan ai ba son ta yake ba kuma ko Fanan da tazo itama yana ta6a ta lokacin kuma soyayya suke can kuma wata zuciyar ta tuno mata da labarin Fauzy wanda itama ai tace Mujaheed na ta6ata kuma k'arshe ya yaudareta, rasa tunanin ainihin dalilin canzawar Haisam d'in tay k'arshe jiki a sanyaye ta mik'e ta d'auki laptop d'in bayan ta kashe hasken parlon ta nufi d'akinta don ta san tuni gwaggo tay bacci, kayan jikinta ta cire ta sa na bacci ta haye gado sam tunanin Haisam yak'i barinta wani iri take ji ran ta sai bata yake ko dae da gaske son nata yake in kuwa haka ne da zata yi farinciki to amman mizai sa sai yanzu zai so ta bacin yana da mata wata zuciyar ta k'ara raya mata nan fa ta shiga wasi wasi k'arshe ganin tana neman harmutse kwakwalwarta da tunane tunane ta bar ma ran ta ba son ta yake ba kawae, Fauzy ce ta fad'o mata a rai tay tunanin ko ta kirata ta sanar mata game da zuwan shi sai kuma ta ayyana kamata yay ta bata surprise suje tare da shi to amman ya zata yi wata zuciyar tace in kince ya kai ki ai zai kai ki ne, d'an murmushi kawae tay k'arshe ta jawo d'ayan pillow dake gefen kanta ta rungume shi sosae ta lumshe ido a haka bata san lokacin da bacci ya kwashe ta ba, Haisam na komawa part d'in shi ya nufa duk da bai dad'e da yayi wanka ba da zai je gidansu saida ya k'ara watso ruwa ya fito d'aure da farin towel a k'ugun shi ya nufi press don saka sleeping dress, yana gamawa ya nufi switch ya kashe hasken d'akin kafin ya kunna bedside lamb guda d'aya ya haye gado ya kwanta yana facing sama da alama dae Haisam ya d'aura aure da tunani yana haka wayarshi ta fara ringing ya kai hannu gefen shi ya d'auka sunan Lovely Wife ya bayyana wato Fanan ce ta kira picking yay yasa speaker ya aje wayar kusa da kan shi cike da k'auna ta fara Magana tana nuna yadda tay missing nashi shima yace yayi nata ta tambaye shi ya akai bai bacci ba ko rashin ta by his side ne ya hanashi yi d'an murmushi kawae yay sai kuma yace mata Yeah, haka suka cigaba da hiran yawanci itace mai Maganar shidae saidae yay murmushi mai d'an sauti ko ya bata amsa a tak'aice daga baya sukai sallama har tana ce mashi zata zo a cikin dream d'in shi tayi mashi duk abunda ya kamata yana murmushi ya furta mata Ok had'i da take care, yana cire wayar ya aje akan bedside ya koma yana facing sama kaman da farko had'i da lumshe ido saidae bansan ko duniyar tunanin ya k'ara tafiya ba ko kuma baccin ya yi ba.

Washe gari sai wurin k'arfe 10 na safe Fatuu ta tashi tunda weekend ne ba school, bayan tayi breakfast ta fara gyara gidan zuwa k'arfe sha d'aya da rabi ta gama komae taje tayo wanka ta shirya cikin short skirt da yar vest zaman school ya koya mata sa guntayen kaya dama kuma zafi ake, saman gado ta haye ta d'auki wayarta ta fara lallatsawa nan ta fara doubting na kota kira Haisam d'in tayi mashi Maganar zuwa gidan su Fauzy ko kuwa ta k'yale shi,to in ta Kira kawae sai tace tana son ya kaita gidan k'awarta ita bata iya zuwa ne dole zai ya kaita haka tay ta wasi wasi can dai ta yanke kiran nashi lokacin da kiran ya shiga yana zaune a Parlor bai jima da gama yin Breakfast ba anan part d'in na shi don ko kayan ma ba'a kaiga zuwa an d'auke ba yanata Operating system jikin shi sanye da farar jallabiya jin ringing d'in wayar yasa ya kai hannu gefenshi ya daukkota ya kalli screen d'in kafin yay picking yasa speaker ya aje ta agefen laptop d'in d'an shiru sukae Fatun ce ta fara cewa "Ya Haisam ina kwana an tashi lpy" amsa mata yay da "Alhamdulillah and how was ur night?" Itama tace Alhamdulillah sai kuma tay shiru shi kuma yana ta lallatsa computer d'in gabanshi rasa ta yadda zata fad'i mashi tay sai kawae tace "d..dama na kira in k'ara maka godiyar Laptop" jinjina kai yay tamkar tana gani sai koma ya furta is Ok suka k'ara yin shiru can taji ya furta "then What else?" d'an gwale ido tay jin ya gano akwae abunda take son fad'a cikin yar inda inda tace "d....dama so nike in ba damuwa ka kaini gidan wata k'awata zaku gaisa da ita na ta6a bata labarin ka" shiru yay ita kanta sai taji kaman she sounds stupid da ta fad'i mashi hakan can taji yace "Magana ta kike da wasu kenan" rud'ewa tay bata zaci zai fad'i hakan ba cikin shaky voice tace "a...a wllh Ya Haisam kaji na rantse ni ba Maganar ka nike yi ba ita kadae ce itama don k'awata ce sosae kuma saida taga pic d'in ka a waya na ne ta tambayeni na fad'a mata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login