Showing 159001 words to 162000 words out of 512766 words
Chapter 54 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1587
bar maka in ka ci ka rage sai in ci, kuma ma ai nima ba iya cinye ta zan yi ba ko" yadda tay Maganar cike da shagwa6a saidae ita matsayin lafiya lou take Maganar ta, d'an guntun murmushi taga yayi gashi ya kafeta da ido ita kuma sai faman kikkafta nata take tana d'an juyar da fuskar, wani plate ya d'auka ya rufe kazar ya kai hannu ya d'auki cup d'in shayin ya cigaba da sha, bayan ya cinye waina d'aya ya tura mata bowl d'in ta d'an kalle shi, saida ya k'arasa shanye tea d'in ya bud'e kazar ya d'aukko fork ya fara k'ok'arin 6alla sai dai kuma tak'i 6alluwa ta dad'i, aje fork d'in yayi ya kai hannu wurin cutlery set d'in dake a tsakiyar table d'in ya curo yar wuk'a, d'an jim yay bai sata jikin Kazar ba ganin tana buk'atar a wanke ta tunda anan suke aje lokaci guda Fatuu ta fahimci dalilin dakatawar tashi ta mik'e ta mik'a hannu alamar ya bata ya d'aga ido ya kalleta kafin ya bata, bayan ya mik'a mata ta fita daga cikin kujerar ta nufi hanyar kitchen ya bi bayan ta da kallo har ta shige Corridor sannan ya juya da wani irin yanayi akan Face d'in shi, had'e hannuwan shi yay ya d'aura ha6ar shi a ranshi ya raya yakamata a sa washbasin a wurin Saboda zaryar da yaga tana yi, bada jimawa ba ta dawo ta wanko wuk'ar ta mik'a mashi amman sai bai amsa ba yay mata alamar ta zuba mashi, ganin kazar ta d'an mata nisa yasa ta zagaya daga gefen shi ta jawo plate d'in ta fara yankar mashi, gaba d'aya sun cika juna da fitinannan k'amshin jikin su Haisam har d'an lumshe ido yay slowly ya bud'e ba tare da ta gani ba, tana yanko wurin cinye ta d'aura mashi a plate zata k'ara ya d'aga mata hannu alamar ya isa ta kai idon ta kan shi suka had'a ido, d'an tura baki tay ta marairaice fuska a hankali ta furta mashi gaskiya bai isa ba yayi kad'an, ido ya bita dashi da alama ya kasa ce mata komai ta k'ara yanko wani ta d'aura, kallon shi tay ta d'an bud'a ido ta tambayi ta k'ara ya d'an wurga mata harara ta saki murmushi tace to bari a zuba mashi mahad'in kazar ta d'ebo dankalin ta zuba tana shirin sake d'ebowa ya kai hannu ya ja plate d'in ba tare da ya ce komae ba ta k'ara yin murmushi, tana shirin komawa wurinta taga ya kai hannu ya tura plate d'in kazar wurin da ta zauna, bayan ta koma ta zauna a nutse suka cigaba da yin Breakfast d'in tana yi tana d'an satar kallon shi, saida ya cinye wanda ta zuba mashin ya yago tissue ya goge bakin shi, mik'ewa yay zai bar wurin ya juya suka had'a ido taji yace ya bata space ta cinye komai ta d'an bud'a ido ya juya ya tafi tay d'an murmushi had'i da d'an girgiza kai, ba laifi ta d'an ci sosae bayan ta gama ta mik'e ta fara kwashe kayan tana kaiwa kitchen, saida ta wanke abubuwan da suka 6ata kazar da ta rage ta saka ta fridge wainar k'wan kuma da ledan biredin ta ajiye su saman counter, bayan ta gama fitowa tay ta wuce Bedroom saida ta d'aukko wayar ta daga cikin purse ta koma gefen gado ta zauna, bayan ta bud'eta tunanin wa zata kira ta shiga yi can ta kira Fauzy tana fara ringing ta d'aga,
yar shewar farinciki tay tace "K'awata Amarya ai ban tsammaci ganin kiran ki ba don banyi tunanin zaki tuna da wata Fauzy ba da wuri haka" d'an murmushi mai sauti Fatun tay ta tambayi ya suke da Aunty Mareeya tace mata duk suna lafiya ta k'ara ce mata ya gajiya had'i da yi mata godiya, tana dariya tace ai ita ke tattare da gajiya su tasu tabi jiki tuni har saida Fatun ta d'an girgiza kai, tambayar ta Ya Haisam Ango tayi tace mata yana parlor, hiran School suka shiga yi ta tambayi yaushe zata dawo Fatun tace mata jibi in Allah ya kaimu,
"ah haba dae jibi, ki bari sai kin gama cin Amarci kaman after a week sai ki dawo" tana murmushi tace mata so take ta samu matsala kenan Fauzyn tace to ta bari sai kaman Wednesday tazo amman ba jibi ba, tuna mata tay tace kar Amarci yasa ta manta da Assignment d'in da aka basu ran Friday dai, Fatun tace to zata yi jakarta ma na gida amman yanzu zata kira Kawu Amadu ya kawo mata, daga baya sukai sallama tana ce mata ta gaishe mata da Ango tana murmushi tace zai ji,
Bayan sun gama wayar Kawu Amadu ta kira har saida ta kusa yankewa sannan ya d'aga ta gaishe dashi yana yar dariya yace "Amaryar mu kun tashi lafiya" amsa mashi tay da lafiya lou suma ta tambayi ya suka tashi yace mata lafiya, jin ta d'an yi shiru yasa shi tambayar ta lafiya dai ko cikin yar in ina tace mashi dama don Allah so take ta rok'e shi ya kawo mata jakarta ta makaranta, farko cewa yay shi ba zai kawo ba ta marairaice tana rok'on shi k'arshe sai cewa tay shikenan bari tazo ta d'auka da kanta yana dariya yace ai dama yana cikin shago ya sake ya ganta sai ya zane ta kuma da tsallan kwad'o zai maida ta, itama dariyar take a hankali tace mashi ai yanzu ta wuce wannan a wurin shi yace eh lalle ta isa shi take gaya ma haka ko to ta gwada fitowar zata sha mamaki, rok'on shi ta k'ara yi yace bari ya kawo mata tay mashi godiya ta tambayi gwaggo yace ta na cikin gida, bayan sun gama wayar d'an jimm tay tana son kiran gwaggo amman kunya take ji, can dai tay dialing lambar ta ta fara ringing, bayan ta d'aga a kunyace ta gaishe da ita tana murmushi ta amsa tay mata sun tashi lafiya da tambayar d'anta Haisam Fatun tace mata yana parlor tace to ta gaishe mata da shi tace to, d'an shiru sukai can gwaggon ta ce badai wata matsala ko da sauri tace mata eh ba komai, tambayar ta tay wai ta fad'a ma baffanta zancen gwaggon tay yar dariya tace ta fad'a mashi mana yayi farinciki sosae ma, cikin yar shagwa6a tace amman shine bai kirata ba tace k'ilan ya bari sai an samu natsuwa ne, bayan sun gama ta shiga kiran Baffan nata cikin sa'a ta shiga ya d'aga ta gaishe da shi yana murmushi ya amsa ya tambayi ya take ita da maigidan nata, cike da shagwa6a tace "Baffa shine kasani amman baka kira ni ba gaba d'aya ma ka manta dani" yar dariya yayi "haba ni na isa in manta da inna wuro gaba d'aya, dama zan kira na bari a nutsu tukun, na matuk'ar yin farin ciki da jin abun Alkhairi wllh har bazan iya kwatanta maki ba ashe dai rabon shine mijin naki yasa komae ya faru, kinga sakamakon yi ma iyaye biyayya Allah ya juya komai, Nagode inna wuro ina matuk'ar Alfahari dake matsayin jinina, ina rok'on Allah ya k'ara ma rayuwar ku Albarka ya jikan Mahaifiyar ku" har k'walla sun taru a idanun ta ta amsa mashi da Amin, tambayar ya karatun ta yay tace mashi Alhamdulillah yace Allah ya bada sa'a, bayan ta amsa ta tambaye shi Yadikko yace tana d'aki bari ya mik'a mata tace to, bayan ya kai ma Yadikkon cike da Farinciki tana washe baki suka gaisa tana fad'in Amaryar su, tambayar ya gida da Angon ta tay Fatun ta amsa mata ta shiga yi mata Allah yasa Alkhairi da nuna yadda tay murna da Al'amarin tace Addu'ar da suke tayi ce Allah ya amsa taji mata dad'i sosae wllh da Al'amarin ya juye haka dama haka take ta fata, daga jin yadda take Maganar Fatuu ta fahimci ba k'aramin farinciki take ba, tambayar ta su Mino tay tace basu kaiga dawowa daga islamiyya ba tace to in sun dawo zata kira ta tambayi yaushe zasu zo tace suna nan zuwa in ta Haihu, a shagwa6e tace a'a ita dae bata yarda ba wllh tana dariya tace suna nan zuwa bada dad'ewa ba, bayan sun gama Magana da Yadikkon ta ba Baffan wayan suka cigaba nan yake tambayar ta Haisam yace bai da Lambar shi yana son yi mashi godiya tace ai yana nan ko a kai mashi yace to, mik'ewa tay da sauri ta nufi hanyar fita, Yana kishingid'e kan kujera ta tunkaro shi Wayar kare a kunnanta, tana zuwa daga gefe ta tsaya ta cire wayar daga kunnan ta a hankali tace mashi Baffan ta ne yake son Magana da shi ya d'an d'aga mata kai ta mik'a mashi wayar ya amsa, gyara zama yay a nutse ya gaisa da shi nan ya hau yi mashi godiya sosae da Addu'oi, k'asa k'asa yake amsa wasu wasu kuma yay shiru daga baya sukai sallama ya mik'a mata phone d'in idon shi cikin nata da d'an murmushi ta amsa ta maida ta kunnan ta, har ta juya kaman zata tafi sai kuma ta dakata tana tambayar Baffan yaushe zasu zo to jin yana mata sallama yace mata ba yanzu ba sai an d'an jima, aikuwa cike da shagwa6a ta hau Jujjuya jiki tana ita dae bata yarda ba don Allah su zo kwanan nan kai kace da gayya take juya jikin saidae ita bata ma san tana yi ba kuma da alama ma ta manta da a gaban Haisam d'in take, shi kuwa kafe bayan nata yay da ido da wani kalan expression mai wuyar fassaruwa yake kallon nata, bayan sun yi sallama ta juyo suka had'a ido ta sakar mashi d'an murmushi shima ya d'an yi mata, juyawa tay zata tafi taji yace in ta gama abunda take zasu gaishe da Hajiya ta juyo tace mashi to sannan ta tafi, tana komawa Bedroom d'in bada jimawa ba akai knocking kopar ya bada izinin shigowa, Amadu ne ya shigo ruk'e da jakar Fatun da d'an murmushi ya nufi cikin parlon ya tsaya daga gefe yana gaishe da Haisam d'in, bayan ya amsa ya nuna mashi armchair yace ya zauna mana, mik'ewa yay ya nufi hanyar Bedroom d'in da alama kiran ta zai yi, yana tura kopar daidai ta kawo bakin kopar zata bud'e ta yafo mayafi golden da ta sa jiya da yake a atamfar akwae golden brown harda takalman da ta saka jiyan mahad'in gyalen half cover masu tsini sun k'ara mata tsawo ta tattara gashin ta a baya ta sa red ribbom sai yayi kaman ta saka hular gashi don ya rufe gefe da gefen fuskar, tura kopar da yay ta buge mata goshi da sauri taja baya had'i da sa hannu guda ta dafe wurin da ta bugen, bai yi zaton tana a bakin kopar ba yay moving zuwa inda take tsaye ya kai hannu ya cire hannun ta da ta dafe goshin wurin har ya d'an canza kala, bin wurin yay da kallo ya kasa furta komae don gaba d'aya wata irin kasala yaji ta fara saukar mashi sakamakon K'amshin ta da ya cika mashi hanci, jin yayi shiru yasa ta d'aga ido ta kalle shi suka sauka cikin nashi nan take gabanta ya fad'i ganin irin kallon da yake mata da sauri ta sauke idon ta k'asa, d'ayan hannun nashi slowly ya zagaya dashi bayan ta ya matso da ita suka had'e da juna nan take wutar Fatuu ta d'auke ta fara shiga wani irin yanayi dama kuma a tsume take har saida ta d'an runtse ido, jikinta ne ya canza wata irin kasala ta baibaiye ta wani abu ya fara mata yawo a jiki ga k'afafuwan ta na neman kasa d'aukarta, sauke gudan hannun shi da ke ruk'e da natan yay k'asa ya d'an sunkuyar da face d'in shi Slowly ya d'an fara matsawa da ita saitin tata, jin saukar breathing d'in shi a gab da Fuskar ta yasata d'agowa da sauri har saida gabanta yay wani irin bugu ganin fuskar shi kusan saura kad'an ta had'e da tata, wani irin kallo mai wuyar fassarawa suka shiga bin juna da shi, da k'yar Fatuu ke daurewa gudun kada ta zaqe don ta kai wata ga6a da take neman rasa control idanun ta har sun fara lumshewa sai k'ok'arin daidaita su take amman abun yaci tura kawae sai ta rufe su gaba d'aya, bin dogayen eye lashes d'in ta yay da kallo sai d'an far far suke sakamakon idanun nata dake motsi, numfashin ta ne ya nemi tsayawa jin ya had'e faces d'in su nan take jikinta ya fara d'an rawa ta koma yin numfashi da sauri da sauri shima nashi da d'an k'arfi yake fita yana had'uwa da nata, sun d'an d'auki lokaci a haka suna ta shak'ar scent d'in juna, can ya janye fuskar ta shi a hankali ya maidata gefen tata ta yadda kwantaccen sajen shi ya had'e da gefen tata fuskar cikin wata irin murya mai fuzgar mai sauraro ya furta "am sorry, bansan kina a wurin ba...." Kasa ko d'aga mashi kai Fatuu tay idonta still na a rufe taji ya k'ara furta "Uncle d'in ki na jiran ki a parlor" yana yin Maganar ya d'ago ya cire hannun shi dake tallabe da ita ya juya ya nufi hanyar Laundry ba tare da ya ko kalleta ba, da k'yar ta d'an bud'e idanun ta da suka gama canza kala tabi bayan shi da kallo kar ya shige ya rufe kopar, kasa cigaba da tsayuwar tay don gaba d'aya jikinta ya gama mutuwa da k'yar ta ja jiki zuwa bakin gado ta zauna dabas still breathing heavily, hannu tasa ta dafe goshin ta ta d'an sadda kai, ita kad'ai tasan mi take ji a jikinta, da k'yar ta fara k'ok'arin daidaita kanta tunowa da yace Kawu Amadu na a parlor, mik'ewa tay jiki a mace ta nufi kopar ta bud'e, bayan ta fito saida ta k'ara tsayawa a cikin Corridor ta k'ara daidaita natsuwar ta sannan ta nufo cikin parlon, tana shiga suka had'a ido ta fara mashi murmushi wanda yafi kama dana yak'e shima d'an murmushin yake mata ta nufi inda yake, a d'ayar armchair d'in ta zauna ta gaishe da shi ya amsa shiru ta biyo baya don sai taji kaman muryar ta ba a daidai take ba, hannu ya kai ya d'aukko bag pack d'in daga k'asa ya d'auro ta kan hannun kujera yace mata ga ta nan da k'yar tace mashi ta gode, ganin ya mik'e alamar tafiya zai yi yasa cikin yar rawar murya tace don Allah ya tsaya yay breakfast yay mata wani kallo mai kaman harara ya juya ya tafi ta k'ara ce mashi ta gode ya d'aga mata kai kawae lokacin ya bud'e kopar ya fita, zaune tay turus tama rasa mi yake mata dad'i a hankali ta d'aga ido ta kallo kopar Bedroom d'in ta shiga tunanin zuwa zatai tay mashi magana su tafi ko kuwa, ji tay bazata iya zuwan ba tay zaune zuciyar ta na tariyo mata abunda ya faru a tsakanin su, tana haka bayan wani lokaci taji k'arar bud'e kopar Bedroom d'in aikuwa da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa, nufo cikin parlon yay idon shi akanta ya tsaya daga gefen ta taji yace zasu iya tafiya sai lokacin ta d'ago ta kalle shi ta d'an d'aga mashi kai, mik'ewa tay har zai juya sai kuma ya dakata ya juyo yana kallon ta ta d'an kawar da fuskar ta, "How are feeling, ko wurin na ciwo muje Hospital?" D'an kallon shi tay had'i da girgiza kai a hankali tace a'a yama daina zafin ya jinjina kai yay gaba ta bi bayan shi a ranta ta shiga raya kenan duk abunda yay mata d'azun ban hak'uri ne Saboda ya buge ta, yana gaba tana biye dashi suka shigo harabar gidan, suna cikin tafiyar ta kai idon ta can gefe wurin parking space ta hangi d'awisu ya bud'e jikin shi yana kuka gwanin burgewa, murmushi Fatuu ta saki tunowa da can baya lokacin da ta kawo ma shi Fruit na karin ciwo ta iske zashi Masallaci har suka fito tare ta tsaya a harabar tana ma d'awisun wasa shi kuma ya nufi hanyar Masallacin yana d'an d'angyasa k'afa Saboda raunin da yaji da kwalba, gab da zai shiga ta kware murya tace Ya Handsome kayi man Addu'a Allah yasa in zama likita ya d'aga mata kai ba tare da ya juyowa ba, fad'ad'a murmushi tay bata ta6a kawo wa a ranta wai zasu yi aure ba don ita auren ma bai gabanta a lokacin duk da kuruciya, ko ba aure a tsakanin su Haisam nada daraja a wurinta ta silar shi ne ta san kanta ko lokacin da ta kasa mashi uzuri da abu ya Faru tsakanin su harda girman da yake da shi yasa duk da tana tunanin laifi yayi mata amman bata son girman shi ya fad'i ne gashi hakan ba K'aramin karya mata zuciya yay ba don tana ganin ita tana k'aunar shi shi kuma sha'awar ta yake ashe duk ba haka bane, Kallon bayan shi taci gaba da yi wata irin k'aunar shi na ratsa mata zuciya har tana d'an yin murmushi a haka har suka k'araso part d'in suka shiga,
lokacin da suka shiga basu samu kowa a cikin parlon ba an dai gyara shi fess sai k'amshi ke tashi, Hanyar Bedroom d'in ta ya nufa ta bi bayan shi, knocking kopar ya d'an yi daga ciki ta bada izinin a shiga ya tura da yar sallama ya shiga, tana zaune a bakin gado idanunta sanye cikin glasses hannunta ruk'e da Littafin Addini tana dubawa bata dad'e da komawa cikin d'akin ba bayan ta yi Breakfast, d'ago ido tay ta kalle shi tana niyyar yin Magana Fatuu ma ta shigo da sallama Hajiya ta saki murmushi tana amsa mata kafin tace "Maraba da Amaryar mu" d'an sadda kai tay Hajiyar ta nuna mata gefen ta da hannu alamar tazo ta zauna,