Showing 255001 words to 258000 words out of 512766 words
Chapter 86 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1567
ta hau godiya tace zata masu Magana sai su shirya dama jiya da daddare suke Magana da Baffan Fatun kan bikin yake tambayar ta ko za'a je daga nan tace ya bari sai ta tambaya Abbas na dariya yace ma gwaggo ai ba sai an wani tambaya ba suna da hakki suje itama dariya take tace hakane wai dai kar ayi ba daidai ba, nan yake sanar mata suma ran Wednesday zasu tafi tace to Allah ya kaimu suka yi sallama.
Bayan Fatuu ta koma d'akin Jidderh wayarta ta d'auka ta hau online, sakonni na fara shigowa sai ga sak'on Haulat da sauri ta shiga voice note ne ta turo mata, bud'ewa tay ta fara saurara cike da farinciki take sanar da ita an barta zata zo, sosae Fatuu taji dad'i don tasan Haulat mai kaunarta ce kuma tana ganin komai ya faru da ita hada silarta, fita tayi daga cikin WhatsApp d'in ta fara k'ok'arin kiran Abbas bayan ya d'aga ta gaishe dashi ya amsa yana fad'in Amaryar su an je lafiya ta amsa mashi da lafiya lou, jin ta yi shiru yasa shi tambayarta ko da Wani abu da yar in ina tace dama so take ta tambaye shi yaushe zasu zo yace mata ranar laraba in Allah ya kaimu, k'ara tambayar koda wani abu yayi jin ta k'ara yin shiru tace eh dama don Allah k'awarta ce Haulat zata zo daga Nijar shine take son in ba matsala tazo nan sai a taho da ita, yana murmushi yace "an gama Amarya ai umarni kawai zaki bada bawai ki rok'a ba koda ba Mota da anyi ma Angon naki magana zai iya turowa a d'auketa koda ita kad'ai ce don na lura yanzu ke kike control d'in heart d'in shi" waro ido tay tasa hannu ta rufe baki sai kuma ta cire tana fad'in don Allah ya rufa mata Asiri kar Aunty Fanan taji dariya kawae yayi yace Shikenan dai abar Maganar, bayan sun gama wayar WhatsApp ta koma ta tura ma Haulat sakon voice note ta sanar da ita su gwaggo ranar laraba zasu taho tayi magana taje can sai a taho da ita, bayan ta tura mata sake fita tayi ta kira Fauzy suka gaisa Fauzyn tace ai ta kirata d'azun bata d'aga ba tace eh bata kusa ne, Maganar anko tayi mata tace ai Ya Haisam yayi masu harda Aunty Mareeya su turo measurements d'in su yanzu in sun gama wayar, wata irin k'arar murna Fauzy ta saka ta hau shi ma Haisam Albarka tana Addu'ar Allah ya k'ara mashi Arziki mai Albarka, Fatuu na jinta ta hau kwala ma Aunty Mareeya kira tana fad'in anyi masu anko wllh Fatuu sai dariya take, sanar da ita tay sunyi waya da Ya Abbas yanzu yace ranar laraba zasu taho Fauzyn tace eh Aunty Mareeya ma sunyi Magana da Aunty Feenah ta sanar mata, hira suka cigaba da yi nan Fatuu ke ce mata zata yi ma Aunty zee mai kaya magana tana son taje ta amsar mata sak'o sai ta kai ma Kb tailor Fauzyn tace to tana jira daga baya sukai sallama.
Gwaggo suna gama waya da Abbas ta kira Baffan Fatuu bayan sun gama gaisawa tayi mashi zancen zuwa a d'auke su sosae yaji dad'i shima ya hau godiya nan cikin hikima ta nuna mashi ba gayya za'ai ba ya za6i wanda zasu je tunda ba irin bikin nan bane yace in sha Allahu za'a yi hakan daga baya suka yi sallama, d'akin yadikko ya nufa ya Sanar mata nan ta hau murna har Fuskarta ta kasa 6oyewa, tare da ita suka tsara yadda za'a fad'i ma Ard'o da kuma wad'anda yakamata suje.
Shirye shirye sun kan kama a kwana a tashi ba wuya a wurin Allah ranar laraba Abbas ya taho da Aunty Mareeya da Feenah, Abdul sai Haulat da Mino sai Tk kuma ya taho da Amadu da Fauzy sai Aunty Saude harda Zainab Muhammadu k'awar su da Fatuu tasa Fauzy ta taho da ita don ta matsa tana son zuwa, lokacin da suka iso Sosae Fatuu tay farinciki kamar zata zuba ruwa a k'asa tasha yayin da su kuma wad'anda basu ta6a zuwa ba Al'ajabi ne ya kama su ganin irin d'aular da su Haisam suke ciki har fuskokin wasu sun k'asa boye Al'ajabin, a parlor aka tarbesu ana masu sannu da hanya Hajiya da Mom da Aunty dasu Laila duk sun fito cikin parlon anata gaishe gaishe a mutunce can sai ga Nameer ma ya shigo cikin parlon tarbar Abokin shi Amadu, yana ganin shi ya mik'e ya bashi hannu suka gaisa Nameer d'in yayi mashi an zo lafiya ya amsa yanata washe baki, matsawa yay wurin Tk shima suka gaisa ya zauna daga gefen shi, bin sauran Mutanen yay suka gaisa Aunty Mareeya na Fad'in ga mai kama da mijin Zarah duk akayi murmushi, tunda ya d'aura idon shi akan Mino ya bita da kallon k'urulla don yana ganinta ya gane yar uwar Fatuu ce, duk in Mino ta d'ago sai taga ita yake kallo hakan yasa tasha jinin jikinta ta fara yan kame kame kawae sai gani tay ya sakar mata murmushi har bata san lokacin data mayar mashi ba, bayan an gama gaisawa aka kira wasu daga cikin ma'aikatan da aka k'ara d'auka Saboda hidimar suka yi masu jagora inda zasu sauka, Mino na tafiya tana waiwayen Nameer da ya nufi bene dasu Amadu da Tk zai kai su part d'in shi shima waiwayen nata yake suna niyyar shigewa kopar da zata kai su baya ya d'ago mata hannu tay yar dariya, wani duplex ne a bayan gidan can wurin inda babban Kitchen yake nan aka kai su, ginin part biyu gare shi kowanne yana da babban parlor sai corridor guda biyu kowanne yana da d'akuna biyu da toilet, Fauzy da Haulat da Mino da Zainab Muhammadu d'aki guda suka shiga akwae gado da mirror sai wardrobe din bango kowanne d'aki haka yake tsaf an gyara, Feenah da Aunty Mareeya da Saude suma d'aki d'aya suka shiga ita gwaggo Hajiya taja ta d'akinta wai ta bar ma yara can, bada jimawa ba aka fara shigo masu da Abinci da abubuwan sha wasu suka fara yin salla wasu kuma suka fara cin Abincin,
"Kai! Ashe dai bamu ga komai ba a kud'in su Mijin Zarah, wannan d'aula haka! Kuma fa kina iya ganin ba iya shine gidan su ba anan Abuja d'in" Aunty Mareeya ce dake cin Abinci tayi zaman cin tuwo asaman carpet tayi Maganar, jinjina kai Feenah tayi tace suna fa da kud'i bana wasa ba, Aunty Saude ce tace "aikuwa bashi kad'ai bane gidan su anan, Senator fa yana da kud'i sosae mutumin da keda gidajen mai da kamfanoni daban daban ba a iya Nigeria kad'ai ba ga gidajen haya ko anan Abujar yana da manyan estate guda biyu da ake haya harda babbar plaza ko a Katsina ma yana da gidajen haya da filaye, Unguwar da Hajiya take fa kusan duk filayen shi ne aka saida ma mutane" jinjina kai Aunty Mareeya ta hau yi cike da Al'ajabi tace "tabb kice dai ba K'aramin mai kud'i bane, wllh wasu masu kud'in sai inta mamakin yadda suke tara dukiya" dariya Saude tayi tace "shi kinga gaskiya harda wanda ya gada a wurin mahaifinshi duk da Soja ne yana da tarin dukiya don ko kamfanonin Motocin Senator yawanci asali na mahaifin shi ne, kuma kinsan ita dukiya in dai zaka tsare hakkin Allah ka rink'a kyauta da sadaqa to lillinkuwa take" cike da gamsuwa gaba d'aya suka ce tabbas haka ne kowa zai shaide su da hakan, haka suka cigaba da yin hirar su.
Fatuu ma cikin su Fauzy ta zauna wani irin dad'i take ji sai murmushi take suna ta tsokanarta, bayan sun gama cin Abincin ne Fauzy ta bud'e jakar kayanta ta fiddo d'inkin da ta amso mata a wurin Kb, bud'e kayan Fatuu tay tana dubawa doguwar riga ce akayi gaba d'aya mix and match d'in da lace d'in duk sun yi kyau sosae sai kuma na k'annanta su Aysha suma duk dogayen riguna akai masu, Fatuu na murmushi ta mik'a ma Haulat kayan tace ankon ta ne, waro ido Haulat tayi haka ma Fauzy don ita bata yi tunanin sune ankon ba, kasa cewa komai Haulat tayi da mamaki Fauzy tace "wai dama sune ankon?" Kai Fatuu ta d'aga mata ta k'ara cewa "amman dai da gani zasu yi kud'i sosae" bayanin kud'in su tay mata gaba d'aya suka k'ara zaro ido da yanayin damuwa Haulat tace to maimakon tayi mata Mara kud'in sosae sai ta takura kanta tayi mata mai kud'i haka Fatuu na dariya tace ai ba takura kai bane tana da su ne kuma duk ita akayi sai full embroidery d'in, sosae Haulat ta hau yi mata godiya har kamar zata yi kuka Fatun ta kai hannu ta rungumo ta tana fad'in ai tafi k'arfin wannan a wurin ta, Zainab Muhammadu ce tace don dai lokaci ya k'ure itama da tayi ko normal Chiganvy gold d'in ce Fatuu tace bata san zata zo ba sai daga baya da itama anyi mata gashi yanzu lokaci ya k'ure ace a kawo har akai dinki masu yin d'inkunan ma aiki ya masu yawa don na su Fauzy ma ba'a kaiga gamawa ba da kuma nata zasu yi mata data bata tana murmushi tace ba komai tasa wasu kawai.
A ranar bayan Magrib yan Adamawa suka iso, da Baffan Fatuu da Ard'o daya sha babbar riga da rawani shi ga mai Mulki yayi kaman wani d'an tsuntsu, harda Yaya da Baffan su Altine da innarsu Altinen sai d'ayar matar Ardo sai Yadikko dasu Aysha da Kamalu harda uban dawon furar su da Nono bokiti bokiti, k'auyanci kam ba sai an fad'a ba nan suka shiga zuba shi duk sun saki baki galala suna kallon Aljannar duniya in ka cire Yadikko da Baffan Fatuu ba wanda bai nuna k'auyanci ba a cikin su harda mai Mulki ya kasa sauke kan shi k'asa sai kace mai ciwon hangum, harda ce ma sauran dama yanata jin labarin cewa Abuja kaman Aljanna take shi dae babban su Fatuu murmushi kawai yake farinciki fal ran shi, su Yaya dai an kasa cewa komai sai faman jinjina kai take kaman k'adangaruwa baki a kwa6e, suma a mutunce aka tarbesu harda Hajiya ta fito suka gaisa tayi masu ya hanya sai faman kalle kalle suke su Aysha ma kaman tsoron gidan suke duk sun shishshige ma Yadikko, daga baya suma bayan akai masu jagora Mazan aka kai su d'ayan part d'in su kuma su Yadikko bangaren da su Aunty Mareeya suke, bayan sun zazzauna a cikin parlon su Feenah suka zo aka gaggaisa daga baya suka nuna masu bedrooms da zasu shiga, su dai ai sai yadda akai dasu ba baki sai idanu kawai suke wuwwurgawa, bayan sun shiga d'akin masu son shiga toilet Yadikko ce ta nunnuna masu yadda zasu amfani da komae gaba d'aya ma tsoron shi suke, Yadikko tunda tazo take ta son ganin Fatuu, kasa jurewa tayi ta fito a cikin parlor suka had'e da Saude ta nufeta tana murmushi ganin haka yasa ta tsaya, gaisawa suka k'ara yi tace mata don Allah ina zata ga Amaryar ne Saude tace basu had'u bane tace mata eh, ce mata tay ta koma d'aki bari ta dubo mata ita tayi godiya, bayan komawarsu aka kawo masu Abinci nan fa suka shiga ci hannu baka hannu kwarya a ran Yadikko ta shiga gode ma Allah daya sa su kad'ai ne, bada jimawa ba Saude ta dawo saida ta kwankwasa kopar sannan ta tura Yadikko na ganinta ta taso, ce mata tayi Fatuun bata nan wai sunje wurin amsar d'inki tace to tay mata godiya. Bayan Senator ya dawo har inda aka sauke su Ard'o yazo tare da Haisam da wasu yan uwan shi maza guda biyu da suka zo, a parlor suka zauna su Ard'on suka fito Kamalu dai Amadu yazo ya tafi dashi inda suke, ganin suna niyyar duk'awa kasa yasa yace masu don Allah kar suyi haka ga kujeru suma su zauna ai duk d'aya ake, bayan sun zauna aka shiga gaisawa suka yi masu an zo lafiya, Baffa ne ya nuna ma Ard'o Haisam yace shine mijin inna wuron ya hau jinjina kai da baban Altine yana fad'in ba shakka, godiya Senator yayi masu suka hau fad'in ba komai wllh ai sune yakamata suyi godiya nan suka hau yin godiya Ardo cikin hausar shi da bata fita sosae yace ai akwae shanu ma da suka taho dashi yana a kan hanya da daddaren nan zai iso, sai kace shi ya bada shanun ba Baffan Fatuu ba, baban Altine ne ya k'ara fad'i masu abunda yace su duka suka yi godiya suna fad'in Allah ya bar zumunci daga baya suka tafi.
Fatuu na dawowa taji su yadikko sun iso tana sanye da riga da skirt na lace da gudu ta nufo bayan, tana tura kopar d'akin da suke suka had'a ido da yadikko ta nufeta tana zuwa ta fad'a mata tana dariyar farinciki sauran yan d'akin ma murmushi suke harda Yaya da alama abun yafi k'arfin ta don dole ta aje makaman yak'in nata, d'agowa tay ta juya tana gaishe da sauran sai washe baki suke suna amsawa ganin ta suke kamar Madara, zama tay a kusa da yadikko ta kama hannun Aysha tana tambayar ta ya Makaranta da d'an murmushi ta amsa mata, hira suka shiga yi gaba d'aya kowa Fatun burge shi take yadda ta koma kalar yan gayu, ganin kaman d'akin bazai ishe su ba yasa tace bari ta duba d'ayan d'akin in ba mutane sai wasu su je can, mik'ewa tay taje ta duba ta dawo tace masu ba mutane a d'akin wasu suje can suka ce to, hira suka k'ara yi da yadikko cike da Farinciki take fad'in taji mata dad'i wllh har bazata iya misalta mata ba tayi Addu'ar Allah ubangiji yasa gidan zaman ta ne na har abada ya kauda idon mak'iya, daga baya ta hau yaba irin kirkin dangin su Haisam tace samun irin su a masu kud'i yana da matuk'ar wahala, ta shiga yi masu Addu'oi Fatun na amsawa nan ta fad'i masu anyi masu anko ita nata sai zuwa gobe su Aysha kuma tace su zo suje ta d'aukko masu nasu suka mik'e cike da Farinciki suka tafi, suna fitowa cikin parlor tayi kacibus da Nameer da ya shigo, a gefen shi ta tsaya tana mashi wani kallo mai kaman harara ya sa dariya yana fad'in "kinga Yayata komai ya wuce tsakanin mu tunda naga wadda zata fanshe ki itama nazo nema don Allah ki turo man ita" cikin rashin fahimta Fatun tace wa kenan, kwatancen Mino yayi mata nan take ta gane ita ce, ta6e baki tay tace mashi to itama da sa rana akanta sai yayi hak'uri da sauri yace "No! Kar muyi haka dake pls am serious tayi man ba kamar kuma da ya kasance kuna kama tunda na rasa ki sai in maye gurbin ta dake" dariya Fatuu tay tace "wai Nameer a yaushe ka ta6a cewa kana sona ne da zakai ta man surutai haka" yar harararta yayi yace "kina nufin duk abubuwan da nike maki baki gane ba kawae fa ni don nasan ba yadda za'ai inyi aure a lokacin yasa na bari sai na gama karatu tunda kema naji likita kike son zama ashe ashe likiciyar gida ce zaki zama" dariya tay ta d'an girgiza kai tana fad'in Allah ya shirye shi, ganin zata wuce yasa da sauri yace pls ta turo mashi ita ta d'aga mashi kai, lokacin data shiga d'akin su Fauzyn suna ta faman gwada d'inkunan su da aka fara amsowa sai faman murna suke, kallon Mino tayi tace mata taje parlor ana neman ta da alamun mamaki tace ita ta d'aga mata kai, saukkowa tayi daga saman gado jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa A-line ta yafa d'an madaidaicin gyale a saman kanta, tana shigowa cikin parlorn suka had'a ido dashi ya sakar mata k'ayataccen murmushin shi tana ganin haka ta gane shine ke nemanta kenan, nufar shi tay ta tsaya daga gaban shi tana d'an murmushi ta gaishe dashi, amsa mata yayi kafin yace in ba damuwa yana son zasu yi magana ne ta d'aga mashi kai don Nameer ba irin samarin da za'a musa mawa bane, da hannu yay mata alamun suje suka jera, suna fita ya nufi Sport field d'in gidan da ita.
A ranar saida su Fatuu suka kai tsakar dare suna hira sai daga baya ta koma d'akin Jidderh lokacin sun samu k'aruwar wata cikin yan uwan su na Daura da Suka zo k'awar Jidderh d'in ce, bayan ta shiga Jidderh d'in tace su kwanta ita bari tayi shimfid'a k'asa da sauri Fatuu tace a'a ai gadon zai ishe su. Washe gari bayan an tashi duk suka yi wanka aka fara yin Breakfast wanda lafiyayyun Abinci aka yi, daga baya kuma aka sa ma'aikatan dake hidiman Abinci suka dama furar da su Yadikko suka kawo aka rarraba ma mutane. Misalin k'arfe 12 na rana Aunty tazo d'akin Hajiya tayi ma gwaggo magana cewa za'a kawo lefen Fatuu cike da Farinciki tace to Hajiya tace mata taje ta sanar ma sauran iyayen nata tace to ta mik'e, d'akin su Yadikko taje bayan an gaggaisa ta sanar masu tace sai su fito parlor suka ce to, bayan ta fito d'akin su Aunty Mareeya taje ta sanar masu suma suka fito cikin Falon haka ma su Fauzy, bada jimawa ba aka fara shigowa da Akwatunan lefen aka shiga jera su a tsakiyar parlon har aka gama, akwati Set hud'u ne masu guda hud'u hud'u guda sha shidda kenan su kan su akwatunan abun kallo ne kala daban daban akwae set d'in bak'ak'e sai na maroon sai na brown sai kuma pink, Su Aunty ne da wasu yan uwan su Haisam d'in suka biyo kayan nan suka sa ma'aikatan da suka shigo dasu suka fara bubbud'a wa, ba abunda ka ke ji sai ma sha Allah da aketa fad'i kaya ne na gani na fad'a kusan duk ma an