Showing 315001 words to 318000 words out of 512766 words
Chapter 106 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1549
d'in wayar Hajiya ya fara k'ara da sauri har tana yin tuntube da carpet taje ta haye gadon ta cure guri guda tana zare ido, har alarm d'in ya yanke ya sake fara wata k'arar shiru bata ji Hajiya ta tashi ba, a saninta tunkafin lokacin salla Hajiya ke tashi tayi raka'atanil fajr a wurin zata zauna har lokacin salla yayi, a ranta ta raya to miyasa yau bata tashi ba, bata kawo komai a ranta ba ta saukko ta nufi wurin kayanta, doguwar riga ta saka ta maida Hijab d'in data dawo da ita ta kabbara salla, har ta gama Hajiya bata ko motsa ba, tana zaune akan prayer mat ta kai idonta kan Hajiyar a cikin ranta ta fara raya to wai lafiya bata tashi ba, zuciyarta ce ta bata taje ta tashe ta, tun Fatuu na kiran sunanta har ta kai ta fara d'an bubbuga hannunta, tsoro ne ya kama Fatuu ganin yadda take ta tada Hajiyar amman ko motsi bata yi ba, tun tana bubbuga ta har takai ta fara jijjigata tana fad'in Hajiya ki tashi don Allah, gaba d'aya Fatuu ta kid'ime tuni ta fara kuka Fuskar ta share share da hawaye zuciyarta ta shiga raya mata kodai maganin nan data bata ya kashe ta, da sauri ta kai hannu ta ta6a saitin Zuciyar ta sam ta kasa gane komai, kai kunnanta tai saitin fuskar ta taji gaba d'aya bata numfashi, d'agowa tay a gigice ta d'aura hannuwa a saman kai tana fad'in ta bani ta lalace badai ta kashe Hajiya ba, Haisam ne ya fad'o mata a rai ta juya tana laluben wayarta don ta kira shi sai dai bata gan ta ba can ta tuna ta baro ta a part d'in shi, a sukwane ta sauka daga saman gadon ta nufi hanyar fita da gudu.............
88
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
..........A daidai bakin k'opa tana k'ok'arin fita cikin parlor sukai karo da Mutum, a razane ta kai idon ta fuskar shi nan take ta gane Haisam ne don gari ya fara wayewa, dawowar shi kenan daga Masallaci ya zo don yaji yadda suka k'are, ganinta a rud'e fuska sharkaf da hawaye yasa shi saurin kama ta yana tambayar lafiya da hannu ta rink'a nuna mashi saitin Hajiya tana fad'in tak'i tashi, kamata yay suka nufi ciki ta bangaren gefen Hajiyar ya zauna a bakin gadon ita kuma ta zagaya ta haye saman gadon idanu waje take kallon Hajiyar sai kuma ta kalli Haisam dake bubbuga Hajiyar yana kiranta, hankalin shi ne ya fara tashi har Fuskar shi ta bayyana ya kalli Fatuu ya ce mata miya faru da ita ne, wani Wahalallan miyau ta had'iya sai motsa baki take gaba d'aya ta zaro ido duk tayi kalar rashin gaskiya, k'ara tambayar ta yay yace ta fad'i mashi miya faru da ita ne cikin kuka murya na rawa tace "Don Allah Ya Haisam kayi hak'uri, wllh bada nufin haka nayi ba na rantse maka da Allah" mamaki ne ya bayyana akan fuskar shi jin abunda tace wanda yake nuni da wani abu tay ma Hajiyar, ce mata yay ta fad'i mashi abunda ya faru zai fahimceta da sauri ta fara fad'i mashi tiryan tiryan abunda tay mata na maganin baccin data bata guda biyu, d'an waro ido Haisam d'in yay cike da Al'ajabi yake kallon ta ganin yanayin shi yasa ta hau yin rantse rantse, gaba d'aya shima Haisam d'in ya rud'e ya rasa tunanin da zai yi ga Fatun ta gigice sosae wanda a halin da take ciki bai kamata ace ta tashi hankalin ta haka ba,
Hannuwanta ya kamo ya shiga rarrashinta yana fad'in ta kwantar da hankalin ta ya fahimce ta zata tashi in sha Allah, ganin ta d'an sassauto yasa shi tambayarta shi maganin data batan ta tabbatar baida illa, da sauri tace wllh baida illa na bacci ne ko su suna sha in sukai karatu sosae suka kasa bacci, jinjina mata kai yay ya maida idon shi akan hajiya, k'ok'arin tada ta yaci gaba da yi Fatun na taya shi, ganin tak'i tashi yasa shi kallon Fatun yace bai kamata suna 6ata lokaci ba bari yaje ya d'aukko Mota sai ya kaita Asibiti aikuwa a rud'e ta kamo hannun shi da duka hannuwanta tana girgiza mashi kai tace "Don Allah Yaya Haisam kada aje Asibitin wllh in aka je za'a gane an bata wani abu ne gashi Nameer ne ya siyo man kuma ba lalle a fahimce ni ba" shiru yay ya rasa miye abun yi don gaskiya ta fad'a saidae kuma yasan kaita Asibitin shi ya kamata, tambayarta yay an rage sauran Furan ne da sauri ta girgiza kai "a'a, duka muka shanye robobin na a cikin dust bin a parlor",
"Ok, ki kwantar da hankalin ki Hospital d'in yakamata akai ta zan san yadda za'ai baza'a gane kin bata wani abu ba muyi Addu'a Allah yasa komai yazo da Sauk'i" da sauri tace Amin, har zai sauka daga saman gadon sai kuma ya maido idon shi kanta yace ta sa mata ruwa ne da sauri ta girgiza mashi kai tace a'a ko taje ta kawo, da hannu yay mata alamar ta tsaya shi ya mik'e ya nufi hanyar parlor, bada jimawa ba ya dawo hannun shi ruk'e da bottle water daya d'aukko daga cikin Fridge ruwan mai d'an madaidaicin sanyi ne, bayan ya koma ya zauna bud'e murfin robar yay ya tarba hannun shi ya cika shi da ruwan, sai da yay bismilla sannan ya watsa mata shi a fuska nan take tay wata ajiyar zuciya, k'ara zaro ido Fatuu tay suka kalli juna da shi atare suka shiga kiran sunanta saidae bata k'ara yin wani abu ba daga haka, da sauri Fatuu tace mashi ya k'ara watsa mata ruwan, yana k'ara zuba mata ta k'ara yin ajiyar zuciya suka cigaba da kiran sunanta, Motsi ta fara yi Fatuu ta fara d'an murmushi, Haisam ne ya rankwafa yasa hannu yana d'an bubbuga gefen fuskar ta yana fad'in "Sweetheart open your Eyes" a hankali ta fara bud'e idanun tana yi tana rufe su yana cigaba da ce mata ta bud'e idanunta, lokacin data bud'e su gaba d'aya sun yi ja sosae tabi Haisam da kallo tamkar mai son gane wanene shi kuma ya d'an rankwafa da kan shi sai murmushi yake mata,
"Kai, wane gardi ne wannan a kai na, lafiyaaa???" da wani irin sauti tay Maganar nan take Fatuu ta bud'a baki Haisam ya d'aga ido ya kalleta gaba d'ayan su sun fahimci maganin bugar da ita yay da alama yayi mata k'arfi ne sosae, k'ara ce mashi tay waye shi ya d'age mata gira yace mata masoyinta ne ta wani k'ank'ance mashi ido fuska a tsuke, kallon Fatuu tay ta k'ura mata ido duk Fatun tasha jinin jikinta sai motsa baki take, hannu Haisam ya kai ya tada ita zaune ta jingina da kan gado yace mata ta kalle shi sosae ta kuwa zuba mashi ido, bayan wani lokaci yace mata to ta gane shi kawae sai ji yay tayi d'an guntun tsoki tace to shi d'in ne bata sani ba, murmushi yay tace wai mi ya faru ne shi kuma miya kawo shi nan, yana murmushi yace "da yake kin samu kan ki ko",
kai idon ta kan Fatuu dake ta zare ido tayi tace ita kuma wannan mi akai mata tayi kuka Haisam d'in na k'ok'arin bud'e baki yay magana a rud'e Fatuu ta hau girgiza mashi kai alamar kada ya fad'i mata, yar dariya yay yace ma Hajiyar hankalinta ne ya tashi tana ta tada ita gari ya waye amman tak'i tashi, hannu ta kai ta dafe goshinta Haisam d'in yace mata lafiya tace ciwo yake mata, sannu yayi mata yace ta tashi tayi salla sai tasha magani, tambayar shi tay anyi salla ne yace eh tun d'azun, da alamun mamaki tace to wai miya faru da ita ne haka ya d'an ta6e mata baki, tunani ta shiga yi can tace mashi tana zargin furar data sha jiya ce ta sata Nauyin bacci haka don tun a parlor jiya ta fara yin bacci da k'yar ta dawo d'aki kuma daga nan bata k'ara sanin inda kanta yake ba gashi yanzu suma sun ce suna ta tada ita bata tashi ba tabbas Furar nan ce, gaba d'aya Fatuu ta rud'e sai zare ido take Haisam ya kalleta suka had'a ido yanayin fuskar shi kamar zai yi dariya, ganin tana ta Maganar furar yasa shi ce mata dama ya ta6a sata haka ne tace a'a yace to ba shi bane, da sauri tace ai dama fura na bugarwa wani lokacin fa yace to tunda tasan hakan ba Shikenan ba miye na dogon magana ta tashi taje tayi salla kawai Allah ya kyauta gaba,
ganin tana ta k'ok'arin saukkowa yasa shi mik'ewa ya taimaka mata ta tashi tsaye tay mashi alamar ya bata sanda sai faman hamma take, ce mata yayi ko baccin bai ishe ta bane a k'ara nemo wani Furan ya saci kallon Fatuu suka had'a ido ta tura mashi baki yay yar dariya, duk da sandar saida ya kaita har bakin toilet don sai fad'i take jikinta ba kwari yace mata sai ta fara yin wanka taji k'arfi ta d'aga mashi kai, tura kopar toilet d'in tay yana ta fad'in tabi a hankali, saida yaga ta shige sannan ya juyo ya dawo wurin gadon ta side d'in da Fatun take idonta akan shi, zama yay a bakin gadon ya mik'a mata hannu ta matso, jawota yay jikinshi kawai sai ta fashe da kuka ya shiga rarrashinta yana fad'in ba Shikenan ba tunda ta farka, bayan tayi shiru ya tambayi ba abunda ke mata ciwo ta d'aga mashi kai alamar eh, shiru suka d'an yi kafin can k'asa k'asa da murya ya rad'a mata ta rage sauran maganin anjima da daddare a k'ara bata suje part d'in shi a zabure ta d'ago ta kalleshi kawai sai gani tay ya saka dariya aikuwa ta kai hannu ta bugi chest d'in shi ta fara k'ok'arin raba jikinsu ya matseta yana cigaba da yin dariyar yace shima ai wasa ne yayi mata ko irin wanda tay mashi tay d'an murmushi tare da lumshe ido ta maida kanta saman chest d'in nashi sosae yanzu hankalin ta ya kwanta amman ba k'aramar razana tayi ba, kai bakin shi yay saitin kunnanta cikin rad'a yace mata kar ta k'ara irin wannan kuskuren da sauri ta d'aga mashi kai kafin a hankali tace bazata k'ara ba ya jinjina mata kai.
Da yake Weekend ne ana abubuwan nishad'i a gidan tuni Fatuu ta washe saidae taci alwashin ita da ta k'ara ba wani maganin bacci har a bada in dai ba patient ba a Asibiti shi ma sai in likita ne yace a bashi duk da tasan laifinta ne ita ta cika ma Hajiyar abun kuma ya had'u da shekaru, da daddare atare gaba d'aya wad'anda ke a gidan suka ci Abinci kamar dai da safe da kuma da rana, bayan sun gama cin Abincin daren sun koma part d'in su taje tayi wanka, bayan ta gama shiryawa da kayan bacci riga da wando tasa hula ta nufi Parlor wurin Hajiya da tuni ta wartsake tana zaune idanunta sanye da glass tana kallo, sannu tayi mata Hajiyar ta d'aga mata kai ta zauna itama, bata dad'e da zama ba Nameer ya shigo hannun shi ruk'e da ledojin Fura bayan sun gaisa ya d'aura akan c-table yace gashi nan Dad yace ya kawo daga haka yay masu saida safe, Fatuu ce tace mata ta d'aukko cup ta zuba mata Hajiyar ta d'an yamutsa fuska tace anya yau zata sha furar nan don gaskiya jiya itace ta bugar da ita wllh, duk sai Fatun bata ji dad'i ba ganin zata haramta mata abunda take so, wani tunani tay da sauri tace ma Hajiyar ita tana ganin ba daga furar bane k'ilan daga naman da suka ci ne ya had'u da furar shine suka bata reaction, Hajiyar tace anya sai kace dai kifi Fatun tace ai shima Naman yana iya sawa an koya masu a Makaranta Hajiyar tay mata wani kallo mai kaman harara tace to kuma shine ta bari suka ci, a dabarbarce tace ai bai cika sa wani abu ba kamar kifin ita tama dai fi tunanin k'ilan naman da aka sarrafa d'in ne keda matsala, ta6e baki Hajiya tay tace koma dai minene mai faruwa ai ta faru, da yake ranta na son furar tace mata ta zuba mata yar kad'an tasha in bata ji komai ba sai ta k'ara cike da jin dad'i Fatun tace to ta mik'e, bayan ta zuba mata ta bata itama ta zuba ta fara sha, suna cikin sha taji Hajiyar tace wai Haisam d'in ya had'a kayan tafiyar ko kuwa, d'an murmushi Fatuu tay ta sadda kai tace mata bata sani ba amman tasan k'ilan ya had'a zuwa yanzu tunda gobe zai tafi, d'an ta6e baki Hajiyar tayi sai kuma tace mata ta tashi taje ta gani in bai had'a ba ta had'a mashi in kuma ya had'a mata aiki ya tafi ya barta da wahala ita ta sani, kunya ce ta kama Fatun ta sadda kanta k'asa tana haka taji tace ta tashi taje, mik'ewa tay zata tafi Hajiyar tace to wa ta bar ma sauran furar ta d'auka taje da ita tana had'a kayan tana sha, d'auka tay sumi sumi ta wuce, a yadda take ta nufi hanyar fita daga parlon ta fuce, ta baya ta fita tana tafiya a ranta take raya gajen hak'uri gashi nan da kanta tace taje, wata zuciyar ta raya mata rabon kowa zai jigata ne tay yar dariya.
Washe gari tunda Fatuu ta tashi cikin damuwa take, a part d'in Haisam tay wanka don nan ta kwana bayan ta koma part d'in Hajiya ta canza kaya, bayan sun gama yin Breakfast part d'in Haisam d'in ta koma, gaba d'aya yini yay aikin rarrashinta don sai kuka take mashi, lokacin daya dawo sallar la'asar tana zaune a bakin gadon shi itama bata dad'e da gama yin sallar ba, zama yay a bakin gadon suna kallon juna slowly ya furta mata zasu wuce don 4:30 jirginsu zai tashi zuwa Lagos yanzu yakamata su tafi don hud'u ta kusa, kai kawae ta d'aga mashi yace bazata raka shi Airport ba, a marairaice tace mashi bata son taje tay ta kuka tunda yak'i daina zuwa, kai ya d'aga mata ya kai hannu ya rungumo ta ya furta zai yi missing d'in ta sosae cikin muryar kuka tace itama, d'ago da ita yay suna kallon juna yay mata d'an murmushi ya kai bakin shi yay pecking duka kumatunta ya furta "I love you My Baby" itama tace mashi haka ce mata yay ta tashi suje ya rakata cikin gida tace mashi a'a zata zauna anan sai anjima zata koma, shiru ya d'an yi kafin yace tay mashi alkawarin ta daina kukan cikin karyayyar murya tace ai shi yake zuwa amman zata bari ya d'aga mata kai, mik'ewa yay ya nufi inda trolley d'in shi yake ajiye dama saida ya gama shiryawa sannan ya tafi Masallaci, juyowa yay ya kalleta ya furta ta kula da kanta sosae ta d'aga mashi kai tana kikkafta ido, har ya kai k'opa yaji ta kira sunan shi ya dakata ya juyo, mik'ewa tay ta nufo shi a gaban shi ta tsaya idanun ta cike da k'walla tace bari ta raka shi, murmushi yay yace indai bata so ta barshi tace a'a zata je, dama ranar k'ananun kaya ce hakan yasa ta d'aura after dress da zata zo wurin shi gyalen rigar na saman kanta, ce mashi tay ya kawo akwatin ta ruk'e ya girgiza mata kai ya kawo d'ayan hannun shi ya kama nata suka tafi,
Gaba d'aya yan gidan sun fito bakin Entry Hall don yi masu rakiya lokacin da suka k'araso, harda Dad da Hajiya dasu Jidderh da Aunty ba wanda aka bari, a Jeep din da za'a d'auki Dad Aunty da Mom suka shiga sai Nameer ya shiga gaba, sai wata Jeep din Haisam ya shiga gaba Hajiya da Fatuu da Jidderh suka shiga baya sai k'aramar Mota Yasmeen da Affan dasu twins suka shiga a k'arshe kuma Hilux d'in escort ce a jere Motocin suka tafi. Bayan anje Airport d'in duk yadda Fatuu taso kar tayi kuka da zasu rabu abun yaci tura saida tayi akaita rarrashinta harda Dad a cikin masu rarrashin nata shi kan shi Haisam d'in wani iri yake jin shi, tana ji tana gani Hubby d'inta ya tafi.
Bayan sun baro Airport d'in ba gida suka koma ba bazama sukai Outing, sosae suka zaga gari harda wani babban park suka je sukai ta hawa liluna iri iri ita dai Fatuu an hana ta hawa sai aikin kallo take tana nishad'i don harda Dad dasu Mom aka hau wasu lilon Hajiya dae itama aikin kallon tayi daga baya kuma suka yi hotuna, bayan sun baro park d'in wani babban shopping mall suka je nan aka ce kowa ya za6i abunda yake so, Su Mom duk kayan shafa da turarurruka suka d'auka haka Jidderh ma da Yasmeen suma cosmetics d'in suka d'auka suka had'a da Undies, Su Twins da Fatuu wurin kayan zak'i suka nufa saida suka cika basket dinsu da su Sweets, biscuits, chocolate da sauran su Fatuu sai ce masu take su barshi haka amman suka k'i wai ai harda Baby d'in su shima za'a d'aukar mawa Fatuu sai dariya take, Hajiya ita k'in d'aukar komai tay tace bata buk'atar komai Senator ne ya za6ar mata turarurruka Mom kuma ta d'aukar mata dogayen riguna da tasan tana sa irinsu harda Fatuu ta za6ar ma wasu dogayen riguna tace zata ji dad'in su nan gaba, Affan ma underwear ya d'auka sai turare da kayan zak'i, kowa dai ya d'auki abunda yake so, suna cikin shopping d'in Haisam ya kira Fatuu ya sanar mata sun isa Lagos ta hau yi mashi shagwabar tana missing nashi, anan Mall d'in suka yi sallar Magrib bayan sun gama suka shiga Eatery d'in wurin, kowa abunda yake so shi aka kawo mashi ya ci, daga nan bayan