Showing 450001 words to 453000 words out of 512766 words
Chapter 151 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1541
gaishe da ita itama fuska a sake ta amsa ta tambayi Salma tace mata tayi bacci, shiru ta ɗan biyo baya can Gwaggo ta sauke yar ajiyar zuciya ta kalleta tace mata dama taji abunda ke faruwa tsakaninta da Amadu sai dai yadda tayi tunani ba haka bane ba wanda ya saka shi ya nemeta tsakanin ita da Fatuu basu ma san da yayi mata Maganar ba in ba yanzu daya faɗi mata ba kuma ita a ganinta koda sashi akai ya nemi Aurenta ai don an yaba da kyawawan halayenta ne,
"Ko akwai wanda kike so ne?" innar su ta jefa mata tambaya ta girgiza mata kai ba tare data ɗago ba Gwaggo tace to in dai har taji tana son Amadun ta bashi dama tunda ba haramun bane wai don yana saurayi sau nawa akai ga misali nan ma akan Manzon Rahama, shiru suka ɗanyi kafin Gwaggo tace mata ta tashi taje ita dama tazo ne don ta Warware mata abunda take tunani in Allah yasa sun daidaita to suna Farinciki, miƙewa tay ƙasa ƙasa da murya tace ma Gwaggon saida safe ta amsa mata, bayan fitar Haulat yar hira sukai da innar tasu kafin Gwaggo tayi mata Sallama suka miƙe tare, har bakin zaure ta rakota tayi mata Godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci sukai ma juna saida safe, lokacin da ta fito Amadu na zaune bisa ɗan dandamalin gaban gidan dake kallon nasu Haulat yana latsa waya, yana ganinta ya miƙe ya nufo ta, a gabanta ya tsaya yace har ta fito tana murmushi tace eh suje ya ɗan sosa ƙeya yace to ya ake ciki tay mashi wani kallo mai kaman harara tace yadda ake waje yay yar dariya ta ƙara ce mashi suje in sunje gida yaji yadda akai, ɗan ƙara sosa ƙeya yay yace ko taje ya taho daga baya tayi murmushi tare da ɗan girgiza kai tace dama ba rakota yay ba kenan abun shi ya kawo shi, daga haka ta juya yana dariya yace mata a'a yanzu zai taho ƙilan ma ya sameta a hanya, bayan tafiyarta wayar shi ya ɗago ya shiga kiran Haulat bayan tayi ringing ta ɗaga tayi mashi sallama ya amsa ta gaishe dashi nan ma ya amsa daga haka tayi shiru yace mata in ba damuwa yana son ganinta a ƙopar gida tay ɗan jimm jin haka yasa yace mata in bazata samu fitowa ba ba damuwa bari ya tafi, a hankali tace mashi a'a gata nan zuwa, shiru tayi tana tunanin yadda zata fita hakanan sai taji wata irin kunyar shi ta kamata can dai ta miƙe ta nufi wurin kayanta ta curo doguwar Hijab ta daura saman rigar jikinta, tsaye tayi bakin kopar ɗakin tana jin nauyin zuwa ta tambayi innarsu can dai ta nufi ɗakin saida ta ƙara yin jimm kafin ta kai hannu ta ɗaga labulan ta shiga da yar Sallama, innar tasu har ta kwanta ta amsa mata tare da ɗago kanta tana kallonta Haulat ɗin ta sadda kanta ƙasa da ƙyar tace mata dama wai Kawu Amadu ne ke son ganinta a waje, murmushi innar tayi tace mata to taje, har ta juya taji ta kirata ta juyo ta kalleta,
"So nike in tambaye ki kina son Amadun ne ko kuwa?" maida idonta tayi ƙasa sannan ta ɗan jinjina mata kai alamar eh,
"To idan kinje yay maki Maganar Aure ki bashi dama a turo kawai" ɗagowa tay ta kalli innar cikin sanyin murya tace ita gani take kamar yayi wuri da yawa kada aita yin surutu, innar na murmushi tace to miye abun surutu abu kusan shekara da rasuwar Mijin nata wasu ma suna gama takaba da sun samu miji suke yin auren su tunda rashin yin auren ai ba abunda zai canza ko to duk miye na jinkiri tunda Allah ya kawo mai sonta kuma ma Mutum kamar Amadu ta amince mashi kawai ta amsa da to ta juya, yana tsaye gefen ƙopar gidan ta fito ta tsaya a jikin kopar ya juyo yana kallonta da murmushi da yake akwae haske itama ɗan murmushin take mashi ta gaishe shi ya amsa tare da tambayar ina ɗiyar shi tace mashi tayi bacci,
"Allah yasa dai kema ba baccin kike ba na tado ki" a hankali ta girgiza mashi kai alamar a'a suka ɗanyi shiru suna kallon juna can yace "na cika naci ko, kiyi haƙuri kinsan abunda rai ke so ba kamar kuma ga baƙon abun gaba ɗaya na kasa samun natsuwa da aka ƙi amince man" Murmushi tayi kawai bata ce komai ba ya sake cewa "Gwaggota tazo kun yi magana ne?" kai ta daga mashi alamar eh,
"To yanzu kin yarda ba tursasa man akai in aure ki ba ni ke son hakan?" kai ta ƙara ɗaga mashi,
"To yanzu an yanke shawara game da buƙatar tawa ko sai na ƙara jira?" shiru tayi tana ɗan yi murmushi kafin a hankali tace an yanke yace to yana saurarenta Allah yasa yaji Alkhairi ya tsareta da ido yana mata wani kallo gaba ɗaya duk sai taji nauyin shi take ji ganin abun take kamar a Mafarki wai ita da Kawu Amadu ne suke soyayya har ma da zancen aure abunda bata ta6a kawo wa a ranta ba, cikin kwantar da murya yace mata pls a tausaya mashi kada aja mashi aji, kallon shi tayi tana murmushi a hankali ta furta "an amince maka" ɗan buɗa ido yay yace "You Mean kin amince zaki aure ni?" kai ta ɗaga mashi ya wani lumshe ido tare da kai hannu ya dafe saitin zuciyarshi ya furta "Alhamdulillah, har bansan yadda zan bayyana daɗin dana ji ba yau dai ɗan Gwaggo zai yi bacci hada munshari da ana niyyar a zautar mata da yaro" Dariya Haulat tayi har haƙoranta suka bayyana tace "Kai Kawu Amadu" buɗe idon shi yay sosae yace "Allah kuwa kullum da tunanin amsar da zaki ban nike kwana kinsan ni ba sanin kan abun nayi ba gaba ɗaya na zurma har na fara tunanin ko ban shiga fagen Soyayyar ba a sa'a da naga kamar ba'a so na",
"Ai kai da wuya ace ba'a son ka kawai don baka cewa kana son ne" ɗage gira yay yace Why ta faɗi Hakan,
"Saboda kana da duk wani abu da mace zata so a wurin Namiji" da ƙyar ta ƙarasa Maganar yana murmushi yace a hakan shi da baida kuɗi abunda yanzu kusan mata saboda su suke son Mutum,
"Ai Kawu Amadu banda kuɗi Kyau ma nasa a so mutum kuma kana dashi" ɗan juya ido yay yace mata kenan ita don kyau take son shi tana dariya tace "a'a, don ka cancanci in so ka Kawu Amadu saboda kana da halin kirki" wani kalan murmushin daɗi yay yace "To nagode Allah ya tabbatar mana da Alkhairi ya ƙara mana ƙaunar junanmu, amman pls ina neman wata alfarma wannan Kawu Amadun da ake ce man a aje shi a gefe a rinƙa kirana da sunan da zansan nima na fara soyayya da aketa man gori da surutu ashe ma ni tuni Allah ya za6a man mata lokaci ne kawae baiba yanzu gashi lokacin yayi ta bayyana" gaba ɗayansu kallon juna suke cikin ido suna sakar ma juna ƙayataccen murmushi cikin kwantar da murya ta furta "Ok My Dear an canza maka in ma wannan bai yi ba sai a canza wani" wani farfar yay da ido yace "yayi sosae Sweetie nah" da sauri ta kai duka hannuwanta ta rufe fuska alamar kunya Amadun ya sa dariya, suna haka Mahaifinta ya dawo yabi su da kallo Amadu ya sunkuyar da kai ya gaishe dashi bayan ya amsa yace "kamar Amadu ko" kai ya ɗaga mashi yace eh shine Mahaifin nata yay ɗan murmushi tare da furta Ma sha Allah, daga haka ya juya zai shiga da sauri Haulat taja gefe tana mashi sannu da zuwa ya amsa kafin ya shige, kallonta Amadu yay yace Allah yasa data koma gidan Baban yace mata ace ya turo tana murmushi tace da wuri haka yace eh mana mi zasu tsaya yi gara suyi auren alabashshi sunyi soyayyar a gidansu tayi dariya, Mahaifinta na shiga ɗakin innarsu ya wuce tana kwancen har ta fara yin bacci saidai bai yi nisa ba, yana yin sallama ta buɗe ido ganin shine ta fara ƙoƙarin tashi zaune tana mashi sannu da zuwa ya nufi wurin gadon yana amsa mata, a bakin gadon ya zauna ta fara ƙoƙarin saukkowa tana faɗin bari a kawo Abinci ya dakatar da ita ta hanyar faɗin tukunna ta koma ta zauna, tambayarta yay mike tsakanin Haulatu da Yaron can Amadu ne ya gansu tsaye a ƙopar gida, murmushi tayi nan ta kwashe komai game da zuwan gwaggo ta faɗa mashi tun kafin ta ida ya hau jinjina kai tare da yin murmushi bayan ta gama faɗi mashi yace amman dai yayi farincikin jin zancen wllh don Amadu ba dai hankali ba ga ƙoƙarin neman na kai itama tace sosae taji dadin al'amarin don tana son Amadu, Mahaifin nasu yay fatan Allah ya tabbatar masu da Alkhairi ta amsa da Amin, bayan shigar Mahaifin Haulat basu jima ba sosae suka yi sallama harda kuɗi ya bata yace da safe ta siya ma Salma abunda takeso tace mashi don Allah ya barsu yay mata wani kallo yace badai iko zata nuna mashi da ɗiyar tashi ba, da sauri ta bashi haƙuri tana murmushi shima shi yake yi ta amsa tare da yi mashi godiya sukai bankwana cike da nuna ƙauna, kamo hanyar gida yayi sai faman sakin murmushi yake sai kace zautacce yana isowa ciki ya shige ya nufi ɗakin Gwaggo lokacin har ta kwanta ya shiga da sallama ta ɗago tana amsa mashi tare da kunna wayarta haske ya kawo tace mashi ya kunna wutar ɗakin, bayan ya kunna kujera ya nufa ya zauna sai faman murmushi yake Gwaggo ta tashi zaune tana kallonshi tace mashi ya akai ya bata amsa da Haulat ɗin ta amince mashi yanzu sai kawai a saka rana, ɗan buɗa baki Gwaggo tayi ta kai hannu ta ruƙe ha6a tace ko kunyarta bai ji da sauri ya sunkuyar da kai yana yar dariya yace yaga kamar tana son yayi auren ne shiyasa ta ɗan ta6e baki tace shikenan Allah ya tabbatar masu da Alkhairi zata yi ma dangin Baban shi magana kan hakan ya ɗago yace to, har zai miƙe yaji tace to yana da kuɗin yin Auren ko ya kalleta tare da ɗan sosa kai yace bazasu gagara ba tayi yar dariya tace yaje Allah ya taimaka yayi mata saida safe ya juya tabi shi da kallo tana murmushin daɗi don yana ɗaya daga cikin burinta a yanzu taga auren autan nata, yana fitowa wayar shi ta fara yin ringing ya duba ganin Haulat ce yasa shi nufar ɗakin shi da sauri saida yaje bakin kopar shiga ya ɗaga tare da ƙarasa shigewa, ce mashi tay dama ta kira ne taji ya ya koma gida jama'a zo kuga washe bakin daɗi wurin Amadu yace haka ta damu dashi wannan in sukai aure yasan ba ƙaramar kulawa zata bashi ba tana murmushi tace mashi in sha Allah fatan itama zai kula da ita da sauri yace tamkar ƙwai in sha Allah duk sukai dariya, a saman ƙatuwar katifar shi daya canza tuni ya kwanta suka cigaba da shan soyayya, sun ɗan ɗauki lokaci kafin sukai bankwana, bayan ya gama kiran Kamalu yayi ta wayar yace mashi ya kullo shagon ya shigo shi gashi nan har ya kwanta, a ranar kwanan farinciki yan gidan su Amadu da Haulat sukai karma dai su Masoyan.
Washe gari wurin misalin ƙarfe goma na Safe Gwaggo ta kira Fatuu bayan tayi ringing Fatun ta yanke ita ta kira dama haka take duk suka kirata, gaisawa sukai ta tambayi jikinta dasu twins da Babansu da Fanan duk ta amsa mata da suna lafiya,
"Dama na kira in maki Albishir ne duk da bansan ko wani yayi maki ba" da sauri Fatun tace mata a'a basu yi waya da kowa ba a ƙagauce ta tambayeta wane Albishir ne nan Gwaggon ta faɗi mata game da Amadu da Haulat, wata uwar ƙarar farinciki Fatuu ta saka ta hau fadin Alhamdulillah ya Allah Gwaggo nata dariya, bayan ta tsagaita da yin murnar da alamun mamaki ta tambayi Gwaggon ita tasa shi ya nemi auren Haulat ɗin ne tace mata a'a ta faɗi mata yadda sukai dashi,
"Kai amma naji dadi wllh, kinsan Gwaggo tun kwanaki nike raya inama Kawu Amadu ya auri Haulat, sai dai gani nike kamar bazai amince ba tunda ba budurwa bace abun Allah ashe har ya furta mata kuma ni bata yi man maganar ba ma" daga jin yadda take Magana zaka fahimci ba ƙaramin farinciki take ciki ba, Maganar saka rana Fatun tayi mata gwaggon tace yau take niyyar kiran dangin babanshi ta faɗa masu sai suzo nema mashi auren daga nan a saka rana gaba ɗaya, da sauri Fatuu tace "Gwaggo don Allah a saka sai bayan na haihu Ya Haisam yace bazan ƙara zuwa ba har sai na haihu kuma yanzu saura wata biyar tunda yayi wata haɗu" a marairaice tayi Maganar Gwaggon na dariya tace ai itama bata son a saka da wurin don tana son ayi ma gidan gyara sosae don anan take son su zauna tare, cike da murna Fatun tace yauwa hakan yayi ta tambayi kamar wata nawa za'a saka Gwaggon tace ko shidda ko bakwai Fatun tace a bari bakwai ɗin lokacin har wanka ta gama tace hakane to sai a barshi bakwai ɗin daga baya sukai sallama, suna gama wayar parlor ta nufa da sauri don taje ta faɗi ma Haisam da yake Weekend ne yana gida, yana kishingiɗe kan doguwar kujera su twins na kwance a kan ƙafafun shi suna yin kallo ta nufo su cikin Washe baki Haisam ya juya yana kallon ta, ganin farinciki akan fuskarta yasashi yi mata murmushi a kan hannun kujerar da ya jingina ta zauna ta kai hannu cikin sumar shi ta fara ɗan sosai mashi, ɗago fuskarshi yay ya kalleta idanunshi a ɗan lumshe ya tambayi ya akai yaga tana farinciki ta kashe mashi ido tace tana Bedroom ta tuno da shine mijinta shine take farincikin, wani kalan murmushin gefen baki yay yace ai kullum tasan shine mijinta yasan bata mantawa da hakan tana murmushi tace hakane in ma ta manta to kuwa bata cikin hayyacinta, faɗi mashi tayi Gwaggo ce ta kirata ta sanar mata da Kawu Amadu zai auri ƙawarta Haulat" sosae shima ya nuna farincikin shi yace Amadun ya kyauta ya tambayi yaushe za'a sa rana ɗin ta faɗi mashi yadda sukai da Gwaggo na sai nan da wata bakwai saboda za'a gyara gidan tana son su zauna anan ya jinjina kai yace Allah ya kaimu ta amsa kafin ta maida idonta kan su twins daketa kallon su kamar suna fahimtar abunda ake a Tv da fulatanci tace basu ga Mom bane Adam ne ya kalleta yana mata dariya shi kuwa miskili Abie ko kallon nata bai yi ba, saukkowa Adam yay da yake sun fara iya tafiya ya nufota yana zuwa ta ɗaukeshi ya kai hannu yana ta6a ƙirjinta alamar yana son tayi feeding nashi saida ta gyara zama sannan ta fara bashi Abie na ganin haka shima ya saukko daga kan kujerar zai nufota ta ɗan harare shi yaja ya tsaya yana kallonta da idanunshi tubarkallah Haisam nata kallon su yana murmushi, ganin kallon da take mashi yasa ya fara ta6e baki zai yi kuka da turanci Fatun tace mashi tunda bai damu da ita ba itama bata ƙara bashi abunta kawai sai ya kife fuskarshi a jikin Haisam ya fashe da kuka, suna haka Fanan ta fito tana sanye da skinny jeans da yar top ta nufo su da sauri tana faɗin waya ta6a mata Little Abie yanzu suyi faɗa, daukar shi tayi tana tambayar waye ya saka shi kuka da hannu ya nuna mata Fatuu ta juya tana kallonta ta ɗan ɗaure fuska tace miyasa zata saka shi kuka kafin ta bata amsa Adam ya saki breast ɗin ta dago yana gwaranci shi ala dole magana yake duk ya basu dariya, tambayar Haisam tayi abunda ya haɗa su yana murmushi ya faɗi mata ta nufi gefen Fatuu tana faɗin ayi haƙuri dasu haka halin su yake ba shareta sukai ba ta zauna kusa da ita tace ma Abie din yace mata Sorry saida ta maimaita mashi kusan sau ukku sannan ya faɗi Sorry ɗin, bayan ta gama ba Adam ɗin ta amshe shi shima ta fara bashi anan take faɗi mata zancen auren Amadu da Haulat itama Fanan ɗin ta nuna farinciki sosae tayi fatan Alkhairi.
A ranar Gwaggo taje ta sanar ma Hajiya itama tayi farinciki sosae tace Amadu ya kyauta Saude ma ta nuna farinciki, Tk na jin zancen Auren Amadun yace aikuwa bazai riga shi yin aure ba shima zaisa aje a nema mashi aure, da yamma Amadu na shago Haisam ya kira shi a waya cikin girmamawa ya gaishe dashi bayan ya ɗaga Haisam ɗin yace mashi yaji abun farinciki Allah yasa Alkhairi Amadun na murmushi ya amsa tare da yi mashi godiya, tambayarshi Haisam ɗin yay akwae gida na kusa da gidan su yana son sanin wanda ke ciki haya suke ko kuwa nasu ne da alamun rashin fahimta Amadun ya tambayi wanne ciki yace duka na left da right ya bashi amsa da na bangaren dama gidan kansu ne sai na hagu wato gidan su Umar su haya suke Haisam ɗin yace mashi yasan mai gidan yace mashi eh wani Alhaji Isah ne shima anan unguwar yake daga can ƙasa yace mashi yana da lambarshi Amadun yace a'a gaskiya, tambayar shi yay zai iya samo mashi lambar tashi da sauri Amadun yace eh yace Ok ya samo mashi harda ta shi wanda yake hayar gidan Amadun yace ita yana da ita yace to ya fara turo mashi ita kafin ya samo mashi ta mai gidan yace to zai tura mashi yanzu