Showing 180001 words to 183000 words out of 512766 words
Chapter 61 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1563
juye hakan sai kowa ya rungumi Al'amarin a matsayin hakan" wani kallo take bin Hajiya dashi ta yamutsa fuska cikin k'unar rai tace "Hajjaju na fahimci goya mashi baya kike shiyasa ma har ya samu k'warin gwuiwar cigaba da zama da ita, haba! ta ya zaki goyi bayan wannan kaskantaccen Auren, Auren wulakanci, in ma k'ara Auren zai yi ai wannan ba class d'in shi bace wllh, kuma ba kowa za'a wulakanta ba face Fanan taya ma za'a had'a ta kishi da wancan abun" sai huci take tayi mitsi mitsi da idanu, d'an murmushi Hajiya tay idonta akanta tace mata ba mace bace ita Fateemar kuma miye aibunta, d'an jim tay fuska a yamutse tana ma Hajiya kallo irin na baka zaci jin Magana daga bakin mutum ba,
"Hajjaju wato na lura dae kin za6i faranta ma bare fiye da naki ko, kin sani matuk'ar auren nan aka ce ya d'ore ba wanda zai cutu irin Fanan, don Allah duka yaushe aka yi auren nasu da za'a ce har an yi mata kishiya, da mi zata ji ne da damuwar lalurar dake tare da ita ko kuwa da wannan damuwar da ake neman k'ara mata, wai ko don cikin da ta samu ne yasa kike goyon bayan auren, Saboda ance Fanan nada lalura ai ba yana nufin bazata haihu ba, tunda anata kokarin nema mata magani sai a bari zuwa wani lokaci aga in bata haihu ba sannan ai tunanin auro wata, kuma shi in ba don ya nuna irin halin nasu na maza ba da ba yan goyo bane ba har alk'awari yayi mata zai zauna da ita a halin da take ciki koda kuwa bata haihu ba shine tun ba'a je ko ina ba zai watsa mata k'asa a ido ya nemi tarwatsa mata zuciya wato ta mutu ma shi ba damuwar shi bane, to wllh bazan zuba ido ta cutu ba Saboda wata kaskantatta can" tana kaiwa k'arshen Maganar ta kai hannu ta warto wayar ta ta mik'e, har ta nufi hanyar k'opa sai kuma ta dakata ta juyo ta kalli Hajiya data bita da ido ta d'an sassauta d'aure fuskar da tay tace mata sun gama Maganar zata fita, d'an murmushi Hajiya tay ta sani duk irin zafin zuciyar ta mai d'a'a ce a gareta yanzu ma tasan Saboda tsoron abunda zai iya faruwa da Fanan yasa ta zauna tana ta mata Magana cikin 6acin rai kuma bata d'auki hakan a wani abu ba don ta san yadda soyayyar d'a da Mahaifi take, kai ta d'aga mata alamar sun gaman ta juya ta nufi kofa, cikin nuna ma kopar k'arfi ta bud'eta ta fuce,
Kuka Fatuu tasha har ta gaji tay shiru don kanta, kiran sallar la'asar ya tada ita taje tayo Alwala tazo ta kabbara salla, bayan ta gama zaune tay kan abun sallar ta langa6ar da kanta jikin gado ta shiga duniyar tunani. Hajiya Maryam na fitowa daga d'akin Hajiya Visitor room ta nufa, tana shiga ta d'aga wayarta tana k'ok'arin yin kira ba tare data zauna ba, d'an kai da komowa ta fara lokacin da wayar da ta kira ta fara ringing , Haisam zaune kan kujera a cikin d'akin da yake aikin injiniyancin shi kira ya shigo wayar shi, hannu ya kai saman desk d'in gaban shi ya d'aukko wayar, bin screen d'in yayi da ido ganin mai kiran lokaci guda ya yanke ba lafiya tasa ta kira shi ba ba kamar da yake dare ne kuma yasan tasan lokacin da suke ciki, shima abu ne ya ishe shi bacci ya k'aurace mashi yasa shi zuwa wurin yay zaune yayin da Fanan ke d'aki tana bacci, saida kiran ya kusa yankewa yay picking ya kai wayar kunne, sallama yayi mata tayi mashi banza cikin cool voice d'in shi ya gaida ita aikuwa kaman tana jira a fusace tace "Ka rik'e gaisuwar ka ban so, ai bamu da girman da zaka gaishe da ni tunda kai isashshe ne ka kai kayi gaban kanka, ashe Haisam baka da Mutunci ban sani ba! mu zaka wulakanta ka nuna bamu kai ba a wurin ka, kai ka Haifi kan ka ne ko mu muka haife ka da har zakai Aure ba tare da sanin mu ba, da izinin wa kaje kai auren???" Shiru yay bai da niyyar tanka mata aikuwa hakan ya k'ara hasala ta cikin daka tsawa tace "bazaka bud'e baki kai man Magana ba don ubanka" d'an lumshe ido yay ya bud'e, in ba ya manta ba tunda yake ba'a ta6a zagin shi haka ba, slowly ya bata hak'uri yace yayi ne don taimako, a fusace tace "then what are u waiting for da baka saketa ba kaman yadda kuka tsaran? Mi ya zaunar da ita" shirun ya k'ara yi saida tace bai jita bane sannan yace "Hajiya ce ta hana"
"Hajiya ce zata zauna da ita ko kai" d'an jimm yay sai kuma yace "I can't argue with her" shiru tay cikin ranta ta fara tunanin kenan ba don Hajiya ba zai saki yarinyar ne, d'an sassauta murya tay tace mashi shikenan zata yi Magana da Hajiyar he should be expecting her call kowane lokaci don ya saki Yarinyar, amsa mata yay da toh tace tasan Fanan bata sani ba to Kada ya sake ya bari ta samu labarin har zuwa lokacin da zai sake ta nan ma da toh ya amsa mata tay mashi sai da Safe ta kashe Wayar, bin wayar yay da kallo tun bayan daya cireta daga kunnan shi, can yay sigh ya fara latsa ta na d'an wani lokaci ya dakata ya zuba ma Screen ido kaman mai kallon wani abu...,
tana ta zaune a wurin cikin duniyar tunani, a hankali take kai hannu tana goge yar kwallan dake zubo mata daga cikin idanuwan ta da har sun d'an kumbura, wayar tace ta fara ringing ta d'aga kai ta kallo ta a saman gadon, ganin zata iya jawo ta yasa ta kai hannu ta jawo tan ta kalli screen d'in, Abbas ne mai kiran nata har saida ta d'an ji sanyi dama duk yau bai kirata ba, d'aga kiran tay ta kara wayar a kunne muryar ta can k'asa tay mashi sallama, bayan ya amsa ta gaishe dashi ya amsa daga haka tay shiru, jin yanayin muryar ta yasa shi tambayar ta lafiya nan ma tayi shiru, ce mata yay ta fad'a mashi inda matsala cikin rawar murya ta fara fad'i mashi duk abunda ya faru, sosae Muryar Abbas ta bayyana rashin jin dad'in abunda ya farun ya shiga bata hak'uri daga baya ya tambaye ta game da reaction d'in Senator nan ta gaya mashi komae tana gamawa ya furta "Alhamdulillah, dama nasan ta 6angaren shi ba za'a samu wata matsala ba, itama Momy Maryam d'in kawae tana taya d'iyar ta kishi ne ba wani abu ba, so kar kisa damuwa a ranki in sha Allah komai zai daidai ta na d'an lokaci kad'an ne" a hankali ta amsa mashi da to,
"Yanzu kin ci Abincin ne?" D'an girgiza kai tay tace mashi a'a,
"Ya zaki sa damuwa har ta hana ki cin Abinci hakan ai sai wani ciwon ya kama ki, ba wani Abincin da zaki ci ne?" bashi amsa tay da eh tace amman bari taje ta dafa indomie yace ta d'an jira ba sai ta dafa ba, har zai cutting kiran sai kuma taji yace bata tambaye shi Mijin ta ba, tura baki tay kaman ya gani yay yar dariya yace koda yake ai yanzu tafi shi kusa da shi daga haka ya katse, wayar na ruk'e a hannunta ta maida kan ta jingina da gadon kaman yadda take ada ta runtse idanu ta sake fad'awa duniyar tunani wanda duk na Haisam ne, gama wayar su da Abbas bada jimawa ba aka k'wank'wasa kopa ta bud'e idanunta ta kallo kopar zuciyar ta na harbawa da sauri da sauri, mik'ewa tay a d'arare ta nufe ta hannun ta har yar rawa yake da zata bud'e, tana bud'ewa suka had'a ido da Saude tana mata murmushi itama ta k'ak'alo d'an murmushin tayi mata a sanyaye ta gaishe da ita, hannu ta kai ta kamo hannunta guda suka nufo cikin parlon, akan kujera ta zaunar da ita itama ta zauna nan ta fara lallashin ta tace ita bata ma san abunda ke Faruwa ba don tana baya sai yanzu da aka kira ta a waya ai da tun d'azun ta kawo mata Abincin kuma itama ai data kirata sai tazo ta kawo mata amman zama da yunwar ga damuwa ai sai suyi mata illa, tasata gaba Saude tay saida tasa taci Abincin sosae daga baya ta k'ara kwantar mata da hankali kafin ta tafi. Bayan Hajiya Maryam ta yi waya da Haisam a bakin gadon cikin d'akin ta zauna hannunta ruk'e da wayar ta d'aura ha6arta saman shi, tunanin ta yadda zata 6ullo ma Hajiya har ta amince a saki Fatuu ta shiga yi, ta d'an d'auki lokaci a haka kafin ta idasa hayewa saman gadon ta kwanta da tunanin zata yi mata Magana anjima. Da daddare bayan kowa yayi shirin kwanciya Hajiya Maryam ta nufi d'akin Hajiya ta shiga da sallama Hajiya dake zaune a bakin gado sanye da kayan bacci idanunta na sanye cikin glasses tana duba wayarta ta amsa mata ta nufo ta, a bakin gadon daga d'an gefe ta zauna tayi mata sannu da hutawa da d'an murmushi Hajiya data d'ago kai ta amsa mata, shiru suka d'an yi Hajiyar ta maida idon ta akan Wayar ita kuma tana kallon k'asa, juyowa tay ta kalli Hajiya tace mata dama Magana take son su yi ne ta d'ago tare da jinjina mata kai idonta a kanta alamar ita take jira,
"Mun yi Magana da Haisam ya fad'a man ke kika hana ya saki Yarinyar can, kinga kenan shima ba wai son zaman yake da ita ba kawai yayi maki biyayya ne don haka ni ina ganin tunda shine mai zama da ita kuma ba so yake ba sai ki bashi dama ya rabu da ita hankalin kowa ya kwanta" d'an murmushin dattako Hajiyar tay jin abunda aka ce Haisam d'in yace, gyara zaman glass d'inta tay idonta akan Hajiya Maryam a nutse ta fara magana "Kaman yadda kika ce biyayya yay man yaci gaba da zama da ita to kema ina son kiman biyayya ki bi yadda nike so, ki yi masu Fatan Alkhairi a auren shikenan komai ya wuce" wani kallo take bin ta dashi baki bud'e alamar Al'ajabin Maganar tata rai 6ace tace "to wai Hajjaju akan mi zaki mashi dole ya zauna da ita ne, ya aureta don taimako da nufin zai saketa sai a sa ya saketan barin shi ya ci gaba da zama da ita ba komai zai ja ba sai 6acin rai" girgiza kai Hajiya ta fara yi "Ba zai rabu da ita ba Maryam dole yaci gaba da zama da ita, in kece ko Fanan a matsayin ta bazan so abunda kike so mata ba" ta k'are Maganar tana girgiza kai bakinta a kwa6e, yarfa hannu tay ta yamutsa fuska tamkar zata saka kuka cikin breaking voice tace "Wai Hajjaju ya kika za6i faranta ma bare ne fiye da naki, kin san idan Fanan ta samu labarin nan ba K'aramin mawuyacin hali zata shiga ba, dame zata ji don Allah ko so kike zuciyarta tay bursting ne, sai nike ganin kaman kin fi damuwa da ita yarinyar ma fiye da Fanan, in don haihuwa ne a ba Fanan d'in time mana kaman yadda nace d'azun duka ai ba dad'ewa sukai da yin auren ba ko" shiru Hajiya ta d'anyi still idanunta na akan ta sai faman huci Hajiya Maryam din take ta gumtse baki idanunta sun Kad'a da gani kiris ya rage ta saka kuka, cikin kwantar da murya Hajiya tace "idan aka zo Maganar Adalci Maryam baka duba bare ko naka indai Adalcin tsakani da Allah za'ai, koda Fateema take 6are ai itama tana da dangi kuma suna son ta suna son farincikin ta, sannan Maganar halin da Fanan zata iya shiga ita ai Musulma ce kuma inada yak'inin tana da cikakken imani hakan kuma na nufin ta yadda da k'addara mai kyau ko akasin hakan don haka in sha Allahu ina sa ran zata rungumi hakan matsayin k'addara kaman yadda ta rungumi ta lalurar ta ake ta neman Magani" Kuka ne ya taho mata tace "Hajiya kar azo ai dana sani, na fad'i maki har Alk'awari fa yayi ma Fanan kan bazai k'ara aure ba koda bata haihu ba kuma akan hakan suke zaune in taji ya k'ara auren nan har matar ta samu ciki mi kike tunanin zai iya biyo baya don Allah, dama kuma ga yanayin ta" cewa Hajiya tay in sha Allahu ba abunda zai faru kuma tasan lokacin da yay mata Alk'awarin ya riga ya auri Fatuu ne don haka shi yasan yadda zai rarrashe ta, a k'arshe ta tabbatar mata da indai ba yarinyar ce tace bata son zama dashi ba to wllh ba zai saketa ba, mik'ewa tay zumbur ta nufi hanyar fita Hajiya na kallonta ta kwa6e fuska.
Bayan ta koma d'aki kai da komowa ta shiga yi ta cize baki, abun ya matuk'ar d'aure mata kai yadda Hajiya ta kafe, a tunanin ta koda cewa akai Fanan bata haihuwa kwata kwata Hajiya bazata matsa ayi mata kishiya ba tunda abun na gida ne, dogon tunani ta shiga a k'arshe zuciyarta ta bata wani tunani kan dalilin Kafewar Hajiyar, A daren Hajiya Maryam ta yanke komawa lagos a yadda take ji ba don dare yayi ba da bazata ma kwana ba, a daren tayi duk wani cuku cukun tafiya saidae ba jirgin da zai je Lagos direct washe gari sai dae Kano ta yanke tafiya Kano d'in daga can sai ta hau na Lagos, a ranar baccin ta ragagge ne Saboda tsabar 6acin rai har gani tay daren yayi mata tsawo, Washe gari tana gama sallar Asuba ta hau shiri duk da bada wuri jirgin nasu zai tashi ba, Misalin k'arfe takwas na safiyar ta kira Senator take sanar dashi zancen komawar tata, tambayar dalilin tafiyar ta a yau yayi tace mashi hakanan ta canza shawara yace da yaushe jirgin nasu zai tashi ta fad'a mashi, ce mata yay in ta shirya kafin ta wuce ta same shi a G.r.a tace to, Misalin k'arfe tara da yan mintuna ta gama shirin ta tsaf cikin wani dandatsetsen leshi ruwan Madara da fulawowi maroon da golden brown, ba K'aramin had'uwa leshin yay ba idanun kansu zasu shaida maka tsadar shi don kuwa d'an dubu d'aruruwa ne, a da tazo da shirin fita taje wasu wurare kafin ta koma, gyale da jaka da takalma maroon ta saka ta fiddo wasu sarka da yan kunne da yan hannu na zinari ta saka ta fito a babbar macen ta, tana janye da d'an madaidaicin trolley d'in kayanta ta fito, Bedroom d'in Hajiya ta wuce bayan ta tura K'opar da yar sallama ta shiga, ganin Hajiyar bata cikin d'akin yasa ta kai idon ta wurin toilet nan ta gane tana ciki ta nufi bakin gado ta zauna, bada jimawa ba ta fito idanunta suka sauka akan Hajiya Maryam d'in ta nufo gadon itama ta zauna, kallonta tay ta gaishe da ita bayan ta amsa ganin tayi shiru yasa ta tambaye ta lafiya ta ganta cikin shiri da safe ko wani wuri zata ta girgiza mata kai kafin tace zata koma ne, d'an jimm Hajiya tay sai kuma tay d'an guntun murmushi tace "an 6ata maki rai shine kikai Fushi zaki tafi kenan" shiru bata ce mata komai ba idanunta na kallon k'asa, Hajiya ta k'ara cewa "shikenan bazan hana ki tafiya ba Allah ya tsare, kin yi Breakfast ne?" Girgiza mata kai tay tace in ta isa tayi ta gyad'a kai, d'an shiru sukai can ta mik'e ta kalli Hajiyar tace ta wuce, Addu'ar Allah ya tsare ta k'ara yi mata ta kama trolley d'in ta juya, har ta kusa k'opa Hajiya ta kira sunanta ta dakata ta juyo, "Kiji tsoron Allah, Kada soyayyar d'a ta tunzura ki kice zaki cutar da yarinyar can domin duk abunda kai ma d'an wani kaima za'ai ma naka ne, idan ranki ya 6aci Kada ki bari hankalin ki ya gushe, ki d'auki Al'amarin a matsayin Alkhairi sai kiga ya kasance hakan, tada hankalin ki shi zai taimaka wurin faruwar abunda kike gudu, ki gaida man Mazajena da K'awaye na" d'an jimm tay tana kallon ta kaman bazata tafin ba can ta furta mata ta gode ta juyo tana janye da trolley d'in ta fice,
Itama Fatuu a jiya bata yi wani baccin kirki ba wanda ta samu yake d'aukar ta ba wani mai nauyi bane gashi cike da mafarkin abunda ya faru tsakanin ta da Hajiya Maryam, kiran sallar farko na Asuba ta farka taje tayo Alwala, bayan ta fito ta zo ta kabbara raka'atanil fajr data gama ta d'aura da karatun Al'qur'ani har lokacin sallar Asuba yayi, bayan ta gama yin sallar kwance tay akan prayer mat d'in cikin sa'a bacci ya d'auketa, Misalin k'arfe tara saura ta farka jin jikinta duk ba dad'i yasa ta tafi toilet tayo wanka, bayan ta fito ta shirya cikin riga da wando, wandon skin tight ne bak'i sai rigar ta kai mata har gwiwa tana da gajeran hannuwa jikinta bak'i da fari ne, bata sa hula ba sai gashinta dake fake yayi tumm, bayan ta gama gado ta koma ta zauna tay tsuru, tana jin yunwa amman fargabar fita take sai kawai ta kai hannu ta d'auko wayar ta daga kan Bedside drawer ta fara dannata, bata dad'e da zama ba aka k'wank'wasa kopar ranta ya bata k'ilan Saude ce amman duk da haka saida taji tsoron bud'ewa, bayan ta bud'e taga Sauden ce suka gaisa harda ce mata tayi kyau inama Angonta na nan sai yafi ganin kyaun kwalliyar yar dariya tayi tace ita ai ba wata kwalliya tayi ba, daga baya tace mata ta fito tayi Breakfast gashi can ta kawo tace to, ce mata tayi ta fito suje taci a gabanta kaman