Showing 165001 words to 168000 words out of 512766 words
Chapter 56 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1645
da kuma kayan breakfast d'in da aka kai yau ba da yake duk akwae sauran Abinci na saka a fridge, sai dai inna koma sai in kawo ko Almajirai in suna zuwa sai a basu kada ya lalace" Fatuu tayi Maganar tana kallon Saude, tace "ai Almajiran ma sun zo tun d'azu da safe na tattara masu wanda za'a basu, amman Abincin nada yawa ne?" d'an jimm Fatuu tay alamar tunani "Eh gaskiya da d'an yawa don na jiyan bamu ci sosae ba sai breakfast d'in yau shima bread d'in da saura sosae sai itama kazar wurin rabi ce don shi cinya kawae yaci ma sai chips d'in shima ba sosae ba" Jinjina kai Saude tay sai kuma tace "amman mi zai hana ki aika dasu gida kawae kinga itama gwaggo ta huta da yin girki tunda daga ita sai Amadu" d'an waro ido Fatuu tay "Aunty Saude in aika dasu gida kuma, in aka gani fa zai zama kaman fa nayi rashin gaskiya ne", yar dariya tay ganin yanayin fuskar fatun tace "to miye abun rashin gaskiya fita da Abinci gidan nan ai ba wani abu bane, kullum cikin fita ake dashi ba wanda zai maida kai ya ga kinyi wani rashin gaskiya" shiru tay kaman tana nazarin Maganar tata can ta kalleta "amman Aunty Saude ba ance ba kyau ka d'auki abinci bada izini ba ka bayar" Saude ta fahimci abunda take nufi wato bada izinin miji ba tace "Wannan ai ana nufin d'anyen Abinci Fateema, amman dafaffe ba laifi in ka bada gudun kada ya lalace ya zama anyi Almubazzaranci kuma kai laifi" d'an gyad'a kai tay alamar ta fahimta, saida suka had'a kunun Aya mai shegen dad'i kafin a tare suka kai wanda za a kai dining table, bayan sun gama Fatuu cikin d'an jin kunya tace mata bari taje tana son tayi wanka Saude na dariya tace ai haka yakamata, da kanta taje d'akinta ta d'aukko gyalenta bayan ta fito ta shiga Bedroom d'in Hajiya don yi mata sallama, bayan ta shiga ta iske ta kwance akan gado tana bacci hakan yasa ta juya zata tafi sai kuma taji muryarta ta kira sunanta ta juyo ta ga ta d'ago da kanta tana kallonta, nufar gadon tay tana niyyar duk'awa kan Carpet da hannu tay mata alamun ta zauna a bakin gadon, cikin Muryar wanda ya tashi daga bacci tace "Bacci ne ya d'auke ni halan Azahar ma tayi tuni?" tace "A'a an dai fara kiran sallar" ta fad'a tana d'an kallon gefe, jinjina kai tay suka d'an yi shiru sai kuma ta sake cewa"har an gama aikin girkin ne" kai ta d'aga "Eh mun gama zan koma can ne" kanta a k'asa tay Maganar, "Ok, sai ki tafin maku da naku ma" amsawa tay da to tana k'ok'arin mik'ewa Hajiya ta dakatar da ita da fad'in "kinga na manta jiya nace zan sa a kirawo balaraba tay maki kitso ko a bari sai yamma kawai" shiru Fatun tay kanta a sadde tana d'an wasa da yatsun hannunta, ganin bata ce komai ba yasa Hajiya tambayar ko bata son kitson ne ta d'ago ta d'an kalleta fuskar ta da d'an murmushi ta d'aga mata kai alamar eh, yar harara Hajiya ta wurga mata "ashe har yanzu halin ki na rashin son kitso na nan Fateema?" Shiru bata ce komai ba Hajiya tace "yanzu in baki yin kitson zaki takura ne, in gayun Amarci kike son kiyi na k'yale ki aita gayu lafiya, amman dole ki rink'a yin kitso, amsa mata tayi da to a kunya ce tace mata taje ta mik'e tay mata sallama.
Bayan ta fito Kitchen ta nufa don ta d'aukko Basket d'in Abincin su ta taras da Saude na gyara Kitchen d'in, bayan ta d'aukka tay mata sallama ta fito, tana isa part d'in nasu bayan ta shiga parlon ta nufi Dining Area, a saman table ta d'aura Basket d'in ta shiga fiddo da warmers d'in tana jerawa, bayan ta gama d'aukar Basket d'in tay ta wuce Kitchen don ta aje, tsaye tay a gaban drawer bayan ta aje ta shiga tunanin Maganar Aunty Saude tana wasi wasin ta aikata yadda tace ko a'a, can ta yanke yin yadda tace d'in ta bud'e fridge ta fiddo sauran Kazar da Abincin jiya ta fara k'ok'arin dumama su a cikin Oven, bayan ta gama ta d'aukko kwalin Warmers masu kyau ta bud'e, mai d'an girma a ciki ta d'auka bayan ta wanke ta juye Abincin, sake d'aukko wata tayi itama bayan ta wanke ta juye Kazar, shiru ta d'an yi tana tunanin yakamata ta samu leda ta saka su ba ta aika dasu haka ba can ta tuno da ledar kayan baccin da Aunty Mareeya ta bata tana da girma Warmers d'in zasu shiga ciki, da sauri ta juya ta fita ta nufi Bedroom, bada jimawa ba ta dawo ruk'e da ledar ta fara saka Warmers d'in ciki hannun ta har d'an rawa yake, gaba d'aya sun shiga harda sauran wuri ma nan ta tuno dasu Snacks da ice cream d'in dake a Fridge d'in parlor ta juya da sauri ta fita daga cikin Kitchen d'in, d'ebo su tay ta saka harda robobin yoghurt da ice cream guda guda, bayan ta had'a komai tay tunanin kiran kawu Amadu don ya turo mata yaro da sauri ta juya ta fito ta shiga Bedroom, Wayar ta ta d'aukka ta kira shi yana d'agawa tunkan tayi magana yace mata miye kuma, yar dariya tay tace ba komai don Allah yaro take son in akwae wanda yazo siyayya ya turo mata shi yace to, aje wayar tayi ta juya ta fita tay tsaye bakin corridor tana dakon isowar wanda za'a turon, bada Jimawa ba akai knocking da sauri ta nufi kopar ta bud'e, wani yaro ne d'an unguwar ya turo tana ganin shi tace mashi tana zuwa ta juyo, ledar ta d'aukko harda dublan ta d'ebo mashi bayan ta kawo tace gwaggo zai kai mawa ta bashi ta dublan d'in tace gashinan ya ci yana washe baki yay mata godiya da Allah yasa Alkhairi ta amsa, juyawa tay da sauri ta koma Bedroom ta nufi gaban mirror bayan ta cire su sark'a da yankunnan ta ta cire kayan jikinta ta d'aura towel ta nufi laundry room, after some minutes ta fito jikinta sanye da bathrobe da ta gan su cikin cabinet d'in laudary ta d'auka, bayan ta fito doguwar riga tasa da hijab ta shimfid'a abun salla ta kabbara sallar Azahar da har angama ta a Masallacin gidan, bayan ta gama ta cire kayan ta linke da abun sallan ta maida kowanne wurin shi ta d'auki towel ta d'aura sannan ta nufi gaban mirror ta fara shafa, tana cikin yi wayarta ta fara ringing ta nufi gefen gado ta d'auka har saida gabanta ya fad'i ganin gwaggo ce mai kiran, bayan tayi picking ta gaidata nan tace mata mi ta aikata haka da sauri ta tari numfashin ta ba kamar yadda taji tayi Maganar cikin yar rawar murya ta fad'i mata duk yadda sukai da Saude, yar ajiyar zuciya ta sauke tace mata duk da haka yayi wuri da yawa ta fara hakan tace to zata kiyaye daga baya sukai sallama, bayan ta gama shafe shafen da goge gogen ta nufi wurin jakunkunan kayanta ta duk'a, tunanin kayan da yakamata tasa ta shiga yi, tana son saka k'ananun kaya don ko a gida tafi saka su ba kamar in ba inda zata je saidae tana gudun yay wani tunanin na daban, d'aya daga cikin Akwatunan kayan ta na gida ta bud'e ta fara ruwan ido can dae ta fiddo wata fitted gown d'in lace yellow da touches d'in dark ash bayan ta rufe akwatin ta bud'e na Undies ta d'auki wanda zatai amfani dasu, bakin gado ta nufa ta fara k'ok'arin sakawa bayan ta gama ta koma gaban mirror tana k'ara gyara kwalliyar da tayi yar light, sosae rigar ta amshe ta dama ita duk kayanta suna amsar jikinta Saboda irin d'inkin da ake yi mata dake fiddo dirin ta sosae, irin d'aurin kallabin d'azun tayi ta k'ara zubo da gashin gaba can kuma sai ta raba gashin na 6arin hagu ta maida shi baya na 6arin dama ta barshi a gaba, sosae hakan da tayi ya k'ara mata kyau sai kace wadda zata gasar kyau, bayan ta feshe jikinta da turare ta gyara komai ta maida bathrobe d'in, a gefen gado ta zauna ta fara tunanin ko akwae abunda yakamata tayi can ta mik'e ta nufi dressing mirror ta d'aukki robar Air Freshener ta shiga feshe Bedroom d'in Bayan ta gama ta juya ta nufi kopar fita, parlor tazo nan ma ta shiga feshe ko ina tana haka taji an turo kopar parlon ta kai idanun ta da sauri, Haisam ne ya shigo shima da alama wanka yayi don ya canza kaya zuwa farin jeans sai yellow polo shirt daga jikin tsayayyar collar d'in akwae ratsin fari haka a k'asan hannuwan ma sannan daga gaba 6angaren dama akwae farin tambarin polo d'in, yadda yasa Yellow d'in riga abun kaman had'in baki da itama tasa kaya Yellow, Cikin parlon ya shigo ya nufi inda ya saba zama ya zauna, slowly ta nufi inda yake hannunta ruk'e da robar freshener d'in, daga d'an gefe ta tsaya tayi mashi sannu da zuwa ya jinjina mata kai tay tsaye suka bi juna da ido tana d'an motsa baki, "Ya gida?" taji ya tambaya har saida taji mamakin tambayar ganin ya kafe ta da ido fuska a sake yasa ta yin d'an murmushi tace mashi lafiya lau ya d'aga kai,
"Sit" ganin tana ta tsayuwa yasa shi ce mata haka, zama tay a bangaren inda take shiru ta biyo baya da d'an murmushi take kallon shi tana yi tana maida idanun k'asa, "Kin yi kyau" kaman daga sama taji Maganar ta kalle shi had'i da d'an waro ido mamaki kwance akan fuskar tata, ya fahimci hakan sai kawai yay d'an guntun murmushin gefe idon shi a Kanta ya maida bayan shi ya jingina da jikin kujerar, Maganar sai ta tuno mashi da Fanan ita ta koya mashi cewa hakan duk in tayi kwalliya bai yaba ba sai tay ta k'orafi daga nan ya fahimci mata basu son suyi kwalliya a k'i yabawa, da k'yar ta furta mashi ta gode bai ce mata komae ba sai ma ya maida idanun shi kan wayar shi dake a hannun shi ya fara latsa ta, "k..Kai ma kayi kyau" da k'yar ta tattaro kalmomin muryar ta na d'an rawa ta furta mashi, shiru kaman ba zai ce komai ba can taga yay mata kallon k'asan ido fuskar shi a sake ya furta thanks kafin ya maida idon kan Screen, bin shi da ido tay ta ayyana sam baka ta6a gane mashi, tana cikin kallon shi ya d'ago suka had'a ido, d'age mata gira yay ya tambayi da wani abu da sauri ta girgiza mashi kai sai kuma tace ga Abinci can kan table ya jinjina kai, saida ya d'an k'ara lallatsa wayar kafin ya aje ta a gefe ya mik'e ganin haka yasa itama ta mik'e ta bi bayan shi, Kitchen ta wuce anan ta aje Freshener d'in ta wanke hannuwan ta sannan ta d'auki duk abunda zata buk'ata na cin Abinci ta fita, bayan ta iso dining d'in ta fara zuba mashi tana sa sakwara guda d'aya ya d'aga mata hannu alamar ta isa kawai sai gani yay ta k'ara d'aukko guda ya d'ago ya kalleta ta d'an tura baki ta fara k'unk'uni a shagwa6e tace "ya za'ai abu d'aya ya ishe ka" wani kalan kallo ya ke bin ta da shi ya d'an d'age gira,
"Ba zai isheka ka k'oshi ba sai dae ko biyu" tana gama Maganar ta k'ara mashi d'ayar tana yi tana kallon shi, yanayin fuskar shi ne ya sauya taga kaman ya d'aureta ta fara d'an kikkafta idanu a marairaice tace "har yanzu fa in baka cin Abinci sosae Ulcer zai iya kama ka" still yay yana bin ta da ido without saying anything, jikinta ne yay sanyi ta kai hannu da niyyar ta cire wadda ta k'aran taji yace "in ya kama ni I have got married now" da sauri ta kalle shi taga ya d'an d'age mata gira kuma ya saki fuskar lokaci guda ta saki murmushi jin bai manta da Maganar data ta6a yi mashi ba, bayan ta gama serving nashi itama ta zuba ta fara ci tana yi tana satar kallon shi yana cin nashi a nutse, sunyi nisa da farawa ta dakata idon ta a kan shi tana d'an murmushi slowly ya d'aga ido ya kalleta don yaji kallon shi take, "ya yi dad'i Abincin?" ta tambaya, bai bata amsa ba ya maida idon shi kan Abincin, saida ya k'ara ci sannan taji yace miye na tambaya tunda ba ita tayi ba, a hak'ik'an ce tace ai tare fa suka yi kuma ko ita kad'ai zata iya yin shi, d'an guntun murmushi kawae yay yaci gaba da ci, sai ga shi ya take duka sakwarar cikin wasa ta tambayi ta k'ara mashi ya d'an wurga mata harara, bayan ya sha kunun ayar ya yago tissue ya goge mouth d'in sa sannan ya mik'e zai bar wurin idon Fatuu a kan shi, dakatawa yay ya kalleta suka had'a ido Slowly taji ya furta "the empty plate is ur answer for d question u asked" daga haka ya juya yana tafiyar shi ya nufi cikin parlon tabi bayan shi da kallo tana Murmushi shi komai nashi na daban ne, saida taci ta k'oshi don ita kanta Abincin yayi mata dad'i sosae, bayan ta gama ta fara kwashe kayan da sukai amfani ta kai Kitchen, saida ta gyara Dining table d'in sannan ta koma Kitchen ta wanke komae da suka 6ata ta maida shi a wurin shi, bayan ta gama har zata fita idanunta suka sauka akan bokitan su cin cin a ranta ta raya tunda aka yi su bata ci ba wata zuciyar ta ayyana shi k'ilan ma baya cin su, tunanin ta d'iba ta kai mashi taga in yana ci tay ta d'aukko plate mai kyau ta bud'e ta d'ebo kowanne bada yawa ba harda alkaki, bayan ta zuba ta nufi hanyar fita yana kishingid'e kan kujera idon shi akan Tv yana kallon American film ta nufo shi tana tafiya a nutse sai kace mai yin yanga, tunda ta tunkaro cikin parlon ya maida idanun shi kanta har ta k'araso ta d'aura plate d'in kan c-table ta k'ara matsar dashi kusa dashi ta d'ago tana murmushi suka had'a ido tace mashi gashi nan ya ci, maida idon yay kan abunda take maganan kafin ya d'ago ya kalleta tana tsaye still Murmushin take tana d'an wasa da yatsun hannunta da ta had'e, ji tay yace a ina zai saka wannan d'in da sigar shagwa6a tace ai su ba Abinci bane,
"Who told u ba Abinci bane, yanzu kaci wannan kasha ruwa bazaka k'oshi ba?" Ya tambaya had'i da d'age gira, d'an tura baki tay "Ya za'ai su kosar da Mutum, saidae in da yawa aka ci kuma ai kai kad'an ne na kawo maka ko" tana Maganar ya kafe bakinta da kallo, sigh yay ya d'an shaking kan shi "bansan ina zan sa shi ba as am stuffed, I couldn't eat another bite" bin juna sukai da kallo na d'an wani lokaci can ta kai hannu a sanyaye ta d'auki plate tana shirin juyawa taji yace zai ci wani lokacin ta juyo suka had'a ido ya d'an bud'a mata ido alamar taji abunda yace ta d'aga mashi kai daga haka ta wuce ya bita da kallo, bayan ta maida su ta fito ta wuce Bedroom, bada jimawa ba ta fito hannunta ruk'e da laptop d'inta da babban hardcover ta nufo cikin parlon ya maido idon shi kanta, a gefen shi ta tsaya a d'an marairaice tace "please, could you help me with this Assignment, ta email malamin yace mu tura mashi gashi harda drawing nayi k'ok'arin in d'aukko in saka na kasa" shiru yay just staring at her har saida tasha jinin jikinta ta d'an juyar da fuskar ta, tana haka taji cool voice d'in shi yace ta kawo ya gani ta matsa, akan c-table ta d'aura ta shiga nuna mashi yadda Assignment d'in yake bayan ta gama ta d'ago ya kai hannu ya fara latsa Computer din, can bayan d'an wani lokaci ya d'ago suka had'a ido yace mata sai ya d'aukko abu a G.r.a za'a iya tura mashi zuwa dare zai nuna mata, murmushi ta shiga yi tayi mashi godiya bai ce mata komai ba ya koma ya jingina bayan shi jikin kujerar, hannu ta kai zata d'auki laptop d'in slowly taji yace an hana ta zama a parlor ne, kallon shi ta d'an yi still da murmushi ta fasa d'aukar laptop da littafin ta koma d'ayan side d'in kujeran ta zauna, remote ya d'auka ya canza daga channel d'in da yake kallo zuwa Arewa 24 lokacin suna cikin yin maimaicin shirin dad'in kowa da yake k'arfe ukku yayi, d'an juyawa tay ta kalle shi ta d'an yamutsa baki nan take ya gane mi hakan ke nufi ya k'ara canza channel zuwa tauraruwa ganin suna yin wak'ok'i yasa ta d'an yi murmushi, voice d'in shi taji yana tambayar yayi mata ta juya ta d'aga mashi kai ya aje remote d'in dama ta dalilin ta ya san channels d'in hausa, tana kallon wakokin tana d'an bi wani lokacin har d'an juya kai take akwae wata da ya lura tana mata dad'i don sosae take bin wak'ar tana juya kai, still yay yana ta kallon ta kai kace ita ta raira wak'ar saidae kuma kunnan shi na akan wak'ar yana sauraro can kaman taji kallon ta yake ta juya suka had'a ido yar dariya tayi mashi shi kuma ya d'an yi mata guntun murmushi, ana yin wakokin kaman guda biyar suka datse suka sako tallar magunguna, juyowa tay tace mashi ya maida channel d'in da yake kallo sun gama fuskar shi a sake kaman zai murmushi ya kalle ta, tambayar ta