Showing 258001 words to 261000 words out of 512766 words
Chapter 87 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1643
d'inka su harda wanda zata saka ranar Dinner, sai faman jinjina kai ake a wani d'an kit kusan duk zinarai ne a ciki harda gold su Fatuu anyi goshi hakanan ma Haisam yayi mata Akwatunan kaya inaga yanzu, bayan an gama dubawa aka hau yin godiya da Addu'oi, Fauzy ce ta koma d'akin da suka sauka da gudu da yake Fatuu na ciki ta hau bata labarin irin lefen da aka mata a rud'e sai faman zuzuta kayan take ita dai murmushi kawae take komai zuwa yake mata kaman a mafarki.
A ranar bayan sallar Azahar Fanan ta iso Haisam ne yaje ya d'aukko ta a Airport ita kadae tazo sai autar su Noor, bayan ta iso a d'akin Mom d'in su ta sauka aka hau haba haba da ita ana mata sannu da zuwa daga baya tace bari taje su gaisa da Hajiya, Jidderh ce taje baya ta sanar ma Fatuu zancen zuwan Fanan d'in suka taho tare, bayan sun je d'akin Mom d'in aka sanar masu tana d'akin Hajiya suka nufi can, tana zaune a bakin gado su Fatuu suka shigo suna had'a ido ta nufeta da gudu suka rungume juna su Hajiya da gwaggo da wasu dake cikin d'akin suna ta murmushi don ba K'aramin burge mutane sukai ba, d'agowa Fatuu tay ta duk'a kasa hannunta cikin na Fanan d'in ta gaishe da ita tayi mata an zo lpy tana ta murmushi ta ke amsa mata tana fad'in Amaryar su, daga baya tare suka tafi harda Jidderh suka nufi baya, d'akin su Aunty Mareeya ta kai ta Feenah na ganinta ta mik'e tana murmushi take fad'in "You are Welcome Uwargidan H,Zakee" murmushi kawae Fanan d'in ke yi ta nufi bakin gado ta Zauna Aunty Mareeya ta bita da kallo don ta gane itace kishiyar Fatuu, gaidata Fanan d'in tayi tana murmushi ta amsa tayi mata an zo lafiya tace lafiya lou, hira suka shiga yi sosae ta burge Aunty Mareeya yadda bata da d'agin kai ko kad'an, suna haka Jidderh da Fatuu suka kawo mata abinci da abun sha Aunty Mareeya na dariya ta kalli Fatuu tana fad'in su Zarah anga Yaya sai washe baki ake duk suka kalli Fatun ta kai hannu ta rufe fuska Fanan ce tace mata ya Amarya ba k'unshi kuma tace anjima zasu je ba wani mai yawa ne za'a mata ba tace Ok, daga baya su Fatun suka fita Aunty Mareeya tace mata taci Abincin mana tace ok ta saukko kan Carpet ta zauna Noor dai na wurin Hajiya, sosae suka shiga yin hira anan har Aunty Mareeya da Feenah na yaba mata kan namijin k'ok'arin da tayi tana d'an murmushi tace ai haka yakamata don in kace zaka ja da hukuncin Ubangiji to kai ne a wahala gaba d'aya suka ce hakane wllh, karshe dai a nan ta wuni.
Misalin k'arfe biyar na yamma lokacin su Fatuu na wurin kunshi dankara dankaran Motoci suka shigo cikin gidan da jiniya nan take aka gane Her Excellency Hajiya Zainab ce ta iso, a gaban Entry Hall na gidan Motocin suka parker nan da nan jama'ar cikin gidan suka fara fitowa wanda suka san itace da wanda ma basu san itace ba kawai jiniyar tasa su fitowa, wani Security ne daga cikin Escort d'inta na Motar gaba ya fito da sauri yazo ya bud'e mata k'opa ta zuro farar kafarta data k'unshi ga wani mayen takalmi golden sanye a k'afar, k'arasa fitowa tay tana sanye da rantsatstsen lace bak'i mai adon green da ratsin golden kad'an, tun daga kunnan ta zuwa wuyanta da yatsun hannunta duk gold ne ta yafa mayafi golden kalar takalmanta da jakarta abun sai dai ace Tubarkallah dama tana d'aya daga cikin Matan gwamnoni da suka san takan gayu, Security detail d'in ta mace ce ta fito tazo bayanta ta tsaya wani daga cikin Escort d'in nata ya nufi Motar dake bayan tata ya bud'e yaran ta ne suka fito cikin shiga ta Alfarma, Mota ta biyun k'arshe wani security d'in ya fito daga cikin Escort d'in Motar baya ya bud'e kopar bayan ta, kai kace ba mutum aka bud'e mawa ba don ba alamun wani zai fito, saida aka d'an d'auki lokaci sannan ya zuro da k'afar shi guda mai sanye da wani dakakken bak'in takalmi half cover daga haka bai k'arasa fitowar ba, Hajiya Zainab nata Murmushi ta tunkari Mutanen da suka fito tarbarta Momyn Haisam ta taho suka rungume juna gwanin burgewa kasantuwar fuskar su iri d'aya ce, bayan sun saki juna mutane suka hau gaishe ta ana mata sannu da zuwa wad'anda ma basu santa ba basu san lokacin da suka hau washe baki ba suna mata sannu da zuwa a mutunce take d'aga hannu tana amsawa, k'arasa fitowa Sameer yayi yana sanye da bak'in jeans da top bak'a sai maroon d'in riga a sama mai ma6allai saidai ba'a sanya su ba a bud'e take hakan ya bayyana bakar ta cikin idanun shi na sanye da wani mayen bak'in glass, agogon hannunshi ma bak'a ce saidae daga wurin glass d'in kan yana reflecting maroon d'in cikin agogon kai da gani ba sai an fad'a maka zata yi kud'i ba ga sumar shi da ta sha gyara a kwance, nufar inda su Mom d'in shi ke tsaye yayi yana tafiya cike da izza, yana zuwa ya tsaya a gefen ta Mom d'in su Haisam ta kalle shi da faffad'an murmushi tace "U'r welcome my son" kai kawai ya jinjina mata fuskar shi ba yabo ba fallasa Aunty ma sannu da zuwa tayi mashi to itama d'in dai kai ta samu aka d'aga mata, Laila ce ta matsa gaban shi tana kallon shi da murmushi tace ita bazata yi mashi sannu da zuwa ba sai ya bud'e idanun ta kuma tabbatar ba makancewa yay ba da yake suna d'an shiri dashi, d'age mata gira yay itama ta d'aga mashi tata sai lokacin yanayin fuskar shi ya d'an canza a K'ok'arin shi na yayi murmushi, hannu ya kai ya cire glass d'in tace Yauwa to amman da ya rufe idanu basu ma san ko yana ganin su ba, sannu da zuwa tayi mashi ya d'aga mata kai daga haka ya fara k'ok'arin wucewa ciki yana maida glass d'in all eyes on him nan aka shiga darewa ana bashi hanya har ya shige ciki, a wurin dai da yawa ya tafi da imanin wasu ba kamar yan mata Aunty Mareeya data saki baki tana kallon shi har ya shige ta jinjina kai tace "banga laifin ka ba wllh, ga kyau ga kud'i ga Mulki ai abun da yawa mutum bama zai san lokacin da zai ringa jin izza ba" Feenah dake gefenta ta saki dariya, nufo shiga ciki Her Excellency tay aka bata hanya security d'inta na biye dasu bayan tayi gaba aka rufa mata baya suka shige ciki........
*ASM 080*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........Sameer na shiga cikin parlon ya nufi bene cike da isa ya haye ya nufi part d'in Haisam, bayan sun shigo d'akin Mom d'in su Haisam suka nufa, a parlor d'in ta duk aka zazzauna wasu akan kujeru wasu kuma a k'asa Security detail d'in ta na daga gefe a tsaye, gaisawa aka shiga k'ara yi ana mata an zo lafiya da fara'a take ta amsa ma kowa, bayan wani lokaci ta mik'e tace ma Mom zata shiga ciki ta d'an hutu before ayi sallar Magrib tace mata to Abinci ba, ce mata tayi bata jin yunwa saidai ko yara daga haka ta nufi hanyar Bedroom, dakatawa tay kafin ta shige tace ma security d'in tata ta zauna anan ta huta ta d'an rankwafa tayi mata godiya Mom ta bi bayanta suka nufi cikin Bedroom d'in.
Abbas da Saleem wanda dama yana a Abujar zaune a cikin parlon Haisam Sameer ya turo k'opar ya shigo duk suka d'aga kai suka kalle shi, mik'ewa Abbas yayi da fara'a ya tarbe shi yana mashi sannu da zuwa kai kawai ya d'aga mashi Saleem dai na zaune yana bin su da ido don shima duk tafiyar su d'aya da Sameer d'in sai dai bambancin shi Salim miskilanci ne kawae Sameer kuma banda miskilanci harda izza ta bala'e, gaba d'aya kowa yasan kowa da kuma matsayin baban kowa tsakanin Sameer d'an Governor da Saleem d'an Deputy Governor, sai bayan da Sameer d'in ya zauna ya kai hannu ya cire glass d'in Fuskar shi sannan Salim ya d'an d'aga hannu yace mashi welcome Sameer d'in ya jinjina mashi kai daga haka ya maida idon shi akan Tv yaci gaba da kallon Film d'in da suke kallo, Abbas ne yace mashi Haisam d'in na wanka ne sai lokacin ya bud'e baki can k'asan mak'oshi ya furta Ok, hannu ya kai ya fiddo wayar shi daga cikin trouser pocket d'in shi ya fara latsa ta, bai dad'e da zama ba Haisam d'in ya fito yana sanye cikin k'ananan kaya kaman ko yaushe yana hango Sameer d'in ya d'an bud'a ido alamar mamaki don koda ya jiyo jiniya ya san Mom d'in shi ce amman bai yi zaton harda shi za'a zo ba don ko jiya sunyi Magana yake ce mashi ba zai zo ba yana da uzuri, nufo shi Haisam yayi yana zuwa ya zauna a gefen shi fuskar shi da murmushi ya mik'a mashi hannu tare da fad'in "What a surprise, u'r Welcome Bro" d'an gutsirin murmushi yayi a hankali ya furta mashi thanks, tambayar shi yay amman da yace bazai samu zuwa ba, kaman bazai bashi amsa ba sai kuma ya d'age gira yace to ya zo ko ya koma ne, yar dariya Haisam yay kawai Abbas dai yana ta kallon su da murmushi akan fuskar shi d'an Deputy kuwa tamkar ma bai san dasu a wurin ba,
Jingina da kujerar Haisam yay idon shi akan Sameer yace "Kai wai sai yaushe zakai aure ne naga alamar ma baka da ko niyya" d'an yamutsa fuska yay idon shi akan Screen d'in wayar shi cikin husky voice d'in shi ya furta " I'm not as promiscuous as you are, ni ba dole sai nayi ba" d'an bud'a ido Haisam yay alamar mamaki yace "U call me dat!" Sai lokacin ya d'ago ido ya kalle shi yanayin fuskar shi yay d'an alamun murmushi Abbas sai dariya yake, ce mashi Sameer d'in yay ai ya fahimci ta farkon bata satisfying nashi ne shiyasa har ya k'ara itama yasan bada jimawa ba zai k'ara, a fiffizge yake Maganar yana yi yana d'age gira, Abbas sai dariya yake hakan ne ya janyo hankalin Salim ya maido idon shi kan su, shi dai Haisam murmushi kawae yake don bai san mi zai ce mashi ba, mik'ewa Sameer d'in yay idon shi akan Haisam yace yana bashi shawara daga wannan yayi hak'uri hakanan don a yawan aure ana samun cuta daga haka ya nufi hanyar Bedroom Haisam ya bi shi da ido yana murmushi haka Salim ma murmushin yake Abbas kuma sai dariyar k'eta yake, har ya kusa Bedroom d'in Haisam ya d'an d'aga murya yace Abinci fa, hannu ya d'an girgiza mashi ba tare daya ce komai ba bai kuma juyo ba har ya shige d'akin, bayan shigar shi ne Abbas yace "ashe ya iya tsokana haka" d'an girgiza kai Haisam yay yana dariya ya furta "d'an iska ne da kake ganin shi" Abbas din ya fashe da dariya.
Sai bayan Magrib su Fatuu suka dawo anyi mata k'unshin a k'afa da hannu yayi kyau sosae ja da bak'i ne saidae jan yafi yawa kuma ba wani mai yawa bane sosae, su Fauzy da Mino duk ba'ayi masu ba don sun yi tun a Katsina kawai rakiya sukai, Jidderh ma anyi nata yan sarkoki masu kyau, d'akin Jidderh Fatuu ta wuce don kayanta na acan Fauzy kuma ta nufi baya, tana zuwa wanka ta shiga bayan ta fito Jidderh ma ta shiga, shiryawa tayi da doguwar riga bayan ta gama ta shimfid'a prayer mat ta kabbara salla da suna a hanya aka yi ta, bayan Jidderh ta fito tana cikin shafa mai su twins suka shigo ganin yadda suka fad'o cikin d'akin yasa ta kalle su tace daga ina suna dariya suka ce daga wurin Momyn Nasarawa suke, d'an waro ido tay tace "Momy ta zo kenan ashe shiyasa naga an k'ara security a gate, aikuwa bari in je mu gaisa" ta k'arasa tana ta washe baki, ba 6ata lokaci ta shirya itama doguwar rigar ta zura ta d'aukko Hijab ta kabbara salla, Fatuu na gamawa ta kalli su twins tana murmushi, wurin ta suka nufa suka zauna a gefen ta duk suka kama hannunta suna yabon k'unshin ta itama ta kamo hannun Mubeena tana yabon nata, Jidderh na sallamewa tace ma Fatuu tazo suje ta gaisa da twin sister d'in Mom d'in su First Lady d'in Nasarawa, d'an murmushi tay tace mata taje kawae Jidderh d'in ta matsa mata tace tasan ma za'a aiko kiran ta don su gaisa gara tazo suje kawae, dole ta mik'e Jidderh ta cire Hijab d'in jikinta ta d'aukko gyalen rigar itama Fatun tace mata ta cire hijab d'in mana, cirewa tayi ta d'auki gyalen rigar ta yafa su twins na ruk'e da hannuwanta suka tafi, part d'in Mom d'in suka nufa security detail d'in na a bakin k'opa suka gaishe da ita ta amsa a raina nace rayuwa kowa da hanyar cin Abincin shi wata na ciki tana hutawa ga wata k'ik'am tana gadin ta, nima dai sannu nace mata ta d'aga man kai na wuce sumi sumi, a parlor suka fara tsayawa suka gaggaisa da Mutanen ciki wasu na nuna Fatuu suna itace Amaryar ita dai sai d'an murmushi take tana Sunna kai, Bedroom suka wuce lokacin da suka shiga gaba d'aya Mom d'in su data Nasarawar suna zaune a saman gado jikin Her Excellency sanye da jallabiya cotton mai gajeran hannu bak'a anyi mata sak'a mai kyau orange a gaba itama Mom d'in su Haisam doguwar riga ce a jikinta gaba d'ayan su ba kallabi a kan su sai tarin sumar su dake a nad'e, daga d'an nesa Fatuu ta tsaya tana kallon su, ba don tasan dama su yan biyu bane to da ba k'aramar razana zata yi ba duk da yanzun ma saida ta d'an rud'e ganin Mutum biyu iri d'aya bata yi zaton haka suke kama ba komai nasu iri d'aya, nufar gadon Jidderh tay da gudu tana zuwa ta fad'a jikinta tana fad'in "Welcome lovely Mom" hannu tasa tana d'an bubbuga bayan Jidderh tace "thank you beloved Daughter" d'agowa Jidderh tay tana dariya itama murmushi take tace sun dawo kenan ai ta tambaye ta ance sun je k'unshi ne da bride d'in, ce mata tayi eh ai gata nan ma tare suka zo ta juya ta kallo Fatuu da tayi tsaye kamar an dasa ta, Mom d'in su Haisam ce tace mata ta k'araso ciki mana tana murmushi, nufo gadon Fatuu tay tayi mata alamar taje su gaisa ta nufi side d'in da suke, kokarin duk'awa tay k'asa Hajiya Zainab d'in ta nuna mata kusa da Jidderh tace ta zauna, a sanyaye ta gaishe da ita tana murmushi ta amsa tace mata ya hidima a hankali Fatuu tace Alhamdulillah, jinjina kai tayi tace Allah yasa Alkhairi Fatun ta amsa da Amin a hankali, daga haka bata k'ara ce mata komai ba ta maida idon ta akan Jidderh tana tambayar ta karatun ta nan ta shiga bata labarin yadda yanzu ta k'ware wurin tsara wuri, tana murmushi tace ma sha Allah zata gayyato ta Government House tazo ta tsara masu wasu wurare, washe baki Jidderh tayi tace da taji dad'i amman ai tasan wasa take tana murmushi tace mi zai sa tayi mata wasa indai ta k'ware yadda ta fad'a, sosae Jidderh ta shiga washe bakin jin dad'i Fatuu dai kanta na a k'asa sai jefi jefi take d'agowa ta kalle su ita mamaki ne duk yabi ya cika ta don bata ta6a ganin yan biyu ba haka masu bala'en kama, Mom d'in su ce tace ma Jidderh sun ci Abinci ne da suka dawo tace a'a ai basu dad'e da dawowa ba salla kawai sukai, tace to ta tashi suje kar a bar Amarya da yunwa Fatuu ta d'an kalleta tana murmushi, mik'ewa Jidderh tayi ta kamo hannun Fatuu ta mik'e suka nufi hanyar fita idon Hajiya Zainab akan Fatuu don Mom d'in su ta bata labarin komai game da yadda har akai Auren. Suna fita parlor Jidderh taga d'aya daga cikin ma'aikatan dake hada hadar Abinci tace mata ta kawo masu Abinci a d'akin su tace to, suna cikin cin Abincin wayar Jidderh ta fara ringing ta kai hannu ta d'auko, ganin mai kiran nata ta saki k'ayataccen murmushi Fatuu na ganin haka itama tayi murmushin, picking tay bayan ta kara ta a kunne ta furta Ok daga haka ta cire wayar tana yar dariya ta fara k'ok'arin mik'ewa tace ma Fatuu ta k'arasa cinyewa heartbeat d'inta ya zo, d'an bud'a ido Fatuu tay tana murmushi tace mata ashe tana da saurayi ai tayi zaton bata kula samari don bata ji tana Maganar su ba,
"Ai Aunty Fatuu na kama dahir ne shiyasa ban Maganar wasu samari, d'an Abokin Dad ne Minister of finance" jinjina kai Fatuu tay sai kuma tace "dashi za'a yi kenan?" Jidderh dake a gaban mirror tana gyara fuskarta tace "in sha Allahu yanzu haka ma shi so yake a sa mana rana nice nak'i yarda nafi son sai Aunty Laila ta fara yi tukunna da ta k'arasa karatunta za'ayi bikinta don har an tsaida magana ma tuni" Fatuu dake saurarenta tace mi zai hana to ta bashi dama sai a had'a su kawae tana murmushi tace shima haka yace amman ita tafi son ta gama Karatun ta gaba d'aya don shima a cikin karatun yake a London yanzu in ko sunyi aure bazasu zauna a wuri guda ba tunda itama Dubai zata tafi k'arin karatu dama ya gama nashi ne tasan zai bita Dubai d'in gara ya gama tukunna, bayan ta gama gyara fuskar tambayar Fatuu tay ko ta canza kaya tace mata ai rigar jikintan ma lafiya lou tunda bata dad'e da sakata ba