Showing 324001 words to 327000 words out of 512766 words
Chapter 109 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1677
Fatuu a tare suka nufi barin wurin sam Mino ta kasa rufe bakinta sai faman juyawa take tana kallon Fatuu da gaba d'aya ta canza mata, inda sukai parking Mota suka nufa daidai lokacin Fauzy ta k'araso cikin Keke Napep, fitowa tay tana sanye da doguwar rigar material tayi rolling bak'in veil a kanta bayan ta biya mai Napep d'in tana juyowa ta hango su Fatun cikin d'an d'aga murya ta k'wala mata kira hakan yasa Fatuu dakatawa ta juyo, nufar su tay gaba d'aya sun dakata suna jiran ta k'araso, tana zuwa ta d'an rungumo Fatuu tace "Welcome back Bestie nah" Fatun tayi mata godiya tana ta murmushi, bayan ta d'ago ta juya ta gaishe da Hajiya tare da yi mata sannu da zuwa, kallon su Kawu Amadu dake d'an murmushi tay suma tay masu sannu da zuwa Mino ma ta gaishe da ita ta amsa da fara'a, maida idon ta tay kan Fatuu da still Murmushi ne akan fuskarta ta kai hannu ta d'an ja kumatunta ta furta "Wannan kumatu haka da kika aje Tubarkallah ko dai ke kike cinye Abincin gidan ne" tana rufe baki Hajiya ta bata amsa da "kamar kin sani" duk sukai dariya, ce masu Hajiya tayi su je a k'arasa gaisawa a gida duk suka juya, ganin Motar kamar bazata ishe su ba yasa Fauzy cewa bari ta samu Napep sai ta bi bayan su Kawu Amadu yace lafiya lou zata isa bari su zauna a gaba shi da Mino, bayan duk sun shiga cikin Motar Hajiya da Fatuu da Fauzy ne a baya suka tafi.
Lokacin da suka iso Unguwar su suna zuwa gab da gida Mino ta kira Gwaggo a waya ta sanar mata gasu sun dawo don da harda ita za'aje tarbar su to sai taga Motar bazata isa ba in aka d'aukko su hakan yasa ta fasa zuwa tace masu in sun dawo sai su sanar mata, A daidai bakin gate Motar ta tsaya su Officer suka taso da sauri suka zo bakin Motar aka zuge glass d'in cikin washe baki suka hau yi masu sannu da zuwa duk suka amsa, bayan an zuge gate d'in suka kutsa cikin gidan, part d'in Hajiya ya tunkara tace mashi ya kaisu cikin parking space kawai yadda ba sai yasha wahalar maido Motar ba tama mik'ar da k'afafunta, lokacin daya parker Motar Officer Jamil mijin Saude ya k'araso da sauri ya bud'e k'opar side d'in da Hajiya take Fauzy ta bud'e ta d'ayan side d'in haka su Kawo Amadu ma duk suka firfito, k'ara gaishe da Hajiya Officer yay cikin washe baki tayi mashi ya aiki ya amsa da Alhamdulillah kafin yace sun yi kewarta sosae cikin Fara'a tace "to ai gani na dawo kewa ta k'are ko" yana yar dariya yace hakane, kallon Fatuu yay ya yi mata ya jiki tace Alhamdulillah, tambayar akwai kaya yayi Hajiya tace mashi ba wasu kaya duk anyo gaba dasu ya je kawai yace to tare da yi masu Allah ya huta gajiya ya nufi komawa gate,
har zasu fita daga cikin wurin Hajiya ta kai idonta kan wata Mota dake a lullu6e da tamfal, dakatawa tay ta nuna Motar da sandar ta tace ma Tk wannan fa yace mata Tahir ne ya kawo ta kusan fin wata kenan yace Ya Haisam ne yace ya kawo, jinjina kai tay tace ko Mota ya canza ne Tk d'in yace bai sani ba, kallon Fatuu tay tace "Mijin ki ya fad'a maki yayi sabuwar Mota ne" shiru ta d'an yi kafin tace a'a bata san ko tashi bace amman dai ya nuna mata hoton motoci yace ta za6a tun ranar da su gwaggo suka dawo Hajiyar tace to k'ilan tata d'in ce, da sauri Tk yace bari ya bud'e taga in itace yace ma Amadu ya kama mashi, lokacin da suka bud'e Motar har saida gaban Fatuu ya fad'i ganin jigunannar Motar matsayin tata don ta shaida wadda ta za6a d'in ce, gaba d'aya maido idanun su sukai kan Fatuu suna son jin tata d'in ce saida Tk yace mata itace sannan ta d'aga mashi kai alamar eh jiki a mace, da tsananin mamaki duk suka shiga bin Motar da kallo don ta had'u dai ba k'arya,
"Yanzu kina nufin wannan jibgegiyar Motar taki ce?" Amadu ne ya tambayi Fatun da mamaki, murmushi kawai take ta kasa magana don itama sosae taji Al'ajabin ganin Motar a matsayin tata, Hajiya ce tay d'an murmushi tace "tunda ta fad'a tata d'in ce, ai ba abun mamaki bane Ahmad, ko kamanta Mijinta sune Mota" Murmushi yay tare da jinjina kai Hajiya tayi mata Allah ya sanya Alkhairi suma suka shiga yi mata Mino sai washe baki take tana ta6a jikin Motar haka Fauzy ma taji ma Fatun farinciki sosae, Saude ce ta k'araso wurin don bata san sun iso ba tana d'akinta acan baya saida Officer ya kirata yay mata Albishir d'in dawowar Hajiyar, cikin washe baki ta gaishe da ita tare da an dawo lafiya Hajiya na murmushi ta amsa tay mata ya gida Sauden tace "gidan duk ba dad'i wllh da baku nan" yar dariya Hajiya tay tace to ai gata ta dawo sai su dasa daga inda suka tsaya Saude ta fad'ad'a dariyarta, kallon Fatuu dake kallonta tana mata murmushi tay suka gaisa itama tay mata an dawo lafiya da ya k'arfin jiki, maida idonta tay kan Motar da taga ana kallo Hajiya tace mata wai Motar Fateema ce suka tsaya kallo Sauden tace "Ma sha Allah, ashe ta Fateema ce amma dai Motar tayi kyau wllh" kallon Fatuu tay tayi mata Allah ya sanya Alkhairi ta amsa tana murmushi, nufar barin wurin Hajiya tay tana fad'in ita dai ta wuce in sun gama ganin Motar sun shigo Saude ta bi bayanta,
tana barin wurin Mino ta had'e hannuwanta ta hau yin d'an tsallen Murna tana fad'in yanzu wannan Motar ta Adda Fatuu ce, dafa Shoulder d'inta Fauzy tay suka kalli juna tace mata ta taya ta murna wllh Allah ya sanya Alkhairi ya tsare ta amsa da Amin tare da Fad'in " kema Allah ya maida ke a damshi na" Fauzy tace "Wai.....to Amin dai" duk sukai yar dariya,
"Ikon Allah, Yanzu wannan bugaggar Motar ta wannan yarinyar ce da aka raina tare da ni" Kawu Amadu ne ya fad'a yana ta tatta6a Motar don ba K'aramin tafiya tay da shi ba duk sukai dariya Tk yace "baka ji ance dare d'aya Allah kan yi Bature ba" da sauri Amadu ya jinjina kai "tabbas na shaida hakan akan yar fillo" duk suka kwashe da dariya, cikin washe baki Mino tace yakamata a d'ana su, Tk yace yanzu tunda yamma tayi kuma ga su Fatuu basu dad'e da dawowa ba a bari sai gobe tunda Weekend ne sai su zagaya gari cike da murna tace to, fitowa sukai daga cikin parking space d'in suka nufi part d'in Hajiya sai santin Motar suke ba ma kamar Amadu har Tk na fad'in ya lura dae Motar tayi mashi yace wllh ai ta had'u ba k'arya,
"kuma kasan Motar can fa zata iya yin miliyan Ashirin wllh" Tk ne ya fad'a duk suka waro ido bama kamar Fatuu sai yanzu ta gane dalilin da yasa Haisam yak'i fad'i mata kud'inta, sosae suka jinjina kud'in Motar har Amadu na rok'on Fatuu akan wai tace a canzo mata guda biyu daidai kud'in wannan sai ta bashi d'aya harda cewa shi ko ma ba mai kud'i ba tata tafi tsada don Allah duk sukai dariya lokacin suka k'araso bakin entrance suka shige, lokacin da suka shiga Hajiya na zaune akan 2 seater gabanta Sofa table ne Saude ta kawo mata bottle water da cup har ta sha Saude na zaune kan one seater daga can gefe suna hira, ciki suka k'araso kowa ya samu wuri ya zauna aka cigaba da yin hirar, bada Jimawa ba gwaggo ta shigo da sallama tana sanye da dogon hijab Navy blue da ta fito da hasken ta sosae, da murmushi ta k'araso ciki duk idanunsu na akanta Fatuu na ganinta ta mik'e da sauri ta nufeta tana ga gwaggonta, tana isa gwaggon ta tareta ta hanyar ruk'e ta tana mata murmushi, a shagwabe tace "Don Allah gwaggota ki bari in rungume ki wllh nayi missing d'in ki sosae" yar dariya gwaggo tay Fatun ta k'arasa fad'awa jikinta, d'agota tay suka nufo ciki gwaggo na yar dariya Hajiya tace "ai ni dai bansan ranar da Fateema zata girma ba wllh, ga dai girman ya kamata amman tak'i ta gane" duk akai dariya, zama gwaggo tay ta shiga gaishe da Hajiya tare da yi mata an dawo lafiya bayan sun gama gaisawa Saude da Fauzy duk suka gaishe da ita da fara'a ta amsa masu, juyowa tay ta kalli Fatuu data sak'alo hannunta ta rungumo kafad'ar gwaggo suka bi juna da murmushi,
"Gwaggo kinga Kumatun Adda Fatuu kamar an tura biredi ko" Mino ce tayi Maganar duk suka kwashe da dariya, Saude tace ma Hajiya table a shirye yake ko ta kawo Abincin nan ta d'an girgiza mata kai "ni kam dai a k'oshe nike saida muka ci muka k'oshi muka taho kuma a jirgi ma mun ci Snacks sai dai ko su Ameenatu in zasu ci k'ilan kuma uwar biyu taci don ba mamaki ta fara jin yunwa yanzu" a d'okance Mino tace "Adda Fatuu yan biyu zata Haifa" d'an yarfa hannu Hajiya tay tace "wama ya sani, in don ta Abincin da take ci ne in akace yan hud'u ma zata Haifa ai ba'a gardama ba" duk akai dariya,
"Ga shi kun zo tarbar baki mu kuma ko tsaraba ba mu yi ba" duk suka ce a'a ba komai Hajiyar ta sake cewa "ai ko ba don ku ba ma dole in nemo tsaraba kafin yaran unguwa su fara shigowa" Saude tace aikuwa kullum ne akai akai ake shigowa tambayar Hajiya ta dawo,
"Ai na sani, bari kiga asan na dawo yanzu a cika parlon anzo yi ma Hajiyar sanata sannu da zuwa" in ji Hajiya, Fatuu ce tace tana da su biscuits da chocolates a cikin kayanta da akayo gaba dasu sai a basu, tana rufe baki Hajiya tace "a'a ruk'e abun ki ban shirya ma rikicin mai juna biyu ba, yanzu in amsar maki abu kizo ki burkice man ke sai irin su kike so ni ina zan nemo maki su tunda ga Ahmad nan yaje shago ya kawo man hankalina a kwance" gaba d'aya aka sa dariya harda Fatun, mik'ewa gwaggo tay zata tafi tay ma Hajiya Allah ya huta gajiya zumbur Mino ta mik'e tana fad'in suje taga hadaddar Motar da aka Siya ma Adda Fatuu, da alamun mamaki tace Mota tayi kenan Amadu yace "Mota kam mai sunan Mota wllh" murmushin farinciki gwaggo tay kafin tayi Allah ya sanya Alkhairi ta juya kan Hajiya ta hau yin godiya Hajiyar tace "to miye na yin godiya kuma Dije don miji ya siya ma Matar shi abu, nima bansan da ita ba sai yanzu da na gani, kinsan ya samu sabbin jini ya watsar da ni" duk akai dariya Gwaggo tace aikuwa dole zai dawo mata don da tsohuwar Zuma ake Magana Hajiya ta ta6e baki tace bata so ta yafe masu shi, k'ok'arin mik'ewa tay itama tana fad'in bari ta shiga ciki Magrib ma ta kawo jiki, a tare da gwaggo duk suka fito suka nufi parking space,
Tk da Amadu ne suka bud'e mata Motar ta gani ta hau yin faffad'an murmushi Mino tace "gwaggo ya kikab ga Motar?" jinjina kai tay tace "Ma sha Allah, tayi kyau sosae wllh, Allah ubangiji yasa Alkhairi ya kuma tsare" duk suka amsa da Amin harda Fatun, Amadu ne yace ta matso ta ta6a tasa Albarka Mino harda fad'i mata kud'in da Tk yace Motar take sosae gwaggo ta jinjina kud'in, bayan ta gama gani an maida an rufe suka fito daga cikin parking space d'in Tk yay masu sallama ya nufi baya inda d'akin shi yake, Fatuu tace ma gwaggon tazo suje part d'in ta tana murmushi tace tayi mata mi tace su k'ara gaisawa sai tayi salla a can, girgiza mata kai tay tace ta dawo wani lokacin a shagwabe tace ita da ba wani zuwa take ba, magiya ta fara yi mata gwaggon tace bafa zata je ba tunda dai sun gaisa, sallama sukai da ita ta tafi tare da Amadu su kuma suka nufi part d'in su Fatuu,
A bud'e kopar parlon take, lokacin da suka shiga wani irin k'amshi mai dad'i had'e da sanyin Ac ne suka tarbe su, parlon tsab da shi yasha gyara a wurin Saude, saman L-shape suka zauna wani irin farinciki Fatuu ke ji ganin ta a parlonta sosae tay missing part d'in nata, cire veil d'inta tay ta aje gefe Fauzy ta kalli kanta tace ba dai ta son kitso Fatun ta d'an yatsina baki tace wllh kitso takura mata yake, Fauzy tace harda don yana da yawa ne gashin ga kuma tsawo, hannu takai ta dafa Shoulder d'in Mino tace "Amaryar Nameer Ali Zakee ya Angon naki halan ana ta shan love?" dariya Mino tay sai kuma ta mik'a mata wayar hannunta wadda Samsung ce, bayan ta amsa Jujjuya ta tay tana k'are mata kallo kafin tace "Amman dai tayi kyau wllh, itace Wayar da aka Siya maki d'in" tay Maganar idonta akan Mino,
d'aga mata kai tay "eh, 300k ya turo sai Kawu Amadu ya siyo man, rannan ma ya k'ara turo man 200k" d'an waro ido Fatuu tay tace "Lalle Nameer ba K'aramin ji yake da ke ba, shi da yake d'alibi yake turo maki kud'i haka, koda yake yi mashi komai ake gara shima ya fara hidiman iyalin shi" duk sukai dariya,
"K'awata ke kuma ya ake ciki tsakanin ki da Sameer ince ko an samu cigaba kun fara shan love ku ma?" Yar dariya Fauzy tay kawai ba tare data ce komai ba, hannu Fatuu ta kai ta d'an bugi shoulder d'inta tace don Allah ta fad'i mata ya ake ciki,
"To ni mi zance maki ai duk abunda ake ciki kin sani, har yanzu yadda kika sani muke muna dai gaisawa yaji ya nake shikenan" d'an jinjina kai Fatuu tay "ba komai ai anyi mai wuyar tunda kunsan juna duk ya gama nuk'u nuk'un shi zai fito ya bayyana abunda ke ran shi ne ai sannu bata hana zuwa zamu yi ta zuba mashi ido har muga gudun ruwan shi" Fauzy na dariya tace haka Aunty Mareeya ke cewa,
"Allah sarki Aunty Mareeyata itama nayi missing d'inta Sosae wllh" Fatuu ta fad'a tana murmushi, Fauzy tace "kinsan kuwa da tare da ita zamu zo Airport don har ta shirya kawai sai tayi bak'uwa amma tace in maki sannu da zuwa sai tazo har gida" Fatun tace zama ta kirata kuma zata je har gidan ba sai ta zo ba. Sai da aka kira sallar Magrib sannan suka tashi suka nufin Bedroom, Fatuu ce ta fara yo Alwala sannan Fauzy ma ta shiga, ganin har zasu kabbara Mino na zaune yasa Fatuu dakatawa tace mata ita bazata tashi tayi sallar bane tay mata murmushi kawai, tambayarta tay bata yi ne ta d'aga mata kai Fatun ta d'an ta6e baki ta kabbara, suna gama sallar Saude ta zo ta sanar dasu ga Abinci can ta kawo kan table da sauri Fatuu ta mik'e daga kan prayer mat tana fad'in "Allah yay maki Albarka Aunty Saude kamar kinsan yunwa nike ji wllh" duk sukai dariya, bayan sun cire hijabs da sukai sallar gaba d'aya suka nufi parlon. Bayan sun yi sallar isha Fauzy ta mik'e tana fad'in bari ta tafi dare yayi Fatuu tace ta tsaya ta kwana mana,
"Kwana kuma?" Fauzyn ta fad'a tana yar dariya, Fatun tace eh,
"a'a gida zan tafi abu dai ana gari d'aya miye na in kwana kuma"
Fatuu tace to ai wanda take mawa dai baya nan kuma Mino ma anan zata kwana, shiru Fauzyn tay Fatuu ta k'ara cewa "Ke Allah ma sai kin kwana, dama bakuyi man kwanan Amarya ba to shi zaki biya ni" gaba d'aya suka sa dariya,
"To ai dama yanzu Kusan so ake a kashe kwanan gidan Amarya in an kaita wasu garuruwan ma dama ba'a yi don haka ba sai na biya ba" kafewa Fatuu tay kan ta kwana tace to ai bata tambayi Aunty Mareeya ba, hannu Fatuu ta kai ta d'aukko wayarta tana fad'in abu mai sauk'i in don wannan ne bari ta tambaya ma da kanta, tana fara ringing Aunty ta d'auka,
"Yar gidana ta kaina an dawo lafiya" tana murmushi ta amsa mata da lafiya lau,
"To ya jiki jikin?" Amsa mata tayi da Alhamdulillah, tace "anata laulayi kenan halan ma har ya fito?" k'asa k'asa ta bata amsa da eh,
"ma sha Allah, Allah ya inganta mana, ai naso in zo tarbar ki wllh sai nayi bak'uwa" tace haka Fauzy ta fad'i mata ai ba komai, tambayarta tay ya mijinta yana can K'asar turawa ko tace mata eh tace to Allah ya maido shi lafiya, bayan ta amsa tace mata dama so take ta roketa don Allah Fauzy zata kwana anan, da sauri Aunty tace "kai haba ba komai Zarah ta kwana, nan gaba ma kad'an ai sai kin fini iko da ita in ta zama Matar d'an uwan mijin ki d'an Governor don ma d'an bantan uban izza ta hana ya fito ya bayyana da yanzu k'ilan Maganar aure ake tunda da gani son ta yake wllh ba don haka ba yaushe zata samu ma ya rink'a kula ta" dariya Fatuu tay tace haka Fauzy ta fad'a mata har yanzu yak'i bayyanawa, a k'ufule Aunty tace "k'yale shi yayi ya gama ai ina nan ina jiran shi ya shigo hannu sai ya rabu da wannan cutar miskilancin don shi sai yama fi mijin ki magantuwa" dariya sosae Fatuu ke yi bayan ta tsagaita tace to shima na Mino a had'a da shi da sauri tace "ahhh anya Zarah,