Showing 48001 words to 51000 words out of 512766 words

Chapter 17 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1582

jikinta sanye da fararen Uniform d'inta ta biya shi kud'in shi ya ja ya tafi tana juyawa zata nufi gida taje da d'an k'arfi ance mata "wait!" da sauri ta juyo idanunta suka sauka akan wanda yay Maganar Matashi ne kaman tsaran Kawu Amadu ko ya d'an girme mashi yana sanye da manyan kayan shadda blue harda hula tsaye tay tana kallon shi ya nufo ta a gabanta ya tsaya yana mata murmushi ita kuma ta k'ura mashi ido gani take tasan mai fuskar amman tana kokonton in shine d'in don ya canza mata sosae ganin irin kallon da take mashi ne yasa shi cewa "halan baki gane ni ba, ko sai nace Aljana sannan" waro ido Fatuu tay baki bud'e da tsananin mamaki tace "GAYE!" d'an d'aure fuska yay yana mata wani kallo yace "Point of correction, ba wannan sunan yanzu Ashiru zaki ce ko kice Malam Ashiru" k'ara bud'a baki Fatuu tay tasa hannu ta rufe baki mamaki ya gama kasheta abunda bata ta6a zaton gani ba ne take gani a gabanta shi kuwa sai faman murmushi yake don ya fahimci Al'ajabi ya hanata magana can yace tunda bazata tay mashi Magana ba bari ya tafi da sauri tace "to ai ni Gaye wllh mamaki yama hana ni yin magana wai don Allah da gaske kaine?" Yar harara ya wurga mata yace "ba nace maki ba wannan sunan ba yanzu ko so kike ki zubda ma Malam Mutunci ne" Fatuu kau mi zatay in ba Dariya harda tafa hannu ta ruk'e ha6a bin ta da kallo yay daga sama har k'asa yace "Oh su Aljana an girma nayi k'ok'ari ma dana gane ki koda yake d'azun da safe naga Amadu na tambaye shike ke yace man kina makaranta shiyasa yanzu ina ganin ki na gane kece a ina kike karatu ne?" ta fad'i mashi still da mamaki akan fuskar tata don gaba d'aya ya canza Maganar ma cikin natsuwa yake yin ta irin ta masu hankali, tambayar shi tay wai ina ya tafi ne ta daina ganinshi yace mata yana Jos,

"Kaci gaba da karatu ne?" ta tambaya yace "Eh mana, ke da ban cigaba ba Kya ganni haka na gama Nce" bud'a ido Fatuu tay tace "inyee yayi kyau gay....au Malam Ashiru, mi ka karanta ne?"

"Islamic studies kinsan d'an Malam ne ni nayi gado" Fatuu na murmushi tace da kyau ta taya shi murna Allah yasa Alkhairi ya amsa mata da Amin tace "ina Abokan ka su goga" wani kallo yay mata irin baiso tambayarba tay yar dariya tace don Allah suna ina yace duk sun yi laifi suna gidan yari Fatuu ta zaro ido tace "kace saida dai suka je gidan yarin saura kai kenan" cike da zolaya tay Maganar aikuwa ya galla mata harara yace "amman gaskiya ke mak'iyata ce yanzu Malam d'in kike ma fatan zuwa gidan yari Saboda rashin Mutunci" sosae Fatuu ke dariya tana fad'in ashe har yanzu bai daina tsoron zuwa gidan yari ba yakamata ya d'an je ko don yaci gabza shima dariyar yake yace wannan ai tata ce ita yakamata ta ci ta koda sau d'aya ne,

"Sai Mutumin ki yay aure" tambayar shi tay wa yace "Yaya Haisam na gidan Hajiya mana ai nayi zaton ke zai aura" yanayin murmushin fuskarta ne ya d'an canza tace waya fad'a mashi son ta yake da zai aureta yace "kawae yanayin yadda naga yana kula ki ya damu dake acan baya yasa nay tunanin ko yana ciki ne" d'an ta6e baki tay bata ce komai ba yace "da kin aure shi da kin more miji wllh ni tunda nike a rayuwa ta ko a labari ban taba jin mutum mai kirki irin nashi ba don kirkin nashi har ya yi yawa kinsan fa shine ya d'auki nauyin karatun da nayi bayan daya sa aka yafe mana laifin nan....." Nan ya kwashe komai tun daga ranar da suka je da mahaifin shi yin godiya ya fad'a mata yace yanzu ma da ya dawo nan aikin teaching za'a samar mashi har ma yasa ya kai ma Hajiyar Sanata takardun shi gyad'a kai Fatuu tay tace mashi ai yasan mijin wata bai auren matar wani kowa da wanda Allah ya kaddaro zai aura yace tabbas hakane tace shi yaushe zai auren ne yana dariya yace "ai bani da budurwa saidae ko in ke zaki taimaka ki aure ni" wata muguwar harara ta watsa mashi kafin tay dariya tace ai ni nafi k'arfin ka gaye ko da can ma saidai ka zama driver na sosae yake dariya yana fad'in yanzun Malam d'in ne zai zama drivern ta, ganin kaman ta gaji yace ta shiga gida ya tsayar da ita kuma yasan ta kwaso gajiya da yunwa ta tambaye shi sai yaushe yace ai ya dawo kenan don haka zai zo su sha hira tace to sai yazo yace ta gaida mashi gwaggo daga haka suka rabu,tana shiga gidan bayan ta shiga toilet ta fito ta nufi d'akin gwaggo tana zaune bata dad'e da gama cin Abinci ba don ko plate d'in bata kaiga d'aukewa ba, zama Fatuu tay akan kujera ta gaishe da ita tana murmushi ta amsa tay mata an dawo tace eh nan ta hau bata labarin Gaye cike da mamaki gwaggon tace ai ba abu mamaki ba ne Allah yana shiryar da bawan shi a lokacin da yaso duk mun munin abunda yake aikatawa da Allah yasa yana da rabon shiryuwa sai kaga ya bari shiyasa ba'a so aita hantarar mutum ana aibata shi in yana aikata ba daidai ba an fi so aja shi a jiki da fad'a da nasiha in da rabo sai kaga ya bari ya dawo kan daidai daga k'arshe ta hau yabon Haisam da Hajiya had'i da yi masu Addu'oi Fatun na amsawa tace taje ta zubo Abinci ta amsa da to saida ta d'auki plate d'in da gwaggo tay amfani ta fita.

Haisam ya fasa zuwa sakamakon d'aga bikin da zai zo da akai aka maida shi sai cikin farkon sabuwar shekara wato bayan Christmas da new year kamar yadda ya sanar da Fatuu da suna waya tace mashi Allah ya kaimu lokacin, a cikin lokacin su Fatuu sukai jarabawar kammala aji d'aya suka shiga aji biyu. Hajiya zaune a Parlor ta tasa Saude dake zaune akan Carpet gaba tun bayan data sanar mata cewa Officer ya mata Maganar yana son aurenta ta sunnar da kai ba tare da ta ce komae ba,

"Saude kin k'i cewa komae ko bakya son shi ne?" a hankali ta d'ago da alamun damuwa akan fuskar ta tace "Hajiya ba wai ban son shi bane ni gaskiya nafi son in ci gaba da aiki na" d'an murmushi Hajiya tay tace "amman Saudatu ai yin auren yafi ko kyata zama ne gashi da sauran yarintar ki ba wani tsufa kikai ba ki dai duba kema in kika yi ai Kya fi samun natsuwa" d'an mommotsa baki ta shiga yi tana kikkafta idanu Hajiya tace indai bata son shi ne karta ji komai ta fad'a mata ita tasan yadda zatai in kuma har tana son shi to tafi son ta amince mashi suyi Auren kawae sai gani Hajiya tay ta fashe mata da kuka da mamaki take kallonta tace to miye na kuka kuma ba tace in bata son shi ba ta fad'i sai ta kama kuka kaman wata k'aramar yarinya girgiza kai ta fara yi cikin kukan take fad'in "Hajiya ba wai auren shi ke banson yi ba nasan aure rufin asirin mace ne ni kawae har ga Allah ban son rabuwa da ke ne shiyasa tun farko da yay man Maganar tun ba yanzu ba na nuna mashi yay hakuri kawae tunda nasan k'arshen ta garinsu zai kai ni ya had'a ni da d'ayar matar shi" yar dariyar jin dad'i Hajiya tay tace "nima ba don dole ba Saude ai bazan so rabuwa dake ba to amman hakan bazai sa in so kaina ba in hana ki yin abunda yakamata ba kuma shi Officern ma yace ke a nan zai sama maki gida ya ajiye ki wannan sai ya daina damun ki" cikin muryar kuka tace "to aikin fa zan ci gaba ko?" dariyar dai Hajiya ke yi ta lura dae da gaske bata son barin gidan can taji tace "to ko ku zauna anan?" Ba shiri da sauri Saude ta kalleta don bata tsammaci jin hakan ba Hajiya taci gaba "in dai kuna so tunda ga d'akuna nan biyu a kusa da na Tukur sai kuyi amfani da su kawae" Saude tace "to Hajiya ba matsala kuwa?" tana dariya tace "Wace matsala kuma ba wata matsala in dae wurin yayi maku ai sai kuyi zaman ku kici gaba da zama da Hajiya kafin mai rabawa kuma ta raba" shiru Sauden tay don Maganar Hajiyar ta k'arshe ta kashe mata jiki kuma dai abune da ya zama dole ko ba dad'e ko ba jima saidae fatan dacewar Ubangiji, ganin tayi shiru yasa Hajiyar cewa shikenan ko tace mashi ya tura Daura Sauden ta jinjina mata kai had'i da sadda shi k'asa alamar kunya Hajiya nata dariya tana fad'in to miye abun jin kunya.....

Ba yawa but manage it pls😔




_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2042*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*




.........A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah har anyi New year su Fatuu sun dawo daga Hutu sun cigaba da karatu, Ranar Monday misalin k'arfe biyu saura suka dawo daga Area d'in class an tashi zasu tafi Hostel da yake yanzu Fatuu tana d'an yawan zama a Makarantar sai Weekend ta koma gida wani lokacin ma a Makarantar suke weekend d'in kaman Asabar sai lahadi ta je gida, tafe suke kowanne yana rataye da jakar shi Fauzy sai faman rangaji take ta d'aura kan ta saman shoulder d'in Fatuu can tace mata "Wai Fauzy so kike ki sauke man kafad'a ne, duk kin bi kin sakar man nauyi" a marairaice Fauzy tace "wllh Zarah wata irin yunwa nike ji baki ji ba gashi bak'in cikina in mun koma Hostel d'in ma dole sai mun dafa" yar dariya Fatuu tay tace "to ba sai ki nemi emergency food ki fara ci ba" yamutsa fuska Fauzy tay tace "irin yunwar da nike ji wannan bazasu rike ni ba kin san fa bamu yi break ba Saboda discussion d'in da muka yi just d'an biscuit muka ci" Fatuu tace to ta d'aga mata kafad'a ko sun yi sauri suje suyi girkin, jin haka yasa Fauzy d'agowa tana kallon Fatuu tace "Gaskia Zarah yakamata kiyi saurayi ko don irin haka kinga da yanzu kawae sai kisa ai mana take away ba 6ata lokaci" Fatuu na dariya tace "to kema kiyi saurayin mana" yar harararta tay tace ai ita ta gama yin saurayi har abada yanzu karatun ta ne saurayinta in ta gama kuma aikinta ne zai zama mijinta Fatuu sai dariya take tace ai shikenan sai suyi ta zama ba samarin tunda haka suka za6a Fauzy ta fara mata magiyar don Allah ta fara saurar su tunda ana cewa ana sonta, d'an ta6e baki tay tace "kema ai ana cewa ana son kin ko don da wuya mu fita wani bai mana Magana ba ji wannan da ya maki Magana a Mall kika k'i saurarar shi da gani d'an gayun mai kud'i ne ga Motar shi had'add'a" yamutsa fuska tay tace "k'yale wad'annan masu Motocin duk mayaudara ne" yar dariya Fatuu tay daidai lokacin suka iso wurin Admin Fauzy ta kai idonta daga gefen wurin parking space d'in Malamai kaman daga sama Fatuu taji tace "Wow ji wata zazzafar Mota can kalar su Yaya Haisam" da sauri Fatuu ta kalli direction d'in idanunta suka sauka akan Motar kalar army green da sai faman d'aukar ido take da gani sabuwa ce kuma da gaske ta had'u ba k'arya d'an murmushi Fatuu tay ta juya tana fad'in wato kalar su Ya Haisam ce kenan Fauzy tace "Eh mana ai ko wacce kalar mota da kalar irin mutanen da ke hawanta waccan ko ban fad'a ba kinsan kalar shi ce inama ace shine tun da kince wannan Month d'in zai zo" wani kallo Fatuu tay mata tace "da yake daga Funtua yake zamu gan shi kwatsam ko" dariya sukai su duka suna niyyar wuce saitin Motar suka ji an latsa horn Fauzy ta d'an juya ta kalli Motar sai kuma ta maida idon kan hanya tana fad'in "Zarah ko dae kin yi kasuwa ne" ta6e baki kawae Fatuu tay suna k'ara taku aka k'ara yin horn d'in Fauzy tace Allah da gaske kodae dasu ake Fatun tace da yake su kad'ai ne a wurin ko wannan Maganar tasa Fauzy yin tunanin k'ilan bada su ake ba suka cigaba da tafiya wayar Fatuu suka ji ta fara ringing ta kai hannu cikin pocket d'in rigar uniform d'inta ta fiddo ta tana kallon screen d'in taga sunan Ya Haisam ya bayyana da d'an mamaki tace "Fauzy da alama Ya Haisam yaji kin yi Maganar shi" kai idonta Fauzy tay kan wayar da d'an mamaki take tambayar ta shine ya kira Fatuu ta d'aga mata kai itama tana kokarin yin picking, bayan ta d'aga tun kafin tay magana taji yace bata ji yana mata horn bane ba shiri ta kai idonta akan Motar da tsananin Al'ajabi take kallonta yana fad'in hakan yay cutting kiran Fauzy da itama ta kalli in da Fatun ke kallo ta juya tace mata ya akai ne with surprise written ol over her face ta fad'i mata abunda yace waro ido Fauzy tay with mouth agape ta sake kallon Motar kafin tace "kenan shine??" Kai Fatuu ta d'aga mata alamar eh sosae itama Fauzyn tay mamaki wani irin arashi ne haka ita tayi Maganar ta duk don ay raha sai gashi ta tabbata kama hannun Fatun tay tace suje, a gaban driver side suka tsaya idonsu akan glass d'in duk da basu ganin shi slowly glass d'in ya fara sauka k'asa har fuskar Haisam d'in ta bayyana, zuba mashi ido su kai su duka yana sanye da riga turtle neck army green irin rigar nan mai kaman ta sanyi wadda ake nad'e wuyanta tana da dogon hannu kuma dama har lokacin akwae yanayin sanyi sai bak'in Jeans har k'iba taga ya d'an k'ara don fuskar shi ta k'ara cikowa ga sajen da ya bari sumar ta d'an k'ara yawa yanzu kwance luff da k'yar Fauzy tay murmushin yak'e tace "Ya Haisam ina wuni an zo lafiya" jinjina mata kai yay kafin cikin cool voice d'in shi ya amsa mata da Alhamdulillah ta k'ara ce mashi ya Aunty Fanan yace tana lafiya juyawa tay ta kalli Fatuu jin bata ce komae ganin ta zuba ma Haisam d'in ido yasa tay d'an murmushi ta kai hannu tace ta kawo jakar bari taje ta yi masu Abincin bayan ta amsa ta juya tace ma Haisam sai anjima ya d'aga mata kai, sam Fatuu ta kasa bud'e baki ta tanka mashi Saboda mamaki don ko jiya sunyi waya fa amman bai ce mata yau zai zo ba ga wani irin bugu da k'irjinta ke yi tunda tay tozali dashi, ganin irin kallon da yake mata ne yasa tay k'arfin halin cewa "an zo lafiya" still bin ta da ido yay dama ya jingina kanshi da headrest kaman bazai ce komai ba can taji yace ta shigo cikin Motar jiki a sa6ule ta zagaya d'ayan side d'in ta bud'e kopar gaba ta shiga har saida ta d'an lumshe ido bayan ta rufe kopar ta juya suka had'a ido ta sake gaida shi had'i da yi mashi an zo lpy sai lokacin ya amsa mata da lafiya suka d'an yi shiru tana kallon glass d'in gaba shi kuma yanata kallonta ta cikin mirror can ta juya ta kalle shi shima ya juyo suka had'a ido tace "ashe yau zaka zo amman baka fad'a man ba kuma ko jiya mun yi waya" d'an murmushi yay calmly yace "komae sai an fad'a ne?" d'an tura baki tay ta sadda kan ta k'asa taji ya k'ara cewa ko yayi laifi ne da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a ba tare data d'ago ba suka d'an yi shiru can ta ji yace mata ya School sai lokacin ta d'ago tace mashi lpy Lou ta tambaye shi Aunty Fanan yace tana Lagos shima daga can yake Fatun ta d'aga kai suka k'ara yin shiru can ya kai hannu yana kokarin tashin motar ta juya ta kalle shi batare da ya kalleta ba taji yace su je a samo masu Abinci bata ce komae ba ta d'an juyar da kanta gefe had'i da yin murmushi ta ayyana Ya Haisam ba dae sanin yakamata ba, saida suka fita daga cikin Makarantar ta tuno da girkin da Fauzy zata masu ta ayyana yakamata ta kirata tace ta bashshi dama wayar na akan cinyoyinta ta d'auka ta fara kiranta bugu d'aya ta d'auka tace "love birds ya ana nan anata soyewa?" d'an murmushi Fatuu tay bata ce mata komae ba gudun kar tay wata Maganar yasa ta tambayeta ta d'aura Abincin ne tace a'a biscuit da Madara ta fara sha don bata iya jurewa har sai ta gama amman gashi yanzu zata d'auran Fatun tace mata ta bar shi gashi za'a siyo wata k'arar murna Fauzy tay tace "Allah maji kan bawa muma ga saurayin zai mana take away" yar dariya kawae Fatuu tay Fauzyn tace "in fad'a maki abunda nike so" tace mata eh, harda su gyara murya ta fara zayyano mata shawarma,pizza,farfesun yan ciki, sakwara......, saida ta fad'i abu ya kai goma cike da mugunta Fatuu tasa speaker tace mata bata ji abubuwan da ta lissafa tana so ba muryar na yankewa ta sake fad'i mata ba tare da ta sani ba ta hau

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login