Showing 147001 words to 150000 words out of 512766 words
Chapter 50 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1662
Haulat ma tazo nan aka fara shirin d'aura girki duk da ba wani abu za'ai ba miyar waina ce da sinasar da ta bada ayo mata sai Fried rice itama Aunty Mareeya ta amsa zata bada ayo harda su coleslaw, bayan an d'aura miyar aka fara had'a kunun Aya da zobo lokacin wasu daga cikin Abokan aikin gwaggon suka zo har an taho da su dublan d'in data bada aikin su nan aka cigaba da hidima, lokacin da su Fatuu suka dawo wurin k'arfe d'aya saura mutane sun d'an taru a gidan ba laifi harda Zaliha d'iyar kishiyar gwaggon da iyalanta da kuma iyalan baba shehu suna shigowa aka hau ce ma Fatuu Amarya Amarya ita dae d'an murmushi kawae take tana gaishe dasu suka wuce d'aki, suna shiga Fatuu ta nufi gado ta zauna dabar Fauzy dake k'ok'arin cire Hijab tace ba zama yakamata tay ba ta tashi taje tay wanka ta shirya kar aita ganin Amarya kamar an koro ta kallo kawae ta bita dashi bata da niyyar mik'ewa, suna haka gwaggo ta shigo ruk'e da plate d'in Abinci da kuma na sobo da kunun aya ta aje masu akan Carpet tace gashi nan su ci in sun gama taje tay wanka ta d'aga mata kai, bayan sun fara ci bata ci wani mai yawa ba ta cire hannunta Fauzy na tambayar ta badae har ta k'oshi ba tace eh rarrashin ta ta shiga yi kan ta k'ara tace mata bata jin dad'in bakin ta ne dole ta rabu da ita tace to taje tayo wankan, bayan tayo wankan itama Fauzy taje tayi suka fara shiryawa doguwar rigar shadda ta fiddo mata a cikin kayan da Hajiya ta aiko ta taimaka mata ta d'an yi make up ta koma saman gado ta zauna Fauzy ma ta hau shiryawa lokacin Haulat ma tazo bayan ta gaisa da gwaggo ta bata gudunmawar data kawo tana ta godiya ta koma d'akin Fatuu, a bakin gado ta zauna ganin yanayin ta yasa ta hau tambayarta lafiya ita da za'a gani tana farinciki Fauzy na yar dariya tace fargaba ce itama Haulat dariyar tayi.
Ana gama sallar Juma'a su Feenah suka iso sun ci gayu Abdul harda babbar riga tunda bai sa yaje daurin aure ba yasa yazo tarewa, harda katan katan d'in lemu da ruwa suka kawo da kwalin Warmers masu kyau harda na had'addan glass jug ga kuma kud'i gwaggo tay murna sosae sai godiya take, daga baya ta koma d'akin Fatuu tana zaune saman gado ta rungume Abdul da tunda suka shigo gidan ya nufi d'akin, bakin gadon Feenah ta zauna ta kalli Fatun da murmushi tace "Amaryar mu kin sha kyau" d'an murmushi kawai tay ta gaishe da ita aka kawo masu Abinci, su Feenah basu dad'e da zuwa ba Aunty Mareeya ta iso tare da k'atuwar kular Fried rice da trays d'in coleslaw anyi sealing, su Amadu ne suka shigo da su tare da Tk da wani abokin su ita kuma suka kamo k'aton kwalin kayan k'amshi ita da Maman taufiq makwabciyar ta da suka taho tare, gwaggo tay farinciki sosae har ta kasa rufe baki sai faman godiya take tana shi Albarka daga baya wasu daga cikin k'awayen su na makaranta da Fauzy ta gayyata suka zo ciki harda Zainab Muhammadu da wadda zatayi ma Fatuu make up dama sana'ar ta ce ba 6ata lokaci aka fara yi mata, lokacin da aka gama baka jin komai sai Tubarkallah da kowa ke fad'a don ba k'aramin kyau kwalliyar tay mata ba ba kamar da yake ba'a ta6a yi mata irin ta ba,nan fa aka shiga yi mata hotuna daga baya aka sa ta canza kaya tasa lace shima akai mata hotunan, haka aka ci gaba da hidima aka ci aka sha abun sai godiyar Allah, Bayan sallar la'asar Haisam na Zaune a Bedroom d'in shi na G.r.a tare da Abbas da Saleem da yasan da zancen auren daga baya Najeeb dae bai sani ba don bai K'asar yana Canada, basu dad'e da gama cin Abinci ba da Abbas ya kawo daga gidan Hajiya don anan ya iske su bayan ya kai su Feenah, gaba d'ayan su kowa na ruk'e da wayar shi yana latsawa jefi jefi suke yin Magana, can Abbas ya mik'e daga kan kujerar da yake ya nufi Haisam dake kishingid'e jikin shi sanye da ash d'in shadda ya zauna daga gefen shi yana fad'in "gafa Amaryar ka ta fito ma sha Allah" d'aga ido yay ya kalli wayar, Abbas yaci gaba da bud'e mashi sauran dama Feenah ce ta d'aura su a status
har saida suka k'are sannan Haisam d'in ya janye idon shi ba tare da yace komai ba, Abbas ya mik'e ya nufi Saleem dake sanye da farar shadda yana latsa waya shima ya shiga nuna mashi d'an guntun murmushi yay cikin cool voice d'in shi tamkar Haisam yace wai yarinyar nan ce har ta girma Abbas na dariya yace mashi eh mana gashi ma har ta d'auke nauyin H,zakee Haisam din na jin shi bai ko kalle su ba Saleem d'in ya k'ara yin d'an guntun murmushi kawai, suna nan har aka yi sallar Magrib suka tafi Masallaci suna can har akai isha ana gamawa Hajiya ta kira Abbas tace mashi ya taho suje su d'aukko Fateema yace to bayan sun gama ya kira Feenah ya tambaye ta akwae Mutane ne da yawa tace mashi ba laifi, Saleem yay ma Magana da yake da Jeep ya zo kan suje su d'aukke su yace ok, kallon Haisam Abbas yayy yana murmushi yace ya taso suje ya d'an girgiza mashi kai alamar ba zai je ba ya juya yace ma Saleem su je ya mik'e har zasu tafi Haisam ya dakatar dasu Abbas ya juyo yana kallon shi ya mik'e yace yana zuwa, dressing mirror ya nufa ya jawo drawer chest ta tsakiya ya fiddo wani makulli, bayan ya rufe ya dawo wurin su ya mik'a ma Abbas yace yay amfani da Motar duba makullin yay ya d'ago da d'an bud'a ido yace "Lalle kana ji da Amaryar nan a Jeep d'in Dad d'in za'a d'auketa" shiru yay mashi ya nufi komawa kan kujera yace ma Saleem suje suka nufi hanyar fita daga Bedroom d'in, Bayan Hajiya ta kira Abbas tay mashi Magana ta kira gwaggo tace mata a shirya Fateema za'a zo a d'auketa tace to, d'akin ta ta nufa su Aunty Mareeya da Feenah da sauran k'awayenta duk suna ciki anata hira Aunty Mareeya sai basu dariya take gwaggo ta shiga ta sanar dasu, wani irin bugu k'irjin Fatuu yay gabanta yaci gaba da Fad'uwa Aunty Mareeya kau harda gud'a ta rafka ta mik'e tana fad'in Fatuu ta tashi ta canza kaya, Wani farin dankareren lace mai adon golden cikin kayan da aka kawo mata ta fiddo mata da gyalen shi golden da takalman shi half cover masu tsini suma golden harda purse d'in su dama barin su akai sai za'a kaita ta saka su, ba 6ata lokaci aka gama shiryata abun saidae ace Tubarkallah tayi kyau har ta gaji sai yi mata hotuna ake ba'a dad'e da gama shiryata ba Hajiya da Saude suka zo Hajiya na fadin gasu sun zo biko tana sanye da lifaya Saude ma tasha doguwar rigar lace da mayafi, nan aka shiga gaishe gaishe Gwaggo tace ma Hajiyar su shiga tace a'a basai sun shiga ba dare nayi a fiddo ta su tafi tace to ta nufi d'akin, tunda taji zancen an zo tafiya da ita ta saka kuka da duk ganin abun take kaman wasa sai yanzu ta tabbatar gaske ne, nan aka shiga rarrashin ta Aunty Mareeya data ruk'ota cike da zolaya take ce mata waya fad'i mata amare na kuka yanzu k'auyanci ne, bayan sun fito aka kaita gaban Hajiya dake tsaye tana jira tace akaita Mota duk aka firfita ta kalli gwaggo dake tsaye jikinta duk yayi sanyi tace itama tazo aje da ita ta rakata d'akinta tace to ta juya don d'aukko Hijab bayan ta dawo suka fita tare da Hajiya.............
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2061*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.......bayan su Aunty Mareeya sun fito saida suka koma part d'in Hajiya suka k'ara yi mata Allah yasa Alkhairi sannan sukai mata sallama tana ta godiya duk aka fito harda su inna Zaliha da tun d'azu suka so tafiya Hajiya tace su bari za'a maida su gwaggo ta biyo su tace suje gida don Allah zata basu kayan biki, Motar Saleem Abbas yace su Aunty Mareeya da Feenah su shiga gwaggo ma ta shiga shi kuma ya d'auki su inna Zaliha da iyalan baba shehu sai wasu abokan aikin gwaggo da suka rage su biyu, a daidai kopar gidan su Fatuu suka tsaya gwaggon ta shiga ta d'ebo ma kowannensu su cin cin harda man shanu, bayan ta kawo masu suka yi sallama tana ta godiya tace ma Fauzy saura ta daina ganin ta tunda k'awar ta ta bar gidan tana yar dariya tace a'a zata rink'a zuwa har weekend ma zata rink'a zuwan mata, sosae gwaggo taji dad'i tace to Allah ya bada iko suka tafi tana ta k'ara godiya tare da d'aga masu hannu, saida sukai nisa sannan ta koma ta kullo gidan ta nufi gidan Hajiya don bata yi mata sallama ba ta taho, tana tafiya tana tunanin autar ta sai murmushi take wani lokacin ta d'an girgiza kai, har ta fara jin kewar ta tana son ta gan ta saidae ba dama don bazata iya zuwa part d'in ba a yanzu.
Feenah aka fara ajewa gida don tafi kusa tay ma Saleem d'in godiya sukai sallama dasu Aunty Mareeya har tana fad'in taga gida zasu rink'a zumunci in sha Allahu tace to shikenan ta gode, dama sun yi musayar lambar waya tun a gidan su Fatuu kafin akai ta, daga nan Goriba road suka nufa aka kai Aunty Mareeya, bayan ta nuna mashi gidan ya parker tay mashi godiya ya jinjina mata kai ba tare da ya ce komae ba ta bud'e kopar ta fita Fauzy dake a gaba ma ta fito bayan sun rufe mashi kopopin yaja ya tafi, tsaye Aunty Mareeya tay baki bud'e tabi bayan Motar da kallo kafin tace "da alama shima wannan lalurar gare shi" kallon bayan Motar da har tayi nisa Fauzy tay kafin ta juyo ta kalli Aunty Mareeya cikin rashin fahimta ta tambayi wace irin lalura gare shi, tace "irin ta mijin Zarah mana, daga gani shima miskili ne na gaske" yar dariya Fauzy tay "na lura da hakan don ko d'azun da za'a kai Zarah da muka hau Motar shi bai ce ma kowa uffan ba sai d'an Music da ya kunna sama sama" Aunty Mareeya dake kallon ta tace "da gani dai wani shege ne ko kuma d'an wani shegen shiyasa harda rufe lambar Mota, baice yana son ki ba?" ta kafe Fauzy da ido alamar jiran amsa, dariya Fauzy tay "taya zai ce yana sona na fad'i maki tunda muka hau Motar shi bai ce mana uffan ba, kema ba gashi kin gani ba har kin fad'a" k'wafa tay tace "Allah ya yabawa aya zak'in ta, ai da ya sake yace yana son ki har abun ya kai ga aure da an taimaka mashi an sashi ya rink'a magana shima yadda za'a sa abokin shi, Allah sarki Zarah...." Murmushi tay kawae bata ida abunda zata ce ba ta nufi gate Fauzy tabi bayanta acikin ranta tana tuna k'awarta Fatuu dama tunda suka baro ta ta tsaya mata a rai, a yanzu kuwa sai taji ta fara sha'awar yin aure itama.
Gwaggo na isa part d'in Hajiya a parlor ta same su kaman yadda ta barsu ita da Saude sai dae ita Sauden tana kitchen tana yin girki musamman don su Fatuu kaman yadda Hajiya ta bata umarni, zama gwaggon tay Hajiya tace har ta sallame su tace mata eh suka d'an ci gaba da yin hira suna kallo, can gwaggo tace bari ta tafi sai Allah ya kaimu ta k'ara yi mata godiya da Addu'oi, tana k'ok'arin mik'ewa Hajiya tace ta tsaya zasu je wurin Zarah yanzu sai suje tare tasan dae bata rasa mararin son ganin ta, cike da Zolaya tay Maganar gwaggo dai d'an murmushi kawai tay ta sadda kai, bada jimawa ba Saude ta shigo cikin parlon hannunta ruk'e da wani had'add'an basket mai d'auke da k'awatattun Warmers, a gefen kujera ta tsaya cike da girmamawa tace ma Hajiya an gama, kokarin mik'ewa ta fara yi tace ma gwaggo suje itama ta mik'e, har zasu tafi tace ma Saude taje saman gadon ta towels na nan da aka manta ba'a saka mata a kaya ba ta d'aukko a kai mata tace to, bayan ta dawo ta d'auki basket d'in d'ayan hannun rungume da towels d'in da ta d'aukko suka tafi. Tun bayan da su Fauzy suka tafi ta kife fuska tana kuka sai da ta d'an d'auki lokaci a haka sannan ta d'ago idanunta duk kwalla tay zuru tana d'an kalle kallen d'akin, can ta kai hannu ta cikin ledan da Aunty Mareeya ta bata ta fiddo abun da ke ciki, bata gane ko miye ba saida tasa d'ayan hannun ta bud'e sannan ta ga ashe rigar bacci ce orange colour ta dai had'u ba karya yadin ta gwanin santsi irin mai bin jiki d'in nan kuma bazata wuce guiwa ba tana da d'an fingilallan pant mak'ale a jikinta, ajeta tay gefe ta zazzago sauran da ke ciki guda biyu, d'aya baby pink ce shara shara wannan da k'yar ta wuce mazaunan mutum irin wadda in aka sa a naked za'a ga mutum har saida Fatuu ta d'an bud'a ido ganin rigar, d'ayar ta karshe cream ce yadinta cotton ne mai dad'in tabawa gwanin taushi daga wurin wuyanta da k'arshen hannun ta da zai iya wuce guiwar hannu duk gashi gashi ne gazar gazar yana d'an walwali harda ribbom gareta, itama tana da pant sai dai gabanta a bud'e yake kawai yan igiyoyi gareta wuri ukku da zaka daure, har saida Fatuu ta d'an sauke ajiyar zuciya fuskarta a d'an kwa6e take bin rigunan da kallo ita kam bata jin zata iya amfani dasu a yanzu gani take zai iya mata kallon mara kunya, maida su tay cikin ledan ta d'an yi jimm can kuma ta mik'e ta nufi wardrobe don ta 6oye su a ciki, saidai duk yadda tay ta bud'e wardrobe d'in ta kasa ta rasa ta ya ake bud'eta don bata ga wani handle da zaka kama ka bud'e ba a jikinta, k'arshe d'aya daga cikin jakunkunan ta dake a gefen wardrobe d'in ta duk'a ta bud'e, a can k'asa ta tura ledan bayan ta rufe ta mik'e, a gaban dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta, ita kan ta taga had'uwar da tayi don lace d'in ba k'aramin had'uwa yayi ba kuma ko ba'a fad'a ba da ka kalle shi zaka gane ba mai k'ananun kud'i bane, ga sark'a da yan hannun ta suma tamkar gold sun yi ma hannunta da ya sha k'unshi kyau ba kad'an ba, zuciyarta ce ta fara hasasho mata Haisam tsaye a bayanta har bata san lokacin da ta d'an yi murmushi ba, bayan ta gama kallon kan nata juyawa tay jiki a sanyaye ta koma bakin gadon ta zauna ta jingina da headboard, bada jimawa ba aka turo kopar ta kai idonta da sauri kan mai shigowar, Saude ce ta fara shigowa suka had'a ido tay ma Fatun murmushi itama tana niyyar mayar mata Gwaggo ta shigo aikuwa zumbur tay ta mik'e da sauri gudu gudu ta nufo kopar tana zuwa ta fad'a jikinta ta fashe da kuka lokacin Hajiya ma ta shigo tana dogara sandar ta idanun ta sanye da glasses har lokacin lifaya d'in ce nad'e a jikinta, sosae ta k'ank'ame gwaggon sai kace zata shige cikin jikinta sai faman kuka take har kallabinta ya fad'i haka gyalen ma ya zamo daga saman kan ta gashinta da ya sha gyara baki wuluk sai salk'i yake an yi parking d'in shi ya bayyana, har cikin ran gwaggo take jin kukan hakan ya karya mata zuciya daurewa kawai take tasa hannu guda ta d'an dafa bayan ta,
"To wannan kukan shagwa6a ne ko na me, sai kace wadda zaku rabu kwata kwata, duka yaushe kika baro gidan kuma gashi har kin gan ta to miye abun kuka Fateema" Hajiya dake tsaye gefe tay Maganar Saude nata kallon su gwanin ban tausayi, d'ago da ita Gwaggo tay suka had'a ido Fuskar ta duk tayi jage jage da hawaye a sanyaye tace mata ya isa hakanan ta kamata suka nufi gado ta zaunar da ita, Hajiya ta kalli Saude tace ta kai towels d'in saman jakunkunan dake gefen Wardrobe in ta tashi ta canza masu wuri tace to, tsaye gwaggo tay a gaban Fatun tana d'an murmushi Hajiya ma ta maido idon ta kan Fatun tace "Fuskar Amarya duk tayi jage jage haka, kar kija Angon naki yazo yay tunanin wani abun mukai maki ya d'auki mataki a kan mu" cike da zolaya tay Maganar Fatun ta sunkuyar da kan ta k'asa,
"Amman Dije ya akai aka bar mata kai haka ba'ai kitso ba" Hajiya dake kallon kan Fatun ta fad'a, gwaggon tace "Wllh naso ai mata shafa'a nayi gashi yau anata hidima ban ko tuna ba" jinjina kai tay tace "shikenan bari in Allah ya kaimu gobe sai a kira Balaraba tazo tay mata" gwaggo tace to cike da girmamawa, sake kallon Fatuu tay "Fateema ga Abinci can a saman Dining table in zaki ci in kuma zaki jira Angon naki ne sai ku ci tare dama can baya ke kike sa shi yaci da yawa yanzu ma sai ki dasa don har yanzu ba wani cin Abincin kirki yake ba" gaba