Showing 360001 words to 363000 words out of 512766 words

Chapter 121 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1554

mata oyoyo, amsar ledojin suka yi ta dafa Shoulder d'in iman suka nufi cikin parlon idon Aunty a kan su tana ta washe baki, a kusa da ita ta zauna tace "yan tafiya an dawo?" Fauzyn ta d'aga mata kai,

"Amman wai tun da kuka fitan kuna government House d'in?" Kai ta d'an girgiza mata ta fad'i mata duk inda suka je, tambayar ina Sameer d'in tayi tace ya tafi kafin ta d'aga kai, hannu Aunty ta kai ta d'aukko jakar kwalin da ta ja hankalinta tace miye aciki Fauzy tace bata sani ba First Lady ce ta bata, bud'e ta Aunty tayi ta kai hannu ta fara fiddo abubuwan ciki, turare na guda ukku iya kwalin su abun kallo ne sai miski a yar babbar kwalba mai kyau tun ba'a fiddo turarurrukan daga cikin kwalin su ba har k'amshin su mai dad'i ya karad'e wurin, sosae Aunty ta yaba bayan ta maida su cikin jakar ta tambayi yadda suka kar6eta ta fad'i mata hakan ma taji dad'i sosae harda 6akar Fauzy a kafad'a tana fad'in ta dai zama dangin gwabnoni ita dai yar dariya tayi, tambayarta yadda Fatuu take ta k'ara yi tace halan tana nan tana ta ja tace mata eh, kallon ledojin tayi da yake akwae tambarin wurin da aka siyo kayan ciki tana dariya tace daga ziyarar chilling kenan suka wuce still Fauzy murmushi kawai tayi, fara janyo ledojin tayi su Hanif na Mik'o mata sauran ta shiga bubbud'a su, tarkacen su ice cream ne flavour daban daban dasu yoghurt sai su shawarma da pizza abubuwa dai kala kala kili guda tana cikin dubawa tace "ashe su suriki na ba iya kud'i aka iya badawa ba" tambayar Fauzy tayi cikin wurin suka shiga aka siyo tace a'a ta fad'i mata kawo masu akai tace ai dama ta d'an ji mamakin ace shiga sukai dashi aka siya, Hanif ne ya d'auki ice cream yace ma Aunty ya sha tace na Aunty Excellency ne ya tambayeta Fauzy ta d'an yamutsa fuska tace "kai Aunty don Allah" tana dariya tace tuba take, babbasu komai tayi kowa ya natsu suka fara ci itama ta d'auki shawarma tana ci, kallon Fauzy data jingina da kujera tayi shiru Aunty tayi tace "wai lafiya Fauziyya, na lura kamar akwai abunda ke damun ki tun bayan da kika shigo kin k'i sakin jiki sosae" d'an ta6e baki Fauzy tay ta furta "uhmm" dakatawa Aunty tayi da cin abun da take gaba d'aya ta maida hankalin ta kanta tace mata ya akai ne, ajiyar zuciya tayi ta fara motsa baki kafin ta shiga bata labarin yadda sukai da Sameer na tambayar da tayi mashi kan dalilin daya sa zai aure ta da amsar daya bata har zuwa yadda suka rabu,

"Ni Aunty ina ganin kaman yayi fushi" shiru Aunty ta d'an yi can tayi yar ajiyar zuciya ta dafa Shoulder d'inta tace "ba lalle ba, in dai da gaske yana da ilimin Addini to bazai ji komai ba tunda yasan gaskiya kika fad'i sai ma dai yaji dad'in hakan tunda ya gane wace kalar mata zai aura, kuma fa tana iya yuwuwa ma gwada ki yake kinsan Mutane in suna abunda suka san ba daidai ba to basu son su Auri mace mai hakan don haka karma ki wani damu wllh" kai kawai Fauzy ta jinjina amman ita tasan ba wani gwadata da yayi Saboda abubuwan da yayi mata, daga baya sakin jiki tayi suka cigaba da cin abubuwan anan Aunty ta ce yakamata ta sa yazo yayi breakfast gobe Fauzyn tace anya zai zo don yace gobe zai tafi amman dai zatayi mashi magana. Bayan ta koma d'aki a bakin gado ta zauna ta shiga tunanin ko ta kira shi saidai tana jin d'ar d'ar can dai tay k'arfin halin kiran nashi, har ta yanke bai d'auka ba ta ruk'e wayar tana dakon kiran shi kamar yadda suka saba bada jimawa ba kuwa sai gashi ya kira d'in har saida tayi murmushi taji d'an sanyi a ranta, bayan ya d'auka ya ya koma tayi mashi ya amsa mata daga haka suka yi shiru can taji yace da wani abu tace mashi eh dama Aunty d'in ta ce tace tayi mashi magana yazo da safe don Allah yayi breakfast, ce mata yay bazai samu zuwa ba don Flight d'in safe zai bi tace to tayi mashi saida safe itama yayi mata, bin wayar tayi da kallo tama rasa tunanin da zata yi jikinta ya d'an yi sanyi can dai ta mik'e don tayi shirin kwanciya...........

93

_ASM BY ZAINAB BATURE _



~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~


.......Washe gari bayan Fauzy taje School Zainab nata son yi mata magana sai dai bata samu damar hakan ba don tana zuwa malamin su ya shigo, saida akayi break sannan tazo seat d'in su da yake yanzu basu fita break Saboda nauyin da Fatuu tayi ita ke zuwa masu da Abinci to yau itama Fauzy tazo masu da shi, zama Zainab d'in tayi a saman desk suna cikin cin Abinci ta fara jero mata tambayoyin yadda akai suka san juna da Sameer shida ko kallon mutane ba yayi, sosae ta rink'a basu dariya yarda ta hak'ik'ance tana fad'in an cuceta, har aka dawo break bata k'yale su ba k'arshe tare dasu tayi break d'in, Fauzy nata so taba Fatuu turaren data kawo mata cikin wanda aka bata amman Saboda Zainab d'in ta k'i fiddo shi don tasan tabbas sai tace a bata shi kuma ita Fatun take son tayi amfani da shi, saida aka tashi sannan ta bata, tare Tk ya d'aukesu saida aka aje Fauzy gida har Fatuu ta shiga tayo fitsari sannan ta fito Fauzy ta rakota suka tafi. Bayan sallar Juma'a wuraren k'arfe ukku na rana Fauzy tayi wanka tayi kwalliyar Juma'a lokacin tuni sunyi waya da Sameer har ya koma, tana zaune a cikin d'akinta tana chat wayarta ta fara yin ringing, bin bak'uwar lambar da aka kira tayi da kallo kafin ta d'auka a nutse tayi sallama, bayan mai kiran ya amsa cikin girmamawa ya gaishe da ita da alamun mamaki akan fuskar ta ta amsa yace dama sak'o ne ya kawo mata yana waje, d'an jimm tay kafin ta amsa da to gata nan fitowa, bin wayar tay da kallo bayan ta cire a ranta ta shiga raya to waye wannan kuma wane sak'o ne ya kawo mata, mik'ewa tay saida ta d'aukko gyale ta d'aura akan gown d'in jikinta sannan ta tafi, lokacin data shigo cikin parlon ba kowa ta nufi hanyar fita, yana tsaye a gaban bak'ar Mota yana ganinta ya shiga washe baki kallo d'aya Fauzy tayi mashi ta gane shi, k'arasawa tayi fuskar ta adan sake suka k'ara gaisawa,

"Yauwa dama sako ne Yalla6ai ya bada akawo maki, Wannan Motar ce yace in kawo maki taki ce sannan ni zan rink'a kai ki Makaranta sannan yace in fara koya maki Motar in kika iya sai kici gaba da zuwa Makarantar" tunda ya fara Maganar tay sototo tana kallon shi har ya gama, ba don tasan yasanta ba da zata ce makuwa ce yayi an aike shi wurin wata duk da haka yanzu ma tunanin makuwar ce yayi tayi tana d'an murmushi tace mashi tana ganin yayi kuskure ba wurinta aka aiko shi ba,

"Hajiya ba kuskure nayi ba ko baki gane ni ba, ni ne wanda nazo jiya da Yalla6ai ba har na kai ku Government House ba, tabbas ke ce aka ce in kawo mawa don yau kafin ya wuce mukai Maganar" ido kawai Fauzy ta bishi da shi don kuwa bakinta ya mutu, mik'a mata makullin Motar yayi kaman bazata amsa ba jiki a mace ta mik'a hannu ta amsa,

"Yanzu yaushe za'a fara koya Motar ko zuwa gobe in yayi sai in zo tunda naga weekend ne kaman ba Makarantar" kikkafta idanu ta fara saida ta had'iyi abu kafin murya na d'an rawa tace "to...ai lambar da ka kira ni taka ce ko?" da sauri yace mata eh tace to zata yi mashi magana kan hakan yana murmushi yace to kafin ya tambayi yanzu za'a shigar da ita ciki ne ta girgiza mashi kai tace ya barta anan, sallama yayi mata ta d'aga mashi kai ya juya ya nufi hanyar barin layin da k'afa, bin bak'ar Camry d'in da akace tata ce da kallo tayi Zuciyar ta na d'an harbawa can ta maida idanunta akan makullin Motar shima ta kafe shi da ido, juyawa tayi jikinta kamar an zare mata laka ta nufi cikin gidan, tana shiga cikin parlon daidai Aunty Mareeya ta fito daga bedroom d'inta taci gayu da doguwar rigar shadda blue tasha aiki mai ratsin red takalman ta da jakar hannunta duk jajaye ne ta coge d'aurin kallabi sosae tayi kyau, tana ganin Fauzyn ta dakata tana jiranta ta k'araso, daga gefen Auntyn ta tsaya tana kallon ta,

"Ke kuma daga ina yaushe kika fita?" Shiru tayi tana kallon ta kawai ganin haka yasa Aunty cewa "lafiya naga kin tsura man ido?" Hannu ta d'ago ta mik'a mata makullin ta kawo hannu ta amsa, bin shi tayi da kallo ganin na Mota ne yasa ta d'ago tace mata makullin Motar miye, a sanyaye ta shiga fad'i mata abunda mai kawo Motar yace, waro ido Aunty tay nan take ta saki jakar hannunta ta furta "Makullin Motar ki ne!!" Kai ta d'aga mata tace wai haka yace dai, washe baki Aunty tay "haka d'in ma ne wllh, kai wannan dankareriyar kyauta haka tun baki shiga daga ciki ba!" Sosae ta shiga yin murna ganin yanayin Fauzyn ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta "wai ya na ganki haka duk kin yi sanyi keda zaki murna abun farinciki ya same ki haka" d'an ta6e baki tay da alamun damuwa tace "Amman Aunty indai tawa d'in ce to ni ya zanyi da ita, Mota fa!" Wani kallo tay mata "kaji ki da wata Magana, bangane ya zaki da ita ba, ba an fad'i maki abunda zaki da itan ba"

"Amman Aunty taya za'a ce kamar ni inada Mota" harara ta balla mata tace "Wllh matsalata dake wani lokacin k'auyanci komai sai kin nuna ke yar k'auye ce duk da kin shigo birni koda yake inda kika fiton ma ai ba k'auye bane kece dai haka, in banda abu irin ki mace nawa ce yanzu wadda bata kai ki ba take hawa Mota yanzu baga Zarah ba" still da alamun damuwa tace Amman ita ai matar aure ce ko, wannan karon k'ular da Aunty tayi a fusace tace "ai da yake ance mace in bata da aure bazata tuk'a Mota ba, dalla kin ma fara bani haushi in baki so ni sai ki bar man ina so, wllh ba za'a maida Motar nan ba in ma haka kike niyyar cewa, a baki abu don ki rink'a zuwa Makaranta ki tsaya kina wani fad'in k'auli da ba'adi ke da ba'a maki gwaninta" yar ajiyar zuciya tayi a sanyaye tace mata to tayi hak'uri cikin washe baki tace yauwa to ko itafa ai kawai ta kira tayi mashi godiya ita an ma yi a daidai wllh dama tana jin haushin hawa Napep, dariya Fauzy tay ita sai lokacin ma ta tuna da Aunty Mareeyar ta iya Mota, iyayensu ta kira gaba d'aya harda Yaya Mubarak d'in su ta sanar masu zancen zuwan Sameer d'in da kuma Motar da ya bata gaba d'aya sun jinjina abun sosae kafin suka sanya Alkhairi mahaifin nasu yace mata don Allah ta k'ara kulawa da ita sosae tunda yanzu a wurinta zata zauna tace in sha Allahu kar ya damu har Fauzyn ta ba duk suka yi mata Allah sa Alkhairi da Allah ya tsare itama Baban nasu saida yay mata yar nasiha kan ta k'ara kula da kanta ta guji duk wani abu data san zai ja mata dasu gaba d'aya matsala tace mashi insha Allahu zata k'ara kulawa sosae, bayan sun gama wayar Fatuu ta shiga kira lokacin Aunty ta tafi ta gano Motar, lokacin data sanar mata game da Motar wata uwar k'arar murna Fatuu ta saka cike da tsananin farinciki ta hau yi ma Fauzyn Allah sa Alkhairi cike da murna tace ikon Allah Yanzu ita tana da mota ita ma haka Fauzy tace wllh, daga baya sukai sallama tace sai tazo ganin Motar, bayan ta gama wayar hanyar wajen ta nufa a cikin harabar gidan sukai kacibus da Aunty Mareeya ta dawo sai washe baki take kamar wadda aka ma Albishir da Aljanna, tsayawa sukai cike da Farinciki ta furta "Fauziyya wannan Mota haka! da gani zata yi kud'i wllh don babba ce kuma sabuwa" dariya kawai Fauzy ke yi da sauri tace mata taje ta shirya suje yinin bikin tare a Motar Fauzy tace to ba matsala in sun hau tayi mata wani kallo tace to miye abun matsala abu tata, kai Fauzy ta d'aga tace bari taje to ta shiryo Aunty Mareeyar ma ta bi bayanta tana fad'in ai itama kaman sai ta sake shiga gaskiya sosae taba Fauzy dariya, gaba d'aya lace suka saka na Aunty bak'i ne da adon flowers pink ta saka takalma da jaka da gyale duk pink sosae tayi kyau ita kuma Fauzy nata Orange ne da torch d'in bak'i tasa takalma da jaka da mayafi bak'ak'e Wow abun sai dai ace Ma sha Allah don sosae sukai kyau,

tunda suka hau hanya suke ta faman sakin murmushin farinciki gaba d'aya sun kasa rufe baki Aunty sai faman santin Motar take, suna akan hanyar ta tuna da bata fad'i ma mijinta zancen Motar ba tasa Fauzy ta fiddo mata wayarta ta kira mata shi, bayan ta sanar mashi shima sosae ya nuna ya taya Fauzy murna Aunty tace ai saima yaga Motar, tambayar shi su Hanif tayi yace daga Masallaci sun wuce gidan Hajiyar shi tace to agaishe mata da mutan gidan, daga wurin yinin bikin da yamma fitowa sukai suka d'an zaga gari daga can suka wuce gidan Hajiya don suje su nuna ma Fatuu Motar.

A kwana a tashi cikin Fatuu har ya shiga wata na bakwai a lokacin tuni dama Hajiya ta hanata driving ganin yadda cikin yay girma ita kanta dama tuntuni ta fara jin rashin dad'in tuk'in, Sosae take samun kulawa don komi take so sai an mata haka ko wash tace sai Hajiya ta tambayi yaya in dai tana kusa da ita don yanzu tafi zama a part d'in, data dawo daga Makaranta nan take zuwa taci Abinci wani lokacin ma har wanka a visitor room take yi don akwai wasu daga cikin kayanta yawanci sai dare take komawa part d'inta tare da Mino, bangaren Haisam akai akai yake kiranta suna kuma yin chat sosae haka yan Abuja ma yanzu kullum sai Mom d'in Haisam d'in ta kirata ta tambayi yadda take haka Senator ma yana yawan kiranta su Jidderh wannan ba'a magana don sosae take kiranta tana tambayar Babies d'in su, bangaren gwaggo ma sosae take kulawa da autar tata kullum sai ta aiko mata da abun ci ba kamar wanda zai k'ara mata lafiya da yawan jini kamar ganyayyaki kullum sai tayi mata kwad'o mai dad'i.

Ranar Monday da yamma Fatuu na zaune a part d'in Hajiya tana yin Assignment hannunta ruk'e da agwaluma tana sha sai faman tsuke baki take tana d'an runtse ido Hajiya na dariya tace to kamar dole ta hak'ura mana tana yar dariya tace wllh wannan ta cika tsami ne Hajiyar tace to ba ga wasu nan a plate ba ta duba mara tsami sosae sai tasha tace to, d'agowa tayi da niyyar ta canza watan suka ji anyi sallama a tare suka kai idanun su kan k'opa Hajiya na amsawa, lokacin da wadda ta shigo ta k'araso ciki Fatuu na ganinta ta fara murmushi ganin k'anwar haulat tace "Mami ce" kai ta d'aga mata Fatuu ta nuna mata wuri tace ta zauna, gaishe da Hajiya tayi ta amsa ta juyo kan Fatuu itama ta gaishe da ita, amsa mata tayi idon ta akan fuskar ta don ta fahimci kaman kuka tayi idanunta sunyi ja sun d'an kumbura ma, a sanyaye tace "Mami lafiya dai ko?" tana yi mata tambayar ta fashe da kuka hakan ya rud'a Fatuu ta d'ago sosae tana tambayar ta abunda ya faru ido a waje, cikin kuka Mamin tace mata dama cewa akai tazo ta fad'i mata mijin Aunty Haulat yayi had'ari jiya an kai shi Asibiti yau Allah yayi mashi rasuwa, gaba d'aya Fatuu ta zaro ido waje tare da kai hannu ta dafe k'irjinta a razane ta furta mijin Haulat ya rasu! Mami dake ta kuka tace eh, kai Hajiya ta shiga girgizawa sosae ta girgiza da jin Maganar don Haulat ma yar gidanta ce, Kuka sosae Fatuu ta saka tana zabga salati tana fad'in Wayyo Allah Haulat, rarrashinta Hajiya ta shiga yi tana fad'in ta kwantar da hankalinta ko don halin da take ciki amman ina ta kasa daina kukan hakan yasa itama Mami d'in cigaba da rusa kukan, Saude ce ta fito daga cikin kitchen jin hayaniyar kukan su, cikin Falon ta nufo ganin su Fatun nata kuka yasa a rud'e ta hau tambayar lafiya Hajiya ce ta fad'i mata abunda ya faru itama ta girgiza sosae ta shiga yin salati, had'uwa sukai suna lallashin su har Fatun ta d'an yi shiru Mami ma ta daina tana ta goge Fuskar ta da gefen Hijab dibta, waya Fatuu ta d'aukko dake ajiye a gefenta ta shiga kiran gwaggo bayan ta d'auka ko sallama bata yi mata ba cikin kuka tace taji abunda ya faru gwaggon tace mata eh yanzu Mamin ta baro nan sai hak'uri lokacin shi ne yayi, cigaba da kukan tay gwaggo ta shiga rarrashinta tana nuna mata halin da take ciki Fatun sai faman fad'in to ta daina take, bayan sun gama waya da gwaggo Haulat ta shiga kira tana cigaba da yin kuka kad'an kad'an saidai wayar tak'i shiga dama haka take wuyar samunta a waya shiyasa sun fi yin Vedio call gashi yanzu tasan ko ta hau WhatsApp ma ba ganinta zata yi ba, aje wayar tayi ta yunk'ura ta mik'e da k'yar fuskarta jage

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login