Showing 246001 words to 249000 words out of 512766 words
Chapter 83 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1555
komai, dole ta amshi wayar a kunyace ta kalli screen d'in tana ganin Fatun ta sakar mata murmushi itama ta d'an yi mata gaidata tayi tana ta murmushi ta amsa kafin tace "My Daughter hope you are doing well" kai Fatun ta d'aga mata kafin a hankali tace yes, gaba d'aya ta kama kanta har Mom d'in ta fahimta tay yar dariya tace mata ta saki jikinta ita Mom d'in ta ce Fatun tace to, tambayarta karatun ta tayi tace taji sun kusa fara Exams Fatun tace eh ranar Wednesday tayi mata fatan sa'a, tambayarta ya grandma d'inta da sauran yan uwan ta tayi tace mata duk suna lafiya, d'an shiru sukai sai murmushi suke ma juna can Mom d'in tace "Ok, bari in bar ki ance kina karatu ne kiyi sosae Allah ya bada sa'a" amsa mata tayi da "Amin Momy Nagode" d'aga mata kai tayi kafin tace mata saida safe itama tace mata haka, mik'a ma Haisam dake zaune gefe wayar tay ta d'an gwalo ido yay murmushi ya amsa, cigaba da Magana sukai saidae da larabci suke dama Fatun tasan yana Magana da ita da larabci harda ma wani yare nasu na Ethiopia kamar fulatanci Saidai shi Haisam d'in bai jin shi sosae in tana mashi yafi maida mata da Hausa ko turanci sai jefi jefi yake yi mata wanda ya iya, daga baya turanci suka koma yi suna cikin Magana Mom d'in ke ce mashi tunda ta kusa fara Exams d'in ya tura measurements d'inta da kuma size na takalmanta harda na undies yace Ok daga baya suka yi sallama, suna gama wayar ya juya ya kalli Fatuu itama ta d'ago ta kalle shi ta d'an yamutsa mashi fuska, d'age mata gira yay yace "What?" A shagwabe tace "ba karatun bane yak'i shiga sai ma wai inta ganin fuskar ka a littafin" baisan lokacin da yayi dariya ba yace shidai karta ja mashi sharri shida har space ya bata don tayi karatun, k'ok'arin mik'ewa ya fara yi yana fad'in bari ya k'ara bata wuri aikuwa da sauri ta nufo shi ta k'ank'ame shi tana fad'in ba inda zaije bacin ko bai nan karatun ba shiga yake ba ita dai yasa ta daina ganinshi a jikin littafin, sai ga abu ya zama kamar kokowa k'arshe suka baje a k'asa daga nan dai aka gama karatun.
Washe gari ma Tk ne ya kawo masu break fast bayan sun gama ci Fatuu ta fitar da kayan Kitchen ta wanke komai, lokacin data dawo Haisam na Zaune saman kujera yana operating laptop d'in shi, d'aga kai yay yayi mata alamar ta zo ta nufo shi jikinta sanye da doguwar riga roba ta bi shape d'in jikinta, zama tayi a kusa da shi yana kallonta yace ta d'aukko bag d'in ta tazo tayi karatu tace to, bayan ta d'aukko a gefen shi ta zauna ta fara yin karatun, sun d'an d'auki lokaci a haka can Haisam ya dakata da aikin da yake ya jingina da kujera yana yin hamma Fatuu ta juya ta kalle shi tace ya gaji ya lumshe mata ido, hannu ta kai tana k'ok'arin kwanto da shi tace ya kwanta to ya huta, a saman laps d'inta ya kwantan ita kuma taci gaba da karatun tana yi tana d'an kallon shi idanun shi a lumshe, bai dad'e da kwanciyar ba ta aje book d'in ta kai hannu tana cakud'a sumar shi tace "Hubby wllh gashin nan naka in aka maka kitso ba K'aramin tsawo zai yi ba, slowly ya d'an bud'e idon shi suka sauka cikin nata, d'age mashi gira tayi tace "in maka kalaba ka gani" still yay yana kallon ta fuskar shi a d'an sake gaba d'aya in tana mashi abu koma mashi take kamar yar shekara ukku zuwa hud'u, ganin ta kafe shi da ido alamar jiran amsa take yasa calmly yace "bazaki karatu ba ko?" tura baki tayi tana yamutsa fuska tace "ai nayi fa da yawa kuma ya zauna yanzu, don Allah in maka kitson?" d'an murmushi yay kaman bazai ce komai ba sai kuma ya d'aga mata gira alamar eh, washe baki tayi ta sauke kanshi ta sauka daga saman kujerar tana fad'in bari ta d'aukko comb, bata dad'e ba ta dawo ta koma saman kujerar ta haye gaba d'aya ta juya ta maida kan saman cinyoyin nata, tambayar shi tayi tace "wane iri zan maka, shuku ko fashin kwakwa ko shade ko kuma 2 step, ko dai ma ayi na fulani?" Bai san lokacin da ya saki dariya ba ko ina shi yasan wani style d'in kitso, ce mashi tay ya fad'i idanun shi a lumshe yace tayi kowanne take so, yamutsa sumar ta fara can tace "kai wllh ta cika santsi ko anyi ma kitson ba zai zauna ba, bari kawai ayi kalaba sai in tuk'e bakin ta sosae yadda ba zai kwance ba" shidai murmushi kawae yake ta hau yi mashi kalabar, sosae yake jin dadin yadda take cakuda gashin sai gashi har da bacci, tana gamawa ta sa dariya tana fad'in wllh kan yayi kaman na mace, kiran sunan shi ta shiga yi cikin bacci ya jita slowly ya bud'e idon cike da murna tace ta gama ya tashi suje gaban mirror ya ga yadda ya koma wllh yayi kaman mace, ba yadda ya iya dole ya mik'e tana ruke da hannun shi suka nufi gaban mirror, tsaye yay yana kallon kan nashi da tayi ma kalaba yar manya manya sun zuba mashi ta gefe he couldn't help it but laugh, sosae itama Fatun ke dariya yana kallonta ta cikin mirror d'in, kasa daurewa yay ya jawota jikinshi......., Duk yadda yaso ya k'yaleta don tayi karatu ya kasa, k'arshe dai kalabar da kanta ta warware kanta sai d'an tukku tukkun ta, duk suna sanye da bathrobe suka dawo cikin d'akin daga toilet, kan front chair ta gaban mirror d'in yasa ta zauna da kanshi ya shafa mata mai ya d'aukko hand dryer ya fara busar mata da gashinta, bayan ya gama mata itama sawa tayi ya zauna ta fara yi mashi kamar yadda yayi mata tana busar mashi da gashin cike da tsokana ta k'ara cewa ta k'ara yi mashi kalaba d'in yayi mata wani kallo mai kaman harara tasa dariya,
Bayan sun gama laundry room suka nufa don su saka kaya, wata rigar shi armless ta saka ta d'an saukko mata saidai duk cinyoyinta a bayyane suke, shima armless ya saka da wando 3 quarter, ce mashi tayi yaje parlor ita zata tsaya ta wanke Uniform d'inta yace bari suyi tare, a cikin washing machine suka fara yin wankin suna cikin yi tace mashi tana zuwa ta nufi hanyar fita da d'an sauri sauri gudu gudu, bata jima ba ta dawo hannunta ruk'e da wayarta ta fara lallatsata, wak'ar Hamisu breaker ta so gaskiya ne ta kunna tana bala'en son wak'ar tun lokacin da tana cikin yin ciwon so duk inta jita sai taji kaman don ita aka yi ta, tana ruk'e da wayar ta kwanta a bayan Haisam d'in tana bin wak'ar kai kace ita ta raira ta shidai sai murmushi yake yana yin wankin, bayan ta k'are wak'ar muradin zuciya itama ta breaker d'in ce ta shiga har saida ta runtse ido don itama wak'ar tana son ta, sakin Haisam d'in tayi ta koma gefen shi ta yadda zata rink'a kallon fuskar shi ta fara bin wak'ar,
" _Burin zuciyaa, had'a da idaniyaa, su samu ganin ka yaaaa mai saka nayi dariyaaa, muradin duniyaaa son ka har yay lubiyaaaa a son ka duka zuciyaaa ta na bar maka taka ce.....🎼_ "
tana yi tana nuna shi sai murmushi yake, can da tayi baitin " _Kai nike so....._" dakatawa tay ta turo mashi baki a shagwabe tace "Hubby kai ma ka rink'a yi man in nace _Kai nike so....._ sai kace _Na saniii...._ " bai san lokacin da yayi dariya ba slowly yace ai bai iya shi ba, sake kunna wak'ar tayi ta kanga mashi saitin kunne tace gashi nan ya saurara ya iya, wai aka ce kowa ya sayi rariya yasan zata zubar da ruwa😂 dole d'an Senator gwanin kamewa ya iya haka ya rink'a amsa mata Fatuu sai dariya take sosae abun ya sakata nishad'in, lokacin da aka zo kan baitin da take cewa " _....So nike ka zamo miji, a garan kai agaji..kaga ba wani jan aji...._ " tun kan ta k'arasa ya katseta da fad'in "ai nayi wannan ko" kyalkyacewa tayi da dariya ta fad'a jikin shi, haka dai akai ta shiriritar yin wankin k'arshe abun harda su yar watsa kumfa. Bayan sun gama cikin d'akin suka fito suka zauna akan doguwar kujera Haisam d'in yace bari ya kira mata Auntie d'in ta su gaisa tace toh, kiran Fanan d'in yay Video call ta cikin laptop Fatuu na gefen shi, suna ta ma juna murmushi Fanan d'in na zaune ta jingina da gado jikinta sanye da k'ananun kaya kanta ba kallabi, bayan sun gaisa suka shiga yin hira da Fatun shi sai jefi jefi yake saka masu baki har tana ce ma Fatuu wai ya Amarci tana dai kula da babe d'in sosae ko ita dai murmushi kawae tay, sun d'auki lokaci suna yin wayar cikin firar take ce ma Haisam sun yi magana ai da Mom da Dad harda Jidderh ma ta fad'i mata Maganar bikin da za'ayi tace harda anko in suka fidda za'ayi mata a can, da yanayin jin dad'i take Maganar shima Haisam d'in sosae yaji dad'i ba kamar data ce Mom da Dad d'in shi sun kirata, ita dai Fatuu bata fahimci Maganar bikin da suke ba don Haisam d'in bai fad'i mata ba, bayan sun gama ne ta tambaye shi wane biki za'ai ya fad'i mata har saida ta d'an waro ido alamar mamaki, tambayar lokacin da zasu gama Exams d'in yayi tace mashi zasu yi 2 weeks don harda practicals, kai ya jinjina sai kuma ya tambayeta ai Kb tailor nada measurement nata ko tace mashi eh, tambayar ta size na Undies nata yay don yasan na takalman da take sakawa, shigar da fuskar ta tayi a jikin wai kunya aikuwa ya kai hannu ya d'an ta6a gefen cikinta ta wani gantsare tana dariya kafin ta fad'a mashi.
A daren ranar ya d'auketa suka fita siyo abun da zasu yi breakfast don gobe da wuri zasu tashi Saboda tafiyarta Makaranta. Washe gari tare suka yi sallar Asuba bayan sun gama komawa sukai suka kwanta Fatun nace mashi ya bari ta tashi tayi Breakfast yace karta damu zai yi ganin zata mashi rigima ya fara k'ok'arin sata yin baccin, ba'a d'auki lokaci ba ta koma baccin shi kuma ya mik'e ya nufi Kitchen, saida ya gama sannan ya tasheta, da kanshi ya rink'a bata a baki har ta k'oshi sannan aka hau shirin zuwa Makarantar dama tun da daddare ya goge mata Uniform d'in.
Bayan taje Makarantar sosae Fauzy ta shiga tsokanar ta tana fad'in lalle da gani ba k'aramar soyewa sukai ba shiyasa ma ko tunawa da ita bata yi ba ace cikin kwana biyu ta k'ara canzawa har haske ta k'ara harda cewa Allah yasa hasken na rabo ne ita dai Fatuu dariya kawae take. Bayan an tashe su shi yazo ya dauke ta suka biya aka d'auki Mino tana ta murnar ganin Adda d'inta data kwana biyu bata gani ba, gidan Hajiya suka wuce don ya lura a G.r.a bazata yi karatun jarabawar ba sosae. Bayan komawar su sosae yake d'aga mata k'afa don tayi karatun yana kuma taimaka mata wurin k'ara yi mata bayanin wani abun da bata gane ba, a kwana a tashi ba wuya tuni sun fara jarabawar har ya rage saura yan kwana ki su gama, bayan sun fara da sati guda ne Haisam ya tafi Lagos wurin Fanan kwanan shi hud'u ya dawo, Ana saura kwana biyu su gama ranar laraba ya gama yi masu shirin zuwa Abuja harda Hajiya za'a tafi da sun gama jarabawar da kwana d'aya wato ranar Juma'a har su gwaggo sun san da zancen tafiyar don har an buga IV na programs d'in da za'ayi an aiko masu da shi IV d'in mai shegen kyau date d'in da za'ayi ya kama bayan gama jarabawar Fatuu da sati d'aya wato ranar Juma'a ta sama, cikin sa'a su Fatuu suka gama jarabawar sai farinciki suke lokacin Fauzy ke mata Maganar anko tace ta bari zata ma Jidderh magana in sun fiddo sai ta turo hoton shi, a ranar bayan Haisam yazo ya d'auketa sun koma gida ba K'aramin faranta ma juna sukai ba, da daddare ya d'auketa suka fita, shagon Kb mai d'inki suka fara zuwa ya amshi d'inkin dandatsetsen lace d'in daya bada a d'inka mata ita da Hajiya wanda ko ita Fatun bata san daya bada ba, sosae tayi murnar d'inkin gashi an mata Fav d'inkin ta wato straight skirt da riga fefflon irin mai bud'ewa daga k'asa yar daidai daidai hannun ma wani irin style akai mashi gwanin burgewa Hajiya ma riga Boubou akai mata harda kwalliyar bakin lace, sosae Fatuu tay murnar d'inkin abun yazo mata a surprise, bayan sun bar nan shagon Zee Collections suka wuce dama a wurinta ya siya leshin lokacin data kawo ba Jaka da takalma da gyalen da zasu hau dashi tace zata kawo mashi, cikin faran faran kaman ko yaushe ta tarbe su bayan sun zauna harda ita suka gaggaisa cike da nuna farinciki tace ma Fatuu ashe dai fatan su ya tabbata tace tayi murna sosae wllh data ji zancen Auren nasu, ita dai Fatuu murmushi kawae take Zee d'in tace ai in sha Allahu zata je Abujar, daga baya ta d'aukko mashi sak'on sukai sallama ta rako su waje. Saida suka tsaya wani Eatery ya siya mata kayan kwalama sannan suka wuce gida. Ranar Friday bayan gama sallar Juma'a suka hau shirin tafiya, sabon lace d'in wanda red color ne da torch d'in ash Fatuu ta saka sosae yay kyau d'inkin ya hau dashi Over, light make up tayi ta parker gashinta ta k'asa da ribbon dark ash, d'aurin kallabi Zarah buhari tayi ta yadda tulin gashinta ya lek'o ta k'asa, gaba d'aya jewellery d'in da ta saka silver ne suma sababbi ne masu tsada, bayan ta gama ta d'aukko takalman wanda ankle strap ne irin masu igiya da tsini sosae sai purse d'in su mai d'aukar ido gaba d'aya ash ne kalar kwalliyar lace d'in, Haisam bai nan ya tafi G.r.a ya dawo tuni shima ya gama shiryawa da ya dawo tafiya zasu yi, bayan ta gama shirin hanyar fita ta nufa jin ta take tamkar wata sarauniya sai faman murmushi take, tana shigowa cikin parlor Mino ta shigo tazo yin rakiya su sai cikin sati mai zuwa zasu je, waro ido tay ganin ta haka da mamaki ta "Furta Adda Fatuu kece haka!" Dariya kawae Fatun take ta taho da d'an gudu gudu tana zuwa ta rungumeta tana fad'in wllh tayi kyau sosae, part d'in Hajiya tace mata suje Minon tace dama gwaggo ma na can itama tazo yi masu rakiya Airport, lokacin da suka je itama Hajiya ta shirya cikin nata lace d'in duk suna zaune a parlorn harda Saude da Tk nan fa aka hau yabon gayun Fatun har Hajiya na fad'in wato Saboda son kai na Haisam shine ita akai mata d'inki mai kyau ita kuma akai mata burgujejiyar riga ai da itama sai ayi mata irin na Fateemar ta cakare duk suka sa dariya, a gefen gwaggo ta zauna suka gaisa, bata dad'e da zuwa ba Haisam d'in ya dawo yana sanye da farin danyen voile haka takalman shi da agogon shi duk farare ne, gaisawa sukai yace ma Hajiya in sun gama zasu iya tafiya tace to duk suka mik'e idon shi akan Fatuu dake sakar mashi murmushi, a gaban shi ta tsaya bayan duk sun tafi ya lumshe ido Slowly ya furta tayi kyau tace ai shi yasa tayi kyaun, tambayarta yay an fiddo kayan su tace a'a yace Ok suje suka nufi hanyar fita, bayan sun fito Tk yace ma ya biyo shi suka nufi part d'in nasu, basu d'auki lokaci ba suka dawo Tk na janye da trolley d'in Fatuu da wata jaka Haisam ma na janye da madaidaicin trolley, a boot aka saka su, Hajiya da gwaggo da Saude suka shiga Jeep Tk ne zai ja sai Mino da Fatuu da Haisam suka shiga k'aramar Mota Officer ne zai ja su, bayan duk sun shiga Motocin suka tunkari gate, bayan sun fito a daidai shagon Amadu Tk ya tsaya don shima yace mashi zai yi rakiyar, fitowa yayi bayan ya kulle shagon ya shiga gaban Motar sannan suka tafi, suna hanya Fauzy ta kira Fatuu ta tambayi sun fito tace mata eh tace to su had'e a Airport d'in, basu dad'e da isa ba Fauzy ta k'araso nan aka hau yin sallama yau su yar Fillo za'a hau Jirgi..........
*ASM 079*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........A business class na jirgi Suke kowa da kujerar shi ta Fatuu na kusa data Haisam sai Hajiya na daga d'an can gefe da yake kujerun ba had'e suke da juna ba saidae ta Haisam data Fatuu gab d'in su kad'an ne, in ka kalleta bazaka ta6a cewa hawa jirginta na farko bane don bata nuna wani k'auyanci ba amman fa gaba d'aya a tsorace take tun farkon ganin jirgin kafin su shigo yadda ta ganshi wani gingimeme dashi bata zaci haka yake ba don bata ta6a ganin shi a fili ba sai a sama kuma bai kai girman haka ba take ganin shi, sai faman d'an wuwwurga ido take tana k'are ma wurin kallo ta yadda baza'a ga k'auyancin ta ba dama kuma basu da yawa a class d'in kowa kuma harkar gaban shi yake, hannu Haisam ya kai ya kamo hannun ta da sauri ta kalleshi yay mata murmushi itama ta mayar mashi, nuna mata yadda zata saka seat belt in an sanar da ayi hakan ya shiga yi bayan ya gama yace tasa ya gani hannunta har d'an rawa yake ta shiga sakawa bayan ta gama ta kalle shi, murmushi yay mata