Showing 138001 words to 141000 words out of 512766 words
Chapter 47 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1601
Bedroom d'in ya fara turaruwa shima Aunty Mareeya da ta gama ta shiga yi ma Fatuu bayanin yadda zatay amfani da wasu daga cikin kayan kamshin ita dae kai kawai take d'aga mata, bayan an gama turara d'akin Fauzy ta hau gyara bedroom d'in duk da ba wani 6aci yay ba tana cikin gyaran Aunty Mareeya ta sake shigowa hannunta ruk'e da cup ta nufi side d'in da Fatuu take ta zauna a bakin gadon ta bata tace ta shanye abun ciki, ba musu ta amsa ta kafa baki saida ta shanyen ta mik'a mata Cup d'in tace ta taso zata nuna mata abu a kitchen tace mata to ta zuro da k'afafun ta ta mik'e suka nufi hanyar fita Fauzy nata sakin wani kalan murmushi wanda da gani da biyu take yin shi, bayan sun je kitchen d'in bin d'akin Fatuu tay da kallo an tsara shi ya koma babban Kitchen a ranta ta shiga tuna lokacin da ta fara shigowa cikin shi yin fitsari da ta zo ba Haisam hak'uri da kuma lokacin da yay mata Assignment d'in maths tuna lokacin har saida ta saki murmushi, waya ta6a tunanin wai d'akin zai zama kitchen d'inta gaba d'aya part d'in ma, wata drawer Aunty Mareeya ta jawo ta ce ta matso, nuna mata abubuwan dake ciki tay wanda sauran magungunan ta ne da aka siya mata a wurin Aunty Bee ta shiga yi mata bayanin yadda zata rinka amfani da kowanne Fatun na d'aga mata kai har ta gama, tambayarta tay ko a cikin kitchen d'in akwae abunda bata iya amfani da shi ba ta gwada mata, a sanyaye tace duk ta iya tana ganin yadda Aunty Saude mai aikin nan gidan ke amfani da su Aunty Mareeyar tace da kyau daga haka suka fito suka koma Bedroom d'in, suna komawa Feenah ta shigo tace ma Aunty Mareeya ance su fito za'a maida kowa gida tace to dama sun gama mata komae ai, ta kalli Fatuu da tay zuru jin zancen zasu tafin ta tambaye ta akwai wani abu ta girgiza mata kai sukuku da ita ta juya ta nufi wurin k'atuwar wardrobe d'in d'akin, a gefenta ta d'aukko jakar ta ta dawo bakin gadon Feenah na tsaye, zuge zip d'in jakar tay ta kai hannu ta ciro wata farar shopping bag mai d'auke da tambari ta d'aura ta akan cinyoyin Fatuu tace "Yar k'anwata Amarya ga tawa gudunmawar nan saura kuma kice zaki k'i yin amfani dasu Saboda wai kunya, ke da shi yanzu ba sauran wata kunya don kun riga kun zama abu d'aya, an san kunya abu ce mai kyau amman yanzu a wani wurin in kika ce zaki saka kunya to zaki k'wari kan ki ne da kuma shi Mijin naki don haka ba a komai zaki rink'a nuna kunya ba....." Katse ta Feenah tay da fad'in "ba kamar yadda take da kishiya kuma ma baturiya, gaskiya dole sai kin zage wllh don su ba wata kunya gare su ba don ma ita tana ruwa biyu....." Aunty Mareeya ta kar6e "kin ji dai ko, wannan nasan har yawo daga ita sai d'an pant in ma tasa kenan tana iya yi a gaban shi, don haka ki zage wllh balle ke da ma kike da surar jan hankali Tubarkallah, ki kuma dage da gyara jikin ki ciki da waje, duk magungunan da nayi maki bayani kada ki wasa da shan su sannan kuma kada ki k'asa a guiwa wurin faranta mashi irin su ta nan wajan aka fi kama su, ki sashi ya susuce ta yadda duk in zaiyi Magana sai ya ambaci sunan ki alamar kece a ran shi koda yaushe" gaba d'aya suka sa dariya harda Fauzy dake can d'ayan side d'in gadon raku6e,
Feenah ta d'aura da fad'in "Bayan wad'annan kuma sai a had'a da biyayya don itace zata k'ara taimakawa wurin siye zuciyar shi duk da nasan ke mai biyayya ce a gare shi tun ba yanzu ba, to ki k'ara akan wadda kike mashi don yanzu ne zata fi yin aiki kuma zaki fi cin ribar yin ta, a k'arshe ina Addu'ar Allah yasa Alkhairi a zaman ku ya had'a kawunan ku gaba d'aya da abokiyar zaman taki ya kauda fitina ya bashi ikon yin Adalci a tsakanin ku, ya albarkace ku da zuria d'ayyiba" su Aunty Mareeya ne suka amsa ita kuma Fatun kan ta na a k'asa, lokacin Abbas ya lek'o cikin d'akin yace su suke jira fa duk suka mik'e ya d'aga murya yana ma Fatuu sai da safe, yana shirin juyawa Feenah tace don Allah ya taimaka mata da Abdul yadda yay baccin nan ba iya d'aukar shi zatay ba ya k'arasa shigowa cikin d'akin ta kinkimo mashi Abdul d'in ya kar6e shi ya sa6a a Shoulder yana fad'in Allah ma ya taimake su da yayi baccin ai da ba k'aramar rigima za'ai dashi ba don yana iya cewa nan zai kwana ba kamar yana ganin gidan Baban shi da Momy d'in shi ne duk sukai dariya ya juya ya nufi kopa suma suka bi bayan shi Fatuu ta fara k'ok'arin saukkowa daga saman gadon Fauzy dake kallonta tace ina zata, jin haka yasa su Aunty Mareeya juyowa suma suka tambayi inda zata fuskar ta kaman zatai kuka murya na d'an rawa tace raka su zatai, waro ido tay tace a ina ta ta6a ganin Amarya tayi rakiya ta koma ta zauna kafin Angon ta ya zo, ba yadda ta iya dole ta koma ta zauna suka tafi banda Fauzy da tay tsaye ta kasa tafiya yanayin fuskar ta ya sauya itama kaman zata saka kukan, bin juna da ido sukai can k'walla suka zubo ma Fatuu sharrr Fauzy ta d'an girgiza mata kai daga inda take tsaye tace "ki daina kuka Zarah lokacin farinciki ne yanzu, Allah yasa Alkhairi ya baku zaman lafiya sai mun had'u School" da k'yar ta k'arasa Maganar, jin kuka na niyyar k'wace mata yasa ta juya da sauri ta fita, tana fita Fatuu ta d'age k'afafunta ta kife fuskar ta tana kuka a hankali.................
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
*ASM Bk2060*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
......... Lokacin da su Hajiya suka fito Abbas na tsaye bakin Jeep d'in da ya zo da ita har an shiga da Fatuu, Aunty Mareeya da Feenah da inna Zaliha da Matar Baba shehu duk suka shiga ya juya kan sauran k'awayen Fatuu da suka rage don wasu sun tafi ya nuna masu Jeep d'in Saleem yace su je su shiga harda Fauzy ita ta shiga gaba sai Haulat, sauran wad'anda suka rage Abokan aikin gwaggo Hajiya ta nuna masu Motar da Tk ya zo da ita suka shiga Amadu na a Front seat, kowa ya samu wuri sai wasu daga cikin Makwabta ne basu samu ba Hajiya tace su taka a k'asa itama a k'asan zata duk akai dariya ta kira Abbas yazo gaban su tace mashi su d'an zagayo da su Fateemar ita ma ta shaida an yi mata d'aukar Amare yana murmushi yace to ya juya, Motar Saleem ya nufa ya zagaya driver side ya bud'e yana zauna ya d'an d'age kan shi jikin headrest ya sanar dashi zasu d'an zagayo dasu roundabout ya jinjina mashi kai ya rufe mashi kopar, saida yaje ya sanar ma Tk shima sannan ya dawo Motar tashi, lokaci guda gaba d'aya suka kunna motacin sai lokacin gwaggo dake tsaye ta tuna da kayan Fatuu ta yi ma Hajiya Maganar ko a d'aukko kafin su tafi tace ta bari in suka dawo sai Tukur yazo ya d'auka tace to, Tk ne ya fara jan tashi dama shine a gaba lokacin da suka baro gidan Hajiya da zasu zo ya mik'i hanya Abbas ne a tsakiya sai ta Saleem k'arshe suka tafi,
Bayan tafiyar su Hajiya tace masu su tafi su jira su acan gidan, har zasu tafi ganin an bar gidan a bud'e yasa Hajiya cema gwaggo akwai sauran mutane ne a gidan za a bar shi a bud'e, sai lokacin ta ankare da sauri ta juya tana fad'in ta manta Hajiya na cewa ko duk tafiyar Fateemar ce tasa ta rikicewa, bayan ta shiga ta d'aukko wayar ta da makulli ta fito ta rufe gidan suka tafi, ta k'aramar kopa suka shiga suka nufi part d'in Haisam, lokacin da suka shiga a gyare harabar take tsaf an gyare shukokin flowers d'in wurin gwanin sha'awa suka nufi kopar shiga parlon, suna shiga makwabtan da aka je da su suka saki baki galala suna bin parlon da kallo ga wani ni'imtaccen sanyin Ac had'i da fitinannan k'amshi da ya karad'e cikin parlon, gwaggo dae sai d'an murmushi take itama tana k'are ma parlon kallo, parlon yana nan yadda yake amman an k'ara wasu abubuwa kaman daga bayan L-shape ansa dining table mai kujeru hud'u suma leather ne bak'ak'e sai daga gaba bangon dake kallon su an sa wani jigunannan console mai jan hankali golden haka saman kujera L-shape an canza throw pillows an sake wasu masu design mai kyau da d'aukar hankali, Carpet d'in k'asa ma an canza wani sabo wanda ke akwae da an maida shi wurin dining table, haka flowers d'in dake a angles d'in parlon an k'ara wasu, d'an madaidaicin Fridge d'in dake parlon an maida shi cikin kitchen sai sabon freezer da aka siya mata a cikin kayan kitchen aka aje shi a parlon daga can wurin dining table, a jikin bangon parlon an manna manyan Frames harda mai Ayatul kursiyyu, blinds d'in jikin Windows ma an canza su zuwa manyan labulaye wanda daka kalla ba sai an fad'a maka ba zaka shaida masu kud'i ne Saboda had'uwar da sukai kuma sun hau da parlon sosae, komae ya hau daidai nan aka shiga yabawa ana sa Albarka tare da Addu'oi, Hajiya tace masu su shiga suga sauran d'akunan suka ce to suka nufi hanyar corridor, Bedroom d'in ma tsab dashi sai k'amshi ke tashi nan ma an canza labulayen ciki haka gadon ma yasha babban bedsheet mai pillows da yawa ko a ido ka kalle shi kasan zai yi mugun taushi, nan ma sosae suka yaba daga baya Hajiya tace suje su ga Kitchen ta juya gaba suka bi bayanta, d'ayan d'akin da yake matsayin Lab d'in shi a da shine aka maida mata kitchen d'in, bayan sun shiga ciki sosae shima suka yaba komae an tsara shi har a sama anyi cabinet haka k'asan ma cikin kankanin lokaci an maida d'akin Kitchen na yan gayu, bayan sun gama gani suka nufi Parlor sai faman yabo da san barka ake, duk suka zazzauna suna dakon isowar su Fatuu farinciki Fal cikin zuciyar gwaggo har fuskar ta ta kasa 6oyewa sai d'an murmushi take ganin wai autar ta ce zata rayu a cikin wurin, sai godiya take ga Allah acikin ran ta,
Tun da suka tafi Fatuu ke ta faman kuka har Abbas saida yay mata Magana yace gidan fa Ya Handsome d'inta za'a kaita ba wani wurin ba ai farinciki yakamata tayi ba tay ta yin kuka ba sai kace za'a kaita inda za'a cuta mata, Aunty Mareeya itama tace abun ya bata mamaki wannan kuka haka sai kace za'a kaita gidan makiyinta Feenah ce tace "ai dole duk da hakan sai taji ba dad'i barin gidan da ka saba rayuwa a ciki ka koma wani wuri ba abu bane da ba za'a ji komai ba", inna Zaliha tace gaskiya ne ba kamar yadda suka shak'u da gwaggon ta,
Aunty Mareeya tace "hakane, amman dae kukan yayi yawa bai kamata ta sama kanta damuwa ba tunda dai ga baki ga hanci ba nisa tayi da gida ba, muda aka d'aukko daga wani gari sai an dad'e kafin muje gida ita kuwa data fito fa zata ga gidan koda bata shiga ba zata ji dad'i, gani ma zatayi tamkar ba ta bar gidan ba tunda duk unguwa d'aya ne kuma in taso ma kullum taje nasan ba zai hana ba" inna Zaliha dake d'an murmushi tace "hakane amman dai kar ace kullum sai anje d'in hakan bai kamata ba, ita mace ta zauna a d'akinta shi yafi mutunci ba kullum ai ta ganinta tana sunturi a waje ba hakan bai dace ba" gaba d'aya suka ce gaskiya ne harda Abbas, saida suka shawo roundabout na Barhim sannan suka koma. A cikin kwanar gate suka parker Motocin bayan sun iso duk aka firfito Aunty Mareeya na ruk'e da Fatun gefenta Abdul ne ruk'e da hannunta guda suka shiga ta k'aramar k'opa da sauran Mutane, lokacin da suka k'araso bakin kopar shiga parlon Aunty Mareeya ta tsaya da ita tace tayi Addu'a sannan ta shiga da k'afar dama wad'anda ke a bayan su duk suka tsaya saida ta gama sannan suka shige sauran suka bi bayan su, suna shiga d'aya daga cikin makwabtan dake zaune suna jiran isowar su ta mik'e ta rangad'a gud'a mai sautin gaske su Hajiya suka shiga sakin murmushi itama ta mik'e ta nuna masu inda zasu shiga da ita kowa ya baza ido yana k'are ma parlon kallo, hardae Aunty Mareeya da Feenah bin parlon suke da kallo don ba k'aramin had'uwa yay ba ya matuk'ar burge kowa ga wani irin k'amshi mai had'e da sanyin Ac da ya baza ko ina na parlon, Fauzy ma ta jinjina had'uwar wurin har d'an jinjina kai take haka sauran k'awayen su Zainab Muhammadu ma baki bud'e take k'are mashi kallo, ba wanda ma yay tunanin kayan ciki wai ba sababbi bane don kana kallon su zaka ga sabunta a tattare dasu tunda dama iya Haisam d'in kadae ne ke amfani dasu kuma masu matuk'ar inganci ne hakan yasa sam basu canza daga yanayin da aka siyo su ba, Saude ce tay masu jagora zuwa Bedroom d'in nan ma saida aka sa Fatun tayi Addu'a a bakin kopar shiga sannan ta shiga da k'afar dama aka wuce ciki da ita wurin gado, nan ma dae sosae Mutane suka yaba anata Addu'oi, a can tsakiyar gadon aka sa ta haye ta zauna ta jingina da headboard kanta na sadde cikin gyale Fauzy ma ta hau ta zauna gefen ta haka Abdul ma har lokacin yana ruk'e da hannunta duk ya damu tun da yaga tana kuka shima a Mota har kukan yayi yana fad'in ta daina kuka, bayan an gama ganin Bedroom d'in har Laundary room da toilet saida mutane suka shiga suka gani harda su Aunty Mareeya, bayan sun gama dubawa suka fita zuwa Kitchen ya rage daga Fauzy sai sauran k'awayen su, su Zainab dake zaune a bakin gadon sai faman santi suke suna Allah ya maida su damshin Fatuu Fauzy na dariya take amsa masu Zainab tace suje suga sauran wuraren suma duk suka mik'e suka nufi laundry Fauzy ta juya ta kalli Fatuu da har lokacin bata d'ago ba ta kai hannu ta d'an d'aga gyalen ta lek'a fuskar ta suka had'a ido idanun nata sun yi jawur Fauzy ta jawota jikinta tana Fad'in "Haba Amaryar Ya Haisam kukan ya isa hakanan, keda zaki murna ki farinciki Allah ya cika maki burin ki yau gaki a gidan shi a d'akin ki mallakin ku keda shi, don Allah kiyi hakuri kar kija ma kan ki wani ciwon a wannan daren mai daraja da zaku idasa dunk'ulewa ku zama abu d'aya" d'aga idanunta da suka sauya kala tay ta d'an kalli Fauzyn dake ta sakin murmushi wanda da gani da biyu take yin shi, yar harara Fatuu ta jefa mata ta maida kan ta k'asa Abdul dake a jikinta shima yace "Aunty Fatuu kar ki k'ara yin kuka don Allah, Baba Zakee ba zai cuce ki ba kuma zai rink'a siya maki kayan dad'i da yawa harda Computer ki rink'a yin game" d'an murmushi tay ta d'aga mashi kai kafin ta kai hannunta da ya sha k'unshi da had'add'un awarwaro yan manya guda hud'u sai zobba guda biyu ta shafi fuskar Abdul d'in yaron yana k'aunar ta sosae, d'aga ido Fauzy tay tana k'ara kallon d'akin tace yakamata a k'ara sa turaren wuta cikin wanda Aunty Mareeya ta kawo tace bari tay mata magana ta sauka daga saman gadon ta nufi kopar fita, tana fita parlon taga ba kowa a ciki tun bayan da suka gama dudduba ko'ina Hajiya tace atafi part d'in ta a ci Abinci kar a 6ata ma Amarya nata shine aka d'unguma aka tafi can, wayar ta ta fiddo daga cikin side bag d'inta ta fara k'ok'arin kiran Auntyn bayan tayi picking ta tambaye ta suna ina ta fad'i mata tace gata nan zuwa, fita tay daga cikin parlon bayan ta fito part d'in duk da bata san in da part d'in Hajiyar yake ba bata sha wuyar gane hanyar da zata bi ba saboda ko ina fayau yake da haske tamkar da rana, tana shigowa harabar ta hango part d'in ta nufe shi, bayan fitar Fauzy a hankali Fatuu tasa hannu ta yaye gyalen kanta yadda fuskar ta ta fito sosae, d'aga kai tay ta fara bin bedroom d'in da kallo har yanzu ganin abun take tamkar ba gaske ba kaman mafarki ne, wai yau itace a cikin bedroom d'in Ya Haisam a saman gadon shi kuma ma a matsayin matar shi Allah kenan buwayi gagara misali acikin ikon sa komai mai yuwuwa ne cikin sauki, cigaba da k'are ma d'akin kallo tay iya fentin shi abun burgewa ne balle kuma rantsattsun tsadaddun furniture d'in ciki, sam d'akin baida hayaniya ga wasu jigunannan labulaye, bedsheet d'in saman gadon cikin wanda Hajiya ta siya mata ne lokacin da za'ai mata aure da kayan kitchen har saida ta kai hannunta ta d'an ta6a jikin shi gwanin taushi, tana haka ta shiga tunano can baya tun daga kan farkon ganin shi lokacin da ya raba su fad'a da Jameela mai awara, a nutse taci gaba da tunanin baya sai faman sakin murmushi take lokacin