Showing 87001 words to 90000 words out of 512766 words

Chapter 30 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1602

fito Parlor ya nufi hanyar fita har ya kusa kaiwa k'opar fitan yaji motsi a bayan shi ya juya da sauri Amarya Saude ce don an d'aura mata aure da Officer tarewa ce kawai ta rage, daga kopar baya ta shigo hannunta ruk'e da yar roba mai fad'i Haisam na ganinta ya tunkare ta yana tambayarta Hajiya ko amsa gaisuwar da take mashi bai yi ba da hannu tay mashi nuni da inda ta fito tace mashi tana baya wurin su d'awisu ya amsa da Ok ya nufi kopar ita kaita saida tay mamakin ganin yanayin shi, yana fita bayan ya hango ta can a zaune akan kujera a gefen wurin Aku da alama fira suke hannunta d'aya ruk'e da sandar ta ta alfarma da take amfani da ita yanzu wurin yin tafiya, tun kan ya isa Aku yace ma Hajiya wai ga d'an ta nan jin haka yasa ta juya ta kalli Haisam dake tunkaro ta kafin ta juyo tana dariya tace ma Akun bata fad'a mashi jikan ta bane ba d'anta ba Akun ya dae yi shiru tamkar bai fahimci mi take nufi ba lokacin Haisam ya iso ya tsaya gefenta ta d'aga kai ta kalle shi sai yama kasa ko gaida ita sai d'an motsa baki yake lokaci guda ta gane akwai abunda ke damun shi tace mashi miya faru d'an shiru yay har saida ta maimaita sannan yace yana son yin Magana da ita ne tace to ta taso ne ko anan zasu yi yace suje Parlor tace Ok ta fara kokarin mik'ewa Aku na fad'in sai kin dawo Hajiyata tace to ya jirata suka nufi parlon tana gaba Haisam na bin ta a baya, bayan sun iso wurin kujeru akan 3 seater ta zauna shima ya zauna daga can gefenta idanunta akan shi yay shiru yana kallon carpet ganin haka yasa tace mashi shi take sauraro ya akai, shirun dae yaci gaba da yi ya rasa ta ina ma zai fara tunda yake bai ta6a jin fargabar gaya ma wani magana ba irin yau saida Hajiya ta k'ara tambayar shi da d'an k'arfi tace "miye wai ka fad'a in wani abu ya faru kayi man shiru zaka tada man hankali!" Sauke ajiyar zuciya yay ya d'an kalleta idanun shi har sun canza sai kuma ya maida su yana kallon gefe cikin raunanniyar murya ya fara cewa "...I want to tell u dat Zarah is pregnant and a.....am responsible for it" daga haka ya dakata wani kallo Hajiya ke bin shi dashi baki bud'e cikin rashin fahimta tace "Fanan nada ciki shine abun damuwa kai da zaka yi farinciki kiran ka tay ta sanar maka?" Tayi tambayar tana murmushi ya fahimci bata fahimci sunan da ya fad'i ba gashi ta kafe shi da ido alamar tana jiran amsa juyawa yay yayi facing d'in ta sosae cike da k'arfin hali yace "I said Zarah Not Fanan" lokaci guda yanayin fuskarta ya canza ta tsuketa cikin d'aurewar kai tace "Wace zarar?" Jimm yay sosae yake jin fargaba can dae ya dake yace "Zarah our neighbor I impregnated her yanzu haka tana d'auke da ciki na a jikinta" da alama mutuwar zaune Hajiya tay baki bud'e take kallon shi shima kallon nata yake sun dan d'auki lokaci a haka kafin ta kai hannu ta gyara zaman gilashin ta wai taga in shi ne da kyau a rud'e tace "Haisam kana da hankali kuwa kasan mi kake fad'a kuwa dama ashe ciwon da kake ba wani abu bane shaye shaye ka koya wurin turawan shine yanzu ka shawo abunda ya fi k'arfin ka kazo kana man zancen hauka to Allah ubangiji ya tsare mu da irin wannan abun kunyan ka bari muji dana shaye shayen da ka fara, yanzu kai Haisam duk yadda muke d'aukar ka mai hankali kowa na yaba halin ka nagari shine har ka bari turawa sukai galaba a kan ka wannan wane irin abun kunya ne ni Hauwa!" tana k'arasawa ta kai hannu ta ruk'e ha6a tay mashi zugudum tana mashi kallon bak'on mutum ba Haisam ba still yana ta kallon ta yasan dama bazata fahimta ba cikin sauk'i d'an matsawa yay kusa da ita yace "ni fa ba wani abu da nake sha ko kuma na sha yafi k'arfi na what am telling u is true Zarah da kika sani tana da ciki 1 month and nawa ne yanzu taje G.r.a ta sanar mani don nima ban san tana dashi ba...." Nan ya kwashe yadda sukai da Fatuu data same shi yanzu harda K'in d'aukar wayar shi da tayi da neman ta daya zo da kuma makarantar su da ya je duk ya fad'a mata, tana ta kallon shi har ya gama mata bayani tay shiru kawae, zuciyarta ta fara gasgata mata zancen shi Saboda yanayin da ta ga Fatun a d'azun tabbas yanayin ta ya nuna kaman na mai d'auke da yaron ciki iya girgiza Hajiya ta girgiza cikin tsananin tashin hankali murya na rawa tace "K.. kenan kana nufin raping d'in yar mutane kai???" d'an cije lips d'in shi yay ya d'aga mata kai alamar eh ta zabga uban salati tana tafa hannuwa ta shiga fad'in ".....Wannan wace irin musiba ce Haisam ya jawo mana, duk yadda nike Addu'ar Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani ashe kai ne zaka jawo hakan Haisam, miya faru da kai ne ka aikata ma Yarinyar Mutane wannan d'anyen aikin yarinyar da take tamkar k'anwa a gare ka, mika sha ne ka aikata mata hakan, ka fad'a man ko don ance matar ka nada matsala shi ne kai tunanin samun d'a ta wannan hanyar kasan mi ka aikata kuwa???" Sigh yay ya kai hannu ya dafa goshin shi kafin ya cire yace "I ave told you ba wani abu dana sha fa abunda ya faru wasn't intentionally kema kin san bazan aikata hakan da wani niyya ba ko don wai Fanan na da matsala nasan nayi kuskure na biye ma son zuciya wannan dalilin ne ma yasa na kasa natsuwa har na dawo nan ban wuce Us ba" kallon dae kawai take bin shi dashi tsananin tashin hankali yasa ko kuka ta kasa yi ganin shi take a matsayin wanda ba daidai yake ba don kuwa da alama ya manta girman laifin da ya akaita da wadda ya aikata mawa, cigaba yay "Yanzu dae isn't the right time da zamu cigaba da Maganan ya kamata ai stopping nata daga aikata abunda tace zata yi u know abortion nada matsala and nayi k'ok'arin in tsaidata but she refused to pick my calls kuma kinsan tunda karatun ta ne zata iya aikatawa pls do something in ya kama ko gidansu ne muje sai a fad'a ma Grandma d'inta" wannan karon kallon mahaukaci Hajiya ta koma yi mashi mahaukacin ma mai hauka tuburan don Maganar k'arshe da yayi a wurinta ta mara hankali ko miskala zarratin ce kaman yasan mi take ayyanawa yasa shi fad'in "nasan abun nada tashin hankali but bai kai na in aka samu Matsala ba don she may lose her life fa in hakan ya faru kuma ya tashin hankalin zai kasance so is better a sanar mata ta dakatar da ita and I will take responsible of everything" bakin Hajiya dai ya gama mutuwa sai ido kawae can ta yunk'ura ta mik'e shima ya mik'e ta nufi kopar fita daga parlon ganin zata fita haka yasa shi cewa veil d'in ta fa banza tay mashi tana dogara sandar ta har ta fice daga parlon shima haka...........



_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2050*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


..........tana fitowa ta nufi hanyar gate shi kuma Haisam ya nufi Motar shi dake a bakin part d'in dama a bud'e ya barta ya shige yay reverse kafin ya juyata ya nufi hanyar gate d'in a daidai saitin Hajiya ya tsaya ya sauke glass yace mata ta shigo, banza tay mashi tana cigaba da dogara sandar ta ganin haka yasa shi bud'e Motar ya fito ya sha gabanta tay mashi wani kallo kafin tace ya jaye ya bata wuri kawae sai ya kama hannunta ya nufi Motar da ita tana ya k'yaleta amman yak'i sakin ta har saida ya bud'e kopar baya ta shiga sannan ya koma gaban ya shige tuni Officer ya zuge mashi gate ya fice yabi Motar da kallo a ran shi yana tunanin ko lafiya, A daidai gaban gidan su ya parker da sauri ya fito ya bud'e ma Hajiya kopar bayan ta zuro sandar ta kafin ta fito ya maida duka kopopin ya rufe suka nufi gidan tana gaba yana biye da ita Amadu dake cikin shago yana ganin su ya bud'e ya fito yazo gaban Hajiya ya gaishe da ita ta amsa mashi kafin ta tambaye shi Dijen na ciki yace eh ta wuce ya k'ara gaishe da Haisam ya jinjina mashi kai kawae, bin su da ido Amadu yay lokaci guda hankalin shi ya tashi don ya fahimci akwae abunda ke faruwa tun ma d'azun da Haisam d'in ya zo neman Fatuu Addu'ar Allah yasa dae lafiya yay kafin jiki a sanyaye ya koma cikin shagon, suna shiga zauren gidan Haisam yaja ya tsaya Hajiya har ta shiga ciki ta juyo ganin bai shigo ba yasa ta tamke fuska tace "Wato ka d'auke ni mutuniyar banza ko ni ce zan shiga in sanar da aika aikar da kayi?" Yana kallonta yace "No just to ask for permission first" wata uwar harara ta zabga mashi tace "kai a tunanin ka yanzu kana da wata kamala ne wanda ya aikata abunda ka aikata ai bai buk'atar a bashi izinin shiga gidan mutane ba kamar Mutanen da ya za6i zubar ma da Mutunci ka shigo muje" wani kallo yake mata ya d'an girgiza kai yay mata alamar suje da hannu ta juya lokacin ta fara yin sallama saida tayi sau biyu sannan gwaggon ta amsa ta lek'o don ganin waye koda ta gansu da sauri ta k'arasa fitowa tana washe baki jikinta sanye da riga umbrella da zani na atamfa ta d'aura kallabi nufo su tay tana masu maraba Hajiya dake bin ta da ido ganin yadda take ta washe baki yasa nan da nan tausayinta ya mamaye zuciyar ta don ta tabbatar da ta san abun da ke tafe da su to tabbas manta yadda ake dariya ma zata yi balle har tayi, gaida Hajiyar tay ta amsa mata tana kokarin daidaita natsuwar ta ta kalli Haisam still da fara'a tace "d'ana Haisam barka da juma'a ya k'arfin jikin?" Slowly ya amsa mata da Alhamdulillah Hajiya ta kya6e baki tana girgiza kai gwaggon tace su shigo cikin parlor, bayan sun shiga a kan one seater Haisam ya zauna Hajiya ta nufi 3 seater gwaggo kuma ta zauna akan 2 seater ta shiga k'ara gaida Hajiyar tana mata barka da juma'a ta amsa fuska a kwa6e shi kam Haisam tunda ya zauna ya sadda kan shi k'asa, shiru duk suka yi gwaggo sai d'an murmushi take sai dae a cikin ranta ta lura kaman akwae abunda ke faruwa ba kamar Hajiya data gani ba ko mayafi saida aka d'an d'auki lokaci sannan Hajiya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya idonta akan Gwaggo ta fara magana "Dije gamu mun zo saidae ba irin zuwan da aka saba bane zuwa ne mara dad'i mun zo maki da Al'amari wanda ban tunanin ya ta6a faruwa a kaf dangin ku...." Dakatawa tay sakamakon kukan da ya taho mata nan fa hankalin gwaggo ya tashi haik'am ba kamar da ta ga Hajiyar na kuka ga Haisam ya sadda kai baida alamar d'agowa bare tasa ran jin bayani daga gare shi a rud'e ta hau ba Hajiya hak'ura tana had'ata da Allah ta daina kuka k'arshe ma sai ta tashi ta koma kusa da ita tasa hannu tana goge mata kwallan tana cigaba da bata hakurin can ta shanye kukan tace "Dije nasan ki ke mace ce mai tsananin k'arfin hali ba k'aramin abu bane ke ta6a maki zuciya don Allah ina rok'on ki da ki k'ara kan wanda ke gare ki don Al'amarin da muka zo da shi zai iya tarwatsa maki zuciya wllh ni kaina da nake maki Maganar nan tuni zuciyar tawa ta tarwatsa Allah ne kawae ke bani iko nake yin komae" tuni jikin gwaggo ya fara rawa duk ta bi ta rud'e a kidi'me ta hau ce ma Hajiyar to tana ji in sha Allahu ba abunda zai faru da ita ta sanar mata abunda ke faruwa cigaba Hajiya tay "Dije kin san duk inda ake zaman lafiya Shaid'an bai da sukuni har sai yaga ya tarwatsa ni dake zumunci ne mai k'arfi a tsakanin mu tsawon lokaci Saboda dage wa da Addu'oi da su Azkhar yasa tsawon lokaci bai yi nasara akan mu ba sai yanzu, dije sai yanzu....." Share k'walla taci gaba da yi hankalin gwaggo in yayi dubu ya gama tashi a lokacin ta rasa ma hasashen da zata yi kan abunda ke faruwa ganin Hajiyan tak'i fad'a mata abunda ke faruwa yasa ta juya kan Haisam tace "d'ana Haisam don Allah ka sanar dani abunda ke faruwa in sha Allahu zan fahimta ai ni musulma ce...." Tun kan ta k'arasa Hajiya ta katse ta da Fad'in "k'yale wannan Dije dashi shaid'an yay amfani yayi galaba yake son ganin ya tarwatsa mana farinciki zan sanar maki abunda ke faruwa amman ina rok'on ki da girman Allah ki fahimce ni" da sauri gwaggo ta hau jinjina mata kai alamar zata fahimtan Hajiya tace mata ina Fateema gwaggon tace mata bata kai ga dawowa ba har yanzu amman dae yau zata dawo Hajiyar tace mata ta kirata a waya yanzu ta ce mata duk abunda take ta bari ta taho gida da sauri baiwar Allah gwaggo ta mik'e ta nufi hanyar fita tana Fad'in bari ta d'aukko wayar to, bada jimawa ba ta dawo hannunta ruk'e da wayar ta fara kiran Fatuu ba tare da ta koma ta zauna ba saidai har ta yanke bata d'aga ba wasa wasa sai da ta kirata sau kusan goma amman ba'a d'aga ba Hajiya dake ta kallonta tace "halan tak'i d'agawa?" Kai gwaggo ta d'aga mata ta girgiza kai tace "dole ta k'i d'agawa don itama tana cikin tashin hankali" a razane gwaggo dake kallon ta tace "kodae wani abu ya faru da Fatun ne ko tayi had'ari ne, don Allah Hajiya ki sanar man!" ganin yadda ta rud'e yasa Hajiyar kwantar da murya ta na kokarin fahimtar da ita ba abunda take tunani bane ya same ta kawai dae akwai dalilin da ya sa ba lalle ta d'aga kiran ba, ta nuna mata lalle dole sai Fatun tazo zata ji abunda ke faruwa gwaggon tace to yanzu ya za'ai gashi ta k'i ta d'aga kiran, tambayar ta Hajiya tay ko tasan d'akin da Fatun take a can Makarantar tace a'a ta dai san Hostel d'in amman bata san d'akin su ba tunda bata ta6a zuwa ba Hajiyar ta sake tambayar ta bata san wata k'awar Fatun ba ta kirata tace ta sani amman bata da lambar wayar ta don duk in zasu gaisa da wayar Fatun suke gaisawa, shiru kowa yayi gwaggo dai na tsaye k'ik'am can Hajiya tace "ina ga tashi zamu yi mu tafi Makarantar tasu kawae alabashshi sai mu nemi d'akin nasu in mun je" shiru gwaggo tay fuskarta duk ta canza an barta a duhu sai faman sak'e sak'e take a ranta can tace ma Hajiyar "ina tunanin Amadu bai rasa lambar k'awar tata bari in mashi magana" da sauri Hajiya tace to taje taji in akwai ta juya har tana yin tuntu6e wurin fita daga parlon Hajiya na ta bi a sannu, bayan fitar ta ta maida idonta akan Haisam da still kan shi na sadde ta hau jefa mashi wani mugun kallo fuska a kwa6e, Saboda tsabar rud'ewa a yadda take ba lullu6i babu itama ta fita har bakin shagon Amadu yana ganinta ya bud'e ya fito ya hau tambayar ta lafiya ba kamar yadda yaga yanayin fuskarta murya na rawa tace "ban san abunda ke faruwa ba Amadu amman dai gaskiya da matsala gashi sun k'i sanar dani abunda ke faruwa wai sai Fatuu ta zo Hajiya harda kuka fa gashi anata kiranta a waya tak'i d'agawa" zaro ido Amadu yay ba kamar daya ji tace Hajiya harda kuka yama rasa mi zai ce Gwaggon ce ta tambaye shi ko yana da lambar Fauziyya da sauri yace "eh akwae Fatuu na kira na da ita" tace to ina wayar ya d'aukko mata ita yace to had'i da juyawa da sauri ya koma cikin shagon without wasting time ya dawo ruk'e da wayar ya fara kokarin kiran Fauzy.........,

Tun bayan da ta yi mata allurar ta haye saman gadon ta ta jingina da bango duk ta takure a guri d'aya har yanzu jikinta rawa yake d'an yi Saboda zullumin abunda zaije ya dawo idanunta akan Fatuu dake kwance akan gadonta ta rufe ido bacci ne ya kwashe ta tana cikin jiran tsammani bayan da aka mata allurar, duk in tayi motsi sai gaban Fauzy ya fad'i daramm! Tana haka wayarta dake gefe ta fara ringing da sauri ta kalle ta kafin ta kai hannu ta d'aukko lokacin da tay arba da sunan Uncle Ahmad kamar yadda tay saving no d'in shi har saida gabanta ya fad'i tabi kiran da kallo har ya kusa yankewa kafin hannu na rawa tay picking yana jin ta d'aga da sauri ya mik'a ma gwaggo wayar ta karata a kunne ta rafka sallama wani irin rassss Fauzy taji murya na rawa ta gaishe da ita ko amsawa gwaggo bata yi ba ta jefa mata tambayar suna tare da Fatuu ne da sauri tace mata eh gata nan kwance tana bacci gwaggon tace "wani abu ya samu wayarta ne inata kira bata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login