Showing 285001 words to 288000 words out of 512766 words

Chapter 96 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1637

ta kalle shi, ya lura da canjin fuskar tata hakan yasa yace koda wani abu ba sun gama magana ba kuma ta amince zata aure shi, da d'an yanayin damuwa tace mashi eh kawai tana tsoron kar a k'i amince mashi ya aure ta, wani kalar murmushi yay yace "to akan mi za'a k'i amince man tunda ni nace ina so kuma in hakane shima Big bro ai da an k'i amince mashi" shiru yay ya d'age gira ya sake cewa "We are meant for each other shiyasa muna had'uwa muka fad'a son Junan mu so Don't Worry babe you will soon be Mrs Nameer Ali Zakee" k'ayataccen murmushi Mino tayi tace "Promise me bazaka dawo ka canza ra'ayi ba" wani kalan lumshe mata ido yay ya furta "I promise u My yar fillo" dariya Mino tayi shima yar dariya yay yace mata yana bala'en son yaji tana magana shiru tay tana ta murmushi bashi kad'ai ba ko a school haka ake cewa ba kamar in tana yin karatu, d'an juyawa tay ta hango Fauzy tsaye tana jiranta tace mashi bari taje ana jiranta, lumshe ido yay yace Ok amman tayi mashi abunda zai ta tunawa yay bacci mai dad'i, had'e lips d'inta tay tana murmushi a hankali tace "like what" rolling eyes d'in shi yay k'asa k'asa yace "blow me a kiss" sai da ta waiga taga Fauzy bata kallon su sannan ta d'aga hannu ta hura mashi kiss d'in ya bud'e hannu kafin ya rungume su ya wani lumshe ido dariya Mino tay ta juya da gudu ta bar wurin ya bita da kallo yana dariya, yana d'aya daga abunda ke k'ara burge shi da ita ta cika kunya, daina gudun tay data kusa zuwa wurin Fauzy, bayan taje inda take tsaye hak'uri ta bata tace ta sa tana ta jira Fauzyn ta d'an yi murmushi idonta a kanta tace "tsuntsayen love na lura dai ba k'aramar soyayya kuke sha ba da zafi zafi" rufe fuska Mino tay tana dariya suka tafi, bayan sun fito bayan sun tunkari part d'in Fauzy na murmushi tace inama su Aunty Mareeya basu yi bacci ba su ji abun farinciki Mino tace wllh itama tayi farinciki Fauzy tace sai fatan Allah ya inganta ya raba su lafiya wayaga su Zarah an haihu tayi Maganar had'i da sa dariya Mino ma yar dariyar take Lokacin suka iso part d'in suka shige.

Bayan tafiyar su Hajiya wurin gadon da Fatuu take kwance gwaggo taje ta tsaya tana kallonta Fuskar ta d'auke da Murmushi, har bata san ina zata kai farinciki ba rayuwarta ta kasance fin yadda take mata mafarki, sai murmushi take tana haka fuskar Mahaifiyar Fatun ta rink'a dawo mata, girgiza kai ta shiga yi a ranta ta furta Allah kenan ya d'auke wata ya bata wata, a fili ta shiga yi ma mahaifiyar Fatuu Addu'a itama ta rok'a mata lafiya da kuma inganta abunda take d'auke da shi, juyawa tayi ta nufi kopar dake cikin d'akin wanda tasan toilet ne, Alwala ta dauro ta dawo cikin d'akin tunanin abunda zata shimfid'a tayi sallar tayi k'arshe ta yanke ta shimfid'a kallabinta kawai, bayan ta gama sallar Nafilar sosae tayi ma Fatuu Addu'a bayan ta shafa zama tayi taci gaba da tasbihi, tana haka aka k'wank'wasa kopar ta gyara zamanta tace a shigo, Abbas ne ya shigo da sallama hannuwan shi ruk'e da katan d'in ruwa da lemu bayan shi Haisam ne ruk'e da k'atuwar leda, sannu da zuwa gwaggo tayi masu suka amsa acan gaban gefen gadon suka aje kayan kafin suka juya suna gaishe da gwaggon da fara'a ta amsa tayi masu sannu, mik'ewa tayi ta d'auki kallabin tana ruk'e da shi ta nufi hanyar k'opa ta fita, tsaye sukai suna kallon fuskar Fatun gaba d'ayan su fuskokin su d'auke da Murmushi, wata irin sabuwar k'aunarta Haisam ke ji na ratsa zuciyar shi,

"Allah kenan gwanin hikima masanin sirrin 6oye, wato a duk lokacin da na kalli Mom Zarah sai na tuno farkon gani na da ita a kopar gidan Hajiya ranar an aiketa ta d'ebo ruwa" Abbas ne yay Maganar idon shi akan Fatuu, Murmushi ne akan fuskar Haisam don bai mance da ranar ba, Abbas yaci gaba "lokacin har ta tambaye ka bak'o kayi na bata amsa da ba bak'o bane d'an uwan ka ne nace mata Mom d'in mu d'aya aikuwa ta buga k'afa tace ita bata yarda ba yo ya zata ga wake da shinkafa kuma in ce gidan mu d'aya, duk na tuna Maganar nan sai nayi dariya, lokacin dana fad'i mata inada mata da yaro ne tayi man magana k'asa k'asa wai kai to ya kai bakai auren ba, ina niyyar bata amsa ka d'ago kayi mata magana gashi tana tsoron ka hakan yasa ta tafi, k'ilan dana fad'i mata da sa rana akan ka da bata kamu da son ka ba" murmushi Haisam kawai yake yana tuna komai a lokacin,

"Mom Zarah an yi kuruciya mai saka nishad'i ina rok'on Allah ya baku D'iya mai irin halinta sai kuyi ta tunawa da tata kuruciyar" yar dariya Haisam d'in yayi, Abbas ne yace mashi suje ko gwaggo ta komo ciki yace Ok ya sake cewa gashi ma ya gan tana salla asaman kallabi yakamata ace akwae prayer mat Haisam d'in yace zai zo da wuri sai ya taho dashi, matsawa yay wurin gadon ya sunkuya ya manna ma Fatuu kiss a saman goshinta Abbas nata sakin murmushi, gwaggo na zaune ta d'age kanta suka fito, sauke kan tayi ganin su yasa ta mik'e sukai mata saida safe ta koma ciki.

Misalin k'arfe biyu da yan mintuna Fatuu ta fara motsi, a hankali ta fara bud'e idanunta har ta ware su gaba d'aya, k'ura ma saman d'akin ido tay tana kikkafta idanu, hannu ta d'ago ta ta6a mask d'in hancin ta nan take ta gane inda take, cire mask d'in tayi ta juya kanta idanunta suka sauka akan gwaggo dake kishingid'e akan kujera idanunta a rufe, bin ta da kallo Fatuu tay fuskarta da d'an murmushi, motsi gwaggon ta fara yi dama tana cikin yin tasbih baccin ya kwashe ta, kokarin gyara kwanciya ta fara cikin disasshiyar murya Fatuu ta ambaci sunanta, bud'e ido gwaggon tayi suka had'a ido, da sauri ta tashi zaune kafin ta mik'e ta nufi gadon, zama tay bakin gadon suna kallon juna da murmushi tace mata ta tashi ta d'aga mata kai, sannu tayi mata nan ma kai ta d'aga mata suka d'an yi shiru,

"Gwaggo miya same ni ne har aka kawo ni Asibiti?" Fatuu ta fad'a tana ta kallonta, tana murmushi tace mata ta fad'i ne a wurin hidimar da akayi shine aka kawo ta, shiru Fatuu tay lokacin komai ya shiga dawo mata na lokacin data fad'i,
"To mi akace yake damuna?" ta sake tambaya gwaggo dake ta murmushi tay d'an shiru idonta akanta can tace mata gajiya ce tayi mata yawa anata zirga zirgar hidima, shiru Fatun tay bata kawo komai a ranta ba don tasan hakan na faruwa, mik'ewa gwaggon tayi tace bari ta fad'i ma nurse ta tashi koda abunda za'a mata ta d'aga mata kai, bayan fitar gwaggo maida idonta tay tana Kallon sama ta shiga tunano komai daya faru a wurin dinner, tuno da lokacin da Haisam ya bi Wak'a yayi mata tay nan take ta fad'ad'a murmushi sosae taji dad'in hakan da yayi mata don ya nuna zai iya yin komai don son da yake mata, gwaggo ce ta dawo tare da nurse suka nufo gadon, sannu nurse d'in tayi mata tana murmushi Fatun ta d'aga mata kai, tambayar ta tayi ba abunda ke mata ciwo nan ma ta d'aga mata kai alamar eh, cire mata oxygen mask d'in tayi da drip d'in da aka saka mata bayan ta gama yi mata abunda zata yi mata ta k'ara mata sannu sannan ta tafi, bayan fitar ta Fatun ta fara k'ok'arin tashi zaune cike da kulawa gwaggo ke mata sannu, zuru k'afafunta tay gwaggo ta tambayi ina zata tace fitsari take ji ta mik'e ta taimaka mata, nad'e mata rigar tayi ta baya kafin ta kamata Fatun na murmushi tace mata zata iya, cewa tay bari dai ta taimaka mata, a bakin toilet d'in ta saketa ta bud'e mata kopar Fatun ta shiga gwaggo na fad'in tabi a hankali don Allah ta d'aga mata kai kafin ta maido kopar ta rufe, cikin d'akin gwaggo ta koma ta gyara mata gadon bayan ta gama ta nufi inda kayan da su Haisam suka kawo suke ta bud'e ledar, fiddo robobin take aways d'in da ke ciki tayi, bayan Fatuu ta fito tace mata tazo to ta ci Abinci ta d'aga mata kai don kuwa yunwa take ji, a saman kujera ta zauna gwaggo ta bud'e robobi biyu fried rice ce da naman kaza sai guda biyu kuma na sakwara ne gwanin sha'awa a ido da gani ta daku sosae, da murmushi ta tambayi to mi zata fara da shi ta nuna mata sakwara gwaggon tace dama tayi tunanin ita zata ce Fatun tay murmushi, bayan ta fara cin Abincin gwaggo ta mik'e tana fad'in bari a cire wannan d'aurin ko ta sha iska, bayan ta cire head d'in gado ta nufa ta d'aukko net d'in data yafa tazo ta d'aura mata akan Fatun nata murmushin jin dad'in yadda gwaggon ke ta bata kulawa, bayan ta zauna a gefen ta Fatun ta kalleta tace itama taci Abincin mana tace mata taci dai, tura baki Fatun tayi a shagwabe tace "Don Allah ki ci, in baki ci ba zan aje nima in daina ci" dariya gwaggo tay ta d'an girgiza kai tace mata wai sai yaushe ne zata girma ta daina shagwaba tafa girma yanzu, tana murmushi tace mata ba rana kuwa, gwaggo da har lokacin dariya take tace lallai kam za'a rinka abun kunya in ta haihu uwa na shagwa6a d'a na shagwa6a Fatuu dake dariya tace kyau kenan ai, daga baya gwaggon ta fara ci, sosae Fatuu taci Abincin don saida ta cinye sakwarar tass gwaggo tace ta k'ara ta d'ayar robar dama Saboda ita yasa bata ta6a ba ita ta d'auki shinkafa tana ci, ce mata tay bari taci shinkafar itama, sai gashi itama ta cinyeta ganin gwaggo na kallonta tana murmushi yasa tace "Gwaggo ko dai hada ciwon cin Abinci nike yi" yar dariya tay tace waya sani, mik'a mata robar sakwara d'in tay tace ta k'ara da sauri ta girgiza mata kai tace cikinta fashewa zai yi in ta k'ara, leda mai kyallin data gani a ciki ta fiddo ta fara warwarewa tana fad'in bari taga minene a ciki, bayan ta bud'e tsire ta gani yasha kayan had'i su tumatir da koran tattasai da albasa tun kafin ta fara ci ta hau had'iye miyau kallon gwaggo tayi tace wai ta ci tana dariya tace to dama ai don aci aka kawo ko, sosae yayi mata dad'i tace ma gwaggo su ci tace taci ta rage mata in ma duka zata cinye ta cinye da sauri tace a'a zata rage mata, sai ga wadda tace cikinta zai fashe sai faman cin tsire take tana zuba har da tambayar yadda aka kawo ta Asibiti gwaggon ta shiga bata labari don dad'i take ji ganin ta haka saidai bata fad'i mata ainihin abunda ya ja komai ba, tambayar gwaggon tay ina wayar ta tace mata ta barota gida bata ji dad'in hakan ba don tana son jin muryar mijin ta.

Bayan su Haisam sun koma, wanka ya fara yi ya zura jallabiya Abbas ma ya shiga wankan, sallar Nafila yay ya kara godiya ga Allah da ni'imomin da yay mashi yayi ma Fatuu Addu'ar samun ingantacciyar lafiya harda Fanan ma yayi ma Addu'ar Allah ya k'ara bata lafiya, sosae yayi Addu'oi lokacin daya gama tuni Abbas ya kwanta Sameer yau ba anan zai kwana ba dama shi Abbas ranar da suka zo ne kawai ya kwana a wurin Salim yake kwana, bayan ya gama zaune yay yana ta tunanin ko zuwa yanzu Fatuu ta farka, sosae yake jin kewarta yana son jin muryar ta amman yasan ba waya a hannun ta daga baya ya mik'e yaje ya kwanta fuskar shi cike da annuri, ya d'auki lokaci idanun shi lumshe yana tunanin baby d'in shi a haka bacci yay awon gaba da shi..........




_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM 084*


~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~



*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


............Washe gari bayan Haisam ya dawo daga sallar Asuba a main parlor ya tsaya ya kira Jidderh a waya, lokacin tana akan abun salla kiran ya shigo, mik'ewa tay ta nufi bakin gado ta zauna sannan ta d'aukko wayar, picking tay tun kafin tace wani abu taji yace ta same shi a parlor ta furta Ok, mik'ewa tay dama jikinta tana sanye da hijab ta nufi hanyar fita, yana zauna akan kujera one seater hannun shi ruk'e da waya ta iso wurin a kujerar kusa dashi ta zauna ya d'ago ya kalleta da fara'a ta gaishe da shi bayan ya amsa ta sake cewa "ya kwanan farin ciki" murmushi yayi ya amsa da Alhamdulillah, Addu'ar Allah ya bata lpy tayi bayan ya amsa yace mata so yake ta shiga Kitchen ta had'a mashi breakfast ba mai taking time sosae ba, tambayar shi tayi Asibitin zai kai ya d'aga mata kai, cike da zumud'i ta mik'e tana fad'in to yanzun nan zata had'a. Fauzy na gama sallar Asuba ta nufi d'akin su Aunty Mareeya lokacin data shiga a zaune kan abun salla ta iske ta da Saude Feenah na kwance kan gado don bata salla Abdul kuma dama tunda suka zo yana wurin su twins, da fara'a ta k'arasa cikin d'akin ta zauna daga gaban Aunty Mareeya, gaishe da Saude tay ta amsa tana murmushi ta maida idonta kan Aunty Mareeya dake bin ta da kallo, ganin tana ta faman zabga murmushi yasa tace ya zata zo tunda safe ta tasa su a gaba tana faman yi masu murmushi kamar wata zautatta, yar dariya Fauzy tay kafin tace Albishirinta da sauri tace goro harda su gyara zama shiru Fauzy tay Aunty Mareeyar duk ta k'agara ta ji miye har sai da ta kai hannu ta bugi shoulder d'inta tace dalla miye wai, fad'i masu abunda ya faru jiya ta shiga yi tana rufe baki Aunty Mareeya ta buga wata uwar shewa ta furta "Da kyau yar gidana Zarah, kwalliya ta biya kudin sabulu wllh wannan iya biyan bashi haka, kai Alhamdulillah Wllh naji dad'i nayi farincikin jin Maganar nan" Saude ma Alhamdulillah ta shiga fad'i, shewar da Aunty Mareeya tayi ce ta tashi Feenah ta bud'e ido, jin abubuwan da take fad'i yasa ta d'ago kai tana tambayar abunda ke faruwa cike da Farinciki Aunty Mareeya ta hau bata labari, jinjina kai Feenah ta hau yi fuskarta da faffad'an murmushi tace kai ma sha Allah abu yayi dad'i Allah ya bata lafiya ya inganta, amsawa sukai da Amin Aunty Mareeya tace ana ta shan Dinner d'in biki ashe Amarya da juna biyun ta mak'ale,
labarin yadda likita ya kasa fad'a Fauzy ta shiga basu sukai ta dariya suna fad'in ai dole ya kasa fad'a don wannan ba K'aramin Al'amari bane.

Bayan su Laila sun gama salla take ma Fanan Albishir don jiya ta riga tahowa kuma lokacin data dawo tayi bacci, waro ido Fanan tay ta kai hannu ta rufe bakinta alamar mamaki Laila nata Murmushi, cire hannun tayi cike da farinciki tace kenan duk abubuwan nan da ake Zarah is pregnant Laila tace wllh ai Allah ma ya taimaka da ba abunda ya same shi, mik'ewa Fanan tay da sauri ta nufi bakin gado ta kai hannu kan bedside ta d'auki wayarta, Haisam ta kira lokacin ya koma part d'in shi don ya shirya, yana tsaye a gaban dressing mirror kiran ya shigo ya juya ya kallo wayar dake saman bedside kafin ya nufeta, yana ganin mai kiran yay murmushi ya kai hannu yay picking, daga muryarta zaka fahimci tana cikin farinciki tace mashi ashe jiya abunda ya faru kenan bayan ta baro wurin yana ta murmushi yace mata eh, ce mashi tay shine ko ya kirata ya sanar da ita abun farincikin daya same su tama yi fushi dashi, yanayin yadda tay Maganar har saida yayi yar dariya, hak'uri ya bata yace tayi bacci ne yana son ta huta sosae tace to miyasa yanzu da aka tashi bai sanar mata ba ai kamata yay ace shine mutum na farko daya fara sanar mata, hak'uri ya k'ara bata yace mata yana niyyar yazo ne da kan shi sai yay mata Albishir yanzu haka yana gaban mirror yana mata Kwalliyar da zai zo yi mata Albishir d'in, yana jiyo sautin dariyar ta dama ya fad'i ne don ya faranta mata, ce mata yay gashi nan zuwa yi mata Albishir d'in a d'okan ce tace she's waiting for him,

Bayan Jidderh ta gama komai ta had'a mashi a cikin basket part d'in taje ta sanar mashi ta gama yay mata godiya yace ta aje mashi a dining area tace to, har zata juya ya tsaidata, ce mata yay ta d'aukko ma Fatuu kayan da zata canza ta sa towel da brush d'inta sai ta aje mashi a wurin basket d'in tace to kafin ta tafi, bada jimawa ba ya fito yana sanye da k'ananun kaya bak'in jeans da dark blue t-shirt sumar nan ta sha gyara sai baza k'amshi yake, part d'in Laila ya wuce lokacin daya shiga ba kowa cikin parlon hakan yasa ya wuce Bedroom, knocking k'opar yay aka bashi izinin shigowa ya tura ya shiga da yar sallama, Duk suna kwance akan gado Laila tuni ta koma bacci sai Fanan ce idonta biyu ta kasa komawa baccin sai tunane tunane take, sosae taji farincikin samun cikin da Fatuu tay saidai ta wani bangaren zuciyarta ce ta k'ara sarewa ta shiga tunanin anya kuwa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login