Showing 1 words to 3000 words out of 512766 words
Chapter 1 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1530
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2032*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
..........Tafiya mai d'an tsawo sukae cikin sand'a suka karaso katangar dake bayan gidan wadda take gajera bata da tsawo sosae Fatuu ce ta taimaka ma Haulat ta dira ta mik'a mata jakunkunan nasu sannan itama ta hau ta dire duk suka d'auki kayan suka bar wurin da sauri, Tafiya suke cikin sauri sosae Haulat duk a tsorace take ganin ko ina dumd'um ga haushin karnuka da ya karad'e ko ina cikin ranta tana ta yin Addu'oi Fatuu kuwa sam bata wani jin tsoro burinta kawai taga sun bar k'auyen ita ke ma Haulat jagora tana haska masu da fitilar wayarta saidae tana yi tana kashe wa ne, cikin sa'a suka k'araso bakin garin lokacin aka fara kiran sallar farko na Asuba tsaye sukae suna jira ko zasu samu abun hawa amman har bayan wani lokaci ba mai abun hawan da ya wuce Fatuu duk ta damu ganin an fara kiran salla tasan yanzu ayi sallar gari ya fara wayewa, Haulat dae saboda tsananin gajiya duk'ewa tay a wurin ga gabanta dake ta faman fad'uwa can Fatuu tace mata ta daure su d'an yi gaba kar azo a gan su ta yunk'ura da k'yar ta mik'e ganin haka yasa Fatuu ta d'aura trolley d'inta a saman kai ta d'auki jakar Haulat d'in a hannu tanata ta kawo ta ruk'e tace mata a'a ta bashshi zata iya, tafiya suka ci gaba da yi k'arfin hali kawae Fatuu ke yi amman ta gaji itama ga kaya, suna cikin haka sai ga wani mai amalanken shanu ya taho ta gabansu zai wuce da sauri Fatuu ta tsaida shi amman sai yak'i tsayawa tana ganin yana niyyar wuce wa ta sha gabanshi da sauri tana fad'in Don Allah ya tsaya, tsayawa yay cikin harshen fulatanci yace ta bashi wuri ya wuce hakan yasa ta fahimci k'ilan bai jin hausa ta bud'a murya cikin fulatanci tace Don Allah ya taimaka masu ya kaisu Jimeta, wani kallo yay mata duk da duhu ne yace bazai d'auke suba don ba can yay ba, rok'on shi ta shiga yi tace zasu biya shi yana kallonta yace yasani ko Aljanu ne su zai d'aukesu ta shiga yi mashi rantsuwar Mutane ne su zasu koma garin su ne, shiru ya d'anyi kafin ya tambayi nawa zata bashi ya kaisu da sauri tace dubu ukku d'an bud'e ido yay alamar mamaki sai kuma ya tambayeta ta tabbatar zata bashi hakan tace eh wllh yace to su hau cike da jin dad'i ta hau yi mashi godiya yace ba sai ta gode mashi ba su da zasu biya, saida ta taimaka ma Haulat ta hau suka saka kayan su sannan itama ta hau ya tambayi sun hau tace mashi eh sannan ya juya amalanken suka tafi Fatuu sai sauke ajiyar zuciya take Haulat dai tay zuru zuru jininta akan a kaifa yake in ba gani tay sun fita daga garin ba gaba d'aya hankalin ta bazai ta6a kwanciya ba, Anata sallar Asuba suka isa Jimeta suna shiga garin yace to su sauka anan zai aje su Fatuu ta rokeshi ya kaisu tasha sai sun je can zata fitar da kud'in da zasu biyashi basu dasu a hannu, fuska d'aure yace dama tasan ba kud'in suka ce zasu bashi tace ai akwae kud'in a cikin banki suke a tashar motar tasan ana fitarwa sai su bashi yana kunkuni yace to gaskiya saidae su k'ara mashi dubu biyu sannan ya kaisu da sauri Fatuu tace suje zasu bashi, Lokacin da suka isa cikin sa'a akwae mai Pos Fatuu ta fitar da sauran kud'in da suka rage mata gaba d'aya wanda Baffanta yace ta bari 20k ta biya mai amalanken dubu biyar d'inshi yana ta washe baki yay masu Allah ya kiyaye, Cikin sa'a suka samu Motar da tay Katsina direct suka hau aka shigar masu da kayan su aka ce su shiga seat d'in baya su zauna, bayan sun zauna zuru sukai kowacce kirjinta na bugawa zuciya na raya masu za'a zo a kama su sai Addu'oi suke acikin ran su, shiru shiru Mota bata cika ba har gari yay haske gaba d'aya tsoro ya kama su can Fatuu tace ma Haulat su sauka su hau ta Kano kawae tace to anata ce masu su k'ara hakuri mana ta cika suka ce sauri suke dole aka fiddo masu da kayan su suka koma ta Kano da ta kusa ciki suna shiga duka Mutum biyu suka k'aru Motar ta tashi har saida Fatuu ta d'an saki murmushi, Sai fatan Allah ya sauke su Lafiya.
Koda Yadikko ta shigo da safe sam bata kula da babu su a saman gadon ba duk tunaninta sunyi salla sun koma bacci, sai bayan da ta gama had'a Breakfast a falo tace ma Mino taje ta tashe su Suzo su karya in sun gama sun ci gaba da baccin ko don bak'uwa, lokacin da ta shiga bata ga kowa ba ta dawo ta sanar mata sam yadikko bata kawo komae ba a ranta tace k'ilan ko sun fita ne ko wurin Amadu, bayan su Mino sun gama suka wuce Makaranta, har Yadikko ta gama gyara d'akin shiru basu shigo ba tana tunanin zuwa ta duba su sai ga Kamalu ya shigo amsar masu abun karin kumallo nan ta tambaye shi ko su Fatuu na wurin su yace a'a su yanzu ma suka tashi da mamaki ta ce to ina suka je da sanyin safiya Kamalu yace basu nan ne tace eh yanzu aka je taso su aka ga basu nan yace k'ilan wani wuri suka je zasu dawo, tun dae abun bai damun yadikko har ta fara damuwa ta fara neman su har bathroom d'in cikin d'akin ta duba duk da tasan ba yadda za'ai su shiga nan su biyu, cikin gidan ta fita ta zaga d'akuna tana tambayarsu cikin hikima ta yadda baza'a zargi wani abu ba ko ina aka ce basu zo ba, bayan ta dawo d'aki zaune tay kan kujera tana ta tunanin to ina suka je ne can ta mik'e ta nufi k'uryar d'aki tay tsaye tana kalle kalle idanunta suka sauka akan babban akwatin Fatuu ta k'ura mashi ido tana kallo can ta ankare da guda d'aya ne a wurin kuma tasan guda biyu ne, to ina d'ayan ta jefa ma kanta tambaya tare da nufar wurin shi da sauri, duk iya dubawar da tay bata ga trolley ba nan ta tuna da jakar Haulat da ita ta aje mata ita da hannunta ta juya da sauri inda ta aje ta idanunta suka gane mata wayam wani irin bugu k'irjin Yadikko yay lokacin da zuciyarta ta raya mata kodae guduwa sukae in ba haka ba mi zai sa aga ba kayan su kuma babu su, nan da nan jikinta ya fara rawa k'afafuwanta sukai mata nauyi da k'yar ta koma falo ta zauna kan kujera ta rafka uban tagumi. Sai Azahar Allah ya sauke su kano baiwar Allah Haulat ta mugun gajiya anan tasha Fatuu ta siya masu Abinci suka ci bayan sun gama ba 6ata lokaci suka hau Motar Katsina da gasu nan available sai ka za6a ka darje nan da nan suka hau hanya sai fatan a sauka Lafiya, kiran duniya Yadikko tay ma layin Fatuu amman sai ace mata a kashe yake har waje ta fita tasa Kamalu ya kira wai ko laifin wayarta ne kiran yak'i shiga shima yayi mamakin jin har yanzu basu gidan, to shima dae a kashen aka ce mashi wayan take dole ta dawo cikin gida tama rasa tunanin da zata yi da k'yar jiki ba kwari ta tashi don yin girki,
Bayan da su Fatuu suka kama hanyar Katsina ne ta bud'e wayarta sakamakon tunanin halin da su Yadikko suke ciki daya tsaya mata a rai, sak'o ta rubuta ta tura ma Kamalu ta sanar dashi bata son Auren nan don haka ta koma gida tana tura mashi ta k'ara kashe wayar, lokacin suna tare da Amadu a kopar gida message d'in ya shigo wayarshi da tsananin mamaki yake karantawa har Amadu ya lura da yanayin fuskarshi ya shiga tambayar shi ko lafiya ya mik'a masa wayar shima ya karanta, kasa Magana Amadu yay Saboda tsabar mamaki da Al'ajabi shi yazo biki Amarya ta tafi ta barshi, tare da Kamalu suka tashi suka shiga cikin gidan don sanar ma yadikko a d'aki suka isketa ta rafka uban tagumi su Mino da suka dawo daga Makaranta suna zaune suna cin Abinci ita ta kasa ma ko ci don zuciyarta ta gama yanke mata cewa Fatuu guduwa tay ita da k'awarta tana ganin su Kamalu sun shigo ta mik'e tana tambayar su ko sun dawo Kamalu ya girgiza mata kai da alamun damuwa ya fad'i mata sak'on da Fatuu ta turo ba shiri Yadikko ta saki salati tana fad'in dama tayi zargin hakan wllh yanzu ya zasu yi da wannan babbar matsalar, miyasa Fatuu tay tunanin ta gudu ba tare da ta yi tunanin abunda zai iya biyo baya ba duka saura yan kwanaki a d'aura Auren, jin hakan yasa su Mino mik'ewa ba shiri jin Adda d'in su ta gudu, gaba d'aya sun yi jugum jugum sai kiran layin Fatun ake kaman yadda Yadikko ta buk'ata saidae kiran bai shiga sakamakon wayar da ake cewa a kashe take can Yadikko ta d'aukko wayarta ta kira Baffan su Fatuu hankali tashe ta sanar dashi abunda ke faruwa yace ya akai tun d'azun bata sanar dashi halin da ake ciki ba tace sam ita bata yi tunanin guduwa suka yi ba yace gashi nan zuwa gidan, zama su Amadu sukae haka su yadikkon duk suka zazzauna sai jimami kowa yake suna a haka har Baffan ya dawo, lokacin da ya shigo da alamun tashin hankali a kan fuskarshi yana shigowa yadikko ta mik'e shima tsayen yay murya na rawa ya k'ara tambayarta game da abunda ta fad'a mashi a waya nan ta sake kora mashi bayani da tsantsar tashin hankali yake kallonta can ya tsugunne don kafafunsa nema suke su kasa d'aukarshi yadikko na ganin hakan ta juya tace ma su Mino da tuni sun fara zubar da k'walla su fita waje ko su shiga cikin kuryar daki, suna tafiya Kamalu ma ya fara kokarin tashi Yadikko ta ce ya tsaya ya kawo wayarshi yaga sak'on da ta turon, bayan ya shiga cikin message d'in ya mik'e ya kai ma Baffan nasu hannu na rawa ya amsa ya k'ura ma screen d'in ido can ya d'ago ya mik'a ma Kamalu wayar ya idasa zaunewa k'asa idanunsa har sun canza sun yi ja cikin tashin hankali ya fara fad'in "Miyasa inna wuro zata man haka, in tasan bata son auren ai da tun farko bata nuna ta Amince ba sai ta k'yale mu duk halin da zamu shiga mu shiga ba sai yanzu da lokaci ya k'ure ba, sam inna wuro bata kyauta mana ba ban ta6a zaton zata iya aikata haka ba duk da tasan irin halin da hakan zai k'ara jefa mu amman ta za6i mu shiga cikin matsala, da ina Alfahari da ita don ta damu da damuwar mu tana jin tausayin mu ashe sam ba haka bane tunda zata iya za6ar k'ara jefa mu cikin mawuyacin halin yanzu ina amfanin haka ya take so muyi, duka saura fa yan kwanaki bikin nan....." Kasa cigaba yay sakamakon Muryar shi da ta karye kwalla suka fara zubo mashi da sauri Yadikko tace "Don Allah kar ka zubar mata da hawaye kar hakan ya zame mata matsala wllh duk abunda kaga ya faru laifin su Zakiyya ne har cikin ranta ta amince da Auran nan amman sune suka fara cusa mata k'in auran ta hanyar fad'a mata Maganganun da suka tashi hankalinta" nan take ta kwashe komae ta sanar mashi ba iya wannan ba harda abubuwan da shi Khalid d'in ke mata da gidan gona daya kaita yasaka mata maganin bacci a lemu duk bata 6oye mashi ba duk da su Amadu na a wurin gaba d'ayan su sun matuk'ar girgiza da jin hakan kowa ran shi ya sosu ba kamar Baffan nata da tsananin mamaki yake bin yadikko da kallo kafin rai 6ace yace yanzu dama yaron bai canja hali ba aka fad'a mashi ya shiryu yadikkon tace wai don ya biya sadaki a fusace Baffan yace biyan sadaki d'aura aure ne da zai nemi lalata yarinya su Kawu Amadu dae sun kasa cewa komae saidae kowa ran shi ya 6aci da jin wannan Magana shi dama Kamalu ya tsani Khalid d'in sanin halayen shi marasa kyau da yay shi kam Kawu Amadu wani irin tausayin Fatuu ne ya kama shi taya nutsattsiyar yarinya kamarta za'a had'a ta da irin wannan Mutumin nan take cikin ran shi ya goyi bayan guduwar da tayi duk da yana shakkun ba lalle Gwaggo ta saurareta ba amman tabbas zai kira gwaggon ya k'ara tunzura abun duk yadda za'ai a fasa, shima Baffan tunani na daban ya fara yi a cikin ranshi yana jin bai kamata ya k'yale a Aura mata wannan Mutumin ba saidae taya zai dakatar da auren shine abunda ya tsaya mashi a rai, tsam ya mik'e ya fice daga d'akin yana fita Kamalu ya fara Maganganu kan rashin dacewar Aura ma Fatuu Khalid yana fad'in shi dama yasan ba wani canzawar da yay za'a cuce ta ne kawai.
Sai wurin la'asar suka iso tun kafin su shigo Katsina Fatuu na hango Welcome to Katsina taji wani irin sanyi a ranta koda suka shigo har saida ta juya suka had'a ido da Haulat tay mata Murmushi itama ta yi mata amman fa na yak'e don ta gaji har ba sauran wuri, suna zuwa roundabout d'in Liyafa suka ce a sauke su anan don in suka wuce tasha tafiyar ta k'ara nisa, bayan sun sauka suka tsaida Keke Napep suka hau bayan sun fad'i mashi inda zai kai su yaja suka tafi Fatuu sai kalle kalle take sai take ganin kaman ta shekara da barin garin, tunda suka k'araso bakin Unguwar su gabanta ke fad'uwa har suka iso kopar gidan, bayan ya tsaya suka fito harda kayan suka biya shi, tsaye Fatuu tay tana zare ido suna kallon juna da Haulat itama dae gabanta fad'uwar yake don bata san irin tarbar da gwaggon zata masu ba can dae tace ma Fatun su shiga, Gwaggo na a wurin filin wanke wanke tana yin Alwala gamawarta kenan ta yunk'ura zata mik'e Fatuu ta sako kai ba tare da tayi Sallama ba, cak ta tsaya sakamakon had'a ido da sukae da gwaggon da ta ida mik'ewa tsaye, bin Fatun da ido kawai tay saidae a bad'ini ta matuk'ar razana da ganinta a ranta ta fara tunanin ko gizo take mata saidae kuma ganin Haulat ta sako kai itama yasa ta gasgata Fatun ce dae, hannu Haulat ta sa ta d'an zunguri Fatuu a hankali suka had'a ido tay mata alamar taje da ido, aje trolley d'in tay anan slowly ta nufi gwaggon duk ta kame kanta a d'an gabanta ta tsaya murya na rawa tace "G.. gwaggo......" kallon ta kawae take can kuma ta fara k'ok'arin wucewa ciki aikuwa da sauri Fatun ta durk'ushe gabanta ta kama k'afarta guda ta fashe da matsanancin kuka tana fad'in "Don Allah gwaggota ki yi hak'uri ki yafe man nasan nayi maki laifi, ke mahaifiyata ce dama ya'ya suna yi ma iyayen su laifi kuma su yafe masu Saboda k'aunar da suke masu, kiyi hakuri gwaggo banda hankali ne banda wayau shiyasa na kasa gane abunda kike jiye mun...." Dakatawa tay tana cigaba da kukan Gwaggon ta d'age kanta sama tana jin wani iri a ranta har idanunta sun fara tara kwalla, tun da Fatuu ta tafi bata k'ara lafiya ba kusan kullum sai ta zubar da kwalla har rama tayi Amadu bai fad'i ma Fatun bane don kar ta tada hankalinta, Allah ya jarabeta da tsananin k'aunar Fatuu kallon Ayshar ta take mata, ganin tak'i cewa komai ga Fatuu nata kuka yasa Haulat k'araso wa ciki inda suke itama ta duk'a ta kai hannu ta kama d'ayar kafar itama kwalla suka fara zubo mata cikin muryar kuka tace "Gwaggo don girman Allah kiyi hakuri ki yafe mata ta gane kuskuren ta na k'in goya maki baya" d'an ta6e baki gwaggon tay still kanta na d'age sama, cigaba da rok'on ta suka yi can ta sauke ajiyar zuciya tana kokarin maida kwallan idonta ta saddo kan tana kallon Fatuu da fuskar ta tay jage jage itama kallon gwaggon take, d'an nisawa tay kafin murya can k'asa tace suje ciki aikuwa da sauri Fatuu ta mik'e ta fad'a jikinta ta k'ank'ameta tana wani irin Kuka saida dai tasa k'wallan gwaggon zubowa ta d'agota suka nufi ciki ta kalli Haulat itama tace mata ta taho, wucewa tay da sauri inda kayansu suke ta jawo trolley d'in da jakar ta sannan ta bi bayansu suna zuwa saitin d'akin Fatuu Gwaggo tace su shiga kafin tay salla har suna had'a baki wurin cewa to suka nufi ciki Haulat ma ta shiga da kayayyakin, Gwaggo na shiga d'aki kujera ta nufa ta zauna tay tagumi tama rasa tunanin da zata yi kan dalilin dawowar Fatun don tasan tabbas ba hakanan ta dawo ba ana saura yan kwanaki a d'aura mata aure dole da dalili can ta mik'e dai ta kabbara sallar bayan tasa Hijab, bayan ta sallame ta kai hannu saman gado ta d'aukko wayarta da tunda tana salla taji tana ta ringing tana dubawa taga Amadu ne tabi bayan kiran ringing d'aya ya d'aga bayan sun gaisa yana d'an inda inda ya tambayeta Fatuu ta iso k'asa k'asa tace mashi eh, dama tun d'azun yake son ya kira zullumi ko Fatun bata iso ba yasa yak'i kiran sai yanzu da yay tunanin sun isa isowa sallama yay mata kawai don baisan ko basu yi Magana ba ta kashe wayar, suma su Fatun sallar sukae bayan sun gama sukae Zaune jugum, bayan da gwaggo ta gama Addu'oi shiru tay kaman mai nazari can bayan d'an wani lokaci ta k'wala ma Fatuu kira