Showing 312001 words to 315000 words out of 512766 words

Chapter 105 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1540

bari kowa ya gani ba gashi nan zuwa, wani irin sanyi ta ji a ranta ta koma ta haye saman gadon, dama Aunty shigowa tay su gaisa da Hajiya bayan sun gama gaisawar ta tambayi ya mai bed rest Hajiya ta d'an ta6e baki tace tana cikin d'aki tana ta nukurci miji zai tafi, murmushi Aunty tay tayi mata sai da safe,

bayan kaman minti ashirin da tafiyar Aunty Nameer ya shigo cikin parlon Hajiya na a d'an kishingid'e da yake yaran gidan duk yini suke a School shiyasa basu cika zuwa mata hira ba Saboda gajiya kuma wani lokacin da daddare aikin Assignment suke da angama kuma aka ci Abinci da wuri suke kwanciya sai Weekend suke samun lokaci sosae har ayi abubuwan nishad'i, kujerar kusa da ita ya nufa ya zaune yana sakin faffad'an murmushi idon ta akan shi itama d'an murmushin take mashi, gaishe da ita yayi ta amsa tana gyara zamanta idonta a kan farar ledar hannun shi mai d'auke da tambari an rubuta Special soya, ce mashi tay mi ta samu ne ya d'an kalli ledar kafin ya kalleta ya girgiza ma ta kai yace ba nata bane Yayar shi ya kawo mawa taci ko Babyn su shima ya ci, ta6e baki tay tace ai kafin ai d'aran akai kwand'i dai masu Baby, yana dariya ya mik'e yace bari ya kai mata in ta ci sai ta yan mata, Fatuu na kwance tayi tsuru ta ji sallamar shi aikuwa da sauri ta d'ago suka had'a ido, cikin d'akin ya nufo ta yunk'ura ta tashi zaune, a bakin gadon ya zauna idon shi akanta yana murmushi ya gaishe da ita ta amsa itama da d'an murmushin, hannu ya kai cikin aljihun jeans d'in shi ya fiddo maganin dake cikin farar ledar magani a jiki anyi alamar guda d'aya za'a sha ya mik'a mata da sauri ta kawo hannu ta amsa tace mashi ta gode, mik'a mata ledar hannun shi yay yace gashi nan aba baby d'in su tay murmushi kawai ta amsa yay mata fatan Allah yasa tay baccin yau harda miyau tana dariya tace Amin, mik'ewa yay yayi mata saida safe ta amsa, yana fita da sauri ta kai maganin ta tura a cikin bra dinta sannan taji ta d'an samu natsuwa sai kuma ta shiga tunanin yadda zata ba Hajiya, tunanin ko taje ta d'aukko lemu a fridge ta saka mata sai ta bata tayi wata zuciyar ta raya mata ai ba lalle tasha lemu ba da daddaren nan, gaba d'aya ta rasa tunanin yadda ya kamata tayi duk fuskarta ta yamutse can furar da Dad ke kawo masu ta fad'o mata a rai tabbas a ciki yakamata ta saka mata to amman ta Yaya, zuciyarta ce ta bata ta koma parlon don yanzu Dad ya kusa zuwa in yazo sai tasan yadda zatai ta zuba mata, da sauri ta saukko daga gadon har zata tafi sai kuma tayi tunanin tayi dubarar tafiya da abunda Nameer ya kawo mata ta kai mata, d'aukar ledar tay ta nufi parlon gabanta nata fad'uwa, cikin parlon ta fito Hajiya ta d'aga ido ta kalleta ta nufe ta, daga gefenta ta zauna tana d'an murmushi ta gaishe da ita bayan ta amsa tace mata Allah yayi kenan ta fito, shiru tay bata ce komai ba sai kuma ta mik'e ta kai mata ledar tace gashi, d'an ta6e baki tay tace ta ci abunta tunda ita ya kawo mawa da yayi niyya ai da ya had'o da ita dama ba so yake taci ba don haka ta k'oshi, hak'uri Fatun ta bata tay d'an murmushi tace mata wasa take mata taci, juyowa tay taja table gaban Hajiyar bayan ta d'aura ledar ta fiddo nannadaddar foil paper d'in ciki, warwareta tayi wani uban k'amshi mai dad'i ya daki hancin su baki d'aya, wani had'addan gasashen nama ne a iya ido kawai sai ya burge mutum irin kalar suyar da aka mashi yasha su Albasa da koran tattasai harda soyayyan dankalin turawa naman dai yayi ba k'arya😋 bayan ta bud'e ta kalli Hajiya tace don Allah taci tay d'an murmushi tace ta ci ta k'oshi in ta rage sai taci, a marairaice Fatun tace a'a ita ta fara ci in ta rage sai taci, ganin in ba ci tay ba bazata k'yaleta baà kuma dai naman ya burgeta yasa tace ta zauna to sai su ci tare sosae Fatuu taji dad'in hakan ta zauna, a nutse suke ci sai faman dakon shigowar Dad take can wata zuciyar ta bata ta tambayi Hajiyar ko zata sha lemu sai taje ta d'aukko mata daga nan ta saka mata maganin, koda ta tambaye tan ce mata tay a'a bazata sha lemu ba ruwa kawai zata sha shima sai sun gama in kuma ma an kawo mata Furar ta Shikenan ita zata sha tana d'an murmushi tace to, sai Addu'ar Allah yasa akawo furar take a lokacin, cikin sa'a basu kaiga gamawa ba Dad d'in ya shigo lokacin Fatun kad'ai ke ci Hajiya ta daina ci, yana ganin su yay murmushi yana sanye da farar shadda babbar riga ya k'araso cikin parlon yana fad'in shagali suke haka Hajiya na yar dariya tace Nameer ne ya kawo ma d'an su abun dad'i ita kuma ta cinye mashi duk sukai dariya, zama yay ya gaishe da ita bayan ta amsa Fatuu ma ta gaishe da shi ya amsa cike da kulawa ya tambayi ya take badai wata matsala ko tace mashi eh yace haka ake so, yunk'urawa yay ya mik'e ya nufi kan c-table ya d'aura ledojin yace to shima ga nashi a had'a aci gaba da party duk sukai dariya Hajiya tay mashi godiya da sa Albarka Fatuu ma tayi mashi godiya yay masu saida safe, wani irin bugu k'irjin Fatuu ke yi ga k'oshi ga kwanan yunwa, ga dama ta samu amman bata san taya zata zuba ba, can ta mik'e tana fad'in bari ta zubo mata a cikin cup Hajiyar ta d'aga mata kai, hannu ta kai za ta d'auki ledojin furar Hajiya tace mata ta bar su taje ta d'aukko cup d'in mana da sauri tace to, kaman ta saka ihu haka take ji ta nufi Fridge d'in, bayan ta d'aukko glass cups d'in ta dawo ta kai hannu ta fiddo robar furar tana cikin bud'ewa taji Hajiyar tace ta matsu bari ta je toilet ta dawo yadda zata sha a nutse har Fatuu bata san lokacin data washe baki ba tace to, d'aukar sandarta tay dake gefe ta nufi hanyar shiga d'akin ai tana shigewa jiki na rawa Fatuu ta kai hannu ta fiddo ledar maganin sai kerma hannun ta Keyi duk ta rud'e tana yi tana kallon kopar shigowa da kuma ta bedroom, fiddo guda d'aya tayi har zata saka zuciyarta ta raya mata ba lalle ya narke da sauri ba don furar kitif take kuma k'ilan ma guda d'aya bazai gaurayeta ba har yayi aiki, k'ara ciro d'aya tay da sauri ta maida ledar cikin bra d'in duk ta rud'e, kamo ha6ar kallabin ta tay ta saka magungunan ta rufe ta kai baki ta d'an tattauna sannan ta bud'e ta kai bakin robar furar ta zuba, sakin ha6ar tay da sauri ta rufe robar ta d'auka ta hau Jijjiga ta, maida ta tay ta aje a saman table d'in tana ta zare ido da sauri ta gyara kallabin ta sai faman zare ido take zuciyarta ta shiga raya mata ta daidaita natsuwar ta kar a gane ta, fiddo d'ayar robar furar tay ta bud'e har lokacin hannunta rawa yake ta zuba a d'ayan cup d'in bayan ta rufe robar ta d'auki cup d'in ta fara sha, gaba d'aya idanunta na akan kopar Bedroom har bata san tana kai cup d'in bakin hancinta ba sai taji take ankara, bayan wani lokaci Hajiya ta sako sandarta ganinta wani irin Fad'uwa gaban Fatuu ya hau yi, k'arasa fitowa tay ta shigo cikin parlon, bayan ta koma inda ta tashi ta zauna da sauri Fatuu ta aje cup d'in zata zuba mata tace ta barshi bari ta zuba, idanun Fatuu akan furar dake sauka cikin cup d'in tsoronta kar taga 6ar6ashin maganin, bayan ta gama zubawa ta d'auka ta kai baki duk da hakan hankalin Fatuu bai kwanta ba ta shiga tsoron kada kuma ta tauna maganin, har Hajiya ta shanye tata Fatun bata gama ba saida tayi mata magana kan tayi sauri ta gama ko taje ta watsa ruwa ta cire wannan d'amammun kayan ta kwanta tace to, bayan ta gama ta maida robobin cikin ledojin ta kwashe su ta nufi bakin k'opa inda dustbin yake ta saka, saida safe tay ma Hajiyar tace mata Allah ya tashe su lafiya, koda ta shiga toilet ba'a nutse tayi wankan ba, bata d'au lokaci ba ta gama bayan ta fito cikin sand'a taje ta lek'a cikin parlon ta hango Hajiyar zaune a inda ta barta idon ta akan Tv, jiki a mace Fatuu ta juyo ta dawo cikin d'akin ta nufi bakin gado ta zauna jikinta sanye da rigar wanka, tunanin kodai maganin bazai mata aiki ba ta shiga yi, ta dan d'auki lokaci a haka can ta mik'e sukuku da ita ta nufi wurin kayanta, doguwar rigar bacci ta fiddo bayan ta saka ta d'auki ta wankan ta nufi toilet, koda ta fito saida ta sake zuwa ta lek'a still Hajiyar na a yadda take, yanayin fuskar Fatun ne ya canza idanunta suka ciko da k'walla ta nufi gado, gajiya tay da zaman a hankali ta kwanta tay shiru k'walla suka fara gangaro mata, a hankali take kai hannu tana gogewa k'wallan, sosae ta damu da tafiyar da Haisam zai yi gashi bata san lokacin da zai dawo ba don da ta tambaye shi ce mata yake daya samu time zai zo ya ganta,

"Fateema da kika ji ni shiru ba sai ki lek'o ba kiji lafiya ban taso ba ina can bacci ya fara d'aukata akan kujera" Hajiya ce data shigo tay Maganar tana yi tana hamma, gwalo ido Fatuu tay tayi shiru da sauri ta runtse idonta tana jin Hajiyar na fad'in ko bacci take a haka, gadon ta nufa bangaren da take kwanciya ta hau ta kwanta sai zabga uwar hamma take, tana kwanciya taci gaba da baccin dama da k'yar ta kawo kanta d'akin yau dai ko zaman yin Addu'a bata yi ba, Fatuu na jin saukar numfashinta da k'arfi ta gane tayi bacci, tashi tay zaune idonta akan Hajiya sai kace ta dad'e a kwance a yadda take baccin, hannu ta kai ta d'aukko wayarta ta duba time har k'arfe sha d'aya tayi, tunanin ta k'ara bata time tayi tay zaune tana yi tana kallon ta gaba d'aya ma sai taga time d'in bai gudu, bayan kaman minti goma ta yanke ta tafi sai kuma tay tunanin ta gwada tashin Hajiyar ta gani ko baccin bai yi nauyi ba in ta tashi sai tace mata dama taga bata canza kaya bane, da wannan tunanin ta mik'e ta zagaya side d'in da take ta fara kiran sunanta shiru hannu ta kai ta d'an bubbuga hannunta tana cigaba da kiran nata nan ma shiru, d'agowa Fatuu tay tana murmushi ta nufi wurin kayanta ta curo Hijab, bayan ta saka ta nufi bakin gadon ta d'auki wayarta, saida ta je ta ja duvet ta rufe ma Hajiyar rabin jikinta ta kashe wutar d'akin sannan ta nufi hanyar fita, a parlon ma saida ta kashe kayan kallon da hasken cikin shi sannan ta nufi hanyar fita, saida ta tsaya ta lallek'a ta tabbatar ba kowa sannan ta fito sauri sauri gudu gudu ta nufi hanyar baya, tana tafiya zuciyarta na raya mata to yanzu in Hajiyar ta farka kuma fa, girgiza kai tay ta tabbatar ma kanta tunda maganin yayi aiki bazata farka ba tasan har ta koma don maganin nada k'arfi gashi biyu ta saka mata,

Lokacin data haye benen k'opar parlon nashi a rufe take, da sauri ta d'ago wayarta ta shiga k'ok'arin kiran shi, yana yin picking tun kafin yace wani abu tace mashi yazo ya bud'e mata k'opa saida yaji mamakin hakan ya tambayi wace k'opa tace mashi ta shigowa part d'in shi ta baya, yana bud'e kopar suka had'a ido ta sakar mashi murmushi yana sanye da rigar bacci kimono broad chest d'in shi a bud'e, d'an waro ido yay alamar mamaki da sauri ta fad'a mashi ya kai hannu ya rungume ta, komawa yay ciki da ita bayan ya tura k'opar ya d'ago ta har lokacin murmushi take, da alamun mamaki yace mata ya akai tazo nan yanzu, farko shiru tay ta shiga tunanin bazata ce mashi magani ta bata ba sai kawai tace mashi ba tun d'azun take fama da ita ta barta tazo ta had'a mashi kaya ba amman ta k'iya shine yanzu da taga tayi bacci ita kuma ta taho, d'age gira yay sai kuma yay faffad'an murmushi yace mata bata tsoron ta tashi taga bata nan ta d'an tura mashi baki bata ce mashi komai ba,

"Yanzu kayan kika zo had'a man kenan?" ta d'aga mashi kai wani kallo ya bita dashi ta tura mashi baki, d'an murmushi yay yace mata to ai shi ya riga ya had'a kayan nashi ya za'ai kenan da sauri ta fad'a jikinshi tana fad'in suje a wargaza su ta sake had'a mashi, sosae yake dariya sai mutsu mutsu take mashi da kanta a chest nan take ta fara turning nashi on, hannu ya kai ya murd'a key k'opar ta rufe ya kai hannu ya d'auketa ya nufi ciki da ita. Duk yadda Haisam yaso kar ya xamo uncontrollable kaman yadda yake duk ya kasance da ita abun ya ci tura ba kamar kuma daya kasance ga halin da take ciki gaba d'aya ta canza mashi, bayan ya samu natsuwa hak'uri ya shiga bata yana tambayar is she Ok, shiru bata amsa mashi ba ta duk'unk'une guri guda, Jijjiga ta ya shiga yi yana kiran sunanta amman shiru, da sauri ya sauka daga saman gadon ya je ya kunna Switch, har saida gaban shi ya fad'i ganin yadda tay ta runtse ido hannunta guda dafe da cikinta, wani irin bugu gaban shi yay a rud'e ya dawo ya hau gadon, d'ago ta yay ya fara tambayarta lafiya miya faru shiru bata ce komai ba sosae ya razana, maida ta yay ya kwantar ya fara k'ok'arin sauka yana fad'in bari ya kaita hospital, ji yay ta ruk'e mashi hannu da sauri ya kai idon shi kanta kawae sai gani yay ta kyalkyace da dariya, wani kallo yake bin ta da shi ya d'an yamutsa fuska ta d'age mashi gira kawai sai ya yarfa hannu yace "Zarah wannan wasa ne?" Yadda ya kwa6e fuska yasa ta k'ara kyalkyacewa da dariya, hannu ya kai ya dafe goshin shi ya maida idon shi k'asa, da sauri ta tashi zaune ta kai hannu tana k'ok'arin cire mashi hannun tana fad'in yayi hak'uri, k'in bata dama yay ta cire hannun a shagwabe tace in bai hak'uri ba Baby zai fito ya bashi hak'uri yanzun, juyowa yay yayi mata wani kallo idanunshi sun d'an yi ja, wara mashi ido tay tana murmushi ya d'an harareta, ta6e baki tay ta kai hannu ta kama kunnuwanta ta furta "i'm very sorry My Hubby bazan k'ara ba" yadda tayi ne ya bashi dariya yayi har fararen hak'oran shi suka bayyana ya kai hannu ya jawota ya rungume ta a wurin kunnanta ya rad'a mata so take tasa heart d'in shi tay bursting ne da sauri ta girgiza mashi kai yace to karta k'ara mashi irin wannan wasan da sauri ta d'aga kai, tambayar ta yay wai yaushe zata girma ne tana murmushi tace mashi ba rana, zamewa yay ya kwanta tare da ita ta yadda kanta na a saman chest d'in shi, shafa kanta ya shiga yi wani irin nishadi suke ji suna haka taji ya furta Allah yay mata Albarka tana murmushi idanunta a lumshe ta amsa tace shima Allah ya yi mashi Albarka ya amsa da Amin a haka bacci yay awon gaba da ita, jin saukar numfashin ta a hankali yasa shi kwantar da ita ya saukko ya nufi toilet,

Kiran sallar Farko ya farka kamar koda yaushe, tashi yay zaune ya kai hannu ya kunna lamp, juyowa yay ya sauke idon shi a kan Fatuu dake ta shan bacci, ji yay kamar ya k'yale ta amman bai son Hajiya ta tashi taga bata nan ya zama wani issue kuma duk da bai san ma ko ta tashi ba, tashin Fatun yay bayan ta bud'e ido yace ta tashi ya rakata kar Hajiya ta tashi tana jin hakan da sauri ta mik'e, tare suka fito ta baya, lokacin da suka shigo cikin main parlon a d'arare Fatuu take, tare suka shiga cikin parlon Hajiya ya tsaya anan yace ta duba taga ko ta tashi, gabanta na d'an Fad'uwa ta nufi Bedroom, cikin sand'a ta zagaya side d'in da take kwanciya saida ta d'an saurara sannan ta kai hannu ta kunna lamp d'in wurin,tsaye tay tana kallon Hajiya dake kwance kan gado tana ta bacci, d'an murmushi tay don ta fahimci bata tashi ba don data canza kaya zuwa na bacci Saboda bata kwanciya ba tare data saka kayan bacci ba, juyawa tay ta koma parlon ta fad'i mashi bacci take ya jinjina kai sai kuma yace mata to in ta tashi da daddare fa bata gan ta ba, d'an waro ido tay sai kuma tace ita dai in tayi mata magana kan hakan to zata ce shi yazo tana bacci ya d'auketa, yar dariya yay ya kai hannu ya kamo ta jikinshi yace sharri ko tanata dariya, saida yay pecking kumatunta sannan ya juya ya tafi ita kuma ta nufi Bedroom d'in, bayan ta shiga cikin sand'a ta nufi side d'in da take kwanciya ta cire Hijab d'in jikinta sannan ta hau gadon ta kwanta, tunawa tay da she needs to take bath a hankali ta tashi saida ta kallo Hajiya sannan ta mik'e ta nufi toilet, tana fitowa aka fara kiran salla na biyu nan take alarm

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login