Showing 462001 words to 465000 words out of 512766 words
Chapter 155 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1644
zata kira Kamalun ma tayi mashi magana Gwaggon tace gashi can ɗaki bari ta bashi tace to, bayan sun gaisa ta tambayi ya karatu ya amsa mata tambayar shi tayi wai mike tsakaninshi da Farha ne yace mata shi wllh ba komai daga dai abotar data ce mashi tana son suyi shikenan Fatuu tace to ita bata son yana amsar mata abubuwa ko yace zai tambayeta wani abu don zai iya zama matsala duk abunda yake so ita ya kirata in sha Allahu indai baifi ƙarfinta ba zata mashi yace mata to tare da yi mata godiya daga baya sukai sallama.
Bayan su Farha sun shiga Camp sosae take kiran Kamalun a waya su kuma yi Vedio call a lokacin aikin da ake yazo kan inda suke zaune aka buƙaci sai sun tashi Gwaggo ta yanke kama masu hayar inda zasu zauna kafin a gama anan unguwar, a bakin Kawu Mani Hajiya taji zancen hayar da Gwaggo zata kama ta kirata tace ba sai ta kama wata haya ba tunda ga wurin zama a gidanta su dawo nan kawai zuwa a gama aikin, ba dama ta musa mata tayi godiya sosae, a ɗakin Tk Amadu da Kamalu suka koma sai ita kuma Gwaggo Hajiya ta bata ɗakin dake kusa da nata, tun gwaggo bata saki jiki ba har dai ta saki in dai tana gida tare suke aikin gidan da Saude har Hajiya saida tayi mata magana kan waya sakata ta rinƙa yin aiki tana dariya tace mata ta saba ne in bata yi ba jikinta bai mata daɗi Hajiyar tace to kar dai taja mata sharri tunda ita dae bata sakata ta rinƙa yin aiki ba Maganar har saida taba Gwaggon da Saude dariya, zaman su a gidan gwanin daɗi tare suke cin Abinci da Hajiyar wani lokacin harda su Amadu in suna gida, ana haka su Farha suka fito daga Camp lokacin data dawo ta iskesu a gidan sosae ta nuna jin daɗin hakan shaƙuwa sosae taci gaba da shiga tsakaninsu da Kamalu koda yaushe in tana gida zaka gansu tare in kuma suna shago ta bishi can har Assignment in an ba Kamalun take taya shi suyi harda lesson suke yi ta koya mashi turanci da yake tana yawan yi mashi magana da turanci ya ta6a ce mata shi ba sosae ya iya ba shine take koya mashi ita kuma sai tace ya koya mata fullanci yadda suke abun gwanin sha'awa in suna yi a gaban su Hajiya da Gwaggo suyi ta burge su shidai Kawu Amadu yanzu ya zura masu ido kawai har abinci wani lokacin tare suke ci su biyu.
A kwana a tashi cikin Fatuu nata ƙara girma yana gab da shiga wata tara, ta bangaren Arɗo kuwa tuni an kai shi Asibitin da taimakon Khalid anyi mashi duk abunda ya dace ba'a samu wata babbar lalura ba a tattare dashi ba kawai tsufa ne da gajiya sai yan ƙananun cututtuka an bashi magunguna da abubuwan da zai kiyaye ba laifi yanzu ya ƙara samun lafiya duk harkokin shi na mulki kuma Baffan su Fatuu ya ɗaura akai masu tsegumi nata yi. Lokacin da cikin Fatuu ya kai wata tara har an kammala aikin gidansu Gwaggo gida ya zama na yan gayu wanda yana ɗaya daga cikin gidaje masu kyaun gaske a unguwar abun sai wanda ya gani yanzu ta gate ake shiga gaba ɗaya harabar gidan interlock ne duk da bata da girma sosae don ginin ya cinye filin amman Mota biyu zata iya shiga daga jikin gidan gefen gate aka fitar ma da kawu Amadu babban shago wanda yana da ƙopa da zai rinƙa shiga gidan ta ciki, gidan part biyu ne na Gwaggo da kuma na Amadu sai akwai ɗaki da falo daban matsayin na baƙi, a kowane bangare na Gwaggo da Amadu akwae ɗan babban falo sai Bedroom guda biyu da toilet a tsakiyar su sai kuma Kitchen daya sha cabinet sai akwae toilet na waje cikin haraba, iya fentin gidan da yadda aka tsara ginin da ƙopopi zuwa winduna da fitilun da aka saka abun kallo ne kana ganin ginin zaka san ba ƙaramin kuɗi aka kashe ba su Gwaggo baki yaƙi rufuwa sai farinciki ake mutane yan'uwa da abokan arziƙi nata zuwa yin Allah ya sanya Alkhairi har Hajiya ma tazo taga gida itama ta yaba sosai ta kuma yi Addu'o'i, lokacin da Fatuu taga Vedion gidan zo kaga murna harda cewa ba don cikin jikinta yayi girma sosae ba da sai tayi tsallan murna Gwaggo nata dariya haka Mino ma data gani ita harda tsallan tayi tace bada daɗewa ba zata zo ta gani Gwaggo tace ta bari tunda ga bikin Amadu ya matso sai tazo tace ita dai tana son zuwa kusan wata biyar fa yanzu rabonta da Katsina in bikin yazo ta ƙara zuwa, Bayan gama ginin kuma sai ga kuɗi Haisam ya turo ma Kawu Amadu wai a siya furniture Gwaggo harda ƙwalla tayi ma Haisam da tasa aka kira mata shi Vedio call tace hidiman nan tayi yawa shima yaji da nashi hidindimun yace mata ba wani abu ai duk ɗaya ne, godiya sosae suka yi mashi harda Baffan su Fatuu ya yi mashi godiyar, Kawu mani ma yazo yaga gida ya yaba ya kuma yi Allah a sanya Alkhairi sannan shima ya bada gudunmawar shi ta siyan furniture har Baffan su Fatuu da Hajiya duk saida suka bada gudunmawar kuɗin siyan furniture daɗi har yayi ma Gwaggo yawa sai godiya take ga Allah, cikin sati guda aka zuba furniture ɗin gaba ɗaya Bedrooms ɗin part ɗin gwaggo an saka set na gadaje sai falon ma an saka kujeru masu kyau da carpet harda kayan kallo da labulaye komai dai na ƙawata wuri an saka kai kace part ɗin yarinyar mace ne, haka part ɗin Amadu a bedroom guda ɗaya an saka set ɗin gado sai falon an saka carpet da labulaye sai ɗayan ɗakin mai falo wanda yake matsayin na baƙi a bedroom ɗin irin ƙatuwar katifa da bata hawa gado aka saka da carpet da labulaye sai falon kujerun falon gwaggo na da aka gyara suka koma sababbi aka saka ko ina dai ya fito yayi kyau daidai daidai.
Cikin Fatuu har yayi wata tara da yan kwanaki lokacin su twins shekararsu guda da wata biyu har sun yaye kan su don da kansu suka daina shan Nono, Ranar wata laraba da safe gidan ba kowa sai ita kaɗai da mai aikin su Fanan da Haisam na wurin aiki haka su twins ma suna makaranta tana cikin baccin safen data koma wani irin ciwon mara ya tasheta, jin tana jin fitsari yasa ta lalla6a ta tafi toilet don tayi, tana duƙawa don yin fitsarin taga discharge irin wanda ta gani da haihuwar su twins tana gani ta gane haihuwa ce ba arziƙi ta fito daga cikin toilet ɗin ta nufi wayarta dake a gefen filo ta shiga kiran Fanan dama kullum sai tace mata data ɗan ji ciwo ko yaya ne in bata gida tayi sauri ta kira ta, tana fara yin ringing Fanan ɗin ta ɗaga kafin Fatun tace wani abu ta rigata tambayar haihuwan yazo ne cikin nishi tace mata eh gata nan mararta ta fara mata ciwo da sauri tace Ok gata nan zuwa ta katse kiran, tana katse kiran mai aikin su ta shiga kira wadda babbar mace ce baturiya bayan ta ɗaga ko amsa gaisuwar da take mata bata yi ba cikin sauri ta bata umarnin taje part ɗin Fatuu ta fara labour ta taimaka mata ta shirya gata nan zuwa da sauri mai aikin ta amsa mata tana katse kiran ta nufi part ɗin Fatuu, bayan wasu mintuna Fanan ɗin ta iso a Motar asibitinsu tare da wasu nurses guda biyu lokacin da suka shiga bedroom ɗin da Fatuu take ta shirya da taimakon mai aikin nasu ciwon kuma ya ɗan ƙara tsananta ba 6ata lokaci suka ɗaurata akan wheelchair da nurses ɗin suka shigo da ita Fanan kuma cikin sauri ta ɗauki abubuwan da za'a buƙata dama ashirye suke, saida suka hau hanya sannan ta kira Haisam ta sanar mashi nan take hankalinshi ya tashi jin Babyn shi na naƙuda don bai manta yadda aka sha wanccan gumurzon ba da sauri yace ma Fanan gashi nan zuwa asibitin don Allah kada ta bari ta wahala sosae tace mashi to suyi mata addu'a, suna isa asibitin aka nufi labour room da ita aka shiga yi mata duk abunda ya dace kan kace mi naƙudar ta ida kankama gaba ɗaya Fanan ta ruɗe sai faman yi mata sannu da Addu'o'i take kaman zata mata kuka, cikin ikon Allah basu fi minti talatin da zuwa ba ta haiho san6aleliyar jaririya dama tun wurin scanning an faɗi masu mace ce sai gashi hasashen su ya tabbata zo kaga murna a wurin Fanan sam ta kasa rufe baki sai faman faɗin Alhamdulillah take, koda Haisam ya iso ai saidai ya taras da Baby shima har fuskarshi ta kasa 6oye farincikin sosae yaji daɗin yadda bata sha wahala ba kamar tasu twins, lokacin da aka bashi Babyn zuba mata ido yay yana kallonta da murmushi sak fuskar Fatuu ta ɗaukko in akwae abunda za'a ce ta ɗaukko nashi to ƙilan saidai ko farinshi don jajir take da gani zata fi Fatuu fari amman komai na fuskarta na Fatuu ne Fanan ma saida tace Zarah ta biyo, tun a asibitin bayan yayi mata huɗuba ya raɗa mata suna AISHA wato sunan Mahaifiyar Fatun, yan Nigeria sai farincikin jin haihuwar ake kowa daya ga Babyn a Vedio sai ya faɗi kamanninta da Fatuu, Sosae itama Fatun tayi farinciki ganin Babyn data haifa koda Fanan ta faɗi mata sunan da aka saka mata saida tayi ƙwalla wata irin ƙaunar yarinyar ta mamaye mata zuciya. Bayan sati biyu da Haihuwar suka iso Nigeria nan aka Shiga shirin yin suna wanda na iya yan Family ɗin su ne, sati guda da dawowarsu akayi sunan duk yan'uwa sun zo su Gwaggo da Hajiya har Aunty Mareeya ma tazo Farha dai na Katsina bata biyo Hajiya ba, su Hajia Zainab ma sun zo Fauzy dai ba'a zo da ita ba a Nasarawa aka barta don tayi nauyi sosae haihuwa ko yau ko gobe gashi itama an tabbatar da yan biyu ne, Aunty Laila ma ciki ne da ita har ya fito sosae don zaiyi wata biyar, Mino na ganin cikin Lailan ta ƙara shiga damuwa dama tana ta zura ido taga ta samu ciki amman shiru har yanzu kusan wata bakwai da yin aure, bayan an gama yin shagalin sunan da daddare Mino ta samu Fatuu a Bedroom ɗinta cikin sa'a ita kaɗai ce sai Baby Esha kamar yadda aka yanke za'a ringa kiranta, a bakin gado ta zauna Fatuu na kallonta ta gane akwae abunda ke damunta cike da kulawa tace "Amaryarmu ya akai kamar akwai abunda ke damun ki ko?" kai Minon ta ɗaga mata Fatun ta tattara hankalinta gaba ɗaya a kanta tace ta faɗi mata miye kaman zata yi kuka tace dama ce mata zata yi ita taga har yanzu bata samu ciki ba kuma ga Aunty Laila nan da aka yi bikinsu tare har ta samu nata harma ya girma Fatun tay kasaƙe tana kallonta tama rasa mi zata ce mata can ta tambayeta tana period lafiya lou da sauri tace mata eh tana yi kamar yadda ta saba kuma shina abunda tace mata sai anayi ake samun cikin sosae suke yi, kunya ce ta kama Fatun ta juyar da kanta gefe a ranta ta raya bata san ranar da Mino zata rabu da wauta ba, juyowa tayi Minon ta ƙura mata ido a nutse tace mata ta kwantar da hankalinta tunda ba wata matsala zata samu dama ba daga anyi aure ake samu ba kowa da yadda yake har ta bata misali da Fanan tace mata bata ga har yanzu itama bata samu ba kuma ga Auntyn su Nameer ma itama har yanzu bata haihu ba....katseta Minon tayi idanunta sun cika da ƙwalla tace yanzu itama bazata haihun ba kenan da sauri Fatuu tace "ni bance bazaki haihu ba, kawai na baki misali ne don haka ki kwantar da hankalinki don shi in ka tada hankalinka to baka samu, sannan kada ki sake kiyi ma wani irin wannan Maganar da kikai man za'a ɗauke ki mara kunya ne in dae kina da wata matsala game da gidan auren ki ni zaki rinƙa sanar mawa kamar yadda kikai yanzu" da sauri ta ɗaga mata kai Fatuu tace ta saki ranta in sha Allahu kwanan nan zata samu Minon tayi ɗan murmushi kawai, miƙewa tay zata tafi Fatuu ta tambayeta anan zata kwana ne tace mata eh tace to ta kwanta anan mana tunda ita kaɗai zata kwana su twins ba anan zasu kwana ba Minon tay ɗan jim kafin da ƙyar tace mata Ya Nameer yace a part ɗinshi zasu kwana Fatun tay ɗan murmushi tare da ɗaga mata kai tace taje saida safe ta juya ta tafi Fatuu nata kallonta har ta fice ta ɗan girgiza kai a ranta ta raya ta zata haihuwar sauƙi ne da ita, dasu Gwaggo zasu tafi Fatuu ta bata akwatuna set guda data siyo ma Amadu acan na lefe tace mata da set biyu ma taso ta siyo to kayan zasu yi yawa ne Gwaggon tace ai dama sun siya set guda, da shi Amadun ma set biyu yaso a siya tace mashi tunda Fatun tace zata taho da wasu a barsu haka. Bayan sati biyu da yin sunan Fatuu Fauzy ta haiho twins duk mata saidai ita Cs aka mata, yaran saidai ace Tubarkallah masha Allah sak Sameer suka biyo gasu identical ne suma kamar na Fatuu amman su ta gashinsu ake banbanta su Hassanar nata baƙi ne wuluk hussainar kuma kalar na sameer ne baida baƙi sosae kowa yaga yaran sai ya yaba zo kaga murna wurin dangin Fauzy karma Aunty Mareeya taji sam bakinta ya kasa rufuwa sai kiranta ake itama ana mata barka, saboda aikin da aka mata akace baza'ai taron suna ba saidai duk akaje Nasarawa aka yi masu barka aka kuma yi ma maijego alheri sabon Baba Sameer sai nan nan yake da Babies ɗin da kuma mamansu ko kunyar mutane bai ji yaran sun ci sunan Mahaifiyar Sameer data Fauzy wato Zainab da Haleema. Sati guda da haihuwar Fauzy Fatuu ta tafi Katsina dama haihuwar ta tsaidata lokacin saura sati ukku bikin Amadu da Tk, saida taje ta ƙara jinjina yadda gidan nasu ya haɗu, tana zuwa Washe gari suka tafi kasuwa da gwaggon don ƙarasa siyayyar kayan lefen daga can wurin K.b tailor suka wuce dama Fatuu tasa Kawu Amadu ya kai mashi wasu kaya ya ɗinka lokacin da suka je har ya gama su suka bashi wasu cikin wanda suka siyo Fatuu tace don Allah nan da sati ɗaya suke son su kai lefen za'ai, yana dariya yace ai tasan bai mata wasa ko don kada ya 6ata ran Maigidanshi Haisam itama saida tayi dariya don ta fahimci da biyu yayi Maganar saboda tun farkon fara kawo mashi ɗinkinta da akai, bayan zuwan Fatun tayi ma Aunty Mareeya magana kan tana son magunguna masu kyau da Haulat zata yi amfani dasu ta can bangaren Haulat ɗin ma tana amfani da wasu da aka kawo mata daga Nijar, kwana biyu da zuwan Fatuu aka kai lefen Tk akwatuna set ukku masu guda huɗu guda sha biyu kenan kuma bako ƙwandalar Tk a ciki komai Hajiya tayi mashi sai su Senator da Hajiya Maryam da suka bada gudunmawa, a yadda Hajiya ta tsara a nan part ɗinta zai zauna Senator har Maganar siya mashi gida yayi amman tace a kusa da ita take son ya zauna, sam hakan baima Hajiya Maryam daɗi ba tace ma Hajiyar ba gwara ta bari a siya mashi gida ba yanzu nan part ɗinta a ina zai wani zauna Hajiyar tace lafiya lau tunda falonta yana da girma sosae zata sa a maida shi bangare biyu sai suyi amfani da ɗaya bedrooms kuma tunda guda huɗu ne biyu ita ke amfani dasu biyu kuma na baƙi sai su zauna a ɗaya in kuma biyu suke buƙata sai ta basu na baƙin sai ɗayan nata ya koma na baƙi Hajiya Maryam ɗin ta nuna yanzu kuma idan wata hidima ta kama ko suka zo taya bedroom ɗaya zai ishe su in ta basu biyu Hajiyar tace to ba ga Bedroom ɗinta ba sannan ga wangamemen gidan Yayanta can a G.r.a sai a tafi can, duk da haka ta nuna hakan bai mata ba ƙarshe Hajiya tace shikenan in taga da takura daga baya zata sa a ƙara wasu Bedrooms ɗin a can ɗayan bangaren falon wurin Dining Area tunda akwae fili sai a barsu matsayin na baƙi amman tare zata zauna da Tukur don matsayin ɗa yake a wurinta yaron da tun yana ɗan ƙarami aka bata shi miye don ta zauna tare da iyalinshi dole Hajiya Maryam ta haƙura, har kiran Tk Hajiya tayi ta faɗi mashi yadda ta yanke game da zaman su tare tace bata san ko hakan zai takura mashi ba amman in yafi son zama daban lafiya lou sai a siya mashi gidan bawan Allah harda kukan daɗin shi yace mata Wllh dama damuwarshi kenan yadda zai rabu da ita yana kuka yake mata godiya da Addu'o'i, har iyayenshi ya kira yana kuka ya faɗi masu irin gatan da Hajiya tayi mashi Mahaifinshi har saida yazo yayi mata godiya shima harda kukan nashi, to Kamar yadda Hajiyar tace haka akayi ma falon nata ba raba shi akai ba kawai anyi wani ɗan gini mai kamar ado ta yadda falon ya koma bangare biyu sai Kitchen ma da yake yana da faɗi da tsawo shima aka maida shi bangare biyu sannan gaba ɗaya gidan aka yi mashi Fenti mai kyau don ba wani gyara da yake buƙata komai lafiya lou don gini ne bana wasa ba. Ana saura sati biyu bikin aka kai lefen Haulat akwatuna takwas harda babbar ghana must go, ba laifi an zuba