Showing 267001 words to 270000 words out of 512766 words

Chapter 90 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1546

ta k'arasa tare da d'aga mashi wayar don ya gani, in bango ya tanka to shima ya tanka haka yanayin fuskar tashi ma bai canza ba, yan kame kame Fauzy ta shiga yi tana haka idanunta suka sauka akan Wayar shi da glass d'in dake yashe a k'asa, da sauri ta duk'a ta d'aukko su Allah yaso glass d'in bai yi komai ba, tana juya wayar zata mik'a mashi taga glass d'in yayi lafiyayyun tsaga har kusan hud'u, zaro ido tay ta bud'e baki gabanta ya shiga wani irin bugu, ganin reaction d'in fuskar ta yasa slowly ya kai idanun shi kan wayar idanunshi suka sauka akan glass d'in dake a tsattsage, wani irin kallo ya d'ago yana mata da sauri ta fara ja da baya tana yamutsa fuska daga d'an can gaban shi ta tsaya, kawai sai gani tay ya fara nufota, tana shirin k'ara ja baya cikin husky voice d'in shi ya furta "Stay where you are!!!" har saida cikinta ya yamutsa, a gabanta ya tsaya ya mik'a mata hannu da sauri ta mik'a mashi wayar ya k'i amsa ta bishi da ido cike da tashin hankali, a kausashe ya furta ta bashi glass hannunta har kerma yake ta mik'a mashi ya amsa, saka shi a idanun shi yayi bayan ya gama ya tsaida kallonshi akanta duk da bata ganin idanun, k'ara Mik'o mashi wayar tay murya na rawa tace don Allah yayi hak'uri wllh bada niyya bane, banza yay mata sai da ya mula sannan ya furta "ki biya shi!" Wani irin miyau Fauzy ta had'iya ko ba'a fad'i mata ba daga ganin wayar tasan mai tsada ce balle kuma daya kasance ga wanda ke rike da ita, da yake dare ne kowa ya gaji wasu kuma basu a gidan ba wasu mutane da ke shigowa wurin sai wanda ba'a rasa ba sun fito su kuma ba lalle su fahimci abunda ke wakana ba don daga yanayin su sai kaga kaman magana suke, Magiya taci gaba da yi mashi kan yayi hak'uri tana cewa tasan bazata iya biyan shi ba, ringing wayar ta fara yi ta kalli wayar kafin ta kalle shi tana kikkafta idanu, hannu ya mik'a ya amsa ya furta mata "ki biyo ni" daga haka ya juya, tsaye tay duk da taji abunda yace aikuwa ya juyo cikin daka tsawa tace "I told you to Follow me!!!" bin shi tay ya nufi hanyar fita daga cikin parlon, daidai gaban wata Mota da aka parker a gaban Entry Hall ya dakata itama ta tsaya daga d'an nesa dashi, dama wayar da ya taho yana yi umarni yake badawa na azo a d'auke shi suka yi karon, hannu ya kai ya bud'e kopar gaba, da kai yayi ma driver d'in alamun ya fito, bayan ya fito tsayawa yay daga gefe ya d'an russuna kai, ce mashi yay yaje zai driving da kan shi yayi mashi godiya ya juya, juyawa yay ya kalli Fauzy da tay tsuru tsuru a kausashe yace "come and get in to the car!" Nan take k'wallan da suka tarun mata a ido suka fara zubowa taci gaba da yi mashi magiya tana yayi hak'uri don Allah, kai ya jinjina ya d'an cize baki can cikin d'an d'aga murya yace "I don't allow anyone to argue with me! Ki shiga Mota else, yanzu zan sa aje a kulle ki!" yarfa hannu Fauzy ta shiga yi a hankali ta fara fad'in ta bani, matsawa ta fara yi a hankali tana tunkarar Motar, ganin yadda take tafiya ya k'ara ce mata kada tay wasting time nashi, tana niyyar bud'e k'opar baya ya galla mata wata muguwar harara ba shiri ta fasa bud'ewa da kan shi yay mata alamar taje ta shiga gaba ta zagaya tana kuka k'asa k'asa, saida ta shiga sannan ya kai hannu cikin aljihun jeans d'in shi ya fiddo wani farin hanky ya shimfid'a a saman seat d'in sannan ya shiga, bayan ya zauna da k'arfi ya rufo k'opar, dama Motar a kunne take aikuwa a tsiyace ya ja ta bayan yasha round d'in ya Mik'i hanyar Gate ya fuce............

*ASM 081*


~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~



*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


.........Suna fita daga cikin gidan suka hau hanya, hankalin Fauzy in yayi dubu to ya tashi tunanin ta ina zai kai ta kuma mi za'a mata, basu dad'e da hawa titi ba wayar Fatuu dake hannun Fauzy ta fara ringing, a hankali ta juya ta kalli Sameer da idon shi na akan titi yana driving, a d'arare takai hannu zata d'auka a kausashe taji yace "Don't pick it!" fasa d'agawar tay ta juya ta kalle shi fuskarta a yamutse har lokacin k'walla na zubo mata, wani kiran ne ya sake shigowa bayan wanccan ya yanke taji yace ta kashe wayan gaba daya, cikin muryar kuka tace "Don Allah ka bari in d'auka in fad'i mashi bana gidan, Ya Haisam ke kiran matar shi wayarta ce dama ita na taho in kai mawa Saboda yanata kira shine har na buge ka ban gani ba" banza yay mata yana ta driving d'in, saida kiran ya kusa yankewa ya bata umarnin ta d'aga, hannunta har d'an rawa yake tay picking kiran, tun kafin yace wani abu ta riga shi ce mashi k'awarta ce wayar na a hannunta kuma bata gida ya Furta Ok kawae daga haka ya katse kiran, tafiya suke ta faman yi a saman shimfidaddun titinun Abuja, tun Fauzy na yin k'walla tana kai hannu tana gogewa har ta saduda taci gaba da kallon hanya ta widescreen don glass d'in Motar blacktinted ne ba'a ganin waje sosae ta cikin su, saida suka d'auki kusan mintuna 30 sannan suka iso wata unguwa mai d'auke da had'add'un manyan gine gine ga fitilu ta ko'ina kaman da rana, yar tafiya sukai a kan titin Unguwar suka iso bakin wani katafaren gida da jami'an yan sanda guda biyu ke gadi kowannensu na rataye da bindinga a jikin shi, karya kan Motar yayi ya tunkari dank'areren gate d'in gidan da sauri su duka jami'an suka hau zuge gate din, bayan sun gama ya nufi shiga cikin gidan duk suka d'aga ma Motar hannu, ko horn baiyi masu ba balle ya tsaya ya shige ciki da Motar da gudu, babban parking space d'in gidan ya nufa bayan ya parker ya kashe Motar, sai lokacin ya juya ya kalli Fauzy tun bayan da suka fito ya furta mata "come out!" bud'e baki tay da niyyar yin Magana ya bud'e kopar ya fita, hannunta sai rawa yake ta bud'e kopar ta zuru k'afafunta dake sanye da takalma masu d'an tudu kafin ta k'arasa fitowa, hankali tashe take bin gidan da kallo wanda ba k'arya ya matuk'ar Had'uwa, ba wani mugun girma gidan gare shi ba kuma ba k'arami bane, bene ne hawa d'aya iya fentin gidan abun kallo ne don ya tsaru sosae, a harabar gidan akwae had'add'un Flowers su kan su an tsara shukar su gasu a gyare luf luf dasu, daga can gefe runfunan shak'atawa ne guda ukku kowacce na d'auke da k'ayatattun kujerun katako a zagaye da table, zagaye da runfunan akwae manyan shukokin Flowers harda irin Xmas tree da ake ma adon fitilu itama anyi mata hakan tana ta sakin haske kala daban daban haka sauran flowers d'in akwae masu reflecting hasken dogayen fitilun dake a wurare daban daban a cikin harabar gidan sun haske ko ina ta yadda ko allurar ka ta fad'i to zaka iya ganinta, a cikin hall d'in sama wata jigunannar katuwar fitilar sama ce mai adon sarkoki kai kace in mutum ya tsaya zata fad'o mashi,

Bayan ya rufe k'opar hanyar fita daga cikin parking space d'in ya nufa, har ya kusa fita ya dakata ya juya yana kallon Fauzy da tayi tsaye a bakin kopar Motar da ko rufeta bata yi ba sai zare ido take a iya fuskarta zaka fahimci ba K'aramin tashi hankalin ta yay ba, cikin d'an d'aga murya yace zata tsaya anan ne, yamutsa fuska tay ta fara kuka tana mashi magiyar don Allah yayi hak'uri, tsaye yay yana mata wani kallon rashin Arzik'i ta cikin glass d'in daya maida bayan daya fito daga cikin Motar, ganin zata 6ata mashi lokaci yasa shi ce mata ta tsaya anan za'a shigo da ita, jin haka yasa ba shiri ta biyo bayan shi don gaba d'aya a tsorace take, har ta fito cikin harabar ya dakata ya juyo hakan yasa itama ta tsaya, ce mata yay waye zai rufe mata kopar da sauri ta juya ta nufi komawa cikin parking space d'in tana yi tana waiwayen shi yana tsaye yana kallon ta, bayan ta rufo k'opar ta dawo ya juya yaci gaba da tafiyarshi mai cike da k'asaita, ganin ya kusa shiga cikin ginin gidan yasa ta k'ara saurin da take, a bakin dakakkar kopar shiga gidan dake a cikin entry hall ya tsaya saida Fauzy ta k'araso wurin ta tsaya daga d'an nesa dashi sannan ya kai hannu cikin d'ayan Aljihun jeans d'in shi wata farar wallet ya fiddo ya bud'eta, wani d'an card ya ciro ya kai shi jikin kopar cikin wani d'an rami dake kusa da handle d'inta, yana zura shi sai gashi tayi wata yar k'ara, zaro katin yayi ya maida shi a cikin wallet d'in sannan ya kai hannu jikin handle d'in ya tura k'opar ta bud'e, shiga yay ciki ya juyo yana kallon Fauzy, ganin irin kallon da yake mata yasa cikin fad'uwar gaba ta tunkari k'opar tana tafiya a d'arare aikuwa ya daka mata tsawa yace kar ta 6ata mashi lokaci baiwar Allah har saida ta firgita da sauri ta nufi ciki, matsawa yay gefe ta wuce ya kai hannu ya rufe k'opar aikuwa a firgice ta kalli kopar kafin ta maido kallon kanshi ta fashe da kuka mai sauti ta hau rok'on shi don Allah yayi hak'uri ya k'yaleta ta tafi, kai kace bada shi take ba ya shige cikin Corridor d'in da suka shigo, yana niyyar karya kwana ya dakata ya juyo yana kallon Fauzy dake ta kuka tayi tsaye a wurin hannunta d'aya ruk'e da kopar sai jan ta take amman sai kace tana jawo bango, jinjina kai yay yace mata in ta bari ya shige zata ga abunda zai same ta a wurin aikuwa tun kafin ya rufe baki da sauri ta nufo shi, bene ne a wurin shi kan shi abun kallo ne don ya tsaru tunda ga kan Matattakalar zuwa yadda akai design d'in shi ya wani markwad'a, da sauri da sauri take hawa saman shi har tana yin kamar zata fad'i tana yi tana waiwayen bayanta,

bayan ya haye a cikin wani Corridor ya tsaya cikin shi akwae flower vases masu kyau d'auke da kayatattun Flowers haka saman wurin akwae fitila mai kyau da tsari, kopopi ukku ne a wurin a gaban d'aya daga ciki ta bangaren hagu ya tsaya, hannu ya kai jikin kopar ya ta6a wani d'an circle na glass nan take k'opar tay wani d'an sauti alamar ta bud'e, tura ta yay ya shiga ya tsaya daga bakin kopar yana kallon Fauzy da tay fiki fiki duk ta firgice gata daga ita sai rigar jikinta ko gyale babu, "Come in" ya fad'a tare da yi mata nuni da kai, yamutsa fuska ta fara yi k'walla suka cigaba da zubowa ba tare data matsa daga inda take ba, hak'uri ta fara bashi kawae sai ya saki kopar yace mata ta bari ta rufe, a rud'e ta kutsa kai ciki bayan ta shiga kopar ta maida kanta ta rufe, Ya Allah kai mana Arziki mai Amfani shine abunda na furta, had'add'an parlor ne daya amsa sunan parlon masu Arziki sosae, komai na cikin shi fari da golden ne tun daga kan kujerun, labulaye, carpet, hatta fitilun cikin shi fari da golden ne kai kace da gold akai adon wasu abubuwan, sam parlon baida hayaniya komae tsaf tsaf sai ni'imtaccen sanyi mai had'e da daddad'an k'amshi ke tashi, a yanayin parlon kai kace mutane basu rayuwa a cikin shi yadda fararen abubuwan suke K'al da su, tsaye tay a bakin kopar duk da halin da take ciki sai da ta bi parlon da kallo fuskarta duk hawaye, cikin parlon ya shiga a saman farin c-table shima da adon golden ya d'aura wallet da wayar shi, hannu ya kai ya cire glass d'in Fuskar shi shima ya aje a wurin, saida ya d'an juyo ya kalleta suka had'a ido kafin ya juya walking majestically ya nufi hanyar wani Corridor ta bi bayan shi da kallo har ya shige, lokacin ta samu damar k'ara bin ko'ina na cikin Parlon da kallo baki a d'an bud'e, bai d'auki lokaci sosae ba ya fito ya cire yellow rigar ta sama sai farar ta ciki da ta kama jikin shi kirar k'arfin shi ta bayyana ya cire takalman k'afafun shi ya sanyo wasu bak'ak'en slippers masu d'an tudu, da sauri Fauzy ta maida idanunta cikin Corridor d'in jin sautin tafiya, yana fitowa suka had'a ido ya wani k'ara tamke fuskar da sauri ta maida idon gefe gabanta na bugawa da k'arfi da k'arfi, cikin parlon ya shigo ya nufi inda fridge yake a can gefe, bud'ewa yay bayan yaje gaban shi Fauzy ta kai idon ta wurin, hannu ya kai ciki ya fiddo wata k'atuwar bak'ar kwalba an nad'e saman marfinta da wata leda mai k'yalli haka ma a jikinta akwae takarda mai d'auke da rubutu zagaye da ita, d'aurata yay a saman fridge d'in ya k'ara kai hannu ciki ya d'aukko tumbler, bayan ya rufe fridge d'in ya kai d'ayan hannun shi ya d'aukko kwalbar tana ganin zai juyo da sauri ta kauda idonta daga barin kallon shi, cikin parlon ya dawo ya nufi kujera ya d'aura abunda ya d'aukko kafin ya kai hannu ya jawo c-table d'in gab da kujerar, d'aukar kwalbar da cup d'in yay ya d'aura su a saman table d'in kafin ya zauna ya kai hannu ya d'aukko kwalbar ya kaita baki yana cizge ledar da aka nad'e bakin ta, sakin baki Fauzy tay tana kallon shi cike da Al'ajabi don ita a saninta irin wannan kwalbar ta giya ce, lokacin daya gama bud'ewa ya fara tsiyayawa a cikin cup d'in wani irin harbawa zuciyar Fauzy ta shiga yin don kuwa ganin kalar abunda ya zuba a cikin cup d'in ta tabbatar ma kanta da giya ce, kaman rabi ya zuba bayan ya rufe kwalbar ya d'auka ya kai baki ya fara sipping a hankali, yana cikin sha yayi mata kallon k'asan ido da sauri ta sunnar da kanta k'asa gaban ta na cigaba da fad'uwa, yana cikin sha ya kai hannu kan table d'in ya d'aukko remote da ke a saman shi daga d'an can gefe ya kunna Tv, bayan ta kama ya shiga caccanza channel ya kamo wadda yake so sannan yaci gaba da shan lemun d'ayan hannunshi ruk'e da remote d'in ya d'aura kafa d'aya akan d'aya idon shi akan Tv yana kallo, fara gajiya da tsayuwar Fauzy tay daurewa kawai take don k'afafunta har sun fara mata zafi sai wuwwurga ido take sai ta kalle shi sai kuma ta kalli Tv shi kam gaba d'aya ya maida hankalin shi akan Tv ko kallonta bai yi sai kace ma ya manta da ita a wurin, sun d'auki lokaci a haka gaba d'aya Fauzy ta gaji da tsayuwar har k'afafunta sun fara mata zunga sai kallon shi take tana yamutsa fuska tare da kikkafta idanunta da suka cika da kwalla, matsawa ta d'an k'ara yi gaba kad'an cikin rawar murya tace "Don girman Allah kayi hak'uri ka k'yale ni in tafi, nasan ana can anata nema na wllh" da alama dae bango take ma magana don kuwa sipping d'in lemun shi da ya k'ara zubawa kawai yake, kuka Fauzy tasa sosae mai sauti sai lokacin ya juyo yana mata wani kallo, cigaba da magiya tay mashi tana nuni da hannuwan ta, janye idon shi yay daga kan ta ya ci gaba da kallon shi, bayan ya gama shanye abun cikin cup d'in d'aura cup d'in yayi saman table, tsam ya mik'e ya nufo cikin parlon ganin inda take yake nufowa yasa ta zaro ido ta fara ja da baya gabanta na wani irin bugu tamkar ana mata luguden ta6are, cigaba da tunkararta yay tana ja da baya can ta juya a rud'e ta kama k'opa ta fara jijjiga handle d'in a K'ok'arin ta nata bud'e tana yi tana waiwayen shi duk ta gigice ba kamar da take ganin giya ce ya gama sha, tana haka ya cimmata kokarin bi ta gefe ta ruga tay ya kai duka hannuwan shi ya dafe kopar ta yadda ya sakata a tsakiyar su yay mata rumfa, gaba d'aya jikinta 6ari yake har bakinta sai numfashi take da k'arfi tunda take a rayuwarta bata taba shiga firgici irin wannan ba, ko lokacin da aka sanar Mata Mujaheed yayi Aure batai irin wannan firgicewar ba Saboda sumewa tay lokacin yanzu kuwa bata fatan ma ta sume d'in, gaba d'aya ganin shi take a buge yake hakan yake k'ara tada mata hankali, kafeta da ido yay yana mata wani matsiyacin kallo sai kerma bakinta ke yi tama kasa cewa komai, wayarta ce da har lokacin tana ruk'e a hannunta tare da ta Fatuu ta fara ringing da sauri ta kai idonta kan screen d'in ganin Aunty Mareeya ce me kiran yasa a kid'ime ta fara k'ok'arin d'auka don ta sanar mata halin da take ciki kwatsam taji ya kawo hannu ya buge wayar ta fad'i k'asa ta daki tiles, daga jin sautin fad'uwar ba sai an fada ba glass d'in ya fashe, cikin rawar murya ta fara fad'in "D...don girman Allah, don son ka da Manzo SAW kayi hak'uri, wllh bada sani na na buge ka ba har wayan ta fad'i kaji na rantse..." abun ka da fara fuskarta har tayi jajur tunda take a rayuwarta bata ta6a kasancewa da Namiji haka ba don kusancin yayi yawa, bin ta kawae yay da ido da suke a d'an lumshe wanda suna daga cikin abun da ke tafiya da mata a tattare da shi, komai nasu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login