Showing 378001 words to 381000 words out of 512766 words

Chapter 127 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1679

tace "I..I don't understand you Sis Zarah", saida Fatuu ta had'iyi abu kafin tace "dama na fad'i ma Ya Haisam cewa in na haihu zan baki Babyn koda kuwa d'aya ne sai gashi Allah yasa na haifi biyu shine na baki d'in, Aunty Fanan wllh na baki shi har abada ga su Hajiya nan inason su zama shaida shiyasa nayi hakan a gaban su" da k'yar ta k'arasa Maganar Saboda karyewar da muryarta tayi, hannu Fanan ta kai da sauri ta rufe bakinta alamar Al'ajabin Maganar don abu ne da bata tsammaci ji ba, bin juna sukai da kallo ita da Fatun lokaci guda idanun Fanan suka ciko da k'walla cikin rawar murya ta furta "Yanzu Sis Zarah kina nufin duk wahalar da kika sha ta rainon cikin shi da kuma haifuwar shi kin bani shi ya zama nawa har abada?" Kai Fatuu ta jinjina mata itama idanunta sun ciko da k'walla kawai sai ji sukai Fanan d'in ta fashe da kuka itama Fatun k'wallan ne suka fara zubo mata gaba d'aya sun karya ma kowa zuciya can Fanan ta kai hannu ta karbe shi ta bishi da kallo tana murmushi,

"Ban ta6a tunanin wani zai man irin wannan kirkin ba a rayuwata har na rasa mi zan ce ma" cikin muryar kuka tayi Maganar tana kallon su Hajiya dake mata d'an murmushi, maida idonta tayi kan Fatuu bayan ta goge k'wallan tace "All i can say to you is thank you. Thank you so much for your generosity Zarah. You have shown me a kindness that I will never forget. Never" ta k'arasa tana jujjuya kai alamar tabbatar mata da abunda ta fad'a, jinjina kai Fatuu tay tana goge kwallanta gaba d'aya sauran Mutanen cikin dakin sunyi shiru suna bin su da kallo, mik'a mata Babyn tayi bayan Fatun ta amsa tana murmushi tace "Ba sai kin bani shi ba Zarah, We're one Family so duk abunda d'aya ya mallaka tamkar na kowa ne, I'm I right?" Da sauri Fatuu ta jinjina mata kai alamar eh Fanan d'in taci gaba "Gud, ko baki bani shi ba gaba d'ayan su yarana ne kuma in sha Allah zamu raine su mu basu tarbiya mai kyau tare" atare gaba d'aya aka had'a baki wurin furta "Allahu ya sha" Fanan tay d'an murmushi tace Ameen, Hajiya ce ta d'an yi gyaran murya duk suka maida idonsu kanta a nutse ta fara magana tace wannan abun daya faru babu wanda ya kai ta jin dad'i wllh, Fateema itama tayi abunda da k'yar a samu wadda zata iya yin hakan ga abokiyar zamanta kamar yadda itama Fanan d'in tayi gaba d'aya suka jinjina kai, kallon Haisam tayi tace "ina son ka sani duk Wannan sadaukarwar da suke Saboda son da suke maka ne hakan yasa duk suka fifita farincikin ka fiye da nasu don haka ina k'ara jan hankalin ka da ka k'ara jajircewa wurin ganin ka ruk'e su da amana ka kyautata masu, kaima ka fifita farincikin su fiye da naka don kuwa ba K'aramin dace kai ba wllh ka k'ara gode ma Allah, samun mata irin wannan a zamanin nan da muke ciki ba zan ce babu irin su ba amman ina mai tabbatar maka da samun su da wahala don koda mata suna son miji zaka ga basu damu da Farincikin shi ba Saboda haukan kishi kullum cikin tada mashi hankali suke a haka kuma wai don ana son shi ne, ina rok'on Allah daya k'ara had'a kan ku ya Albarkaci rayuwar ku gaba d'aya ya k'ara shirya mana ku ya kuma k'ara rufa mana asiri fiddunya Wal akhira yasa mu gama da duniya lafiya" a tare gaba d'aya suka amsa da Amin fuskokin su d'auke da Murmushi ta juya kan su Fatuu ta k'ara masu Nasiha kan su k'ara had'a kan su ta nuna masu hakan da suka za6ar ma kan su shi yafi masu Alkhairi don ko ba komai zasu kasance a cikin farinciki suma su cigaba da kyautata ma mijin su hakan shine kishin daya dace, sosae tayi masu Nasiha mai tsuma jiki duk fuskokin su d'auke da d'an murmushi suke jinjina mata kai, bayan ta gama dasu ta juyo kan Nameer dake manne da ita ta kai hannu cikin sumar shi tace "na dawo kan ka mage sarkin son jiki ko kuma in ce mazuru...." Gaba d'aya aka saka dariya, taci gaba "Allah kaima ya nuna mana bikin ka lafiya kaida yar fillon taka duk da dai ina jin ki shi" tay Maganar tare da d'an kwa6e fuska duk ta basu dariya, hira suka cigaba da yi gwanin sha'awa saida aka yi sallar Azahar duk suka tashi Fanan anan tayi sallar tun tana cikin yi yaran suka tashi suna kuka tana sallamewa ta taso ta nufo gadon tana tambayar mike damun su suke kuka Fatuu dake murmushi tace mata k'ilan yunwa suke ji tace to tay feeding nasu ta daina bari suna yin kuka pls yadda tayi Maganar har saida ta ba Fatuu dariya, ita ta taimaka mata ta fara shayar dasu saida duk suka k'oshi sannan Fanan ta d'auke su gaba d'aya tana masu wasa tana fad'in ga Mom d'in su tazo duk sukai mata k'uri da ido sai kace sun san mi take cewa sai faman saka Fatuu dariya take.

Bayan Fanan ta koma d'akin Laila dama anan take sauka in tazo gidan ta shiga kiran Mom d'inta wato Hajiya Maryam, bayan tayi picking suka gaisa tayi mata anzo lafiya Fanan d'in ta amsa mata tace ai tayi zaton zata tsaya Lagos ko duk murnar sunyi Y'ay'an ce tasa bata biya ba Fanan na dariya tace mata Kusan hakane ta k'agara da ta gansu gashi tare da Nameer suke tace to, "Mom you know What?" Fanan ta fad'a Mom d'in tace mata a'a mi akai, labarin abunda ya faru tsakaninta da Fatuu ta shiga bata yadda ta d'auki d'aya daga cikin yaran ta bata kyauta, d'an ta6e baki Hajiya Maryam d'in tayi tace mata in duk cikin salon neman wurin zama ne fa da sauri Fanan tace mata Wallahi har cikin zuciyarta ta bata don a gaban kowa akayi tace kuma su zama shaida, "to ce mata akai ke bazaki haihun bane?" Kai Fanan ta girgiza fuska a d'an yamutse tace "No Mom, kawai ta bani ne saboda k'aunata da take kuma taga ita ta riga haihuwan dama na fad'a maki wllh tana zaune dani da zuciya d'aya Mom, sam bata d'auke ni a matsayin kishiya ba" still bakin Hajiya Maryam d'in na a d'an ta6e tace mata to yanzu ita ta amshi yaron kenan tace mata a'a nan ta fad'i mata yadda sukai ta k'ara da cewa "nasan ko ban amsa ba bazata ta6a man iyaka da yaran ba so nima zasu zama kamar nawa ne kinga ko ban haihu ba na samu wanda zasu kira ni da Momy, don Allah Mom ki manta komai ki so Zarah sannan ki mana fatan Alkhairi" yar dariya tayi tace ita dama ai bata ce ta tsaneta ba tana masu fatan Alkhairi Allah ya k'ara had'a kawunan su itama kuma tana mata Addu'ar Allah yabata haihuwan, cike da jin dad'i cikin washe baki Fanan d'in ta amsa da Amin tare da Fad'in shiyasa take k'aunar ta Saboda she's a Mom like no other tana jiyo dariyar Hajiya Maryam d'in, tambayar yaushe zata zo taga Babies tayi tace mata tunda ita tana nan ba sai tazo ba, a shagwabe murya kamar zata yi kuka tace"Haba Mom, yanzu fa kika nuna man komai ya wuce kuma ai ni zuwana daban naki ma daban, don Allah ki zo, haka fa da biki kika k'i zuwa pls kizo hakan zai sa aga kin manta komai kuma ma yaran nan fa grandchildren d'in ki ne" tana dariya tace mata "to sarkin tsara zance wasa nike maki zan zo in sha Allah amman gaskiya sai Ranar suna don akwae kaya na da zasu iso ranar Asabar dole zan tsaya in ga isowar su" cike da Farinciki Fanan d'in tace to ba komai ai tunda zata zo d'in Allah ya kaimu Ranar lahadin harda tambayarta a cikin kayan da tayi Order d'in akwae na jarirai tace mata eh Fanan din tace to ta za6o ma Babies d'in su Unique ones masu yawa Hajiya Maryam d'in ta amsa da tunda ita ta bata kudin da ta siyo ko Fanan ta saka dariya, hira suka cigaba da yi Fanan bata tambayi Dad d'inta ba don tasan ta baro shi a America, kafin suyi sallama ta tambaye ta Farha tace mata tana d'akin ta k'ilan ko bacci take. Bayan sun gama wayar Farha ta shiga kira lokacin da tayi picking tana jin muryarta ta gane bacci take ta bata hakurin tashin ta da tayi tace mata ba komai, tambayar ta tayi tazo ne tace mata eh gata a Abuja nan ta shiga bata labarin irin kyawun Babies d'in da aka Haifa masu fuskar Farhar da d'an murmushi take sauraronta bayan ta gama tace Allah ya raya, tambayarta tayi zata biyo Mom tazo suna ko tace mata No, cikin sigar rarrashi tace mata don Allah ta manta komai ta d'auki Zarah matsayin yar'uwarta itama don tana da kirki sosae kuma tana k'aunarta, nan ta shiga bata labarin yadda ta bata kyautar Babyn da ta haifa tace in ba don tana kaunarta ba taya zata mata haka, daga k'arshe dai saida tayi nasarar shawo kan Farhar tace mata zata biyo Mom d'in nasu zo kaga murna a wurin Fanan.

Ranar Friday da rana Laila ta iso itama ta nuna farinciki sosae ganin yaran nan suka shiga shirye shiryen yin gagarumin suna, a ranar da daddare bayan sallar isha Haisam na zaune a parlon shi na saman bene yana operating laptop d'in shi jikinshi sanye da ash d'in jallabiya wayar shi tay k'ara alamar shigowar sak'o, hannu ya kai gefen shi ya d'aukko wayar ya shiga dubawa, bin sakon yayi da kallo bayan ya bud'e wanda credit alert ne na kud'i Naira miliyan d'aya da rabi daga Sameer, sam bai yi mamakin ganin kud'in ba duk da bai san na minene ba amman ba yau ya fara turo mashi kud'i ba don koda bikin shi da Fanan miliyan biyu ya bashi, fita yay daga cikin sak'on ya fara kokarin kiran Sameer d'in, saida ta kusa yankewa sannan ya d'aga suka gaisa Haisam d'in yace mashi suyi Vedio call ya furta mashi Ok, bayan ya maida kiran na gani Sameer d'in na zaune akan doguwar kujera a gidan shi dake a England wanda Company d'in su suka bashi, suma dare ne can har yayi shirin bacci yana sanye da robe da ta bayyanar da k'irjin shi wanda shima ke d'auke da kwantacciyar suma kamar dai yadda na Haisam yake, k'ara gaisawa sukai Haisam yay mashi ya aiki ya amsa da Alhamdulillah,

"Ya akai bakai bacci ba kai da kake gauro" Haisam ya fad'a yana murmushi Sameer d'in yay d'an guntun murmushin da iyakar shi lips d'in shi slowly yace mashi yana shan coffee ne Haisam d'in ya jinjina mashi kai suka d'an yi shiru kafin Sameer d'in ya tambayi ya Babies d'in su ya bashi amsa da suna lafiya, ce mashi yay yaga sak'on kud'i yanzu shiru Sameer din ya d'an yi kaman bazai ce mashi komai ba can yace mashi ya d'auki 1 million yaba wife en shi 500k yaran shi kuma a fad'i masu zai musu zuwa na musamman, murmushi Haisam yay yayi mashi godiya kafin ya tambayi bazai zo suna ba yace mashi yaso hakan amman aiki yayi mashi yawa amman yana nan zuwa bada dad'ewa ba Haisam yace Ok Allah ya taimaka ya amsa mashi da Amin, tambayar shi yay ina Amarya ya d'an ta6e baki ya bashi amsa da yanzu suka gama magana Haisam na murmushi yace abun nata matsowa Allah ya nuna masu can kasan mak'oshi Sameer ya amsa da Ameen suka dan k'ara yin shiru,

"Ina son zaka taimaka man da abu" Sameer ya fad'a Haisam ya jinjina kai tare da dan gyara zaman shi ya tambayi miye yace mashi dama yana son zai siya ma su bride d'in tashi gida ne, kai Haisam ya d'aga kafin ya tambayi to wane taimako yake son yayi mashi yace bai san taya zai yi hakan ba tunda shi ba sanin garin su yayi ba kuma bai san kowa ba so yana son ya bashi shawarar yadda za'ai Haisam yace ya yi Maganar da Fauzy ne ya girgiza mashi kai alamar a'a kafin yace yafi tunanin yin Maganar da wani babba ba ita ba, shiru Haisam yay alamar tunani can yace mashi ya bari zasu yi Maganar da Wife d'in shi sai ta kira Yayarta tayi mata Maganar Sameer d'in yace Ok zai jira shi ya fad'i mata in tayi ma Yayar tata Maganar tace mata su duba gidan da suke so mai kyau in za'a samu Haisam yace Ok, hira suka d'an k'ara yi yawanci duk akan bikin Sameer d'in ne daga baya sukayi sallama, suna gama yin wayar ya kira Fatuu lokacin suna zaune a Bedroom d'inta da su Aunty Laila anata shirya yadda za'ai suna, bayan tayi picking tambayar ta yay tana tare da mutane ne tace mashi eh yace Ok bari zai tura mata sak'o ta WhatsApp tace to, lokacin da ta karanta sak'on daya turo matan d'an waro ido tay alamar mamaki sai kuma ta hau yin d'an murmushi, sai wuraren k'arfe goma da rabi sannan duka aka watse daga hirar da ake a d'akin Jidderh ma da anan take kwana tace ma Fatun bari taje ta dawo, suna tafiya cike da zumud'i ta shiga kiran Aunty Mareeya, saida ta kusa yankewa sannan ta d'auka bayan sun gaisa ta tambayi twins Fatun tace mata k'ilan ma har tayi bacci ta tada ita ko tace mata a'a bata kusa da wayar ne, tambayarta ina Fauzy tay tace mata tana d'akin ta bata san ko tayi bacci ba ta tambayi ita zata ba wayar ne da sauri Fatun tace a'a dama sak'o ne aka bata da alamun d'an mamaki tace mata to waye ya bada sakon tace mata Sameer har saida Aunty ta maimaita sunan Sameer d'in kafin ta tambayi sak'on miye ya bada, bayanin da yayi Fatun tayi mata bayan ta gama da tsananin mamaki Aunty Mareeya ta maimaita abunda ta fad'a tace mata eh haka yace,

"Kinga Zarah wllh nama rasa mi zance maki tsabar Al'ajabi, yanzu duk uban hidiman da yake ma Fauziyya kuma harda wannan gingimemiyar dawainiyar Gida fa!" Dariya Fatuu tay jin yadda tayi Maganar tace " Wllh Aunty, yana da halin ne kuma k'ilan yana son canza gidanne Saboda bikin tunda kinga ba k'aramar hidima za'ai ba manyan mutane zasu zo" Aunty tace "hakane kam, dama muma munata shirin yin gyaran gidan don har an gama Magana ma da masu gyaran za'ai gyara sosae Saboda hakan yanzu kuma kinga ga Maganar da yayi ni bamma san to mi zan ce ba, amman abunda za'ai Zarah zan kira babban yayanmu sai muyi magana kan hakan tunda ma gobe zamu taho nan in muka zo komi mukai dashi zan fad'i maki sai ki fad'i ma Mijin naki" amsa mata da to Fatun tay tace Allah ya kawo su lafiya duk ta k'agara ta gan su wllh Auntyn na dariya tace suma bata ga yadda suka k'agara da su ganta ba amman sun fi k'agara da suka ga twins d'in su Fatun nata dariya Aunty Mareeyar ta k'ara cewa "ni kinsan abunda ma yafi damuna Zarah?" Kai Fatuu ta girgiza kafin tace mata a'a,

"Wllh abunda nike gudu kada sai mun zo munyi kayan d'aki suce basu so tunda kinsan Manyan nan yadda suke" kai Fatuu ta jinjina tace hakane kuma fa, Aunty tace wllh abunda take ta tunani kenan, shiru Fatun ta d'anyi kafin can tace mata to ko tayi ma Ya Haisam magana kan hakan da sauri Aunty tace "kice mashi mi Zarah! A'a kada kiyi mashi magana kan hakan kada kuma aga kamar so muke ace kada ayin, za'a yi mata komai iya karfin mu dama mun yanke za'a siya mata kayan ne kawai Babanmu ya yanke zai siyar da gonakin shi guda biyu sai a had'a da sauran kud'in da aka tanada in sha Allahu za'ai komai yadda yakamata" Fatuu tace Allah ya bada iko ta amsa da Amin,

"Ni kinsan ma abunda nafi so wllh shine in da zai yuwu da yaje Funtua sun gaisa dasu don duk fa ba wanda ya san shi in ba a hoto da aka nuna masu shi ba to kuma hakan nasan da kamar wuya tunda yanzu ma bai K'asar tun kafin ya tafi nayi ma Fauziyya Maganar kan tasa shi yazo sai ce man tayi wai ita gaskiya bata iyawa ni in yi mashi, to wai kar aga kai talaka ka zaqe yasa ban yin ba kuma ma dai nima nasan halin surukin nawa baud'add'e ne" Dariya Fatuu tasa Auntyn tace Allah kuwa yanzu dai ai sai kawai da biki sun gan shi, hira suka d'an k'ara yi kafin sukai sallama ta kira Haisam d'in tayi mashi bayanin abunda Aunty tace yace Ok Allah ya kaimu goben ya kawo su lafiya, cikin yar shagwaba ta tambayi yana ina yana murmushi yace mata gashi a part d'in shi tace mi yake ya bata amsa da yana wani aiki ne tay shiru yayin da zuciyarta ta shiga raya mata kilan ma a part d'in shi Fanan ke kwana jin tayi shiru yasa shi tambayar ta koda wani abu ne da sauri tace mashi a'a tayi mashi saida safe yana murmushi ya amsa har zata kashe taji yace tana tare da mutane ne a hankali tace mashi a'a ita kad'ai ce Jidderh taje ta dawo yace Ok bari yazo suyi bankwana da Babies tay d'an murmushi tace to, aje wayar tayi ta juya tana kallon yaran dake kwance saman gadon suna bacci sam basu da rigima da sun yi kuka yawanci yunwa suke ji, bada jimawa ba sai gashi ya shigo cikin d'akin da sallama ta d'aga kai ta kalle shi ya sakar mata murmushi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login