Showing 369001 words to 372000 words out of 512766 words

Chapter 124 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1665

itama haka jin yayi shiru ta kai idanunta da suka shishshige ta kalle shi ta furta "hakan yayi maka?" lumshe mata ido yay tace to wane suna zai za6ar mashi yay d'an shiru kafin yace sunan Dad d'in shi ta jinjina kai tace yayi, tambayar ta yay ita wane suna ta za6ar ma shi tana ta murmushi tace sunan Kakan su Mijin Hajiya yanayin kallon da yake mata ne ya sauya da d'an alamun mamaki yace ita bata so asa mashi sunan Dad d'inta ne tace "ina so, amman dai nafi son asa wanda nace Saboda Hajiya nasan zata ji dad'i sosae" shiru yay yanata kallon ta can taji yace hakan bazai zama son kai ba kuwa har saida tayi yar dariya tace to miye abun son kai ai duk d'aya ne ko kuma sunan Baffan nata ko in ta k'ara haihuwar ba sai asa ba, da mamaki ya furta "zaki k'ara kenan?" shiru tay ta kasa bashi amsa a ranta tana tuna wuyar da tasha wadda yanzu har ta zama labari don bata wani jin ciwo a jikinta saidai rashin k'arfi tana jin ta wani irin fayau daba cikin, ce mashi tayi ai dole ta k'ara tunda yanzu ta fara, "amman dai wahalan yayi yawa gaskiya I think ba sai kin k'ara ba"

"Baka son Ya'ya ne?" Amsa ya bata da yana so amman tunda abun akwae wuya sai a hak'ura kawai tana yar dariya tace to ai duk haka ake haihuwan a haka ma ita nata da Sauk'i ya d'an ta6e baki yace haka wai Aunty tace, ce mashi tay yayi masu hudubar ya ce to bayan ya gama ya d'ago tace ko na hannun shi asaka mashi sunan Grandpa din tunda shine babba sai wannan asaka mashi sunan Dad ya d'aga mata kai slowly ya furta hakan yayi, mik'a mata Adam d'in yayi ya d'aukko na jikinta wato Aliyu shima ya fara yi mashi yana gamawa Aunty tazo ta tambayi an saka masu sunan yace mata eh ta tambayi wanda aka saka ya fad'i mata, jinjina kai tayi tace "Ma sha Allah, Allah ubangiji ya raya mana su ya Albarkaci rayuwarsu" Haisam ne ya amsa ita kuma Fatun a cikin rai ta amsa Auntyn ta k'ara cewa "Yakamata a kira gida a sanar masu nasan yanzu tunda Asuba tayi zasu gane bamu nan gashi duk mun taho ba wayoyi" Haisam ne yace mata bari in yayi salla sai yaje gidan ya fad'i tace to, bayan tafiyar Haisam su Nurse Haleema wurin gadon suka zo suka tsatsaya sai faman santin yaran suke gaba d'aya suma sai faman washe baki suke Nurse Chioma tace ita tunda ake haihuwar Twins a Asibitin ba'a ta6a haihuwan wanda suka matuk'ar bata sha'awa ba kaman wannan wllh ji take kaman a bata su kyauta Aunty dake dariya tace ai ga Mom d'in su nan ta tambayeta ta bata da sauri Chiomar tace ita tama fara bayan agabanta akai nak'udar su, Nurse Haleema ma Addu'ar Allah ya bata irin su tayi da sauri Chioma tace aikuwa ba bak'ar fata ba wllh bazata haife su ba ita bak'a bak'a mai d'an hanci Mijinta bak'i hancin shi mai d'an fad'i taya zasu Haifa irin su gaba d'aya aka saka dariya Haleemar ta kai hannu ta 6aketa a shoulder, mik'ewa Aunty tayi tace masu su kai babies d'in d'ayan gadon bari ta taimaka ma Mom dinsu ta tsaftace jikinta duk suka ce to, bayan ta taimaka ma Fatuu ta mik'e rigar jikinta duk ta 6aci da yake mai haske ce Aunty na ruk'e da ita suka nufi toilet wani iri take jin tafiyar ta don ma Allah ya taimake ta ko K'ari ba'a mata ba don Aunty harda Olive oil tayi mata amfani wurin fitowar na farkon.

Fitowa Dad yay don tafiya Masallaci saida yaje ya taso su Affan da Mubeen kamar ko yaushe suka tafi, lokacin da suka je parking space yayi tunanin ganin Haisam acan amman sai bai gan shi ba hakan yasa shi cewa su d'an jira shi, bayan d'an wani lokaci yayi tunanin kiran shi saidai har wayar ta yanke bai d'aga ba hakan yasa shi k'ara yin tunanin ko ya riga ya tafi duk da yasan ko yaushe a tare suke tafiya, koda suka je Masallacin basu gan shi a can ba har aka gama sallar suka juyo Dad nata d'an tunanin to ko lafiya Haisam d'in bai je salla ba, lokacin daya shiga Bedroom d'in shi Mom na zaune akan prayer mat bata dad'e data gama sallar ba tana tasbih, zama yay daga gefenta a bakin gado ta juyo ta kalle shi da d'an murmushi ta gaishe shi ya amsa, ganin yayi shiru yana kallon k'asa kaman mai tunanin wani abu yasa ta tambayi Lafiya ya d'ago yace mata Son ne bai je Salla ba kuma yanata kiran layin shi yana shiga bai d'auka ba tace to ko ya makara ne shine yayi sallar a gida, girgiza mata kai yay yace ai tun da zasu je ya kira shi bai d'aga ba sai yayi tunanin ko ya tafi ne to acan ma basu iske shi ba har aka gama sallar kum bai zo ba yanzu bayan sun dawo saida ya k'ara kiran shi tana ta ringing still bai picking ba,

"To ko lafiya?" Mom ta fad'a bayan ta d'an yi shiru, ce mata yay shima abunda yake ta tunani kenan, mik'ewa Mom tayi tace bari ta kira Daughter aji da sauri Dad yace yauwa, wurin side drawer ta zauna bayan ta d'auki wayarta ta fara kiran Fatuu, to itama dai har ta yanke ba'a d'aga ba da alamun mamaki ta kalli Dad yace itama bata d'auka ba ta jinjina mashi kai, sake kira tay nan ma dai shiru nan take dad ya hau girgiza kai yana fad'in anya kuwa lafiya Mom da har gabanta ya d'an fara fad'uwa ta mik'e tana fad'in bari taje part d'in nasu shima ya mik'e suka fito tare, a bakin part d'in ya tsaya ita ta shiga ba kowa a parlon ta nufi Bedroom a bakin kopar ta tsaya takai hannu ta fara knocking shiru ba'ai magana ba gashi ta lura da kopar ba'a datse take ba, d'an jimm tay zuciyarta ta fara raya mata abubuwa can dai cike da fargaba ta tura k'opar ta shiga harda yar sallama, tsaye tayi daga bakin kopar tana kallon d'akin da yake wayam ba kowa gashi tsab yake ba wani abu na alamun tashin hankali, tunanin to ina suke ta shiga yi zuciyar ta ta raya mata ta duba toilet ta raya to mi zasu zauna yi a toilet tsawon lokaci duk da haka ta nufi toilet d'in shima knocking tayi shiru ta tura kopar nan ma dai wayam ne, dawowa tayi cikin d'akin har zata nufi kopar fita idanunta suka sauka akan packet d'in gloves dake a yadde saman floor da sauri ta nufi wurin, d'aukko shi tay taga a bude yake ta lek'a tana kallon safunan dake ciki nan take ta shiga tunanin to ko Daughter nakuda ta fara ne sai lokacin ta lura da wayoyinsu d'aya na akan gadon gefen filon d'aya kuma na akan side drawer, da sauri ta fito tana ruk'e da ledar safar, Dad na ganinta ya tambayi ya akai ta nuna mashi tace tana tunanin nakuda ce ta kama Daughter d'in cikin dare k'ilan ko asibiti suka tafi da mamaki Dad yace "Asibiti kuma ba tare da sun fad'a ma kowa ba?" shiru Mom tay yanayin fuskar ta da d'an alamun damuwa can tace to ko da Aunty suka tafi da sauri Dad yace bari ya kirata su ji, to itama dai d'in Wayar har ta yanke ya k'ara kira duk ba'a d'aga ba lokacin gaba d'aya Hankulan su sun tashi da sauri Mom tace bari ta dubo ta a dakinta, lokacin data je d'akin nan ma wayam ne sai wayarta dake a gefen pillow, fitowa Mom tayi ta nufi d'akin Jidderh lokacin bata dad'e da komawa ta kwanta ba bayan tayi sallar Asuba, tura kopar tayi ta shiga ta nufi gadon Jidderh tana kiran sunanta jin kiran Mom d'in yasa ta bud'e fuskarta ta juyo tana kallon ta, tambayar ta tayi tasan ina su Daughter suke ai tana jin haka da sauri ta yunk'ura ta tashi zaune da tsananin mamaki tace "Mom basu nan ne?" Kai ta d'aga mata ta shiga fad'i mata an tashi duk ba'a gan su ba harda Aunty kuma duk wayoyin su na a gida a d'an firgice ta kai hannu ta dafe kirjinta da hannu guda baki bud'e take kallon Mom d'in da itama take ta kallonta can ta juya zata fita aikuwa da sauri ta saukko ta bi bayanta, tsaye sukai cirko cirko bayan ta sanar ma Dad d'in Auntyn ma bata nan da tashin hankali yace to in ma Asibitin suka tafi anya kuwa lafiya zasu yi irin wannan tafiyar Mom tace ita ma abunda ya tada mata hankali kenan jin haka yasa Jidderh ta fara yarfa hannu kaman zatayi kuka tace " Dad bai kamata muna wasting time ba don Allah mu bisu nasan bai wuce Asibitin su Aunty suka tafi tunda da gani suna tare" da sauri ya furta Ok dama jikinshi jallabiya ce Mom kuma akwai Hijab data yi salla Jidderh kuma kayan bacci ne riga da wando sai hula ko tunanin ta koma ta d'aukko mayafi bata yi ba suka nufi hanyar fita dama akwae makullin Motar da su Dad suka je Masallaci a aljihun shi, suna niyyar fita Haisam ya sako kai cikin parlon gaba d'ayan su kaman an latsa masu pause duk suka tsaya cak suna kallon shi atare kuma duk gaban su ya hau fad'uwa, kallon su ya shiga yi da d'an murmushi Mom ce ta fara magana tace "Habiby ina kuka je ne, ina Daughter take?" Kafin ya bata amsa Jidderh tace "Big bro ina sister Fatuu tana lafiya don Allah?" itama tana rufe baki Dad yace "Son, ya zaku fita baku sanar ma da kowa ba kuma duk kun bar phones d'in ku anan miya faru ne ina Daughter?" Yar dariya yayi jin yadda suka jera mashi tambayoyi, fad'i masu yay sunje hospital ne da sauri Mom tace nakuda Daughter d'in ta fara ne yace eh,
"To kuma sai ku kama ku tafi ba tare da kun sanar da mutane ba?" Dad ne ya fad'a ya d'an d'aure fuska Haisam d'in yace mashi lokacin sunga duk suna bacci ne shiyasa yana rufe baki Dad ya dalla mashi wata uwar harara da sauri Haisam d'in ya matsa wurin shi yana zuwa ya rungumo shi jikin shi yana sakin k'ayataccen murmushi yace "We're very sorry mun yi laifi amman yanzu time en farinciki ne, guess what?" da sauri Dad d'in ya girgiza mashi kai yadda suka yi sai kace wasu abokai,
"Kayi abokai..."tun kafin ya rufe baki Dad ya d'ago shi da sauri kafin yace wani abu Mom ta riga shi fad'in "ta haihu ne??" Kai ya d'aga masu kafin yace eh an samu baby boys yay maganar yana dariya gaba d'aya suka shiga washe baki Jidderh ta saki k'arar farinciki tare da daka tsalle Su Dad suka shiga fad'in Alhamdulillah, Mom ce tace su tafi ta nufi k'opa da sauri gaba d'aya bakinta yak'i rufuwa, juyawa Jidderh tayi da gudu ta nufi d'akin su Yasmeen da Affan ta fad'i masu nan fa suka shiga murna tare duk suka fito lokacin Haisam ya tuna da wayar shi yace bari ya d'aukko, Dad ne yaje ya d'aukko Jeep Mom da Jidderh suka shiga su kuma su Yasmeen da twins suka shiga ta Haisam a tare motocin suka fara tafiya bayan sun sha round suka nufi gate,

Bayan Aunty ta taimaka mata ta gyara jikinta sun fito ta d'aukko mata doguwar rigar da ta sako mata cikin kayan ta saka ta d'aura gyalenta, Aunty da kanta ta shirya mata pad a jikin pant d'in da zata saka ta bata ta sa kafin ta bata turare ta fesa bayan ta gama kimtsawa ta haye saman gadon da aka canza mata acan wani bangaren d'akin, juyawa tayi tana kallon babies d'in dake kwance a gefe da murmushi Aunty ma zama tay daga bakin gadon tana kallon su bada jimawa ba Nurse Haleema ta shigo ruk'e da d'an babban tray an d'auro kayan tea da bread a leda da yake a Vip d'in har Abinci ake badawa ta d'aura akan drawer tace ma Aunty gashi nan dama ita tasata taje ta amso bayan ta ajen ta juya ta fita, Aunty ce ta had'a mata kakkauran tea ta bata ta fara sha sosae taji dad'in tea d'in biredin ne take ci kad'an tana cikin sha Aunty tace bari ta amso mata magunguna da in ta gama zata sha tace to, bayan fitar ta juyawa tay tana kallon yaran nata tana sakin k'ayataccen murmushi gaba d'aya har yanzu ganin abun take kamar wasa wai ita ta haife su ita kanta sosae take ganin kyaun yaran sai kace larabawa duk da dai akwai jinin larabawan a jikin su, lips d'in su sak kalar na Haisam wato peach saidai nasu yafi cizawa gashin girar su ma a tsare yake kwance lub gashi bak'i ne sosae komai dai nasu mai ban sha'awa ne, bada jimawa ba Aunty ta dawo lokacin ta gama shan tea din ta bata magungunan tana cikin sha Hassan d'in ya farka yana motsi can ya kai hannun shi dake cikin mitten ya fara tsotsa Aunty dake kallon shi tace "da alama dai grandpa acici ne, tun ana goge shi ya fara mamulan hannu" Fatuu dake yar dariya tace d'azun ma da ta d'aura mata shi saida ya tsotsi hannun har ta fad'i mata abunda Haisam yace na siyo mashi Madara tana dariya tace ina ruwan sabon Baba, ce ma Fatun tay ta fiddo breast d'in aga in milk d'in ya zo tace to, bayan ta fiddo tasata ta matsa ba ruwan sai yellow d'in farko tace ta bashi ya sha ruwan zai zo, koya mata yadda ake ruk'on babyn in za'ai feeding ta shiga yi Fatun nata murmushi yayin da take jin wani iri daya kama sosae yake sha Aunty na mashi tsiya tana fad'in duk da suruki ne ta wani bangaren, suna haka aka tura kopar a tare suka kai idanun su wajen Jidderh ce ta fad'o cikin d'akin da sauri su twins na biye da ita suna ganin su Fatun suka nufo su da d'an gudu gudu daga baya Mom ta shigo Dad da Haisam na biye da ita duk suka nufo gadon, tsaye duk sukai a gaban gadon da sauri Fatuu ta maida breast d'in nata ganin su Dad tuni Jidderh ta d'aukko Hussein su Yasmeen da twins duk suka mik'a ma Fatuu hannu suna yar rige rigen wanda zai amshe shi sai dariya ake ganin d'aya yak'i hak'ura a ba d'aya yasa Aunty saka baki tace su bi a hankali kowa zai d'auka, gaishe da Dad Fatuu tayi yana ta faffad'an murmushi ya amsa tare da Fad'in "Sannu, sannu da kokari Daughter" kai ta jinjina mashi tana ta murmushi Mom ma tayi mata sannu da tambayar jikinta tace lafiya lou, had'a ido sukai da Haisam suka shiga yi ma juna murmushi Mom data k'agara ta d'auki jaririn ta mik'a ma Jidderh hannu tana fad'in tunda ta gani ta kawo,
"Ma sha Allah lakuwwata illa billah, Yanzu Daughter da kanki kikai wannan aiki?" Mom ta tambaya idanunta akan Fatuu tay murmushi kawai Aunty tace "ai gaskiya tayi kokari wllh" jinjina kai Mom tayi ta furta sosae kafin tace amman saida aka k'arata wannan ko Aunty tace a'a har saida fuskarta ta nuna mamaki ta shiga k'ara yi ma Fatuu sannu fuskarta d'auke da murmushin farinciki haka Dad ma sannun yake ta ma Fatuu, gaba d'aya kowa tsantsar farinciki ne akan fuskokin su kai kace ba'a ta6a yi masu haihuwa ba duk da dai an d'auki lokaci ba'ayi ba gashi wad'annan ne jikokin Farko, sai faman k'arba k'arba ake tsakanin yaran Jidderh ma sai sannu take ma Fatun, Dad ne ya tambayi an saka masu suna Aunty tace eh ta fad'i mashi har saida ya d'an waro ido alamar mamaki,

"Wannan dad'in bai mana yawa ba kuwa?" Dad ya fad'a idon shi akan Haisam dake murmushi ya k'ara fad'in "Son banda son kai fa halan kai ne ka zabi sunan gaba d'aya?" Kai ya d'an girgiza calmly yace shi ne ya za6i nashi ita kuma ta za6i na grandpa, kallon Fatuu Dad yay tana murmushi ya furta "Daughter in akai haka bamu so kan mu da yawa ba kuwa karfa ayi kura da shan bugu gardi da k'wace jaka" gaba d'aya aka saka dariya a hankali tace a'a ai duk d'aya ne duk suka jinjina kai Dad harda yin godiya ya tambayi waye abokin nashi waye kuma Baban nashi duk aka nuna mashi Aunty tace sun kasa gane yadda zasu bambance su shiyasa suka bambanta masu kaya dama fin set biyu ta d'aukko wai ko zata haifi fin biyun duk akai dariya, jin haka yasa Momy ta fara k'ok'arin duba su taga ko zata samu abunda za'a rink'a Gane su, tunawa tayi da yadda ake gane ta ita da Mom d'in Sameer hakan yasa ta k'ura ma na hannun Dad wanda ta bashi wato Aliyu ido tana kallon idon shi dake a bud'e dama tunda Jidderh ta sunkuce shi yana bacci ya farka sosae ta k'ura ma idon nashi ido harda d'an bud'awa taga k'wayar bata ciza ba sosae ta d'an yi brown, juyawa tay kan d'ayan dake a hannun Affan shima ta shiga dubawa sai gashi tashi bak'a ce wuluk tana ganin haka ta d'ago tana dariya ta fad'i masu suma ga yadda za'a rink'a bambanta su duk saida suka ji mamaki ganin abu yazo d'aya suka shiga fad'in ikon Allah, Addu'oi Dad duk yayi masu bayan ya gama ya tambayi an fad'i ma su Hajiya Aunty tace a'a Saboda ba waya yace Ok bari ya sanar mata, Lokacin da kiran ya shiga bata dad'e da tashi daga kan abun salla ba ta koma ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login