Showing 297001 words to 300000 words out of 512766 words

Chapter 100 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

2309

tay ta kai hannu ciki tana k'ok'arin fiddo abunda ke ciki, kwalin waya ne ta fiddo lokacin da idanun ta suka sauka akan rubutun jiki Kusan sik'ewa ta nemi yi ganin hoto da kuma sunan wayar wadda iPhone 15 ce irin ta Fatuu, wani irin bugu k'irjinta ya hau yi idanu waje baki bud'e take kallon kwalin, juyawa tay a razane ta kallo hanyar daya bi Al'ajabi ne ya kamata a ranta ta shiga raya don ya fasa mata waya shine zai bata wannan tsadaddar wayar, gaba d'aya tsoro ne ya kamata maimakon farinciki ta shiga tunanin yadda zatai da wayar, yankewa tay kawai taje ta nuna ma Aunty Mareeya ta kuma fad'i mata gaskiyar abunda ya faru tsakanin su, da sauri ta maida ta cikin kwalin kafin sauri sauri gudu gudu ta nufi part d'in nasu.................




_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

85
Lokacin da ta shiga parlon Aunty Mareeyar ta tashi ita da Feenah, har zata bita d'akin sai kuma ta fasa ta juya, bakin kopar shigowa ta komo ta tsaya ta fara k'ok'arin kiran ta,saida ta kusa tsinkewa sannan ta d'auka cikin murya ta wanda ya fara bacci tace mata ya akai ne har ta fara bacci ta tasheta, hak'uri ta bata daga haka tay shiru saida Aunty Mareeyar tace miye to ta kirata sannan murya na rawa tace don Allah tazo taga wani abu, tambayar ta tayi wani abu da alamun mamaki, rasa abunda zata ce mata tay kawai sai tace dama akan wannan ne data fad'i mata abokin mijin Zarah ai tana jin Haka da sauri ta mik'e ta zuro k'afafunta k'asa, hanyar fita daga d'akin ta nufa tana ce mata gata nan zuwa, bayan ta fito cikin parlon ganin bata ciki yasa ta nufi d'akin su, nan ma bata ganta ba sai su Haulat da Mino dake bacci Zainab dai tana a parlon suna son k'arasa kallon Film d'in, a bakin kopar d'akin ta tsaya ta fara kiran ta, bayan ta d'aga a d'an hasale tace wai tana ina tasa ta fito kuma ita bata ganta ba tace mata tana a bakin kopar shigowa, jin haka har saida gaban Aunty Mareeyar ya d'an fad'i da yar fargaba ta nufi hanyar fita, tana tsaye a gefen kopar ta fito suka had'a ido, bin juna sukai da kallo ganin yadda Fauzyn tay zuru zuru yasa ta bita da kallo tun daga sama har k'asa, tsaida idon ta tay kan yar jakar hannunta sai kuma ta maido idonta cikin nata tun kafin tace mata wani abu Fauzyn ta Mik'o mata jakar, hannu ta kai ta amsa ta bi jikinta da kallo kafin ta kalli Fauzy da alamun rashin fahimta ta tambayeta miye tace ta duba abun ciki, hannu ta kai ta fiddo kwalin wayar koda tay arba da sunan wayar da sauri ta kalli Fauzy tace "Wannan fa, ta waye?" Sai faman zare ido take tace mata wai cousin brother d'in Ya Haisam ne ya siya mata, cikin d'aurewar kai ta tambayi waye cousin brother d'in nashi muryarta na d'an rawa tace mata Sameer, waro ido Aunty Mareeya tayi cike da Al'ajabi ta maimaita sunan Sameer d'in Fauzy ta d'aga mata kai, gaba d'aya kanta ya gama daurewa tama kasa magana baki a d'an bud'e take kallonta can tace "to ke taya akai kuka san juna, mike tsakanin ku da har zai baki wannan tsadaddar wayar?"

abu Fauzy ta had'iya kafin tace "d..dama shine wanda nace maki rannan ya d'auke ni mun fita tare kuma shine ya aiko man da kud'i in yi lik'i a wurin dinner" k'arasa bud'e baki Aunty Mareeya tay tsabar Al'ajabi, a rud'e tace mata amman taya wai ya santa da har hakan ta faru tsakanin su shi da ko kallon mutane bai yi balle ya tanka masu Saboda izzar bala'e, labarin yadda komai ya faru tsakanin su Fauzy ta shiga bata, lokacin data gama gaba d'aya Aunty Mareeya ta zaro idon ta sai kuma ta washe baki tana dariya cike da Farinciki tace "Allah buwayi gagara misali, wani hanin ga Allah baiwa ne, inyee yar gidan Hajiya, wannan dank'areren kamu haka, ashe ashe dai babban rabo ne ke bibiyar ki" dariya Maganar tata taba Fauzy tana yi tace mata itafa ba soyayya suke da shi ba bata fad'i mata yadda komai ya faru ba, baki a washe tace mata ai da hakan wani lokacin dama ake farawa,
still dariya Fauzy ke yi tace "Wannan ne zai so ni kema dai Aunty Mareeya, mutumin da farko kafewa ma yayi akan sai na biya shi ko yanzu fa da zai bani wannan wayar sai da yayi man maganar saura ni in biya shi nayi ta mashi magiya, amman ina ganin yanzu dai ya hak'ura tunda yace in taho" karaf Aunty Mareeya tace "in ma bai hak'uran ba sai mu biya shi ai, don nasan tunda ya kafe bayan kin nuna mashi baku da halin biyan to na gane biyan da yake nufi da soyayyar ki zaki biya shi baki ga har gwada ki yay ba, ai yasha kurumin shi in dai wannan ne za'a biya shi fin yadda yake zato, ana son shi wllh" dariya sosae Fauzy ke yi jin wani hak'ilo na Aunty Mareeya gaba d'aya ta hak'ik'ance kan wai son ta yake bacin ita dai tasan ko abu d'aya mai kama da nuna so bai yi mata ba in ba tamke mata fuska ba wanda tasan hakan bai cikin alamun so gashi k'arshe ma ai cewa yay taba masu sonta dama zata samu mutumin daya dace, Aunty Mareeya sai faman farinciki take bakinta yak'i rufuwa sai juya wayar take tana jinjina kai,

"Yanzu yaushe yace zai zo Katsina?" ta tambayeta taci serious Fauzy kau mi zatai in ba dariya ba, harara ta wurga mata tace ba tambayarta tay ba, cikin dariya tace "to ni Aunty Mareeya bansan mi zan ce maki ba sai kace baki fahimci bayanin dana yi maki ba, ni fa bai ce yana sona ba bai kuma nuna ko alamar hakan ba kece kike ganin haka, ba har na fad'i maki shawarar da ya bani dana bashi labarin abunda Mujaheed yay man ba" d'an jimm tay tana nazarin Maganar can ta sauke ajiyar zuciya tace "na fahimci komai, amman kinsan mi, ina tunanin yana son ki ba tare daya sani ba don mutum irin wannan hakanan bai iya sake maki haka gaskiya, in ma ace yana da kirki zai iya biyan ki wayar taki gaskiya bana tunanin da irin wannan tsadaddiyar duk gadai wayoyi iri iri nan cike da gari sai kawai ya siyo maki wannan don ya fasa maki glass d'in waya, ai kawae yar gidan Hajiya komar ki ta kamo mana gingimemen kifi wllh, Allah Ubangiji ka tabbatar mana da abun nan wllh har bansan irin farincikin da zan yi ba" ta k'arasa tana ta washe baki ita dai Fauzy murmushi kawai take can tace "to Aunty koda ace sona d'in yake ni ba sai in yayi man ba...." Tunkan ta gama Maganar ta kai hannu zata buge ta tana fad'in "Wllh yayi maki mak'aryaciya kawai, wannan d'in zaki ce wani bai maki ba, ke ko bai maki ba indai ya nuna yana son ki Allah kema sai kin so shi tunda ni yayi man, yanzu irin wannan yaushe ma ake jira sai sunce suna so ai da mutum ya samu dama yake cusa kan shi in da rabo sai kiga an dace haka kema ya kamata ki yi" tura baki tay tace Allah ita bazata wani cusa kanta a wurin shi ba hakanan ya wulakanta ta,

"Ai dama ba ina nufin kice kina son shi ba, tunda kinga kin samu dama ke zaki rink'a yin abubuwan da zaki jawo hankalin shi gare ki har ya furta yana son ki" shiru Fauzy tay tana jinjina zancen wai Sameer ya bud'e baki ya ce yana son ta tirkashi, tambayarta tay ai tana da lambar shi ko tace mata eh d'azun daya kirata, tace Yauwa to yanzu ta kira shi tay mashi godiya, d'an waro ido Fauzy tay tace amman fa dare yayi sosae ta bari sai gobe mana, harararta tay tace da zafi zafi ake bugun k'arfe ai sai yaga ma bata yaba ba tunda yasan dole a daren zata bud'e ta gani su fa ta irin haka ake janyo hankalin su, ba yadda Fauzy ta iya haka ta fara k'ok'arin kiran nashi Aunty Mareeyar sai kwatanta mata yadda zatai mashi godiyar take ita kuwa gabanta sai d'an fad'uwa yake, kiran ya shiga yana ta ringing amman bai d'aga ba har ya yanke, cire wayar tay tace mata ta sake kira k'ilan bai kusa da wayar yanzu kuma tunda yaji ringing d'inta zai taho don ya d'auka, yamutsa fuska Fauzy tay tace ita gaskiya bazata sake kira ba hakanan ta ja ma kanta wulakanci sufa irin su ba'a zak'e masu don ba'a cika yi masu gwaninta ba, jinjina kai Aunty tay alamar yarda da Maganarta tace Shikenan suje, Fauzyn ta tambaye ta yanzu ya zatai da wayar ita bata son a gani gaskiya tace mata to ta 6oye ta in suka koma gida sai taci gaba da amfani da abunta ta d'aga mata kai, suna niyyar juyawa su shiga wayar Fauzy ta fara ringing da sauri gaba d'ayan su suka kai idanun su kan screen d'in, ganin lamba yasa Aunty Mareeya ce mata waye idon Fauzy a d'an ware tace mata shine,

"Yauwa to, ki d'auka sai kice dama kinga wayar ne shine kika kira ki yi mashi godiya, kar kiyi mashi magana kaman wata sakarai kiyi exactly yadda na kwatanta maki d'azun" Aunty Mareeya da tay k'asa k'asa da murya ta fad'a har saida tasata dariya, picking kiran tay ta kai wayar kunne sai had'iyar miyau take Aunty na mata nuni da ta natsu da hannu, shiru yay bayan ta d'auka cikin kwantar da murya tay sallama nan ma shiru bai amsa ba, d'ago ido tay ta kallo Aunty da ta gwale ido tana kallon ta, alamun miye tay mata da hannu Fauzyn ta girgiza mata kai tay mata alamar bai yi magana ba, yi mata alamar taci gaba da magana kawai tay ta d'aga mata kai, a nutse tace mashi dama ta ga wayar ne shine ta kira tayi mashi godiya, tana rufe baki taji yace "You ave done that already" abu ta had'iya cikin yar in ina tace "eh, dama naga wayar babba ce shiyasa nace bari in k'ara yin godiyar, Allah ya saka da Alkhairi ya k'ara bud'i na Alkhairi" d'an shiru yay daga baya ya furta "Ameen" shiru sukai Fauzy sai kikkafta idanu take Aunty Mareeya tay mata k'uri sai tsuma take, can bayan wani lokaci taji ya furta "Gud nyt" da sauri tace mashi haka itama, tana ciro wayar Aunty Mareeya ta kai hannu kan kafad'unta ta jawota jikinta cikin washe baki tace haka yakamata tace "Gud nyt Masoyi na" yadda ta mak'e muryar ne yasa Fauzy kyalkyacewa da dariya itama dariyar farinciki take suka nufi ciki, lokacin da suka shiga cikin parlon ba kowa duk sun tashi an kashe kayan kallon, sakin kafad'ar Fauzyn tay cikin washe baki tace "ranki ya dad'e kije ki kwanta" dariya Fauzy ta saki tana fad'in kai Aunty Mareeya, sai da Safe tay mata tana washe baki tace "to your excellency Allah ya tashe mu lafiya" sosae Fauzy ke dariya ta juya ta tafi itama Aunty Mareeyar dariyar take ta nufi d'akin su, bayan Fauzy ta shiga bakin gado ta nufa ta zauna ta kai hannu cikin jakar ta fiddo kwalin wayar, bin shi tat da kallo can ta d'aura a saman cinyoyinta ta bud'e, bin wayar tay da kallo cikin ranta tana k'ara yin mamakin ta, Maganganun Aunty Mareeya ta shiga tunanowa na Sameer son ta yake, acikin ranta ta shiga mamakin taya hakan zata kasance wanda tasan tabbas dole yana da yan mata kuma bama k'ananu ba kamar ta, sannan y'ay'an Mayan masu kud'i da Mulki, zuciyarta ce ta tambaye ta yanzu in da gaske son nata yake zata so shi? jimm tay ta kasa amsa ma kanta don gaba d'aya ita gani take ba abu bane mai yuwuwa ma hakan yasa ta kauda ma tunanin gaba d'aya, d'aukar wayar tay ta fara jujjuya ta tana k'are mata kallo da d'an murmushi akan fuskar ta, aje wayar tay ta kai hannu ta tallabo ha6arta ta shiga tunano duk maganganun da sukai dashi a Mota, sosae tay mamakin yadda ya sake mata har sukai magana haka sai faman sakin murmushi take can ta maida wayar acikin kwalin ta saka cikin jakar ta mik'e, wurin kayanta ta nufa bayan ta bud'e akwatinta ta saka, ko tunanin ta saka kayan bacci bata yi ba ta wuce gado ta haye, rufe ido tay nan take zuciyarta ta shiga dawo mata da suffar Sameer.

Washe gari da wuri akai gama Breakfast saboda masu tafiya kuma ranar aiki ce, Senator na cikin yin Breakfast jikin shi sanye da jallabiya yan'uwanshi da suka rage maza suka zo part d'in shi don su gaisa su kuma yi sallama wanda ya'yan yan'uwan mahaifinsu ne suma duk dattawa ne, bayan sun gaisa ya tambayi sunyi breakfast d'in suka ce eh yanzun nan suka gama, zancen wadda Nameer yake so yay masu yace bari ya gama sai suje suyi ma iyayen nata magana cikin nuna farinciki suka ce mashi to, bayan ya gama a tare suka mik'e har zasu tafi Senator ya dakata yace masu yana d'an zuwa duk suka tsaya suka ce to, hanyar Bedroom d'in shi ya nufa ya shige, bada jimawa ba ya fito ruk'e da babbar leda mai rubutu a jiki, d'aya cikin yan uwan nashi Alhaji Musa ne ya nufe shi da sauri wanda matsayin K'ani yake a wurin shi ya kai hannu ya amshi ledar suka nufi part d'in da su Ard'o suke, lokacin da suka shiga parlon ba kowa basu dad'e da gama yin Karin kumallo ba suna ciki suna shirin Tafiya, Alhaji Musa d'in ne yaje bakin k'opar tasu ya kwankwasa tare da yin sallama, Baban Altine ne yazo ya bud'e yana ganin shi ya k'arasa fitowa cikin washe baki ya gaishe dashi tare da d'an sunkuyawa bayan ya amsa ya sanar dashi tare suke da mai gidan suna son yin magana dasu ne yayi ma su magana, da sauri idanu a d'an waje ya tambayi lafiya dai ko yana murmushi yace mashi lafiya lou sai ma Alkhairi da sauri ya jinjina kai ya juya d'akin, ba'a d'au lokaci ba sai gasu sun fito su duka duk sun saka kaya da zasu tafi dasu Ardo yasha babbar riga da hula ha6ar kada, cikin parlon suka nufo su Senator na zaune suka nufe su da sauri, hannu suka basu suka shiga gaisawa don Senator ya hana su duk'awa k'asan da suke in zasu gaisa amman duk da haka in zasu gaisan dasu sai sun d'an sunkuya, bayan sun gama gaisawar yay masu nuni da su zauna duk suka nufi kujeru suka natsu, a nutse Alhaji Ibrahim ya fara magana yace dama abun Alheri ne suke tafe dashi duk suka jinjina kai, bayani yay masu d'an shi k'anin wanda ya auri yar wajen su ne shima ya ga yar'uwarta yana so to shine suka zo sake rok'on iri in ba'a yi mata miji ba, tun kafin ya rufe baki baban Altine ya hau girgiza kai bayan yayi shiru da sauri yace mashi ba'a yi mata miji ba wllh kuma koda an yi ma za'a warware a ba d'an wajen nasu ko don Mutuncin su a gare su, shi Baffan Fatun ma ya kasa magana tsananin mamaki had'i da farinciki ne suka lullube shi don kuwa yasan wadda ake Magana koma wacece d'iyar shi ce tunda da iya yaran shi su Aysha aka zo, shi Ard'o sam bai fahimci inda aka dosa ba tunda dama ba wani fahimtar hausar yake sosae ba cikin harshen fulatanci yake tambayar Baffan Altine abunda aka ce cike da farinciki ya hau sanar dashi, ai tun kafin ma ya k'arasa da sauri Ard'on har yana yin kaman zai fad'o daga kan kujera tsabar saurin yayi Magana Baffan Altine ya tare shi, cewa yay an ba yaron duka don haka yanzu ma sai a d'aura aure kawai, gaba d'aya murmushi su kai Senator yace masu yaron yana karatu ne yanzu kuma ba'a K'asar nan ba amman nan da shekara guda zai gama zuwa lokacin sai ayi masu Auren dama akwae Yayar shi da za'a ma Aure a lokacin sai a had'a su yanzu sun yi magana ne don asan da Maganar, Baban Altine ne ya k'ara yi ma Ardon bayani yadda zai fahimta sosae sai faman d'aga kai yake, Senator ne ya sake cewa yakamata a kira yaran aji ta bakin su don a tabbatar kafin a tsaida magana duk suka ce hakan yayi, kiran Nameer yayi a wayar shi bayan ya d'auka saida ya amsa gaisuwar da yay mashi sannan ya bashi umarnin ya iske shi a part d'in sannan ya kira itama yarinyar da yayi ma Hajiya Magana akan ta, bayan ya cire wayar ne daga kunnan shi ya kai hannu kan k'atuwar ledar da suka zo da ita ya d'an tura saitin su yace gashinan suyi amfani da su, Baban Altine ne ya taso ya d'auka har da duk'awa yana godiya haka Baffan Fatuu ma sai da ya d'an zamo daga kan kujera yay godiya Ard'o ma sosae ya hau yin godiya, after some minutes Nameer ya shigo jikin shi sanye da k'ananun kaya, amsa mashi sallamar da yayi sukai ya k'araso ciki kan shi a k'asa, daga gefen su Dad d'in shi ya zauna a k'asa duk idon su na akan shi, d'an d'ago da kai yay ya gaishe dasu Dad bayan sun amsa ya juya kan su Ard'o ya gaishe dasu cikin washe baki babban Altine ya amsa shi kuma Baffan su Fatun murmushi yake ya amsa, bai dad'e da shigowa ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login