Showing 279001 words to 282000 words out of 512766 words

Chapter 94 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1606

itama tasa gefen gyalenta tana goge ma Fatuu, bayan sun gama goge gogen hawayen a tare suka kama hannun Fatuu ta yadda suka saka ta a tsakiya suka nufi komawa saman nan Mc ya shiga kwarzan ta su yana fad'in "What an emotional occurrence, What a beautiful Family...." Bayan sun koma saman a tare suka zaunar da ita ta sadda kanta k'asa tana ta sheshsheka, Mc ne ya sanar za'a jira Amarya tayi shiru sai aci gaba duk akai murmushi, after some few minutes yace ma Haisam saura shi suna so ya bayyana farincikin da yake ciki, tun kafin ya rufe baki ya girgiza mashi kai alamar bazai ce komai ba Mc hada kwa6e fuska ya juyo yace to anyi ma Ango laifi an sa Amaryar shi kuka don haka bazai yi magana ba aikuwa su Laila suka mik'e suna basu yarda ba yadda itama tayi shima sai ya yi nan fa wasu ma suka sa baki harda su Aunty abun sosae ya bada nishad'i, ganin an fi k'arfin shi yasa shi yi ma Mc d'in alamar ya kai mashi lasifikan, da sauri ya nufi saman ya mik'a mashi, yana amsa abunda yace shine yana matuk'ar son matanshi kuma zai yi matuk'ar kokarin ganin ya zama mai Adalci a gare su, yana fad'in hakan ya mik'a ma Mc mike d'in gaba d'aya aka hau tafi da sowa harda Sameer sarkin kamewa saida ya d'an yi guntun murmushi, mik'ewa Laila tayi ta nufi bayan hall d'in, cikin wani d'aki ta shiga inda ma'aikatan da zasu serving mutane Abinci suke gaba d'aya jikinsu sanye da farar t-shirt mai d'auke da tambarin wurin da suke aiki na k'awar Mom, umarnin fara kai Abinci ta basu dama abunda suke jira kenan ba 6ata lokaci suka fara zuzzubawa suna d'aurawa a saman manyan trays, a wuri na musamman aka zuba ma su Her Excellency da sauran manyan matan, ko ban fad'a ba ansan abinciccika ne na musamman nan suka shiga kai ma mutane duk abunda mutum yake so zai d'auka in ma fin plate d'aya ne mutum ke so na wani Abincin zai iya dauka, masu raba lemuna ma suka shiga kawo ma mutane shima ko nawa mutum ke so zai d'auka, samun wuri Mc yay yana fad'in bari yay refilling cikin shi ya k'ara samun karsashi duk aka sa dariya don cike da barkwanci yayi Maganar, a nutse kowa ke cin Abincin kuma ba wanda ya damu da yadda wani ke cin nashi har lokacin Fanan na saman tare suke cin Abincin harda ba Fatuu a baki tana murmushi ta bud'e mata bakin daga baya itama ta bata, Mc na gamawa ya mik'e yana fad'in to basu da lokacin 6atawa bari aci gaba da abunda ya tara su duk aka sa dariya ana fad'in sai da ya gama yasan basu da lokacin 6atawa, abu na gaba Ango da Amarya aka buk'aci su sauko su taka Haisam nuna wa yay bazai je ba Fanan ta nuna mashi kar yayi hakan baza'a ji dad'i ba, tare suka mik'e ya kama hannun Fatuu ita tayi gaba suka biyo bayanta, tana saukkowa ta koma cikin hall din Mc ya nuna masu inda zasu tsaya, suna zuwa wurin kawai aka fara sakin fireworks da dry ice smoke, Ya Allah har tsuma nike Saboda kayatuwar yadda ake sakin hayakin da kuma tartsatsin wutar kowa ka gani murmushi ne akan fuskar shi wasu kuma washe baki sukai, ita Fatuu ma d'an tsoron abun ne ya kamata yadda hayakin ya turnuk'e su da kuma yadda tartsatsin ke fita da k'arfi,

"Dama nasan da wuya H,Zee bai auri yarinyar can ba, tun da naga yak'i amince man in nemeta dama I ave suspected something ever since" Najeeb ne da yake zaune gefen Abbas yayi Maganar, yar dariya Abbas yayi yace mashi wllh ba wani abu a ranshi a lokacin daya wuce taimaka mata kawai Allah ne ya k'addaro zasu zama ma'aurata yace baya fad'i mashi yadda komai ya faru ba, hararar Abbas d'in yayi fuska d'aure yace "ai kaima ba sona kake da ita ba in ba haka ba why not ni ka kirani kai man Maganar Aurenta kaga in ban aureta ba" Sosae Abbas yake dariya bai dai ce komai ba acikin ran shi ya raya ai duk k'anwar ja ce, Salim dai d'an murmushi kawae yayi, kamata Haisam yay har hayakin ya washe, wak'ar Fall in love aka kunna masu yana rik'e da ita sai murmushi yake mata itama d'an murmushin take duk kunya ta lullube ta, a hankali yake d'an motsawa da ita har lokacin tartsatsin wutar na tashi a bangaren daman su da hagun su abun gwanin k'ayatarwa, masu hoto da Video nata yi harda wanda aka daukko, bayan d'an lokaci kafin wak'ar ta k'are Laila ta nufi wurin Dj ta fad'i mashi ya canza masu Wak'a tace yasa wak'ar breaker ta burina, a hankali taken wak'ar ya fara da kid'a mai sanyin dad'i kafin baitin wak'ar ya fara fita,

_Dubaaa kan ki ana kallonaa....babban buri na ki kasance dab dani, in zaakii k'irga masoya naki ki sanyo danii, dubaaa kan ki ana kallonaa majnunii ni kuma nace in dai kai na ki ne baan fad'i ba, sak'o ya bayyana ni tun daga zuciya, sannan k'aunar ki tana kaman zuciya......_

Kowa kaga ni fuskar shi d'auke da Murmushi wasu suna d'an juya kai suna bin wak'ar, lokacin da aka zo baitin da ake cewa _" kin rikirkita dukka tunani na, taimaka ki bani wurin kwana, son ki ya hana min bacci na, ina ganin ki har a mafarki na, son ki yanaiii min dad'i ban san mu rabu......"_ Laila da ke tsaye tana masu Vedio ta d'aga murya tace "Big Bro yi mata zaka rink'a yi fa" Murmushi kawae Haisam d'in yay Jidderh ma ta k'ara d'aga murya tana cewa ya saurara za'a k'ara maido mashi, baitin na k'arewa Laila tace ma Dj d'in ya maido baitin, yana maido shi duk aka maida hankali kan su Laila da Jidderh harda sauran k'annansu da wasu yan uwansu suka shiga fad'in yayi mata har saida suka ba Haisam d'in dariya Fatuu ma haka duk kunya ta rufe ta, lokacin da baitin ya kusa zuwa k'arewa kawai sai gani sukai ya bi harda nuna ta, wani irin ihu aka sa Fatuu ta 6oye fuskarta tana dariya, sosae abun yaba mutane nishad'i, Hajiya Zainab ce ta mik'e tana murmushi Momy ma ta mik'e suka nufi gaban Security detail d'inta na biye dasu hannunta ruk'e da jakar ta, wurin su suka je ta mik'a ma security d'in hannu ta bata jakarta, bandir d'in yan dubu dubu ta fiddo guda biyu haka Mom ma su ta fiddo daga cikin jakarta nan fa suka fara masu ruwan nera, ai kamar sun bud'e k'opa sauran manyan bak'in ma duk suka mik'e suka nufi gaban ai masu kid'an ganga na ganin haka ba 6ata lokaci suka hau bugun gangunan su suna wasa manyan matan nan fa Hall ya karad'e kid'a ko ta ina abun sai ya ba mutane ma dariya, Laila ce tayi ma Dj magana sannan ya kashe nashi, Laila ma lik'in ta fara masu Jidderh ma saurayinta ya fiddo bandir d'in d'ari biyar biyar ya bata taje haka su Nameer ma, daga wurin lik'in su Her Excellency da Mom dasu Aunty sauran manyan bak'in duk tafiya sukai, nan aka cigaba da rawa ana lik'i, wai ashe haka Laila da Jidderh suka iya rawa harda kama Haisam suna yin rawar, Yadikko ma saida taje ta amshi canjin yan d'ari biyu biyu tayi ma d'iyarta lik'i koda Fatuu ta ganta rungume ta tayi, gwaggo dai bata yi ba Saboda kunya tana zaune sai dariyar farin ciki take, Kawu Amadu da Tk da Nameer ma duk saida suka yi, Haulat ma saida taje tayi canjin yan d'ari biyu taje tayi haka Saude ma Hajiya dai dama bata zo ba, rud'ewa Fauzy tay tana son yin lik'in amman bata da ko sisi duka yan kud'inta dasu ta siya takalma da jaka da mayafi da zasu zo, tana ganin Aunty Mareeya ta nufo cikin hall d'in ta gama lik'in nata da sauri ta tare ta kaman zata yi kuka tace mata don Allah ta bata kud'i itama taje tayi, wani kallo ta mata tace wllh bata da kud'in da zata bata itama wanda tayi k'arfin hali ne kawai, komawa tayi ta zauna jiki a mace Zainab ce tace mata tana da yan kud'i suje suyi canjin ko d'ari biyu biyu ne, girgiza mata kai tayi tace taje tayi kawai, ba yadda bata yi ba amman tak'i k'arshe ta tashi ta tafi ita, takaici duk ya kama Fauzy abu goma da asirin, ga Vedio ta kasa yi Saboda wayarta data kwankwatse bata iya fiddo ta a wurin ga rashin kud'i, k'arshe kife kanta tayi saman table d'in jin tana niyyar yin kuka, bata dad'e da kife kan ba taji ana mata sallama, d'agowa tayi ta kalli mai sallamar wanda d'aya daga cikin ma'aikatan dake hidiman Abinci ne, gaida ita yay da d'an alamun mamaki ta amsa mashi kawai sai gani tay ya Mik'o mata kud'i bandir d'in yan dubu dubu guda biyu dubu d'ari biyu kenan, ce mata yay gashi aka ce ya kawo mata taje tayi lik'i, waro ido tay da alamun Al'ajabi ta tambayi waye yace a batan, nuna mata saitin da su Sameer suke yayi yay mata kwatance wanda ya badan don ya juya kan shi yana a Hakimce iya sumar shi kawae suke iya hangowa, jimm Fauzy tay saida ya k'ara ce mata gashi sannan a tsorace ta amsa ya juya ya tafi, bin kud'in tayi da kallo kafin ta kai duban ta kan su Aunty Mareeya dake ta hira basu ma lura da abunda ke faruwa ba, a hankali ta juya ta kai idanunta kan Sameer ta bishi da kallo ji take kamar ta je ta maida mashi saidae tsoro bazai barta ba, tana haka kwatsam ta ga ya juyo ya kalleta suka had'a ido, wani mugun kallo yay mata ya janye ido ya koma yadda yake, ba shiri ta mik'e hannun ta ruk'e da kud'in ta nufi gaban hall din a d'arare, koda tazo saitin su ta kai idon ta kanshi bai ko kalleta ba, tana zuwa ta shiga yin lik'in bayan bandir d'aya ya k'are ta bud'e d'ayan ta raba biyu ta mik'a ma Zainab data saki baki tana bin ta da kallon mamaki, cikin makad'an ne wani yazo ya tambayi sunan Fauzy ita bata san dalilin ba ashe wak'e ta zasu yi kaman daga sama taji ana angaida Hajiya Fauziyya mai ruwan naira har bata san lokacin da tasa dariya ba tana d'an kare fuska, kirarin da ake ma Fauziyyar ne ya jawo hankalin Aunty Mareeya ta Ankara da lik'in dubu dubun da Fauzyn ke yi,

wani jiri Fatuu taji yana niyyar kwasarta da sauri ta kai duka hannuwanta ta kama jikin Haisam, kallon ta yay ganin yadda take lumshe ido yasa shi tambayarta tana lafiya ta d'an yamutsa fuska ta kai hannu ta dafa gaban kanta a hankali tace mashi jiri take gani ba shiri ya kamata ya fara k'ok'arin barin wurin da ita wad'anda suka ankara suna tambayar lafiya yace masu eh, su Laila ne suka cigaba da yin rawar ya koma saman da ita, bayan ya zaunar da ita shima ya zauna cike da kulawa ya tambayi har yanzu tana ganin jirin, d'an murmushi tay ta girgiza mashi kai a hankali tace ya bari yace ta tabbata kodai su tafi gida still da murmushi tace mashi kada ya damu tasan tsayuwar da tayi ne yasa, Fauzy na son yin rawa amman ta kasa Saboda Sameer duk da bata san ko yana kallonta ba, bayan ta gama yin lik'in nufar komawa tay cikin hall d'in idon ta a k'asa, tana zuwa saitin Sameer ta saci kallon shi karaf suka had'a ido da sauri ta janye idon, tana zama a wurin zaman su Aunty Mareeya ta nufo ta da sauri har tana bugewa da kujera, zama tay a d'aya daga cikin kujerun ido a waje tace "Ke, ina kika samu kud'i haka da kikai lik'i har ana Wak'e ki?" murmushi tay tace mata Allah ne ya bata, wata uwar harara ta zabga mata tace zata gaya mata gidan uban wa ta same su ko kuwa, tana dariya tace mata wani ne ya bata, k'ara zabga mata harara tay tace wani wa, satar kallon Sameer tay sai sumar kan shi ta hango, maido idonta tay kan ta tace mata mutumin jiya ne ya bata, washe baki Aunty Mareeya tay a k'agare tace mata yana ina Fauzyn tay d'an jimm kafin tace mata ya fita bayan ya bata kud'in,

"Da alama dai Addu'a ta zata amsu, koma har yace yana son kin?" dariya Fauzy tay ta girgiza mata kai, tace ai duk aje a dawo in kaga kare na sunsunar takalmi to d'auka zai yi, tambayarta tayi har nawa ya bata tayi lik'in ta fad'i mata, zaro ido tay tace "ba dai duka kika lik'a ba??" Kai ta d'aga mata kafin tace duka, bud'e baki tay alamar Al'ajabi tace "amman dai ke anyi shashasha wllh taya zaki je ki lik'a duka wannan uban kud'in ba tare da kin rage ba, maimakon ma ki saka bandir d'aya a jaka ki lik'a d'aya" fuska d'aure ta k'arasa Maganar, ce mata tay ai lokacin yana kallon ta fa taya zata d'au wasu Aunty Mareeyar tace eh to gara da bata d'auka ba kada yay tunanin tana da son abun duniya gara abi komai a hankali ya shigo hannu ita dai Fauzy dariya kawai take.

Sai wuraren k'arfe sha biyu da wasu mintuna taron ya fara tashi, Kusan duk an tafi wasu daga cikin Abokan Haisam d'in ne suka rage su Abbas da Najeeb sai Na'eem Salim ya tafi haka Sameer ma tuni ya tafi, Aunty Laila bata tafi ba tana waje tana k'ok'arin ganin an maida kowa Nameer ma bai dad'e da tafiya dasu Fauzy ba, su Abbas suna tsaye a sama inda su Fatuu suka zauna Haisam ma na tsaye tare dasu suna magana, Laila ce ta lek'o cikin hall d'in ta sanar dasu kowa ya tafi fa Haisam ya d'aga mata kai, Abbas ne ya kalli Fatuu dake zaune yace "Mom Zarah an sha gajiya ko" d'an murmushi tay Najeeb ya kai idon shi kanta suka had'a ido shima d'an murmushin yayi mata, Kallonta Haisam yay yace ta tashi su tafi ta d'aga mashi kai, tana mik'ewa ta fara ganin jiri da sauri ta kai hannu ta dafe goshi bakin ta a d'an bud'e, wani irin duhu ta fara gani lokaci guda ta fara fita hayyacin ta, Abbas ne ya kai idon shi kanta yaga halin da take ciki da sauri ya furta "Mom Zarah lafiya??" gaba d'aya suka kai idon su kanta ko kafin suce mata wani abu gaba d'aya ta tafi zata fad'i cikin zafin nama Haisam ya tareta ta fad'a jikin shi, cikin tashin hankali ya shiga fad'in "Baby! Baby can you hear me? Mike faruwa?" tun tana lumshe ido tana bud'e su har ta k'arasa rufe su baki d'aya............

*ASM 083*


~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~



*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


...........Cikin tashin hankali yake jijjigata yana kiran sunanta, Abbas ne ya d'aukko robar ruwa bayan ya bud'e ya mik'a ma Haisam ya tara mashi hannun shi ya zuba mashi, sau biyu ya shafa mata amman ba alamar zata farfad'o, Najeeb ne da shima fuskar shi ta nuna tashin hankali yace bai kamata su tsaya suna wasting time ba ai rushing d'in ta hospital, Na'eem ne yace akwae wani private hospital daya sani bada nisa sosae ba, yana rufe baki Abbas yace ma Haisam ya d'aukko ta ya nufi hanyar fita Hall d'in da sauri sauri gudu gudu, d'agota Haisam yay ya d'auketa suka nufi hanyar fita dasu Najeeb, suna fita Abbas ya iso da Mota bakin wurin Najeeb ya bud'e baya Haisam ya saka ta ciki shima ya fara k'ok'arin shiga lokacin Laila ta k'araso hankali a tashe ta shiga tambayar wai mi ya faru da ita don Abbas ya sanar mata game da fad'uwar da tayi da ya fito, Najeeb ne yace hakanan suka ga ta fad'i, Na'eem ne ya shiga driver seat Saboda shi yasan Asibitin Najeeb da Abbas suka nufi inda Motocin su suke Abbas ya shiga Motar Na'eem haka Laila ma da gaba d'aya ta gama rud'ewa, a saman cinyoyin shi ya d'aura kan ta ya shiga shafa face d'inta yana kiran sunanta duk hankalin shi ya tashi, tashin Motar Na'eem yay bayan ya juya ya tunkari gate d'in wurin da gudu Motocin su Najeeb suka rufa masu baya, suna a kan hanya Laila ta d'aukko wayarta ta shiga kiran Mom d'in su, bayan tayi picking tun kan tayi magana cikin Muryar rud'u tace mata gasu a hanyar Asibiti, tambayar ta tay mi zasu je yi Asibiti tace mata Bride d'in Big bro ce hakanan ta yanke jiki ta fad'i, daga muryar Mom d'in zaka fahimci ba k'aramar razana tayi ba lokacin da ta sake maimaita abunda Lailar tace mata, tambayar ta tayi to miya faru da ita ne Fuskar Laila a yamutse kaman zatai kuka tace "Wllh ba abunda ya same ta kawae ta mik'e za'a taho gida ne aka ga ta yanke jiki ta fad'i" tambayar ta tayi an yayyafa mata ruwa tace mata eh an shafa mata har sau biyu amman bata ko motsa ba, salati Mom ta rafka a kid'ime ta tambayi wane Hospital zasu tace mata itama bata sani ba Abokin big bro ne yake jagorantar su shine yasan Asibitin, tun kafin ta rufe baki Mom d'in ta katse Wayar, hannu ta kai ta dafe gaban kanta tana salati Hajiya Zainab dake zaune duk taji abunda suke Magana akai itama daga yanayin fuskarta akwae alamun tashin hankali, tambayarta tayi miya faru da matar Son d'in tayi mata bayanin da Laila tayi mata, jinjina kai tayi tace to Allah yasa lafiya ta yuwu stress ne ya mata yawa Mom dake kallon ta tace to Allah yasa,

kiran Senator tayi a waya saida ta kusa katsewa sannan yay picking, saida ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login