Showing 117001 words to 120000 words out of 512766 words
Chapter 40 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1615
yadda za'ai" kallon Fatuu tay da ke taunar abu a hankali tana saurarar ta wani murmushi tay tace mata "Ke ma kina son auren ya d'ore ne??" Waro ido Fatun tay ta dakata da taunar abun bakin ta batay tunanin zata mata wannan tambayar ba, ganin yadda ta kafeta da ido alamar jiran amsar ta yasa ta girgiza kai a hankali alamar a'a, wata dariya taga gwaggon tayi har saida ta tsargu ta bita da ido can ta furta Allah ya za6a abunda yafi zama Alkhairi daga haka ba wanda ya k'ara cewa komae suka cigaba da cin abubuwan da Suke ci har fruit da naman gwaggo ta k'ara d'ebo masu saida suka ci suka k'oshi sauran ta saka acikin Fridge dake a d'akin, bayan sun gama Fatuu taje tayo brush lokacin data fito har gwaggo ta gyara mata gadon ta maida brush d'in ta haye gado ta kwanta gwaggo ma saida ta wanko bakin bayan ta fito ta d'aukko bargo ta rufa ma Fatun kafin itama ta fiddo wani bedsheet ta nufi kujera tana fad'in tunda harda fruit suka sha tasan zai taimaka wurin saurin narkar da abunda suka ci tunda ba'a son da an ci Abinci a kwanta gashi bacci take ji ta haye kujerar bayan tayi Addu'oi ta tottofe a 6angarorin d'akin ta kwanta, lamo Fatuu tay tana tunanin masoyinta ta ayyana tunda take dashi ba abunda ke shiga tsakanin su face Alkhairi amman bata ta6a tunanin zai amince ya aureta ba don kawae ya taimaketa wani kalan son shi taji ya ratsa zuciyar ta har saida ta lumshe ido Slowly ta furta "Am so sorry for my mistake Ya Haisam and my beloved husband also" wani irin murmushin dad'i ta saki nan ta fara tariyo abunda ya faru tsakanin su a G.r.a tun farko da suka fad'a saman gadon da lokacin da tay mashi magana taji shiru bai ce komai ba ta kai hannu ya nutse cikin sumar shi mai taushi ga santsi wani irin dad'in ta6awa ne da ita, a hankali ta gangaro kan lokacin da ta bud'e baki don sake yi mashi magana bata samu damar k'arasawa ba ya had'e lips d'in su wannan karon kankame jikinta tay tunowa da yadda ya rink'a bata hot and deep French kisses the way she felt at dat moment was like her breathing would cease, haka tay ta tunano abubuwan da suka faru wani lokacin tay murmushi wani ta tsuke fuska wani ta kankame jiki a haka har bata san lokacin da bacci yay awon gaba da ita ba...........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2056*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
........Washe gari lahadi tun wurin karfe 8:30 Tk ya kawo masu Breakfast daga gidan Hajiya haka wurin 9 ma sai ga Fauzy itama ta kawo masu tace ma Fatun zata je ta dawo Aunty ta aiketa Kasuwa, da har gwaggo ta kira Amadu kan ya had'o masu abun karin kumallo ganin sun kakkawo yasa ta kira shi tace ya barshi, wurin karfe 12 na rana saiga Haulat harda innar su sunzo gaida Fatun take ce mata ita bata san tana Asibiti ba sai da k'anwar ta taje siyayya shagon Kawu Amadu yake fad'a mata, cike da nuna damuwa ta tambayi Fatun wai miyake damunta da har ya kaita ga kwanciya Asibiti tana rungume da Babyn Haulat d'in da ta k'ara girma Tubarkallah ta bata labarin sanadin ciwon, sosae ita ma Haulat ta girgiza da jin zancen Aurenta da Ya Haisam tace Allah kenan mai yin yadda yaso a kuma lokacin da ya so cike da farinciki duk da bata ji dad'in rasa cikin ba tace "K'awata kinga abun Allah ko gashi har kin ci ribar hakurin da ki kai, muna ta ganin kaman shi ba rabon ki bane ashe da rabon a kusa ma" ta k'arasa tana murmushi shiru Fatuu tay da damuwa akan face d'in ta Haulat da ta lura da hakan tace "ko baki farinciki ne Allah ya cika maki burin ki, ko kuwa Saboda rasa cikin ne, kiyi hak'uri duk rashin sani ne ya jawo haka Allah ya k'addara hakan sai ya faru" yar ajiyar zuciya Fatun tay a sanyaye tace "haka ne Haulat na sani kawae dae ina ganin auren ba zai d'ore ba tunda ga dalilin yin shi" da sauri tace "in sha Allahu zai d'ore mutu ka raba keda ya Haisam bi'iznillahi ki kwantar da hankalin ki ni ina ganin hakan hikima ce ta Ubangiji dama ya kaddaro shine mijin ki shiyasa komae ya faru, baki ga da akai auran ba duk da ga yadda aka tsara amman kuma sai bai sake ki d'in ba k'arshe ma ga abu har ya shiga tsakanin ku harda rabo ni na tabbatar auran nan zai d'ore ke yama d'ore kawae" ta k'arasa tana yar dariyar farinciki still da yanayin damuwa Fatuu tace "amman fa Haulat Ya Haisam d'in Fushi yake dani kan wannan abun daya faru yana ganin nayi mashi taurin kai Saboda nak'i in saurare shi naje na zubar da cikin" itama yanayin fuskar ta ne ya sauya ta kai hannu ta kamo hannun Fatun guda tace "kinga wannan ma kadae ya isa yasa ki gane ya Haisam ba don ya sake ki ba ya aure ki in ma farko da wannan niyyar ne to daga baya ya canza ra'ayi tunda gashi har bai ji dad'in zubewar cikin ba wanda da yana da niyyar rabuwa dake ai shi dad'i zai ji koma da kan shi yasa a zubar Saboda kar abun da ya shiga tsakanin ku ya bayyana, nasan shi mutum ne mai fahimta sosae zai fahimci dalilin ki yay maki uzuri tunda ai sun san ke baki san da auren ba kuma Saboda ku duka kika aikata hakan, don haka ki kwantar da hankalin ki ba abunda zai faru kawae yana fushin ne don ya nuna maki kin mashi laifi kuma ki gane bai ji dad'i ba ko don Saboda gaba, keda ma kike yar gidan shi dama ko kin 6ata mashi rai da kin bashi hakuri yake hak'ura ki tuna fa tun farkon sanin shi kafin ku saba ma babbar asara kikae mashi harta kud'in shanu goma kuma kina sane kika aikata mashi amman kina zuwa kika bashi hakuri ya hak'ura balle kuma yanzu da kuka zama abu d'aya ya kuma san abunda kika yi kuskure ne sakamakon rashin sani da Kin san komae baza ki aikata hakan ba kuma yanzu da ya baki dama zaki gyara laifin ta hanyar biyan shi abunda ya rasa ba kamar na shanu ba" ta k'arasa tana dariya itama Fatun yar dariyar tayi ba kamar da ta tuno mata da can baya, kwantar mata da hankali taci gaba da yi har saida taga ta washe bayan sallar Azahar suka tafi, wurin k'arfe ukku Fauzy ta dawo harda Abincin rana ta kawo masu Gwaggo tay ta godiya tana fad'in ba'a gajiya da d'awainiya Fauzy na murmushi tace ai an zama d'aya gwaggon tace hakane tay Addu'ar Allah ya bar zumunci, Fauzy da kanta ta zuba ma Fatun ta kai mata saman gado tana ci suna yar fira nan take fad'i mata zancen zuwan Haulat ta nuna bata ji dad'i ba da basu had'u ba amman in suka koma gida zata je ta k'ara ganin Baby d'in su, bayan ta gama cin Abincin Fauzy ta d'aukko mata drugs d'in ta tare da bottle water ta sha, gab da la'asar sai ga su Feenah sun k'ara zuwa yau ma harda Abinci, da Abbas ne zai kawo amman Abdul ya sa rigimar sai anzo aikuwa tunda suka zo ya haye gadon suka kankame juna shida Fatun daga baya Abbas ya shigo ya gaishe da ita tana ta murmushi ta amsa har yana fad'in "Alhamdulillah da alamu Amaryar mu da wuri zata warware ta biya mu abunda muka rasa" murmushi Fauzy da Feenah sukai ita dai d'an sadda kai kawai tay tana d'an murmushi ya tambayi ta ci Abinci tasha magungunan ta Fauzy tace eh, sai bayan la'asar suka tafi da daddare bayan isha Haisam yazo yau ma kaman jiya da manyan ledoji yana sanye da k'ananun kaya yana shigowa Fauzy da har lokacin tana nan don tace yau a nan zata kwana ta mik'e daga kan kujera da suke zaune tare da gwaggo taje ta amshi ledojin tana mashi sannu da Zuwa ya d'aga mata kai ya juya suka gaisa da gwaggo ganin tana niyyar mik'ewa don ta bashi wuri yasa shi ce mata ta zauna zai wuce ne tace to ta koma Fauzy ma bayan ta aje ta dawo kusa da gwaggon ta zauna, slowly ya nufi gadon Fatuu na zaune jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa ta jingina da bango kanta sanye da hula ta kallabin rigar tayi wani fayau da ita ta k'ara haske sosae saidae ta rame ba kamar Fuskarta har idanunta sun fad'a, a gefen gadon ya tsaya tunda ya shigo ta sadda kai k'asa saida taji tsayawar shi a wurin ta d'an d'ago suka had'a ido ta gaishe da shi jinjina mata kai yay slowly ya tambayi jikinta ta bashi amsa da Sauk'i, shiru yay idon shi akanta itama shi take kallo tana yi tana d'an maida idon k'asa tana sake d'agowa da su duk ta kame kan ta can ya d'an ta6e baki ya juya ya nufi hanyar fita su gwaggo su kai mashi saida safe ya amsa, tunda ya tafi tay zugudum Fauzy ta taso ta zo gefen gadon ta zauna ganin yanayin Fatun ta tambaye ta har yanzu fushin yake cikin raunanniyar murya tace mata eh Fauzyn tace "ki daina damuwa k'ilan ma fa ba wani fushin da yake tunda irin su dama gane masu yana da wuya kawai k'ila yana canza maki fuska ne don ki gane kin mashi laifi" shiru kawai tay amma ita ai ta karance shi sosae tana gane yanayin shi, yau ma dai kaman jiya suka sha shagalin su da abubuwan da ya kawo gwaggo ta zubo masu itama ta zuba ta koma kan kujera da Fatuu tak'i ta ci Fauzy ta tursasa mata harda yin k'asa k'asa da murya tace "ki saki jiki ki ci ki k'oshi ta hakane zaki samu sauk'i sosae cikin d'an lokaci ko Kya yi sauri ki biya shi abunda kika sa ya rasa ya daina fushin in ma shi yake yi" wani kallo mai kaman harara tay mata Fauzyn ta sa dariya tana d'an gumtse baki daga baya Fatun ta fara ci suna cikin ci cikin rad'a Fauzy tace "akwae wata mai magunguna da Aunty ke siye jiya dana koma muke Maganar da ita tace yakamata a amsar maki su don suna da mugun kyau wllh tunda ita tana amfani dasu ta shaida ingancin su, haka tace su maza ta haka ake kama su Aunty harda cewa wai ba kamar irin wad'annan miskilan mazan an fi kama su ta nan wai har zaucewa suke kaita mamaki kaman basu ba kinsan mijinta shima miskili ne duk da bai kai Ya Haisam ba" cikin rashin fahimta Fatuu da tayi sototo tace mata wai wane irin magunguna ne Fauzy tay mata wani kallo tasa hannu ta ruk'e ha6a tace "yanzu nan wai ke baki gane inda aka dosa ba sai kace wata yar primary magungunan mata fa ake nufi wanda mata ke sha don gyara jikin su Saboda su kama mazajen su badai wai baki san su ba?" Shiru Fatuu tay kaman mai tunani can tace mata ta san su taga ana tallan su a Tv kuma da suna secondary school lokacin da suka kusa gamawa wad'anda zasuyi aure da sun gama suna zuwa da su suyi ta sha harma su samma su har da wani mai kaman chocolate da kwakwa a ciki tana son shi yana da dad'i don Haulat har badawa tay aka siyo mata da yawa suna sha, da sauri Fauzy tace "Chocolate gumba kenan akwae ma ta kwakwa da dabino d'an banzan dad'i ne da ita wllh duk ni ke sace ta Aunty Mareeya tay ta fad'a harma ta gaji yanzu in aka kawo mata sai ta d'ibar man a yar roba ta bani tace in na satar mata nata wuta bal bal" gaba d'aya suka sa dariya Fauzy ta k'ara cewa "kinsan akwae su fa da yawa wasu gari ne da Madara ake sha wasu da Zuma wasu na ruwa ne ke harda itatuwan tsarki tarkace ne sosae ake had'o ma mutum, kuma fa wai kinsan kaman gumbar nan da kika ce kina son ta tana da dad'i wai fa haka suke ji mazan in ku kai Meeting" waro ido Fatuu tay don ta gane meeting d'in da take nufi Fauzy tasa hannu ta gumtse dariya Fatun ta girgiza kai a hankali tace "Allah ya shirye ki Fauzy nidai ba ruwana" da sauri tace "ke kau keda ruwa wllh don ba k'aramin gyara zaki sha ba Aunty tace duk sai an sauke mashi miskilancin da Matarshi ta kasa sauke mashi wai sai an sa duk inda ya zauna sai ya ambaci sunan ki nace mata Aunty kaman wani zautacce tace ai haka zai koma a kan ki" gaba d'aya suka saka dariya har saida suka ja hankalin gwaggo dake cin abu tana saurarar radio ta juyo ta kalle su Fauzy data lura ta wutsiyar ido ta zaro ido had'i da rufe baki da ido tay ma Fatuu nuni da gwaggo itama ta gumtse dariyar, suna haka Amadu ya shigo dama gwaggo ta kira shi don ya kawo mata abun shimfid'a ta kwanta k'asa ita kuma Fauzy sai ta kwanta kan kujerar da fara'a ya shigo ya nufi gwaggo ya kai mata kayan suka gaisa ya juya ya nufi gadon ya tsaya a bakin gadon yana fad'in "kuce kuna nan kuna shagalin ku wannan to jinya kuke ko party" duk dariya su kai Fauzy ta gaishe dashi ya amsa Fatuu ma haka ya tambayi jikinta tace mashi ta samu sauki yace ai gashi nan kam ya gani suka k'ara sa dariya Fauzy tay mashi bismilla yace suci gaba da shagalin su ya juya ya koma wurin gwaggo ya tambaye ta yaushe za'a sallame su ne yaga ai ta samu sauk'i sosae tace to suna dae jiran Dr har yanzu bai ce komae game da sallamar, da zai tafi ta k'ulle mashi sauran abubuwan da suka rage tace in yaje sai yaci ya amsa yay godiya sukai sallama ya tafi, Washe gari wurin k'arfe tara da yan mintuna Dr ya shigo lokacin Fauzy ta tafi tuni Saboda zata makaranta Fatuu tayi wanka tana zaune gefen gado tana yin Breakfast da Tk ya kawo masu bayan sun gaisa da gwaggo dake zaune kan kujera tana shan tea yay mata ya mai jiki ta amsa ya nufi Fatuu ya tsaya bakin gadon itama ta gaishe shi da murmushi ya amsa yay mata ya jiki tace ta samu sauk'i yace Alhamdulillah haka ake so ya tambayi tana cin Abinci sosae ko tace mashi eh, jinjina kai yay daga nan ya shiga yi mata wasu tambayoyin tana bashi amsa daga baya yace bari ya duba bp d'inta ta maida kayan breakfast d'in kan drawer ya fara gwada ta harda idon ta ya bud'e ya duba bayan ya gama yace zata iya cigaba da yin Breakfast d'inta tace to, juyowa yay ya dawo wurin gwaggo yace mata yana ganin tunda komae lpy lou za'a sallame su yanzu sai taci gaba da shan magungunan ta a gida tana murmushi ta amsa da to had'i da yin godiya ya juya ya tafi, bayan ya koma Office ya kira Haisam ya fad'i mashi za'ai discharge d'in su yace mashi gashi nan zuwa yana kan hanya, bayan ya iso Office d'in Dr ya nufa yana sanye da jallabiya bayan sun gama tattaunawa ya fito ya nufi Amenity, kwankwasa kopar yay aka bashi izinin shiga sannan ya tura da yar sallama gwaggo da har ta fara packing kayan su ta juyo tana kallon shi da murmushi ta amsa sallamar tay mashi sannu da zuwa bayan ya gaishe da ita ya fad'i mata Dr ya sallame su tace to Alhamdulillah Allah ya k'ara mata lafiya ya kyauta gaba a hankali ya amsa da Amin kafin ya tambayi ko akwae kayan da za'a fitar tace eh ga wasu nan ta juya ta d'aukko mashi jakar kayan Fatuu da Basket ya amsa yana shirin juyawa Fatuu tace mashi ina kwana ya dakata ya kai idon shi kan ta bai amsa ba slowly yace mata ya jiki ta amsa sannan ya juya tabi bayan shi da kallo, bayan ya fita gwaggo ma ta d'auki su bargo da wani basket d'in tabi bayan shi, bayan an kai komae Mota Fatuu ta saukko daga saman gadon ta yafa gyalenta suka tafi bayan sun fito saida gwaggo ta lek'a d'akunan dake kusa da nasu tay masu sallama da Addu'ar samun lafiya sannan suka wuce, lokacin da suka isa Motar Haisam d'in bai ciki gwaggo ta bud'e mata gaba ta shiga itama ta bud'e kopar baya ta shige basu dad'e da shiga ba sai gashi ya fito hannun shi ruk'e da ledar magunguna da Dr ya sake rubutawa bayan ya iso ya bud'e driver seat ya zauna ya rufe kopar a gefen shi ya aje ledar ya tashi Motar suka tafi, tunda suka taho idon Fatuu na gefe tana kallon hanya har suka iso Amadu dake cikin shago yana ganin Motar ta parker da sauri ya bud'e ya fito ya nufo Motar yana washe baki shi ya bud'e ma Fatuu kopar ta fito lokacin itama gwaggo ta fito yana ta washe baki alamar yaji dad'i yace ma gwaggo ashe yau za'a sallame su tace eh suma basu sani ba saida safen nan da likita yazo, kallon Fatuu dake tsaye yay yayi mata sannu ta d'aga kai ya juya ya nufi Haisam da ya fito yana kokarin bud'e boot ya gaishe dashi, tare suka fiddo kayan